Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Romance

Chapter   18 / 107

51K to 54K   out of 320.4K words

mashi, “she just saved me”
Abundaa keta faman yawo a zuciyarshi kenan, take memory din lokacin dayaci peanut a dining ya fado mashi,abun kamar an bude mashi faifai lokacin haka yake gani, fuskarta na mashi flashing lokacin da take kuka, he was struggling sosai nunfashinsa na fira kyar, abunda yafi daure mashi kai kuwa yanda yafa kusan kowa na zaune a dining din lokacin da abun ya faru, kuma sabeehar ce da kanta ta saka mashi peanut din, lokaci guda ya shiga confusion again, maganganun da akayi a lokacin duk sun dishashe mashi, dukda yaga itace ta shafa peanut din a cikin bread din da yaci hakan baisa zuciyarshi ta aminta da cikin rashin sani tayi hakan ba, don he can clearly see yanda take faman kuka, sautin kukan ta alokacin yana echoeing akanshi, yayi zurfi sosai cikin tunanin nashi baima ji maganar data fara yi mashi ba saida ta sake cewa, “didi!!!!”
Yaune second time dayaji ta kirashi da wannan sunan tun bayan a asibiti, saurin rintse idanunshi yayi ya budesu ahankali ya maida dubanshi gareta yace “what are you exactly?, why re you confusing me?”
Calmly yayi maganar kamar bashi bane ya gama daga mata murya dazu, saurin dagowa tayi ta kalleshi cikin idanunshi da sukayi jaa, jijiyoyin kanshi zun fito rudu rudu,kwata kwata babu walwala a tattare dashi,koba a fada mashi ba tasan akwai abunda ke damunshi kuma its eating him up,
Miqewa yayi tsaye ya wuce bathroom kawai, tana ganin haka ta wuce ta dauka hijab dinta sannan ta fuce daga dakin ta sauka kasa wajen ammu.
Atare suka futo ita da ammu zuwa compound din gidan, daya daga cikin motocin gidan ammu ta dauka suka fuce daga gidan sabeeha na daga zaune a gaba.
Hira suka dunga yi sosai ita da ammu, yawanci ammu ce ma ke janta da magana, saidai ta amsa ta da uhm ko uh uh, tunanin takeyi tunda suka fito har suka isa insa zasuje.
Gaban drgon mall suka tsaya, ammu na parking suka fito atare, yau ce rana ta farko data futo ita kadai ba tare dashi ba yawanci duk fitar da zasuyi itada taj dinne sai jamid, tunda suka fito take bin wajen da kallo,wajen ya burgeta sosai daga waje ma kenan ba a shiga daga ciki ba.
“Muje ko fatima”
Girgiza mata kai sabeeha tayi sannan suka shige daga ciki, sayyayya sosai ammu tayi mata kamar babu gobe, itadai sabeeha binta kawai take da idanu don batasan ita akema sayyayar ba, wato ammu ma wata rich anty ce, tana da nata kudin sosai, ga inheritance din mijinta data samu donma ba a gama settle kudadenshu ba don shima attajirine haka ta dawo saudi ana kan wannan gabar bayan rasuwarshi.
Daga kan mayukan zamani na jiki zuwa ga na gyaran kai da personal hygiene babu wanda bata saya mata ba, harda wasu arnayen nighties masu shegen daukar hankali da kyau ta kwaso mata, da turarruka masu kamshi sosai, sun dade sosai a wajen kafin su fito su shiga shagunan da ake saida sutura masu kyan gaske na larabawa, yawanci dogayen riguna ne haka ta sayo mata masu kyau, don ta lura kamar bata da wani kayan arziki sosai, sun dade sosai a wajen sabeeha na biye da ita kamar akala,batayi yunkurin daukar komai ba haka zalika ammu batayi forcing dinta ba don ta lura sabeehar akwai kawaici, kuma tana jin nauyinta wannan yasa ta yanke zatayi mata komai kawai dan dole ta cire kunyar da tsoron da sabeeha ke mashi, ita yanxu burinta bai wuce cikin ya tabbata da gaske ba, ta yanda zasu kamashi da kyau, shiyasa takeson su kasance tare.
Daga nan suka wuce spa akayi masu pedicure da manicure sannan aka gyara ma sabeehar gashi, ammu tayi mamaki ganin irin yawan gashin yarinyar sosai, badan tasan yar africa bace zata rantse iyayen ruwa biyu ne, ko ta hada jini da larabawa, sai a lokacin ne ma take ganin yanayin halittar yarinyar, kamar halfcast take, kuma tana da haske sosai wanda baiji mai me tsada ba da zai fidda kyauwun shi,batama san lokacin data furta “masha allah ba” tana kallon yanda ake warware gashin sabeehar data nannadeshi kamar ta nade kaya, wani irin dauri ta mashi sosai saboda karya kwance, masu gyaran na kwance gashi take ya sauko gaba dayanshi har bayanta masha Allah, silky and oily, shima sai baiji gyara bane a haka.

Ammu na daga zaune aka gyarata tsaf, sabeeha sai kallon ikon allah kawai takeyi, yauce rana ta farko data taba samu wannan special gurly treatment din, ba a taba mata irin wannan gatan ba, bata taba benefiting irin wannan jin dadi ba, she feels so soecial ayanxu taci albarkacin wasu, ada saidai taga anayima wasu bata taba tunanin itama za a mata ba saboda talaucin da suka taso cikinshi, bayan wannan ma ta isa ta samu irin wannan gatan? Take tunanin mahaifiyarta ya fado mata da irin rayiwar da sukayi a baya.

Tunda ta doka tagumi take tunani batamasan an gama mata ba saida ta dago ta kalli fuskarta daketa sheqi anyi mata kitso weaving guda hudu saboda santsin gashinta yasa akayi hudun sannan aka nade jelar aka kitse yanda bazai dameta ba, ana hango yellowish fatar kanta data haska baqin gashin bata sosai, ada tana ganin gashi yana wani brown brown yanxu da aka gyara saita ganshi baki siddin, ko wadda ta gyara mata saida ta kalleta ta sake kallonta, muryar ammu sa sukaji ne yasa ta dago ta kalleta “masha allah abnati”
Murmushi sabeeha tayi mata, ita kanta ba karamin dadi taji ba ganin ta sauya gaba daya kamar ba itace ba.
Sallamarsu ammu tayi suka fito zuwa mota suka zauna, suna zama sabeeha ta dago ta kalli ammu tace “jazakallahu khair ammu, nagode..”
Saurin tarar nunfashinta ammu tayi tace “karki godemin kinji, ina fata da rokon zakiyi amfani da wannan damar da kika samu yanda ya kamata fatima,”
Girgiza mata kai sabeeha tayi kafin subar wajen, wani wajen suka kara nufa lokacin har dare ya somayi don garin ya soma yin duhu, tunda ta juya wajen window babu abunda take sai appreciating view din garin, Allah mai yanda yaso, ya kaika inda allah bai taba kaika ba, bata taba tunanin kaddararta zato zo wata kasar ba daban, kasa mai tsarki kamar wannan, kuma yanxu da auren wani akanta.
“Yayi kyau ko?”
Ammu ta katse mata tunaninta, “eh akwai kyau sosai ammu”
“Danma bakiga makka ba, you’ll love it more there, chan yafi nan jedda kyau”
Cikin hanzari sabeeha ta dago ta kalleta tace,”makka makka dai?”
“Eh,insha Allah wata rana zamuje muyi umra idan komai ya lafa…. insha Allah”
Cikin jin dadi sabeeha ta girgiza mata kai, take taji wata ni’ima ta saukar mata, wayaganta yau a makka, allahu akbar.

Tunda ammu tayi parking ta futa ta barta cikin motar bata bar yin murmushi ba, haka kawai taji zuciyarta tayi mata sakayau.
Cikin swiss arabia ammu ta shiga cikin yan mintuna kafin ta futo, tana futowa ta shiga motar ta ajiye jakar data futo da ita a baya sannan ta kunna motar sukabar wajen.
Hanayr gida suka nufa, cikin mintuna qalilan suka iso, ammu na yin parking ta dubi sabeehar tace “idan ya tambayeki ina kikaje kice mashi munje asibiti, nasan da wuya ma ya tambaya”

“Tohm ammu”
“Wannan sayyyar duk takice fatima, duk abunda muka sayo na ki tabbatar kinyi amfani dasu kinji,…karki gode min, kiyi abunda kawai ya dace okay?”
Sauke kai sabeeha tayi muryarta chan kasa tace “insha aallah ammu”
Wannan jakar ammu ta dauko wadda ta shigo da ita daga swiss arabia, ta miqa mata, “tauraruka ne masu kyau, ki dunga amfani dasu idan zaki kwanta”
Girgiza mata kai tayi suka fito daga cikin motar inda ammu ta taimaka mata da wasu few kayayyakin suka shiga cikin gidan daidai nan motar hidaya Ta kunno kai, tundaga bakin gate ta hangosu har suka shige cikin gidan.
Tana parking ta janyo wayarta takai kunenta, ana daga wayar ta soma magana,ta dade sosai tana wayar kafin ta ajiye wayar.

Har sama ammu ta rakata suka ajiye kayan a sitting room kafin ta mata sallama ta sauka kasa, ita kuma ta shige daga ciki.
Sallama tayi ta shugo, idanunta ya sauka akanshi, yana zaune ya saka wani fari glass akan idanunshi ga hasken system din dake gabanshu gabanshi yayi relaxing bayanshi yana sanye da fararen kaya.
Chan kasa kasa ya amsa sallamar tata yanda ba lallai taji ba.
Sadaf safaf ta wuce wajen closet don ajiye jakukunnan da ammu ta bata, wajen kayanta ta nufa ta ajiye kayan data saya mata a ciki, sai a lokacin ta lura da kayan barci data kwaso mata da inner wears masu kyan gaske da daukar hankali, bata bubude su ba saboda a gajiye take don haka ta ajiye jakkunan kawai a wajen da kayanta suke sannan ta ajiye turarukan data bata,
futowa ta sakeyi zuwa sitting room ta kwaso sauran sannan ta dawo dakin, duk wannan shige da fucen da takeyi zaka rantse bai sanma anyi ruwanta a wajen ba nan kuwa yana kallonta ta w idanu,inda taje ba damuwarsa bane don haka ya kauda kanshi ma kawai.
Sabulan da ammu ta saya mata ta kai bathroom wajen inda nashi suke ta ajiye a gefen, sauran abubun personal hygiene dinta kuma ta ajiyesu cikin cupboard din mirorr dake bathroom din suma ta jerasu kafin ta fito, tunawa da sallolin dabata samu tayi ba yasa tayi wanka gaba daya ta dauro alwala ta futo.
Misalin wajen karfe goma ya kashe laptop din dake gabanshi ya ajiye gefe sannan ya tashi ya wuce bathroom, tundaga array row din dake connecting tsakanin bathroom da closet ya soma jin wani irin kamshi mai dadin gaske wadda yayi capturing sensing dinshi lokaci guda, kallon closet room din yayi yasan tana ciki don tunda ta shiga wajen bata futo ba, kauda kanshi yayi ya nufi bathroom din. Sabeeh dake dakin kaya tana jin karar kofa ta tabbatar ya shiga bathroom wannan ya bata damar saurin ajiye turarukan da ammu ta bata ta fito da kayan barcinta ta shimfida su sannan tayi kwanciyarta ta jawo hijab dinta.
Fitowarshi kenan saga bathroom ya nufi cikin daki, daga nesa ya hango ta kwance a kasa,shuru ya danyi yana wasu nazari, ya zaiyi ya hanata kwanciyar kasa? Which ya gani is not good for a pregnant woman saboda sanyi zai iya shigarta, ya dade sosai yana wannan nazari baima san ya shagala da yi ba, sai daga baya kawai yayi kwafa ya nufi kan gadonsa ta chan daya sakon yayi kwanciyarsa bayaj ya kashe lights din dakin gaba daya ya rage na bedside kawai, tunda ya kwanta yakejin wannan kamshin na mashi ziyara daga inda yake kwance wanda ya fara damunshi sosai.
Haka ya dunga juyi kan gado barcin ma gaba daya ya kaurace mashi, sabeeha tunda ya futo taji motsinshi tayi saurin rufe idanunta,tasan ba magana zai mata ba.
Zumbur ta miqe zaune ta fara gulping saboda aman dataji yana taso mata sanadiyar kamshin turaren daya shigeta itama sosai, dazu kafin tasha maganin nan ba karamin dadi yayi mata ba harta goga duka jikinta yanxu kuma sai takeji ya hau kanta sosai.
Take ta fara neman kwaranyo amai har sautin na fita sosai daga dakin, cikin hanzari ta miqe take, taj dake kwance yanajin yanda ta fara gulping dinnan yayi saurin bude idanunshi,
Tundaga bathroom din yakejin saukar aman da takeyi, ta dade tanayi sosai,

miqewa yayi zaune ganin abun yaqi ci yaqi cinyewa, chan kuka yaji shuru ta daina kakarin, karar faduwar dayaji ya biyo baya ne yasa yayi, ya maida dubanshi ga kofar kamar wani mai yin nazari chan kuma yayi saurin saukowa daga gadon cikin azama ya nufi hanyar bathroom din hankali a tashe,cikin saurin ya bude bathroom din chan ya hangota zaune kasan tiles ta jigata sosai, ga kafarta data malqwaye gefe da alamu ta miqe ne ta fadi, ganinta zaune yasa ya sauke ahiyar zuciya ya tunkari inda take hannunshi na cikin aljihun wandosa yaba fuskantarta ya soma magana kamar wanda aka saka dole, “are you okay?”
Ahankali ta dago da fuskarta ta dubeshi da shanyayyun idanunta da yayi jaa sosai,ganin shi dinne ba kunenta ke mata gizo ba yasa tayi saurin gyara zamanta “eh” tana fadin haka ta fara kokarin miqewa, kafarta tasha jini tana zugi wannan yasa ta koma tana mai kama yar karamar farar kafarta da babu gashi ko kadan tace “washh!!!”
Yana ganin haka ya gane yanayin da take ciki, ba zato ba tsammani ta ganshi a gabanta a tsaye dagowar da tayi yayi daidai da miqo mata hannunshi da yayi, bin huge hannun nashi tayi da kallo, tana kallon yanda fatar tafin hannun tayi jajaja, kwata kwata bata gane helping hand yake bata ba saita zama so confuse,ganin kamar bata gane me yake nufi ba yasashi cewa “hold up and get up”
Tana jin haka tayi saurin kallon hannun nashi, ta kasa motsawa tsabar mamaki, dakyar ta iya daga hannunta daketa faman zufa ta dora akan nashi, ya kama dan karamin hannun nata ya riqe yana mai jin dumin hannunta ya taimaka mata ta miqe tsaye,tana miqewa zugin ya kara jaa wanda ya sata neman dukawa yayi saurin tallabo arms dinta muryarshi chan kasa kasa kamar mai rowar magana baimasan lokacin dayace “sorry ba”
Ita ko kunnenta kasa gasgata abunda taji takeyi, abun mamaki yake bata sosai, meysa hes being nice to her yanxu kuma?bayan magnganun daya fada mata da safe?.
Da taimakonsa suka dawo bedroom din a lokacin kafarta ta rage zugin don haka tayi saurin zame hannunta dake cikin nashi don tunda ya rike mata hannun takejin wani irin “thank you im okay now”
Taba fadin haka tayi kwanciyarta, taja hijab dinta ta rufe jikinta.
Yana kallo tayi barcinta, yanda take wannan aman ya kara convincing dinshi tabbas da cikin shi a jikinta, daman yau gaba daya wuni yayi yana researching akan pregnancy, babu abunda bai dubo ba, kuma alamun sa daya gabi a tattare da ita ya tabbatar mashi da sickness din daya gani a research din da yayi, yanxu dolenshi yayi supporting dinta in some ways, da kyar yakejin zai iya kauda grudges din da yake dashi akan ta yayi focusing akan abunda ke cikinta which happens to his mold of blood, har yanxu baibar jin tsanar abunda tayi mashi ba for taking advantage of him, amma yanxu dole ya kauda wannan kodan abunda ke tattare da ita.

Dakyar ya samu bar ci ya dauke shi da wannan tunanjn aranshi.
*****
Misalin wajen karfe biyu tareeq ya bude idanunshi, hannunshi ya sanya wajen da take kwanciya a gefe yaji wayam, miqewa yayi zaune ya kunna bedside lamb gake haske ya bade ko’ina, kallon gefwn gadon yayi ya tabbatar bata nan, miqewa yayi ya nufi bathroom ya danyi knocking ko zaiji motsinta, nanma yaji shuru, tunawa da mood din datake cikin kwanakin nan yasa yayi tunani ko lafiya, bai kawo komai a ranshi ba don haka ya shiga bathroom cikin yan mintina kasan ya fito, yana futowa ya fuce daga bedroom dinsu ya nufi nata, yana karasowa daidai bakin kofar harya saka hannu zai bude kofar ya jiyota daga cikin dakin, “don’t fucking tell me to calm down, how can i calm down?”
Dake wayar a speaker ne ya bashi damar jin wanda take wayar dashi kuma namiji ne dukda bayaji sosai yanda ya kamata, “baby you need to be calming, karkiyi messing up what we have worked for over the years”
“No…i want her out, zan iya yin komai, i can’t afford to see anyone around him”
Sai kawai ta fashe da kuka, take wanda ke cikin wayar ya soma lallabata, “ki daina kukan shikenan we’ill come up with a plan, we have to be very careful saboda we are at the edge of ending this game,don’t do anything stupid da zaisa ya gano komai, tunda yasan ke kika fada mashi maganar accident din, you need to be meticulous”
Ita ba wannan take son ji ba don haka tayi saurin kashe wayar ma gaba daya ta jefata gefwn gado take ta tarwatse gaba daya, wani irin huci takeyi mai zafi sosai rai a bace, ta furta “khaal!!!! Khaal!!”
Wanna ce kalma ta karshe data furta daya ji kafin yayi saurin barin wajen ya koma bedroom dinsu, kanshi gaba daya ya kulle da wannan almari, “da wa take waya? Koma wanene it has to be someone close to her, kuma daga yanayin yanda mutumin ke mata magana ya tabbatar mashi da saurayinta ne, she’s with someone kenan? Sannan wata fadama maganar accident? Wani accident din?taj!!!! Abunda yazo ranshi kenan, idan har kanshi yayi wrapoing din komai yanda yayi hasashe tasan da plan din accident din da taj yayi kenan? Tunawa da wannan recording din dayayi na maganar accident din da mutabblib yayi da sabeeha yayi, kamar wani karamin mahaukaci haka ya dunga saka yana warwarewa dan dole yakeso ya gano komai saidai ba duka tambayoyinsa ya samu amsarsu ba, karar koda dayaji yasashi saurin kwanciya ya rufo kofa, itace ta shugo dakin, ko kallon inda tareeq din yake batayi ba ta kwanta cikin bacin rai.

Asuba nayi sabeeha ta farka da matsanancin ciwon mara, cikin hanzari ta miqe ta shige bathroom allah yaso bai farka ba, a gaggauce tayi wanka ta gyara jikinta sannan tayi brush ta fito ta wuce closet ta sauya kaya marasa nauyi sannan ta maida hijab dinta ta dawo dakin, kayan barcinta ta tattara ta ninkeau har zuwa lokacin barcinsa yake hankali kwance barcinma yayi nisa sosai saboda bai samu ya tufe idanunshi ba saboda tunanin daya kwashe rabin daren yana yi.
Tundata fito take kallon fuskanshi, yana facing celying ya jango duvet ya rike, saita shagala da kallonsa, ganin lokacin sallah na neman kurewa yasa ta soma tashinsa ahankali, “didi didi”
Muryarta ya soma ji ahanakli kafin kamshin nan na jiya ya soma shiga hancinsa, Ahankali ya soma bude idanunshi harya sauke akanta, cikin sauri tayi baya “lokacin sallah yayi”
Tana fadin haka ta juya ta fuce daga bedroom din ya rakata da idanu, yana mai tuna yanda take tashinsa lokacin da baya cikin hayyacinsa, miqewa yayi ya shiga bathroom din ya dauro alwala sannan ya futo ya tada kabbarar sallah, ya dade sosai yana azkar a zaune.
Chan parlor sabeeha gyara ta tsiri yi da safiyar allahn nan, daman alreday ta saba da wannan lokacin datake aiki a gidan, tun 5 suke tashi a gidan so wannan ba abune mai wuya a wajenta

18 / 107