Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   68 / 107

201K to 204K   out of 320.4K words

ke faduwa, ya karaso kitchen din tana daga tsaye ta juyawa kofar baya tana hawaye.
Tundaga sama har kasa yake binta da kallo, yana ganin abun kamar a mafarki.
“Fatimaa!!” Ya kura sunanta ahankali, yanajin wata iska na kada gaba daya duk wata kofar gashin jikinsa tsikar jikinsa na tashi sosai.
Itako dataji muryansa ta wani zaro ido, gabanta na faduwa sosai taqi yarda ta juyo.
“Bibi… is that you?” Yayi magana da larabci, nanma taqi juyowa tana kokarin hadiye hawayen datake ji.
Ganin taqi juyowa yasashi tahowa kitchwn din gadan gadan ya sanya murdadden hannunshi ya kamo dan hannunta ya juyo da ita tana facing dinshi, heartbeat dinshi ya sauya yana arba da ita ga closure.
Cikin hanzari ta kai idanunta dake azabtar dashi ta watsa mashi su, gaba daya ta daukw wata rahama dake kan fuskarta kamar ba sabeeha ba.
Yakai wajen minti biyu yana kallonta ya kasa cewa komai itama ta kasa cewa komai.
Ya futzar da wata iska sai jikinsa na karkarwa ya wani irin rungumota gaba dayanta zuwa jikinshi ya mata rumfa hannayenshi biyu ya zagayeshi ga waist dinta ya kankameta soaai kamar za a rabashi da ita, tana jiyo yanda zuciyarsa ke bugawa sosai jikinsa na karkarwa ya wani lumshe idanu trying to procesa moment din, its life and direct bibinshi ce wannan, wadda yake tsumayin ganinta dare da safewya wadda kewanta yake mashi illa, wadda ta kasance weakness pount dinshi baima sani ba.
Kuka takesonyi don taj taj kam ya zame mata wata kaddara datake hunting dinta,.
Azafafe ta wani irin tureshi daga jikinta saboda yayi lakwas he’s weak gaba daya, ya nemi sake maidata jikinshi rai a bace cikin harshen hausa tace “malam menene haka??? Wannan wani irin iskanci ne haka?ya zaka zo ka rungumeni? Ance maka ni yar iska ce?”
Tafa san baya jin hausa amma da dage, shiko mamaki bai barshi ba yana kallonta kamar ba didinshi ba.
“Bibi” ya kira sunanta yana kokarin sake kamo
Hannunta tayi baya tace “don’t you dare touch me,”
Jikinta na karkarwa tace “do i even know you? You have the audacity to touch me? Just because we are maids doesn’t give you people the right”
Tana fadin haka ta juya a zafafe zata futa ta barshi tsaye da mamaki fall cike ranshi…..bata ganeshi bane? Kodai he’s mistaken? Kai ina babu yanda za ace kamanni take da fatima, daga muryanta zuwa height dinta kamanninta da komai uwa uba zuciyarshi bazata maahi karya ba fatima ce…then whys she acting kamar bata sanshi ba?
Ay ko taku biyar batayi ba zatabar kitchen din sake kamo hannunta ya jawota sosai jikinsa yana kokarin kallon cikin idanunta taqi yarda su hada idanun, ta fara kokarin kwace hannunta, shi kanshi hes confuse at the moment.
“Ka sakeni mana mene haka wai? Na shiga uku anty rabi, anty rabi”
Ta kwalo ma rabi kira, “fatima!!! Ya sake kiranta, tayi kamar batasan me yake cewa ba,
Rabi ta shugo kitchen din da sauri, “sabee…”
Saurin dakatar da ita sabeeha tayi saboda gudun karyaji sunan data kirata dashi, tunda ya ganta bata da option daya wuce ta nuna batasan shi ba batasan mai kama dashi ba.
“Anty rabi kinga ya wani riken hannu, ni bansan me nayi ba, na shiga uku” ta fada tana neman fara kuka.
Rabi babu english,😂ta rasa yanda zata tambayeshi me yakeso.
“Yallabai kayi hkuri dan Allah,” rabi tayi maganadon ta dauka ko maganganun da maya tayi daxu ne sukayi tasiri ganin yanda kowa hankalinshi ya tashi da aka fitar da anne.

Ay baima san tana yi ba kallon sabeeha kawai yake tana kokarin kwace hannunta kamar kurma.
“Ki fada mashi da turanci bakisan me ya faru ba dazun tunda shiga kika yi kika taddata ta yanke jiki ta fadi”
Sabeeha najin haka tayi saurin kallonshi tace
“Sir please leave me alone, I didn’t do anything, i just went into the room and saw anne,”
Tundata soma magana yake kallon labbanta yana karantar abunda take fada don gaba daya ta gama gaukata mashi kwakwalwa da confusion.

Waye baki rabi tayi ganin yanda yake matsowa dab da sabeehar gashi ya kankame hannunta har suka kaiga bango, jikin sabeeha na bari ta kasa kallon cikin idanunshi trying as much as possible karya gane itace,
“who are you???”…tambayar data futa a bakinsa kenan a zuciyarsa kuwa ga gama yarda da sabeeha ce wannan, amma yabrasa wani tunanin zaiyi.



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 100

Saida yakai ta karshen bangon kamar zai hade jikinshi da nata ya kureta da idanunsa da sukayi jaa sosai hannayensa kuwa har zuwa lokacin da jikinsa bari suke kamar mazari, tsoro gaba daya ya dirar mata amma ta danne sosai taki yarda su hada ido don gani take kamar zai gano ta.

Bakinta na rawa tace “you’re hurting me” ta fada ahankali idanunta na kawo kwalla, allah allah kawai take ta kubce masa.
Word by word yake kallon bakinta yanda take magana, yabi fuskarta da kallo tundaga kan idanunta zuwa hancinta da dan bakinta dake motsawa, ya shagala sosai wajen kallonta kuma bai saki hannun nata ba rabi ko na daga tsaye gaba daya mamaki ya gama cikata.

Wayarsa da karar ta katse moment dinne yasa shi dawowa hayyacinsa, yayi saurin sakin hannunta dayayi jaa tsabar kamawa da yayi, yana sakinta kuwa tayi hanzarin rabawa gefe wajenda rabi ke tsaye, gaba daya a furgice take ita kanta.
Runtse idanunshi yayi bai sake kallon inda take ba ya futa daga kitchen din.

Kallonta rabi tayi tace “akwai wani abu ne tsakaninku?”
Dam gaban sabeeha ya bada ta fara wulla idanu kamar munafuka, “ni ban taba ganinshi bama sai yau,ko magana bata taba shiga tsaknaina dashi ba anty rabi”
Shuru rabi tayi don tunaninta gaba daya bai tsaya ko’ina ba sai kodan maya tace sabeeha ce tare da anne lokacin data fadi, amma da sabeehar ta mata bayani saita fuskanci komai, don tana barin wajen anne ta wuce dakinsu sabeehar ta shiada mata anne na nemanta ita kuma sabeehar ta hau sama.
Gaba daya jikinta mazari yakeyi har ta futa daga kitchen din bata waiwayi rabi ba, gabanta wani irin mumunan faduwa yakeyi ta wuce daki, tana shiga ta tadda basira kwance kan gado, toilet kawai ta shige idanunuta na cicikowa da hawaye ta shiga ta rufe kofar tare da tsayuwa jikin kofar, kukan da take boyewa tun dazu ta fashe dashi sosai, gaba dayan taa koma wata jajawur abunka da farar fata, fuskanta ya kankance sosai batama san ta zube a kasa wajen kofar ba, hade jikinta tayi bakin kofar tare da chusa kanta tsakanin kafanta tana hawaye kasa kasa “ya zanyi? Innalillahi wa inna ilaihi rajiu’n yanxu idan ya ganoni ya zanyi? Noo..i will never let that happen,“ tana fadin haka ta sake fashewa da kuka, daga nan ta fara sakawa da wararwe da zuciyarta, “kodai nace wa mama ta maidani lafiya?” Tunawa da karatunta yasa taji wannan ba option bane, harga allah tana son karatunta sosai, akullum in taji hadiza na cewa zata maidata wajen dangin ubanta saitaji gaba daya hankalinta ya tashi sosai, tsagaitawa tayi da kukan da bazai amfanera ba ta tambayi kanta? Ya zanyi na kubce masa?” Tasan cewa tunda har ya ganta bazata iya masa wasa da hankali ba ta hanyar karyar cewa ba ita bace ba, kuma ta dauki kudirin duk yanda za ayi saitayi denying dinshi, bazata taba bari ya gano ita ce ba.
Maganganu ta soma ji daga cikin daki wanda yasa ta wanke fuskarta gaba daya ta budo kofar tare da futowa,“ yauwa babarku ta shigo yanxu tana kiranki” basira tayi magana tare da juyawa tana latsa yar nokia ta.
Gyaran dankwalin dake kanta tayi tare da fucewa daga dakin ta nufin dakinsu bakinta dauke da sallama.
Hadiza dake zaune bakin gado wayar dake makale a kunenta tayi saurin ajewa tana kallon sabeehar daga sama har zuwa kasa, “zauna mana kin tsaya min a ka” hadiza tayi magana babu wasa.
Zama sabeehar tayi gefe yanda hadizar na fuskantar kafin hadizar tace “daxu da kikaje bangaren hajiya kafin ta fadi kunyi wata magana ne?”
“Ah ah, ina shiga na tadda ta yanke jiki ta fadi”
Shuru hadiza tayi tana wani nazari kafin tace “zamuyi wata magana, yanxu, bawai ina neman yardarki bane ko amincewarki, umarni ne zan baki, kuma daga dangin ubanki”
Tunda hadiza ta soma magana gabanta ke faduwa sosai ba kadan ba.
“Kanin ubanki ya kawo mijin aure kuma na amince don harna bada ke, saboda haka inason ko hajiya ta tambayeki amincewarki kice kin amince kina jina ko”
Ta karashe kamar da fada fada, wani irin gumi ne ya karyowa sabeeha kamar ta watsa mata garwashi a jiki, “zaki iya tafiya”
Tunda ta miqe ko gabanta bata gani kwata kwata, don wani irin duhu duhu take gani, haka ta lallaba ta wuce daki allah yaso basira bata ciki ta zauna gefen gado tare da dafe kanta dake mata azababben ciwo sosai, abubuwan sun mata yawa ta rasa wanne zata dauka.



Ban garen taj bayan futarshi daga main house bai tsaya ko’ina ba sai part dinshi, har zuwa lokacin jikinsa bai dawo daidai ba, kanshi yayi rudu rudu jiniyoyin duk sun tashi, ya karade ya koma jaa sosai.
He’s so confused at the moment ya rasa wani tunanin zai fara.
Yana shigowa bedroom ya wuce sama direct tare da zama gefen gadon ya dafe kanshi moment din dazu na zuwan mashi, ko a mafarki bazaiga fatima ya kasa shaida ta ba balle a zahiri,gaba daya daga jikin shi har zuwa zuciyarsa sunsan da presence dinta a kowane lokaci, tunani da yake yawo akanshi bai wuce “to kodai he’s mistaken ne? Koba fatimarshi bace? Amma zuciyarsa ta rigada ta amince da itace, fatima ce duk denying din da takeyi, amma meysa ta nuna kamar bata sanshi ba? Why? Why?” Shine tambayoyin daya kasa bama kanshi amsa, sai amsa guda, daya bama kanshi, “kodai saboda abunda ya mata a baya? Ko saboda korar wulaqanci daya mata? Infact ay a wajenta babu komai a tsakaninsu, tunda ya yanke duk wata alaqa a tare dasu lokacin daya mata korar wulaqanci, saidai kuma ta bangarenshi daya san cewa matarshi ce har a zuwa yanxu, don bai saketa ba, dukda a lokacin daya gano cewa babu cikinshi a jikinta har ya janyo ya koreta daga gidan har hidaya ta kawo mashi takardar divorce baiyi gangancin rabuwa da ita ba, zuciyarsa bata taba yarda da yin haka ba, kuma bata amince da yin haka ba, don tun a alokacin ya san cewa bazai taba iya rabuwa da fatima ba, ya kasa rabuwa da ita, yakai wajen awa guda bai motsa ba yana wani dogon tunani, kanshi wani irin ciwo yake masa tsabar confusion din da yake ciki.

Acahn asibiti kuwa nanna ce kawai ta lura da baya wajen, sunkai wajen 3hrs lokacin ana gab da magrib har zuwa lokacin anne bata farka ba, nanna tasa hamad ya maido dasu maya da laila, ya rage daga anty fadila sai nanna da ya sameer, matanshi da sukazo suma nanna tasa ya maidasu gida saiya zamana daga nanna sai anty fadila ne kawai yanxu a Asibitin.
Anty fadila ta kira anty bahijja ta shiada mata, yanda hankalin kowa ya tashi itama haka nata ya tashi sosai ba kadan ba.
Misalin karfe takwas sai gashi ya dawo asibitin, cikin dakin ya shiga ya tadda anty fadila gefen gadon inda anne ke kwance ita kuma nanna na kan sallaya bata dade da idar da sallah ba.
Sallamarsa tasa suka juyo gaba daya bayan sun amsa
Nanna tace “ ka dawo?”
“Eh” ya amsata kasa kasa tare da tambayar ya mai jiki sannan ya gaisheda antyy fadila dake zaune.
Wajen da take zaune ta tashi ta bashi waje ya zauna yana kallon anne dake sanye da kayaj asibiti, an daura mata oxsygen a hancinta don ya taimaka wajen regulating nunfashinta, lokaci guda gaba daya ta rame sosai, wani irin tausayinta yakeji don allah kadai yasan irin abunda takeji, cuta ba mutuwa ba Allah ya tashi kafadunta Ameen.
Gaba dayansu kowa tsoron rasata yakeyi, don itace jigon su gaba daya.
Tashi yayi ya koma gefen nannan don tana kusa da 3 leather seater anan ta shimfida abun sallah, kafin kasa kasa ya soma magana da ita “oummi, ina ganin maizai hana a futar da anne kasar waje? I believe sai tafi samun kulawa ta musamman achan tunda akwai kwarrun neurologist around the world”
Shuru nanna tayi tana nazarin maganganunsa kafin tace, “ina ganin mu fara gwada na nan din tunda doctor barau yace she’s under treatment idan abun bai yuwu ba sai a fitar da ita”
Suna cikin magana dr ya sake shugowa da kanshi, aka cire drip din da aka saka mata tare da daura wani sabo, sannan yayi mata yan gwaje gwaje kafin ya futa.
Futarshi babu jimawa uncle sameer ya dawo, yana shugowa nanna tace “harka dawo babban yaya?”
“Eh ya mai jiki?” Ya tambayeta
“Da sauqi”
“Allah ya tashi kafadunta”
Gaba daya suka amsa da Ameen.
Sun jima sosai a asibitin har wajen karfe goma, dinner da aka kawo daga restaurant din asibitin babu wanda ya taba bawai don wani abu ba saidai gaba daya kowa yayi loosing appetite gaba daya.
Taj dai tunda ya zauna kan kujerar nan babu abun da yake sai tunani, he looks so lost and disturbed, ba tun yanxu nanna ta lura da haka ba tunda ya shugo taga hakan a fuskanshi, abunda da farin mutun.
Ahankali nanna ta dafashi ganin yayi nisa cikin tunanin da yake kamar baya jinta gaba daya, tunani take mai zai sashi fadawa dogon nazari haka ta har zata kirashi wajen sau uku amma bai jiba.
“You look disturbed, are you okay?”
Hannunshi ya aza ga fuskanshi ya shafo lallausan gashinsa tare da sauke ajiyar zuciya yace “yes I’m fine”
Shuru nanna tayi kafin tace “ ku koma gida zan zauna da yaya,kai sameer ka maida fadila ta dan huta gashi tabar iyali a gida”
Cikin hanzari tace “ah ah nanna, zan kwana anan kece ya kamata ki tafi saboda yanayinki kema”
Jin fadila tayi magana yasa sameer cewa “gaskia hakan ya kamata, tunda ga yanayinki kema nanna”
“Nidai da kun barni na zauna da yar uwata nayi jinyanta” ta sake magana tana dafe kirjinta dake mata dan ciwo ciwo tun daxu amma ta daure, yawan stress ke jawo mata hawan jini sosai.
Da larabci ya soma magana yana kallon nanna, “please oummi, anne would not be happy idan kema kika kasance a kwance anan, you don’t look alright as well kuma kinsan abunda doctor yace you shouldn’t be stress out okay?”
Badan taso ba tayi shuru kawai batace komai ba.
Dagowa yayi ya kalli anty fadila da sameer kafin ya suake ajiyar zuciya yace “uhm..ina ganin kuje kawai gaba daya zan zauna anan, kamar yanda nanna tace, yayi nuni da anty fadila “she also have a family waiting for her, kuje kawai zan zauna da ita duk wani abu daya taso i will inform you immediately”
Jinjina kawai sameer yayi sukayima taj sallama harda anty fadila wadda itama bataso tafiyan ba suka fita.

Actually he needed alone time specifically a wannan lokacin da kuma situation din da yake ciki, he needs to sit and think critically about everything.
Tun bayan futarsu sau biyu doctor barau ya sake shugowa don duba yanayin anne, ya kara ma taj bayanin situation din nata yanda zai gamsu don harga allah shi yana recommening a futar da ita sainyanxu ya gane a wannan yanayin futar da ita can risk her life dama dai ba a fara treatment bane to da sauqi.
Yana daga zaune by the 3 seater dogayen kafafunshi na kasa while jikinshi gaba daya yayi relaxing a jikin kujerar, babu abunda yake sai tunanin fatima,wani irin fargaba yake jin datake sashi shiga yanayi.

Washe gari da sassafe anty fadila da sameer suka iso asibitin tare da hamad, nanna na gida saboda jininta daya dan hau, bayan sun gaggaisa suka tambayeshi ya jikin anne ya masu bayani kafin sameer yace “ya kamata kaje ka huta, we will handle”
Jinjina kai kawai taj yayi, kana ganinshi kasan baiyi barci ba kwata kwata daren jiya don daga yanayinshi ma zaka gane.
Sallama ya masu ya futa daga asibitin ya shiga motanshi.
Yana kunnata yayi reverse bai tsaya ko’ina ba sai gida lokacin wuraren karfe takwas da rabi ta dan gifta.
Yana isowa yayi packing tare da kashe motar ya futo, ya nufi hanyar part dinshi, bai kaiga karasawa ba ya dan dakata ya dubi main house, a dai dai wajen da idanunshi ya sauka kan inda ta tsaya iiya lokacin daya fara ganinta a gidan, saurin kaud akanshi yayi ya wuce part dinshi direct.
Wanka yayi ko cire towel din jinkinshi baiyi ba ya hau kan gado ya kwanta ko minti goma baiyi ba barci ya kwasheshi.
Barci ne yakeyi bawai don dadi ba saidan jikinsa na buqatar hakan don kwana yayi yana tunani aranshi.

Ta bangaren sabeeha ma hakan ta kasance don bata samu tayi barci ba, kwana tayi tana rokon allah ya shiga lumuranta, maganar auren nan da mama ta bujiro mata ba karamin girgiza ta yayi ba idan zata so kanta harga allah babu maganar auren a burikanta na yanxu, karatu takeso tayi ta inganta rayuwarta, wannan karatun yasa ta taji tana da hope a rayuwa.
Bayan wannan tunanin yanda zasu dunga haduwa da taj take, ta yaya zatayi avoiding haduwa dashi?ya rigada ya ganta, gashi ta kasance itace yanxu mai gyaran part dinshi, tunawa da wannan kadai yanasata shiga tashin hankali.
Gaba daya duk tayi sanyi haka ta futo suka shiga kitchen da su rabi.
Tana tsaye kan counter tana fere dankali gaba daya kowannensu yayi jugum jugum, tun jiya gidan bai dawo daidai ba saboda abunda ya faru da anne.
Cikin abunda hai wuce 2hours ba suka kammala komai kafin a fara jerawa dining, suna gama komai ta koma daki ta zauna tare da tagumi.

Tsoron futa take gaba daya gudun karta hadu da kowa, tunawa da maganganun rabi datayi dazu na cewa duk sun tafi asibiti yan matan ne kawai a gidan da nanna yasa tayi tunanin allah yasa harda shi.

Batasan da shugowar basira ba sai ganinta datayi tsaye a gabanta “bazaki tafi kiyi aikinki ba yau kika zauna?”
Dagowa tayi da rinannaun idanunta ta kalli basira tace “dan allah zaki iya taimaka min yau? Cikina ciwo yake sosai”
“Gaskia bazan iya ba wallahi, ayyuka sunmin yawa lokacin da nake son yi ba a bani ba sai yanxu, bayan wannan ma daman saboda naga balaraben nan ne tunda baya gidan

68 / 107