Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   9 / 29

24K to 27K   out of 85.7K words

Garin Gwamna, sai da Jawad ya biya dasu Mr Biggs sukayi take away, ya kuna tsaya a One Eleven ya siyo musu Kaza da Masa kafin yayi Unguwar rimi Lowcost dadi inda Tsoho ya ba Jawad Gida me dan karen kyau. A gajiye suka shiga gidan, gidan yayi kyau matuqa. Nan suka zauna a parlo suka huta.
Samir ya kira Jawad yace yadai kun isa? Yace shigowar mu kenan, shima Samir din yace mu ma ynz muka shigo bauchi, Allah huta gajia sukayi bankwana…
WasheGari
Ya Suraj ya kai su Yaya Raffiyya Airport don yau zasu wuce Maiduguri bayan su mai nasiha sosai,haka ma Samir ya kaisu Aunties dinsu Airport, Jawad ma ya yankan musu Tickets din komawa Maiduguri…
Maiduguri
Haka ma aka kawo Yazayyad da Hanifa Airport su biyu rak bayan ta sha kuka sosai, suna zaune suna jiran jirginsu da zai tashi zuwa lagos. Shi ko Zaid ya kwashi Aunty Nuratu da Aunty Zainab da Maysah a mota suka bar gidan bayan Tsoho ya kebe da Rumarsa ya qara jaddada mata, sun kusa wajen Garih ne ya latso wayarsa ji kawai sukayi yace Na kusa dags bisani kuma suka ji ya gangara bakin titi ya parker, ba wanda ya tanka mishi, ta gilashin mota ya hangota, ya kalli Maman Samir da ke zaune gaban mota yace Aunty Zee dan koma baya, mun qara samun pasinja, tace pasinja kuma? Be tanka ta ba ya bude murfin kofa duk suka bishi da ido gurin wata suka ga ya nufa, Ta sha Ado sosai ta na janye da Akwatin Trolley, Gaban Maysah ya buga sakamakon wacce ta gani ba kowa vace illah wannan da suka ga ta na bacci kan Gadon Yazayd, wacce sukayii fada da Amira, toh wacece wannan?to ba kowa bace illa Baddiyan Shagali, Da sauri Maysah ta fara maimaita inalillahi da ita zaa Abuja? bude booth yayi ya tura Akwatin Diyyan Shagali, kafin ta zo ta bude gidan Gaba ta fada tana me karya jiki da feleqe ta juya baya ta bi su da kallo daya bayan daya ta watsar, bata da niyyan tankasu, duk irin tsageranci na Zaid sai yaji be ji dadin hakan da tayi ba, a hankali yace Dear, My Aunties, ta dan juya tare ds yin kicinkicin da fuska tace Ina kwananku? Aunty Nuratu ta kasa haquri dai tace Zaidu wai Wacece wannan????

_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
22. Gidan Ganduby Biebee IsaZaid ya danyi gajeran tsaki yace Aunty sunanta Badiyya, Aunty Nuratu ta yi shiru da bakinta haka suka dauki hanyan Abuja, Gudu suke ta shatatawa, sun tsaya sun ci abinci a kano kafin suka dauki hanya kuma.

Lemmie help u wit ur seatbelt, ta galla mai harara tace i dont need ur Help, Zayyad ya yi murmushi ya saka nashi belt din, Jirginsu ya fara tafia Matuqar tsoro ta tsorata, ba yau ta fara hawan jirgi ba amma ta tsorata da tashin Jirgin yau, bata san tym din da tayi saurin dafa YaZayyad ba da jirgin ke niyyan tashi tare da rintsa ido, Zayyad yayi murmushi yace Ashe yarinyan na da tsoro, da sauri ta janye hannunta daga nasa ta galla mai harara, be tankata ba, illa ya ciro Chalbin shi a aljihu ya fara Ja. Haka suka daidaitu a sama suna tafia har bacci dai sai da tayi a kafadun YaZayyad ba tare da saninta ba, Cikin Awa daya da yan mintuna suka iso LAGOS, hanifa ta gaji sosai, Cab ya tsaida musu suka hau, har gidansa da ke wani unguwan da sai na tambayo sunansaGida ne self contained, ya biya me tazi din ya kwashi kayan shi da nata ita ko handbag ta dauka, Nidai nace Waiyo Allah Zayyad Bawan Allah, be dau abun da Zafih ba, idan ta qi bada kai ka zane ta kawai

Zayyad Hussaini Zailani Matashi ne dan kimanin Shekaru 29, yaro ne kyakyawa wanda be da matsala ko kadan, hak’urin shi ya wuce misali, Yana aiki ne a Birnin Lagos A wani Companyn Oil And Gas. Rokonsa daya Allah ya bashi Zaman lafia da wannan er Zafin kai ni dai nace Amin.

Sai dare suka iso Abuja, Straight sai da yaje Garki ya ajiye Diyya yace mata sai yazo, kafin ya dauki hanyar Gidan da Tsoho ya mallaka mai dake Maitama, Gida ne na ‘yan mala’u masu brush da cinyen kaza, gidan ya tsaru iya tsaruwa, Su Aunty nuratu suka shige dakih da huta gajia.
Zaid Mudassir Zailani tsaran Zayyad ne amma Zayyad ya bashi kwana 14, ya na da kwalin degree na likitanci, A gobe ne zai fara HouseManship a National Hospital Abuja, Zaid be da wata matsaala in banda ta shaye shaye da kuma tsageranci, Toh gashi an hadashi da Salihar Mace, toh ko ya tafian nan zaiyuwu?🤔

Ko da Jawad ya kai su Aunty Abida Airport bayan tashin su straight Office dinsu ya nufa, Jawad Mudassir Zailani Matashi me ji da kanshi dan kimanin shekaru 27 ya karanta Industrial Chemistry, ynz haka yana Aiki a NNPC kuma tauraruwarsa na haskawa don yana da himma da qwazo, Jawad na da zafih be son raini kwata kwata, gashi an hada shi da Macen da ba a tabata ta kyale duk girman mutun. Toh ku biyoni dai muje.

Samir kuwa tunda ya kaisu Aunty, ya tafianshi Office, Samir dan kimanin shekara 27 ya karanta Engineering, samir na da sanyin zucia, be da matsala, Samir Injiniya ne wanda ake damawa dashi a garin bauchi, Matashi ne ko shekara daya be rufa da fara aiki a Bauchi ba, Amma ko ina damawa ake dashi, balle gwamnati da ke bashi kwangiloli, Samir Gambo Zailani kenan Matashi me ji da kudi, Young Billionaire. Toh ya zaman shi zai kasance da Psychic lilsismeeranshi?🤔

Hmmm Mu’ammar Labaran Zailani, Matashi me shekaru 28 a dunia, Ya hadu iya haduwa, Shima dai Injiya ne amma na jirgi, wanda ake kira da Air Police Engineers, Mu’ammar na aiki ne a nan Air force Aviation da ke Zaria, Mu’ammar dan zafin kai ne, Shi ya sa abu a gaba to sai ya cimmai, in ko ba haka ba ya shiga damuwa, Tunda ya iso Zaria ya bar Yar baiwar Allah ita kadai ciki, ita kadai ta kwana, ya tare gidan wani Abokinsa Ahmad, don shi gani yake ba zai iya kwana gida daya da Islahulkhair ba, don ya na mata tsana me zafih, toh su Amar ga shawara idan zaka k’i mutum ka k’i shi saisa saisa don ba a san wanda gari zai waya ba.

Suraj Umar Zailani dan shekara 27 a dunia, Matashi ne dogo kyakyawan gaske, ya Karanta Architecture, Yana aiki ne a nan kano mostly Gwamnatin kwankwaso ta tsaya mai wuri zanen Tituna masallatai, makarantu d.s, Suraj ya qware ta fannin zaneh, ko mutum zai zana shi tsaf, Suraj na da kirki yana da haquri amma abu kadan ke bata mai rai baya son raini ko kadan, Arch. Suraj kenan Angon Bilkisu er baba labaran.

Da Daddare
9:30pm;; Samir ne ya paka motarsa ya fito, da take away a leda ya yi hanyar parlonsa, zaune take gaban kofar parlorn, gashi dare ya farayi, kawai ganinta yayi zaune, sai da ta bashi tsoro, ita kuwa tana ganinshi ta miqe da sauri, Ta nufo shi ds niyyar rungumsshi, Ya gimtse fuska tare da matsawa baya, Bigbrosamir, tunda safe ka bar gidan nan, ina ta kiran ka ka qi dauka qarshe ma ka kashe wayanka, ina taji tsoro nikadai a gida, be tankata ba ya raba ya bude kofa ya shiga ciki, ledar take away din hannunsa ya ajiye kan dinning, ya shigewar sa dakih donyin wanka. Zuwa tayi ta bude ledar taga kazah ce da Fresh Yoghurt, ta nufa kicin ta dauko plate tayi dakin samir dashi, tym din ya fito wanka ya na tsane kansa da dan qara min hand towel, dagowan da zaiyi ya ganta tsaye, dan guntun tsaki ya sake, tace bigbrosamir ga abinci kazo muci, kamar ba zai tankata ba yace ni na koshi, wannan nakine, Tace Allah ko? Toh nagode, ta zauna kan kujera kamar zai yi ihu don takaici, ya daure dai yace Amira i want to dress up, ba tare da ta kalleshi ba tace go ahead mana, m ur wife ryt? Ganin idan ya biye mata ranshi zai baci ya zira jallabiyanshi ya koma toilet, ta gama cin kazarta ta sha yoghurt ta kai plate kichin, ta shiva dayan dakin ta yi wanka tare da sa nughtgown, ta koma dakin Samir, har ya kashe wutan Dakin ya kwanta yana latsa waya, Gadon ta haye, da sauri ya miqe tare da kunna side lamp, ya daure fuska, ke Amira Lafia?? Tace menene bacci zanyi, Yace ki fita mana ki koma dayan dakin, tace jar uba, ni kadai ral cikin dakih, to ba zan iya ba, ka fita ka barni ni kadai na haqura ynz u expect me to sleep all alone? Hell No, wlh nan zan kwanta, samir kamar zaiyi hauka don takaici, a hankali yace Amira pls ki fita, tace lallai bari ma ka gani, ta gyara kwanciyarta kan gado, Cikin daga Murya yace Amiraaaa ta dago sosai dan taji muryan sa kamar me shirin yin kuka, yace please leave, tace nifa na gaya ma i aint going anywhere, ya miqe ya dauki pillow yace Please Amira dont make me hate you..
Like · 1 · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
23.Gidan Gandu by Biebee Isa
Mamaki ya rufe Amira, Toh me yayi zafih haka? Ya samir me na maka haka har kana kira min kalmar Tsana? Be tankata ba ya dauki pillow ya bar dakin parlo ya nufa ya kwanta kan doguwar kujera, Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba, a rayuwarta yau ne a ka taba mata abu ba tare da ta rama ba, yau ne aka mata abu ta tsaya tana kuka ba tare da daukar mataki ba, in banda Yasamir wa ya isa ya takata haka? Waiyo Allahnta, ya zatayi? Ga wani son samir da ya shigeta farat daya, haka ta dinga rubzar kuka har bacci yayi awon ga ba da ita.

Kaduna
Ko da Jawas ya iso gidan karfe 10 da wani abu, xaune ya iske hakimar wato Fadila a parlor ta na kallon Series din nan na “Married Again ” Dakinsa ya wuce straight ita kuwa bayan sallamar da ta amsa mai ko kallonshi ba tayi ba. Ta cigaba da kallonta tana kada k’afa daga bisani ta miqe tayi kicin don dafa indomie. kichin din shaqe yake da kayan Abinci ko mi akwai don Tsoho sai da ya cika su da komai na abinci kama daga kayan miya, nama, kaxa, kifi, kai harma da tolotolo

Lagos
Shigowar sa kenan Gidan ya nufa dakih, ka sancewar gidan 1bed room ne amma dakin me girma ne, kwance take kan gado tana hawaye, ya cire bakih ya kirata yace Hanifa, hanifa, banza tayi dashi kamar bata san yanayi ba, da yaga ba zata kulashi ba ya shigewarsa toilet din dakin, ya yayi wankansa ya dauro Alwala yayi shafa’i da wutr, yazo ya chanza kaya zuwa na bacci, ya hau gadon ya kwanta, kukan ta takeyi ba ta fasa ba, Shi filazal baya son kukan mace, ya daure dai ya ce Hanifa donAllah kiyi shiru, bana son kukan nan naki, ko me yayi zafih maganinshi Allah, kiyi haquri mana, cikin tsiwa ta miqe tace kai mallam saurara min, ina ruwan ka da kuka na? In kaji zafih ka sakeni, yayi murmushi yace banji zafih ba Allah ya baki haquri, have a Sound sleep, yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, takaici ya sa ta saki wani kukan da qarfi, shi ko yayi saurin runtse idanuwansa, da yaga taqi shiru pillow ya dauko ya fita sitroom, tsoro ya mamayeta kamar tace ya dawo, Amma taurin kai da irin zuciyar Hanifa ya sa ba ta nuna komi ba, amma harga Allah tana tsoron kwana dakin nan ita kadai, haka ta kwanta rabin ido daya a rufe rabi a bude (lol)

Zaria
Taci kuka har ta qoshi, tayi sallah ba adadi, a tsoroce take, tun jiya rabon da taga Mu’ammar, haka ta kwana cikin tamfatsetsen gidan nan ita kadai, hankalinta ya gama tashi, da qyar ta dafa Taliya tacih, ta kira Wayan Maysah a kashe, ta kira fadila ta ci saan wayar ta kunne yake, amma ba a dauka ba, kasancewar wayar na chan dakin ita kuma fadilar tana parlor tana kallo, wani kukan ya subuce mata, gashi ba ta san kiran Umminta don kar hankalinta ya tashi, Dare kuma Ya Tsala, haka Islahulkhair ta kwana tana kuka, da ta ga kanta na neman Bugawa sai ta dauko Alkurani mai girma ta shiga karatu. Shi ko Mu’ammar na nan Gidan Abokinsa Ahmad, ya ma manta da yana da wata mata a Gida.

Kano
Ya shigo da sallama ta na jinsa amma tayi biris dashi, ya qara doka sallama tayi banza dashi, qarshe ta hau karkada kafarta, da qarfih yace keee bilkisu, ba ki jin ana sallama ne? Ko ba ki iya amsawa ba? Cikin tsiwa ta kalleshi ta haraeshi, tace naji kana sallama, na iya amsawa, ban dai ga damar amsaka bane, fuuu ta wuce dakinta, zuciyarsa tayi k’una, har ya bita dakin don ya lakada mata na jaki, sai zuciyarsa ta haneshi, ya danne zuciyarsa, yayi kwafa. Ita kuwa tana shiga dakin ta dinga murna ta bakanta ma Suraj, haka ta dinga kullah yanda zata dinga chuzguna mai har sai ya saketa kafin Hajia babba tayi na ta aikin.

Abuja
Da Safe, Ya kaisu Aunty Nuratu Airport, bayan sun dade kan Maysah suna mata nasiha don sun lura da take taken zaid, tasha kukanta, haka suka rabu, sai da yaga tashinsu kafin ya wuce National Hospital, yaje yayi reporting dama suna expecting dinshi, aka bashi office da tag dinsa a rubuce an sa Dr. Z.M Zailani Nan take ya fara ganin patients cikin kwarewa, yanda kasan bature haka yake tafiar da Alamuransa. Har misalin karfe hudu, ya tattara yana sa yanasa yayi signing out ya tafiarsa. Hotel din da ya sauke Badiyya ya nufa, ya kirata a waya, ringing daya biyu ta dauka, yace gani na iso,sauko qasa, a yangance tace ba ni kadai ce ba fa, yayi jim chan yace ke da waye? Tace ni da mamana, shirun ya qarayi chan kuma yace yaushe tazo? Tace yau din nan, to ku fito muyi ta tafia, bayan mintina 12 sai gashi sun sauko, ta side mirror ya hangosu, ko wannensu dauke da akwati trolley, maman baddiyya ta qi amincewa ta tsufa, irin shegun matsatsun kayan nan ke jikinta, fuskan nan tasha coiling ga gashin doki a kai, wannan shine like mother like daughter. Kwankwasa mai tayi yayi winning glass da murmushi a fuskanta tace Oga a bude Booth ko? Yayi smilling back tare da bude booth din badiyya da uwarta sukayi kiciniyar saka kaya a booth gogan ko fitowa beyi ba. Suka shiga motar, ko kallon arziqi be ma uwar Badiyya ba yace, Ina wuni mama,Ita ko a ranta cewa take Ashe diyyata bata yi karya ba, Zaidun nata hadadde ne, ta amsa cikin wani murya sai da diyya ta juyo ta kalleta. Zaid ya ja mota sai gidansa dake Maitama.

Ta zage ta dafa Tuwon semo miyan agushi da yaji ganda, ta kai kan dinning ta ajiye, tun dazu take zaman jiranshi, har bacci ya dauketa kan 3sitter, Sun iso gidan suka dinga kwankwasawa shiru, Zaid ya kwala ma maigadi kira yazo jikinsa na rawa, yace kai wata ta fita daga gidan nan? Yace auu akwai mutum ciki? Zaid yace ba tambayar da na maka ba kenan, yace Yallabai indai ka bar mutum a nan to ta na ciki, don tun da safe ina nan zaune ba inda naje. Zaid yayi tsaki ya ciro keys ya kalli su badiyya yace muje Badiyya da ta gama cika tayi fam kamar ta pashe ta ja akwatinta uwar na biye da ita a baya, suka zagaya baya, zaid ya sa mukuli ya bude wani qofa ashe ta kichin ne, tun daga kicin din suke jin wani daddadan k’amshi, har suka iso parlorn, kwance ya ganta tana bacci, kallo daya ya mata ya dauje kai, idonsa ya sauka kan dinning yaga kulolin abinci, ya tabe bakih, Diyyan ta kade ganin tsaruwar gidan, ya kalli uwar diyya yace feel at home mama, ta sakar mai murmushi ok son, ya kalli diyya yace bari na shiga na yi wanka, tace dear, ai da ka barih kacih abinci yar matarka, ta qarashe tana zolayarsa, ya dan bata rai yace nahhh, you go ahead, ya ja briefcase dinsa yayi dakihnsa, suko nan suka dire kayansu suka nufa kan table, Diyya na bude kular miya taji wani qamshi, nan da nan miyonta ya tsinke, sai da ko ta lasa, ta zuba a plate, ta sam mamanta, nan suka hau ci, daman mulmula biyar ne, diyya da Maman ta suka kwashi tuwon nan tassss. Cikin bacci taji ana buruntu tayi sauri ta tashi, idonta ya sauka kan Diyya da mamanta, Gabanta ya yanke ya fadih. Diyya ta juyo ta ganta tsaye, Auu Rumaisah kin tashi? Zo ki kwashe kayan nan ki kai kicin, sannan kizo ki shigar min da kayana dakihna, ki nuna ma mama dakinta, Hantar cikin Maysah ya bada Kulululu. Meke shirin faruwa da ni? Ta tambaya kanta.

_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
24. Gidan Gandu by Biebee IsaJi ta yi abun kamar a mafarki nan ta tsaya kamar robot, tsawan da badiyya ta mata ne yasa ta dawo hayyacinta, ko ba kya ji ne? Cewa nayi zo ki kwashe kayan table din nan, Sannan ki kwashi kayan chan ki kai dakih, Maysah ta hadiye wani mugun miyau, jiki ba qwari ta tako ta harhada kwanukan tayi kichin, Tuwon da ta tuqa domin ta da mijinta, ga wasu nan sun cinye tas, ita ko ko a bakinta, gashi wani yunwa takeji, daman niyyarta sai ya dawo zasu ci tare gashi an cinye, tuni hawaye suka bi kuncinta, ta dawo parlorn ta ja Akwatin su tayi hanyar wani dakih, kasancewar Gidan 3bedrooms ne, Badiyya ta cire bakinta ta kwala mata kira, jikina barih ta zo da sauri in kai wannan akwatin dayan dakin, wanchan akwatin ki kaishi wanchan dakin ta nuna dakin kusa da Zaid, waiyo Allahnta, dakinta take nufi zata

9 / 29