anzo buncike.
Amma kuma duk wani abu da ake mata baza a fasa yinshi ba, kama daga kan karatunta, gatan da ake mata da komai babu abunda zai sauya, laifin uwarta bazai shafeta ba, sun rugada sun karbi kaddarar abunda ya faru, kuma babu wanda zai iya sauya komai tunda ya wuce.
Shugowar hamad da sallamarsa yasa ta juyo tana kallonsa, fuskanta dauke da murmuahi da kullum cikin yinshi take, tana sanye cikin wani dankararrwn lace, zata iya cewa wannan ce sutura mafi tsada data taba sanyawa a jikinta, tayi bulbul, yarinya cikin wata guda ta sauya gaba dayanta, tsabar kwanciyar hankali, da farin ciki da take ciki.
“Ya hamad!!!” Ta kira sunansa firgigi ya dawo hayyacinsa, ya sauke mata wani murmushi mai kyau.
“Ina kwana ya hamad?”
“Lafiya lau my beautiful cousin” baima san ya fada ba, ta sauke fuskanta tana blushing, wannan ne first time daya fadi hakan, shima baisan yayi subutar baki ba saida ya gama fada.
Paper bags din daya shugo dasu ya aje mata a gefe sannan yace “mami tace a kawo maki,”
Ahankali ta danyi blushing sannan tace “mami bata gajiya, ace mata na gode allah ya kara arziki mai albarka”
Ya amsa da ameen, “hmm kije mata godiyan da kanki, daman tace kwana biyu baki shigo ba kinyi breakfast??”
“Ah ah” ta amsa shi tana murmusawa
“Let me wait for you ki gama sai Muje muyi a kasa” ya fada kai tsaye, ta danyi shuru, sannan ta cigaba da gyaran gadon shi kuma ya zamu waje ya zauna kan wani dan pink couch da akeyi decorating dakin dashi, samanshi irin furr blankies ne a jiki, komai fess fess, ga dakin sai kamshin bakhoor yake.
Tana gamawa ta tattara paper bags din ta aje su closet sannan ta futo, ya miqe tsaye, hannunshi ya zuwa cikin aljihunsa ya zaro abu daga ciki sannan ya dubeta yace “can i see you palm”
Dan murmushi tayi surprisingly sannan ta bude mashi palm dinta ya sauke mata wata yar sarka mi kyan gaske jikin pendant din sarkar akwai letter F a jiki fatima kenan, sannan ga wani dan diamond stone pink a tsakiya.
Tana ganin sarkar ta bude baki zatayi magana yace “don’t thank me, its a gift from me”
Shuru ta danyi wani irin dadi na dabaibayeta, tun safe kowa ke gifting dinta da abubuwa ta rasa dalili, koda tajw gaida anne da safe haka ta bata wani zobe har tana bata tarihinshi, tun tana budurwa babanta ya saya mata shi, irin customize unique gemstone ne made of emerald and sapphire akayi zobe dashi, wane diamond wane gold, value dinshi ba karami bane don arziki ne mai zaman kanshi.
Daman bata samu wanda ya chancahnci yayi inheriting dinshi ba tun daga kan yayanta sai yanxu, zuciyarta ta aminta da babu wanda is more valuable da zaiyi inheriting sai sabeehar.
Haka nanna ma ta gwangwajeta da gifts da batama bude wasu ba, don basa gajiya da saya mata abubuwa, set of abayas ne, gadget ne, kai komai ma babu abunda ta nema ta rasa, wasu yan zobunan gold nanna ta saka mata a hannunta da kunenta, wai tana mace ya kamata ace tana gayu karta zauna hannunta babu zobe.
Oh wai hannun sabeeha ma kanshi dauke yake abubuwa masu daraja, haka yan chukwi chukwin hannayenta suka fito fess fess cikin zobunan.
Saukowa sukayi ita da hamad, tana gaba yana biye da ita a baya yana cracking jokes da ita, gaba daya ta gama sakewa da kowa, ta zama wata yar gayu sosai kamar ba ita ba.
Suna karasowa dining din idanunta ya suaka kan na taj, yayi kamar bai gansu ba, tunda suka kusa karasowa ya kafeta da idanu, haka kawai yaji he’s not confortable yanda ya ganta da hamad tunda ba muharraminta bane, kuma har zuwa lokacin akwai aurenshi akanta.
“Kin sauko yarinyar kirki” nannan tayi magana tana murmushi, dan murmusawa sabeeha tayi tace “eh nannan”
Kujera hanad yaja mata zata zauna kenan taj ya dago da idanunshi ya nata wani kallo daya dayasa cikinta rudawa, ta kasa fassara irin kallon gaba dayanshi, don gaba daya yanayinshi ya sauya tunda suka karaso.
Saurin kauda idanunta tayi tana hana kanta sake hada ido dashi, ta zauna a natse, daidai nan laila tayi sallama hannunta rike da warmers mai aikinsu na biye da ita.
“Good morning nanna..good morning uncle taj..”
“Good morning dear” nannan ta amsa ta taj ko ko dagowa baiba ya wani hade hannayenshi a kirjinshi, “mami tace a kawoma uncle taj da sabeeha breakfast”
“Ah lallai mami naji dasu fa, wannan exquisite breakfast haka” nanna tayi magana,
Kamshin turaren da sukaji yasa duk suka dago, anne ce ta karaso da yar sandar ta dake taimaka mata wajen takawa saboda kafa, doctor yace ta dunga yawan saukowa kasa karta lamunci zama a sama tana breakfast, wannan yasa yabxu take saukowa ayi da ita ba kamar da ba da rabi ke kai mata sama.
Rabi dake shige da fuce daa warmers da sabbin yan aiki da aka kawo su biyu tana karasowa ta fara kwasar gaisuwa sabeeha tayi saurin minkewa zata tayasu rabi tace “ah ah kiyi zamanki hajiya karama…”
“Anty rabi ki daina kirana da hajiya karamar nan ki kirani da sunana pls” ta fada adan shagwabe, duk sauta bawa kowa sha’awa so cute har wani lumshe ido take tana tabe baki, hamad ya kasa daina kallonta taj ko idanunshi na kan sa, anne ta murmusa tace “toh kin daiji ko rabi? Karki maida min jika tsohuwa, koda yake hajiya tace, ki jira taje ta sauke farali tukunna saiki kirata da hajiya da hujja”
Duk aka kyalkyale da dariya, rabi ta soma serving abunci cikin jin dadin yanda ake mata a gidan kamar ba yar aiki ba, kowa sonta yake sosai basa kyamatarta.
kai rabi tayi ma sabeeha murna sosai, tayi murna ba kadan ba, daman fa tun farko tana ganin yarinyar tasan jinin masu arziki ce, don akwaita da kyau.
Cikin natsuwa kowa keyin breKfast, babu abunda kake ji sai sautin faranti da chokula, suna gamawa rabi ta futo zasu kwashe sabeeha da laila suka tayasu, su anne kuma suka koma sitting room ita da da nanna da taj.
Laila da sabeeha na futowa suka nufi sitting room, suna karasowa sukaga babu kowa a kasan, daidai lokacin hamad yayi ma laila flashing a wayanta tana ganin call din ta dubi sabeeha sannan tace “muje garden”
Sabeeha dai binta kawai take suka futo tare, suna karyo corner wajen garden daga nesa kawai sabeeha taga an kawata wajen, suna shiga kuwa gaba daya yan kananun yaran gidan suka soma ihu harma da iyayen, “happy birthday!!!”
Wani irin shock sabeeha ta shiga ta bi kowa da kallo daya bayan daya, su anne na daga tsaye da nanna a gefenta ga bahijja da majeed suma a tsaye rike da flower bouquet ga hamad a gefensu da fadila, anty mubina ma da ya sameer na daga tsaye anty laila ce kawai bata wajen, su abla na rike da bubbles da ballons, taj kuma na daga tsaye shima daga chan gefe ya saka hannayenshi cikin aljihun sa, har zuwa lokacin yanayinsa bai dawo daidai ba.
Laila ce ta jawo hannunta zuwa gabansu ta tsaya tabi ko’ina da kallo yanda aka kawata wajen ga wani decor da akayi daga gefw an rubuta Happy 23rd birthday Fatima.
Tana kallonsu batasan sanda hawaye ya sauko mata ba, all this while bata san asalin date of birth dinta ba da cikakkun shekarunta don da an tambayeta saidai tace 20.
She can’t express yanda taji a daidai wannan lokacin saidai hawayen farin cikin kawai.
Bahijja ta tako inda take ta rungumeta sannan ta soma goge mata hawayen fuskanta kafin tace “yau kin cika shekara ashirin da uku a duniya, allah ya yi maki albarka ya kare daga duk wani sharri”
Tana gama fada ta gige hawayen datake kokarin boyewa, tunda sabeehar ta karaso wajen taji wani abu ya daketa, dakyar take dannewa kawai.
Bouquet din ta miqa sabeeha ta karba, “don’t cry okay??” Girgiza mata kai sabewha tayi alamun bazatayi ba, kafin ahankali tace “thank you Maamah na”
“Love you always and forever” bahijja ta fada tana pecking khmatunta,
Majeed ya karaso shima ya rungumeta sosai yana farin ciki yace “happy birthday my princess…”
“Thank you dada” sabeeha ta amsa tana murmushi, haka suka bita daya bayan daya suna rungumeta, she felt their unconditional love har cikin zuciyarta.
Bahijja ta fidda wata dankararriyar set din sarkar gold da tasha wani mahaukacin package, ta fiddota waje sannan ta saka mata a wuyanta, tana gama saka mata tace “toh muje muga gift din daddy ko”
Duk suka dunguma zuwa compound din gidan, suna fitowa maaikatan da sukayi delivering package din suka soma budewa, wani katon kwali ne mai girman gaske suka soma dagawa har sukayi nasarar cireshi gaba daya ballons masu shegen yawa suka zubo, take wata dankareriyar mota ta bayyana, fara tarr irin Porsche dinnan ta mata, shock din data shiga ita kanta ji take kamar ba a dubiyar take ba, daddy ya danqa mata keys din porshe din mai kyan gaske, “this is from daddy, but….saikin gama school zaki fara tuqawa okay???”
Bai gama magana ba sabeeha ta duqa har kasa ta rasa da wnai baki zata masu magana, she’s speechless,
“Oupps anne fa tace kujerar hajji na jiranki next year insha allah” fadila tayi magana tana murmushi, sabeeha najin tayi sujjada ta godema Allah tana kuka, jikinta da bakinta na rawa tace “bansan ta yanda zan gode maku ba, allah yasa da alkairi, ban taba tsammanin zan samu irin wannan gatan ba maamah, dada,.. im bery grateful allah ya saka maku da mafificin alkahiri yaza kufi haka ya daukka ku ya tsareku,” tana gama fada ta dubi ta dubi sauran dake tsaye sannan ta cigaba “anne..nanna…mami,(fadila) ya hamad dady abla (uncle sameer) anty mubina, cous (laila) sunan da take kiranta yanxu kenan, ya hamad..daidai wajen taj ta dan dakata tana kallonshi cikin ido sannan tace “uncle taj… i will like to thank each and every one.. bansan da me zan saka maku ba,“
Yanda take magana saida ta basu tausayi, magana take jikinta na rawa tsabar murna.
“Mami ku bari na daukemu pictures” laila tayi magana aka tsa tsaya ana picture, kowa har rushing suke wajen daukan picture din da ita, laila ta dubi ya hamad tace “ya hamad ka shiga a maku”
Dan matsawa yayi gefen sabeeha rike da bouquet aka dauke su a hoto, ganin sun danyi nesa da juna yasa laila cewa “ya hamad ka matsa sosai mana baiyi kyau ba ka tsaya kamar soja”
Tana fadin haka ta dan matsar dashi kusa da sabeehar sosai, anne da nanna suka murmusa, anty fadila ma murmushin tayi kawai.
Ana gamawa laila ta dubi taj dake tsaye ya hade rai shidai bazaka taba tantance yanayin da yake ciki ba koda yaushe mood dinshi daban ne.
“Uncle taj picturesss”
Kamar bazai motsa ba chan kuka kawai sai ya matso, shi baima tsaya ya bama laila damar cew baiyi kusa da sabeehar ba don baima bada wani gap ba jikinsu na gogan juna,
Laila ta soma daukan pictures din, kai wallahi ba karamin matching sukayi ba abunda, sai wanda ya hango hadewarsu.
Ba a gama daukan hoton ba sabeeha ta zaro idanu gabanta na faduwa jin hannunshi a ta wajen ass dinta, cikin sauri ta dubi su bahijja ganin hankalinsu baya garesu yana ga motar da dady ya saya mata suna dubawa ita kanta lailar bata lura ba don ta baya ya dora hannunshi a wajen, daya tashi ma palm dinshi biyar ya bude yayi ya dora a wajen kamar wanda zaiyi spanking ass dinta.
Juyowan datayi ta dubeshi in so much shock yasa shima ya kalleta fuskar nan babu annuri kwata kwata, jikinta ya soma rawa cikin sauri ta matsa daga kusa dashi kamshinsa ya biyota.
Gaba daya aka tattara aka koma cikin gida.
Maya dake labe wajen entrance din apartmanı dinsu duk abunda ya faru akan idanunta, tun bayan futar bahijja daga dakinta don tana tashi da safe bahijja ta shugo dakin ta don taji ya jikinta, don kwana tayi da ciwon kai, gaba daya ta daina sakewa sosai kullum tana daki, har abun ya soma damun bahijja,ta nuna mata ta cire komai aranta ta mance da komai amma taqi, tana shigowa dakin as usual yanda ta saba duk zagayowar shekara she will be the first da zatayi wishing mayar tare da mata adduar shekaru masu albarka don bazata taba mancewa da ranar haihuwarta ba musamman yanzu da komai ya sauya.
Haka ta shigo mata da gift sannan tayi wishing dinta, gidan yan boko kenan😂
Maya na kuka ta karba gift din tare da rungume mummyn, atleast yanxu ta kara tabbatar da suna sonta kuma yace a wajensu dukda basu suka haifeta ba.
Saidai kuma tunawa da wani abu yasa taji jikinta yayi sanyi sosai, idan yau birthday dinta to tabbas yau ne na sabeeha ma, kai wannan wace iriyar kaddara ce, ta rasa wanne yafi mata zafi aranta the fact that ita ce aka sauya da sabeeha kuma ta kasance itace yar mai aiki ko kuma sabeeha data kasance yar masu gida, duk ci cika bakin nan nata a banza, da wulaqancin data dunga yima sabeehar ta kirata da yar talakawa mara uba mara gata ashe itace da wannan matsayin ba sabeehar ba, idan ta tuna da wannan abu ji take kamar….
Kafin bahijja ta fita daga dakin ta shiada mata ta futo tayi breakfast tace mata kanta na ciwo, hakan yasa bahijja tace toh basira zata kawo mata, allah sarki duk yanda tayi haka bahijja ke binta dashi, babu abunda ta sauya game da kulawa da take mata, tana son maya hakika har cikin zuciyarta sosai ba kadan ba.
Tun bayan futar bahijja ta kasa natsuwa, wani abu na ce mata ta futa, haka kawai taji shes restless tayi gathering courage dinta ta futo, tana futowa bata kaiga shiga main house ba ta jiqo muryoyinsu daga compound tana karasawa taga surprise din da aka shiryama sabeeha, saida taji wani dumm akanta kamar zata fadi, ta kafesu da idanu batasan sanda hawaye ya soma sulalo mata ba ta koma part dinsu da gudu, a daidai lokacin su kuma suka fito daga garden, bata hakura ba ta sake lekowa nan ne kuma ta kara ganin abunda ya sake hargitsa mata lisaafi, ta kafe kaff ta kasa motsawa ta bisu da ido daidai lokacin da daddy ke presenting motar daya sayama sabeeha, daga nesa tana hango fuskar sabeeha ta kafeta da idanu, reaction dinta na sauyawa kamar ba ita ba, da kuka take amma tuni kukan ya kafe abubuwa na running a mind dinta, wani zunzurutun shaidani na tunzirata yana ayyana mata negative abubuwa a mind dinta, take taji tsanar da takema sabeeha a baya ma ay wasa ne, yanxu ne takejin tsanarta ninkin ba ninki, babban farin cikin ta a duniya yanxu shine taga sabeeha bata nunfashi a doron kasa.
A daidai lokacin ne kuma aka fara duakar hoto,gaba dayansu tana kallon yanda sukema sabeehar saitaji dukkansu ta tsanesu suma, sanda taga hannun taj a kan ass sin sabewha kuwa batasan santa ta dunkule hannunta ba zaro zaron farcenta ya soma ji mata ciwo don harta fara bula fatar tafin hannunta, ya soma fidda jini, idanunta yayi jaa sosai, ta soma magana ahankali.. “,sanadiyarki na rasa duk wani farin ciki na, kinyi nasarar kwacemin komai nawa, i wish you never exist, you can have it now while it last kafin na kwace duk wani abu da kika rabani dashi… nayi alkawari bazan barki ba koda kuwa zai zamo na kasheki ne da hannuna saina dandana maki pain din da kikayi sanadiyarsa a cikin rayuwata”
Tana kaiwa nan ta wuce part dinta sai kuka, kuka take wiwi wiwi saida tayi mai isarta kafin ta dakata tunawa da kuka yanxu ba nata bane, dole ta samu hanyar da zatayi ta mallki taj kota halin qaqa, yanxu trick din da takema mommy bazaiyi amfani ba don idan tayi a lokacin tana amatsayin yarta da duk abunda ta nema zata mata yanxu ko ba lallai ta yi mata abunda take so ba, kuma ta tabbata yanxu da suka san asalinta babu wanda zai sake maganar aurwn nasu musamman mummyn ma, balle kuma akaiga anne, da tun tuni daman bata amince ba balle kuma yanxu?, dole tayi fiding solution duk yanda za ayi ta mallaki taj kota halin qaqa ne, atleast tasan daga nan duk wani abu da zai biyo baya mai sauqi ne.
MATAR TAJ (destined with you)
Written by
Queenmarh
Book2
PAID
Chapter 110
wunin ranar dai kowa cikin farin ciki yayi shi banda maya, don har abuncin sadaka saida akayi mai yawan gaske, sannan aka diba kayayyyakin sadaka daga foundation din anne da za akai gidan marayu da marasa karfi.
Su sabeeha na zaune suna packaging abubuwan makaranta na yara wanda za akai gidan marayun sunata hira abunsu sallamar maya da shigowarta yasa duk suka dago suka bita da ido, tana sanye da plain abaya baka, wadda ta saje da skin dinta saboda rashin kulawa da bata bashi cikin kwanakin, kai tun lokacin da gaskiar ala’amarin nan ya bayyana ta ta rasa natsuwarta gaba daya, fuskarta duk ta rame ta fada sosai kamar wadda tayi jinyar shekara guda, kusan gaba dayansu sai yau suke ganinta, kullum tana daki bata futowa, nanna ce ma dai idan ta shiga part din bahijjar take ganinta, fadila ko bazata taba tako kafarta don zuwa ganin yar hadiza ba, danne abunda ke ranta kawai take game da mayar.
Yaqe ta dan soma yi tana susune kai kamar wata ta allah ta kasa hada idanu da kowa, “ya kika tsaya shugo baby” bahijja tayi magana tana dan murmusawa, fadila ko tana dagowa ta mata kallo daya ta kauda kanta.
kamar ana jan kafarta haka ta soma takowa ahanakli ta karaso inda suke ta zauna a kujera dake gefensu ta dan rakube kanta a kasa kamar wata ta allah cikin natsuwa tace “good morning nannan, good morning anne”
Duk suka amsa a tare, fuskansu a sake, juyawa tayi ga anty fadila ta gaisheta, toh dai ciki ciki ta amsa ta ta maida hankalinta ga abunda take, bahijja tayi mirmushi ganin mayar ta futo itama,kuma ta fara sakewa yanxu, it was very hard for her to accept the fact, da yanda abubuwa ya sauya cikin kankanin lokaci, tana tausaya mata sosai har cikin zuciyarta kuma bata blaming dinta da komai, tana kaunar maya har cikin zuciyarta tsakani da allah dukda bata