Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   16 / 107

45K to 48K   out of 320.4K words

mata dining din.

****
Su ammu na daga zaune ita da sabeeha saiga head maid ta shugo kai tsaye, allah yaso ba maganar cikin suke ba, ammu na ganinta ta fara masifa, “waya baki izinin shugowa haka kai tsaye without getting consent”
“Maam, madam ce tace nazo na…”
Bata bari ma takai karashe ba ammu ta dakatar da ita, “ba madam ba koma wanene ya buqaci ganin daughter inlaw karki sake shugowa dakinta babu respect,”
“Yea ma’am”
Tana fadin haka ta fuce, tana futa ammu ta kalli sabeeha tace “muje, karkiji tsoron komai kinji”
“Tohm ammu”
A tare suka fito zuwa sitting room, gaba daya kowa yayi cirko cirko a zazzaune, ammu na karasowa da sabeeha ta dubi sonata dake zaune kusa da taj tace “ke tashi” dake tana masifar jin tsoronta tayi saurin tashi ta koma gefe sum sum, ammu ta dubi sabeeha tace “zauna daughted”
Tunda suka karaso doctor ke kallon sabeeha,
“Check her” hidaya ta umarceshi, miqewa yayi ya karaso inda sabeeha take, daman cikin shiri yazo, komai gaba yake yi zamani ya sauya, wasu abubuwan ma yanxu sun koma digital, mutun basai yasha wahalar zuwa asibiti ba.
Wani dan digital box syringe ya fidda ya dan deba jininta, jinin ya shiga box din, ya fara reading, kowa kallon doctor yake suna sauraron abunda zaice, box din na gama reading blood dinta doctor ya tura review din result din zuwa asibiti, kafin aturo mashi result din cikin yan mintuna qalilan, already yaga result din a jikin syringe din amma saboda conditions din da aka bashi yasa ya tura, ana turo mashi result din ya ajiye masu laptop dinshi a gabansu dake abun online ne, result dinka chan akayi posting,
“Shes 10weeks pregnant”
Yana fadin haka kowa gabanshi ya bada dam, masu calculation din kwanaki sunata faman yi, daga ranar da taj ya samu sauqi zuwa yanxu, ammu kuwa me zatayi banda guda.. harda yar rawarta, taj kuwa kasa gasgata komai yayi, sonata kam miqewa tayi tabar wajen sabeeha ta bita da harara azuciyarta me zatayi banda dariyar mugunta, ganin gaba daya yanda suka rikice lokaci guda, sai ayanxu ta tabbatar su komai a bayyane suke yinshi, kiyayya da baqin ciki basa boyeta sai wanda bai lura da kyau ya bude ido ne zai gani ba, kamar taj din daya kasa fuskantar su, ko yaqi yarda da zahiri.

“ tohm yanxu hankalinku ya kwanta kenan? Gashi nan dai likitanku ya tabbatar da cikin ko? Kai kuma” ta dubu taj dake zaune, yanxu ta daina mashi sauqi shima indai bazqi bude idanunshi ba yayi stepping up, “kasan responsibility dinka basai na fada maka ba,”
Tana kaiwa nan ta miqe taja sabeeha daketa faman lumshe idanu suka bar masu parlorn.

Suna shiga daki ammu ta kalli sabeeha sai kawai suka kyakyace da dariya, abun gwanin burgewa, kusancin su ya karu sosai, musamma tsakanin jiya da yau da ammu ke koya mata yanda zata dungayi don kar a gano su.

Doctor na futa hidaya ta wuce sama fadwa ta biyo bayanta taba masifa, “yanxu haka zamu zauna kina kallon abunda ke faruwa? I thought kince yana tafin hannunki sai yanda kikayi moulding dinshi? Meysa yanxu kika kasa yin komai”
Yanda fadwa ke magana kamar tana balbala mata kero haka takeji a zuciyarta, “shikenan tunda kin kasa yin komai akan idnaunki yarinyar nan zata rabaki dashi, Wannan yarinyar itace zata tona mana asiri, kuma zata fada mashi kece kikayi sanadiyar accident din…”
Rai a bace hidaya ta kalleta, “fadwaaaaa… ki fita min a daki, i want to be alone”

Rai a bace fadwa ta fuce tabar mata dakin ranta na kunci..


***
8pm.
Ya shugo gidan, bai tsaya ko ina ba sai part dinshi, yana shugowa dagowar da zaiyi idanunshi ya sauka kan sabeeha daketa faman shan fruit, taji shugowarshi haka nan ta dake ta biye duk wata fargabarta tayi kamar bata ganshi ba, tunda ya fara takowa take jin shi har cikin zuciyarta, harya wuce cikin bedroom dinshi lallo daya ya mata ya kauda idanunshi,
Ko kallonta baya son yi kwata kwata, ranahi ma baci yake da zarar ya kalleta ya tuna da taga….

Rufo kofar da yayi yasa jikinta ya mutu, ta dauka zai ce mata wani abun saitaga akasin haka, maganganun da sukayi da ammu ne yazo mata arai, gaba daya sai taji anya zata iya kuwa.
Tana nan a zaune har wajen karfe sha daya ta kasa making decision, da kyar ta smau ta tattara courage dinta ta shugo dakin bayan ta bude kofar ahankali without making a sound sanin baya son hayaniya, dakin yayi dim babu haske sai chan wajen gadon datake hangosa, sadaf sadaf ta nufi wajen closet ta shiga ciki ta duako abubuwan kwanciyarta da takw shimfidawa lokacin da bashida lafiya, tana kwasosu ta dawo gefen gadon ta shimfida ahankali sannan ta hau kai ta zauna tana mai fuskantarshi, lokacin da bashida lafiya tasan yana da nauyin barci don haka tayi tunanin har zuwa yanxu ma haka yake, batasan cewa tunda ta shugo ba yake kallonta harta shiga closwt ta dauko abun shimfida ta shimfida a gefe inda take kwanciya, take memory dinshi ya tuna mashi da wani moment, gashi da ita kwance a kasa gaba dayanshi yana jikinta ta saqalo hannayenta a kirjinshi, sai yaji wani irin takaici ya zo mashi baima san lokacin da ya doka tsaki ba, allah yaso bataji ba, don lokacin ta kwanta abunta a gefen gadon, ya dade sosai barci ya kaurace mashi sai daga baya kuma ya fuzgeshi.
Asuba ta gari….
Washe gari da asuba ya bude idanunshi ahankali, kafin ya miqe zaune, gaba daya yama manta da wata a cikin dakin don haka ya sauke kafarshi ya miqe tsaye, taku daya yayi ya take mata hannu daya, radadin ya shiga kwakwalwarta lokaci guda cikin barci ta bude idanunta tarr ta danyi yar kara ahankali, sai a lokacin ya tuna da mutun a wajen, sabeeha na ganin shine a tsaye akanta tayi saurin tashi zaune, wani irin mugun kallo ya mata ya wuce bathroom ya dauro alwala, yana alwala ya fito, ta dade a zaune harya fito hannunta na dan radadi kafin ta miqe ta shige bathroom din itama ta dauro alwala, lokacin data futo harya idar da sallah, bata hango fuskanshi sosai don haka ta kasa tantance me yakeyi, chan saqo ta samu ta zauna ta tada kabbarar sallah tana idarwa ta zauna a wajen itama har barci ya kwasheta tana azkhar.
Hasken futilar daya bade wajen ne ya sauka akan fusknta wannan yasa ta soma bude idanunta ahankali, baccin nata ya soma nauyi shiyasa taji kanta ya fara mata ciwo da hasken ya daketa, dagowar da zatayi idanunta ya sauka kan na taj dake zaune bakin gado ya kafeta da idanu fuskanshi na nan babu sauqi, cikin hanzari ta gyara zamanta.
“Ke!!!!”
Tana jin sautin muryarshi gabanta ya bada wani dam,da hannu ya mata nuni data zo, ahankali ta miqe jiki a mace ta tako zuwa inda yake, daga chan dan nesa dashi ta duqa, “sabahal khair”
Ta gaishesa a natse,bai amsa ta ba haka zalika bai daina kallonta ba yana mamaki yanda akayi har yar wannan yar abar tasan tayi havibg sex, ya gama rainata sosai ba kadan ba, yana mata kallon irin teens dinnan, inbanda ma ta rainashi how did she even hace the audacity to open her legs, he doesn’t even care yanda abun ya faru, baya fatan ma ya tuna don wannan abun baqin ciki ne a wajenshi, he feels so embarrassed and dumb at the same time.
“Shekarunki nawa?”
Ya jefo mata tambaya, kanta a kasa ta amsa shi muryarta na breaking ta soma magana “ thalathatun wa ashruna”
Tana fadin haka yayi saurin runtse idanu ya bude su yana mai kallonta,
“Na barki ne a cikin gidannan only because of this pregnancy, i don’t care how it happens and why it happens, just so you know, i will never accept this marriage inma don shi kikayi taking advantage dina without my acknowledgment, i will take responsibility for it, sannan karkiyi tunanin zan iya yafe maki for…”
Yayi shiru yama kasa fada saboda takaici, dan dagowa tayi ta kalli fuskanshi gabin ya kauda kai yana tave baki, kuma tasan abunda zai fada, sai kawai ya bata dariya, ya dago kenan tayi saurin sauke idanunta tana murmushi, daman ammu tace mata duk maganganun da zaiyi mata kartaji komai, tabishi a haka kawai.
Muryanta ahankali ta soma magana, “nasan duk abunda zan fada maka ayanxu ba lallai ka yarda dashi ba, amma inason ka sani i mean no harm to you tunda nazo gidan ina fatan watara zaka fahimci hakan kayi hakuri…” ta karashe ahankali

Da mamaki sosai yake kallonta yanajin abunda take fada yana nazarin maganganunta, magana take cikin hikima da natsuwa, lokaci guda zuciyarshi ta yarda da maganar datayi mashi yanxu, kamar magnet haka maganarta ta tsaya mashi a zuciyanshi, for her age baiyi tunanin zata iya magana haka ba, cikin sauri ya girgiza kanshi, he dont want to trust her ao easily saiya fara karantarta, amma meysa zuciyarshi ta aminta da maganarta? Why did he feel like gaskia take fada amshi she never mean harm to him?
Kwafa yayi kawai ya miqe ya wuce bathroom ba tare da ya kalleta ba harya futo cikin shirinshi as usual ya fuce





✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 67
Tana kallonshi ya fuce fuskarnan a hade babu wasa, murmushi kawai tayi ta komawarta
barci abunta hankali kwance, ta dade sosai tana barci sai wajen karfe tara ta tashi, a gurguje ta gyara dakin, tana gamawa tayi wankanta fess fess sannan ta shirya cikin doguwar riga daga cikin kayan da jamid ya taba saya mata.

Kitchen ta shiga don neman abunda zata sakama cikinta,dake akwai komai a kitchen din don duk wata ake restocking duk kitchens din dake gidan wannan ya bata damar dafa noodles taci abunta ta koshi.
Fridge ta nufa dan neman ruwa,tana budewa taga uban chocolates dayawa,batayi mamakn ganin yawan suba don tasan yana son chocolates sosai tun lokacin da hankalinshi baya tare dashi,ruwan ta dauka har ta rufe fridge din ta bude ta dauka chocolates guda daya ta rufe.

Shugowar ammu yayi daidai da fitowarta daga kitchen din, ammu na ganinta tace “daughter inlaw kin Tashi?”
“Eh marhaban ammu”
“Shukran abnati”
Zqma ammu tayi kan couch din kujerun tayima sabeeha nuni da kusa da ita ta zauna kafin ta fuskanceta.
“So tell me? Mey yace maki jiya? Did he react? Ko ya maki wani abun?”
Shiru sabeeha tayi na yan sakanni tana tuna maganganun da sukayi jiya, “yace mun wai yabarni ne kawai a gidan nan saboda wannan pregnancy din,kuma kamar…”
Kuri ammu ta mata da idanu tanason jin karahen maganar nata, saurin chanza zancen sabeeha tayi don maganar tayi mata nauyi, taya zata cema ammu ay yana jin haushij yanda akayi aka samu cikin?,kuma tana hango tsanar da yake mata don ta fuskanci yana ganin kamar tayi amfani dashi ne, ganin irin kallon da ammu ke mata yasa tace
“kuma kamar baiyi trusting dina ba,”
“Hmm fatima ay bazaiyi trusting dinki yanxu ba, hasalima haushinki zaiji yanxu saboda zaiga kamar kinyi taking advantage dinshi alokacin da hankalinshi baya tare dashi,namiji ne, ko wane namiji yana da ego, musamman irin shi da baka gane masu,”
Ammu na kaiwa nan sabeeha ta sauke kanta kasa, don ta lura ammu ta fuskanci komai,
“Zamanki tare dashi is not enough for him to trust you, koda kuwa ya tuna da yanda kuke a baya bazai taba treating dinki kamar yanda yayi a bayan ba,saboda yanxu kamar completely different person ne nasan you can see that, earning trust ta hanya mafi sauko shine idan so ya shiga tsakani, now listen to me, i want you to make him fall in love with you, ki nemi kusanci dashi, nasan bazai taba making any move ba, as far as he knows youre a complete stranger to him, ke macece you have all the qualities ajikin mace,most importantly Mijinki ne,”
Nunfasawa ammu tayi tana kallon fuskar sabeehar data marairaice kanta gaba daya ya kulle da maganar ammu, “fatima keba yarinya bace, kinsan menene aure, if i may ask you? Kina son shi?”
Sabeeha najin gabanta ya bada wani dam,sai kawai tayi saurin dauke idanunta daga kan ammu, tass ammu ta karanceta, tundaga fuskanta zuwa yarsunta dake ta faman karkarwa, murmushi kawai ammu tayi ta kauda tambayar “bakida matsala idan yanxu ya koreki daga kusa dake? Zaki iya barinshi da waennnan yan uwan nasa?”
Cikin hanzari sabeeha ta dago ta kalleta, idanunta sun ciciko, cikin hanzari ta girgiza ma ammu kai,ammi na ganin haka tayi saurin cewa “toh dole kiyi duk yanda zakiyi don ganin kin mallaki zuciyarshi, ki kama zuciyarshi ta yabda zai yarda dake dari bisa dari, ki jawo kusanci tsakaninku,“
“Amma ammu ni ban san ya ake ba?”
Murmusawa ammu tayi tana kallonta, koba a fada mata ba ta hango rashin sanin rayuwa a tattare da yarinyar,
“Karki damu kibar komai a hannuna kinji, yanxu abu na farko shine, a dan bunciken da nayi na lura bai yarda da abuncin gidannan ba,koda mun zauna a dining zakiga ba komai yakeci ba, bansan dalilinshi ba amma inason wannan ya zama damarmu na farko, duk safiya idan zai fita ki tabbatar kin tashi kin dafa mashi hot coffee latte yasha, idan baki iyaba ki shiga youtube zakiga videos din yanda akeyi”
Girgiza mata kai sabeeha tayi alamun gamsuwa, “kafin ya dawo be sure that you’re clean ki tsabtace ko’ina, maza irinshi suna da kyankyamin abubuwa,so yanxu you’re the center of the route, sannan few dishes din da kike mashi lokacin da bashida lafiya inason ki dunga yi ayanxu, koda kuwa bazaici ba karki fasa yi, wannan zai taimaka mashi wajen tuna wasu abubuwan, sannan inason ki kasance koda yaushe a kusa dashi, karya dawo ya shige bedroom ki dawo parlor sboda kina tsoron wani abun, bazai maki komai ba, musamman yanxu daya san akwai cikinsa a jikinki,dakinsa dakinki ne, stay there okay? Idan ya buqaci wani abun quickly step up and do it properly, duk wasu abubuwa da kike mashi a baya inason ki dunga yinsu ayanxu, and lastly nasan ba a Daki kike kwana ba ko?”
Shuru sabeeha tayi tana sauraronta saida ta tambayeta last questionta dago tace “anan nake kwana yanxu”
Daga yanda tayi magana ya tabbatarma da ammu amsar tambayarta bazai taje unti details ba, “shikenan anjima zamu fita”
Tana kaiwa nan ta miqe “sai anjima kinji, kinsha maganin nan kuwa yau?”
Girgiza mata kai sabeeha tayi alamun ah ah, “ki dinga sha kullum da safe da daddare”
“Tohm ammu”
Ammu na fita ta sauke ajiyar zuciya tayi tagumi tana tunanin maganganun ammu, anya zata iya kuwa? Bata da irin wannan courage din, amma dai idan har tana son zama tare dashi da samun yardarsa dole tayi abunda ammu tace saidai kalmar so data sako a cikin zancen tafi tsaya mata,ita da ba kowan kowa ba batajin she deserve him, yafi karfinta nesa ba kusa ba,zata wahalar da kanta ne don tasan wannan impossible ne, tambayr da ammu tayi mata ne tazo ranta,inda take tambayarta ko tana sonshi?, amsar data kasa bama kanta kenan balle harta bama ammu.
Hannunta ta kalla har zuwa lokacin chocolate dinnan na hannunta,tabbas itama ta lura da kaurace abuncin gidan da yake, but meysa? Why? Ko ya tuna da wani abun? Take ta tuna lokacin da suka bashi peanut yaci bayan sunsan hes allergic to it, idan ta tuna wannan ranta yana quna sosai,bata taba ganin azzalumai ba irinsu.
Tunawa da maganin da ammu tace tasha yasa ta miqe ta wuce bedroom ta dauko tasha sannan ta dawo sitting room ta zauna jigum.

Island….
Karasowarta wajen kenan, tana shugowa black yayi saurin tunkarar inda take, bayan ya gaisheta suka nufi cikin mansion din, wannan dakin dai suka nufa yauma, suna shiga ta tsaya daga bakin kofa tana fuskantar cikin dakin, dakin dai yana nan duhu babu wani hasken arziki don idan ba cikin dakin aka shiga bazaka san da mutun a ciki ba, sautin karar takalminta ne kawai ke tashi kwas kwas, tana karasowa tsakiyar dakin ta dakata hannunta na kan kirjinta tana mai fuskantar mutunmin dake zaune, “so finally ka farfado kenan”
Shuru babu response, wannan yasa ta gyara tsayuwarta tana fuskantar black ta mashi alamu da idanu kodai bai dawo hayyacinshi ba, saida ya girgiza mata kai ta dawo da dubanta ga mutumin tace “nasan kana jina, I’ve waited for so long,I’m running out of patience,”
“Meysa baki kasheni ba?”
Cikin hanzari ta dago tana fuskantar mutumin,
harzuwa lokacin ya juya mata baya bata hango fuskarshi,take ranta yayi mugun baci
“Saboda kinason sanin baqin sirrin mahaifiyarki data binne shekara da shekaru?”
Ya sake jefo mata tambaya, take idanun ya hade yayi jaa sosai, ranta yayi mugun baci sosai at that point, koda bai kalleta ba yasan yanayin data shiga don haka kawia ya kece da dariya, “rayuwarki gaba daya an gindayata cikin cin amana, bazan fada maki komai ba amma inason ki sani…bai kaiga karashewa ba kawai ya fara wani irin tari, cikin hanzari black ya kalli hidaya yace “madam,” ya mata nuni da hanyar futa, atare suka futo har zuwa lokacin idanunta yayi jaa sosai, duk abunda za a fada daya danganci mahaifiyarta ba karamin tayar mata da hankali yake ba, taba qaunar mahaifiyarta,zata iya yin komai akan mahaifiyarta, saidai maganganunsa sun gama tasiri a zuciyarta wannan yasa ta kasa bari ya mutu,inba don haka ba da tuni labarinsa ya gama yawo, “call the doctor”
Tana fadin haka ta bar mansion din ta wuce wajen motarta.
Tunda suka shigo jirgi take nanata maganar nan a ranta, har suka iso ta shige motarta tabar wajen.

Dagowa yayi ahankali, facing cap din dake fuskarshi ya gyara zamanta, saurayi ne zaune akan kujerun shakatawa yana kallon jiragen dage wucewa akan ocean din, fuskanshi duk gashi kasimba, akan idnaunshi ta fito daga jirginta ta shige motarta, dukda yana daga zaune daga nesa hakan baisa ya hangota ba dakyau, yana nan zaune wani yazo ya zauna agabanshi,dagowa yayi ya kalli wanda yazo ya zauna din,duban gefensu sukayi ganin babu mutane sosai a wajen yasashi saurin cewa, “the money”
Cikin hanzari mai kasumbar ya zaro wata envelop cike da kudi a ciki ya miqa mashi, yana karba shima ya zura hannunshi cikin aljihunsa ya zaro wata envelop din daga ciki ya miqa mashi, yanda sukeyi musanyar envelop dib zaka dauka abokaine suke gaisawa, yana karba ya mike yabar

16 / 107