Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   19 / 29

54K to 57K   out of 85.7K words

komai, a gurguje Maysah ta shige dakih ta fito da jakka ta kalli Amira tace Sisi na tafi, thank u so much u really saved my ass, Amira tace dont mention, jus take care and take ur time kinji, oryt bye..
Amira ta shige dakin da Maysah ta fito, ta rage kayan jinkinta ta dane gado ta bararraje ta shiga sharar bacci.
Maman Baddiya ta ji shiru, ta kalli agogo karfe 3:45, har an fara kiraye kirayen sallah laasar, ita da tace a mata sakwara tun kafin qarfe daya, Har ynz shiru takeji, ko alamun daka bata ji ba, ta miqe dai ta fita parlorn, ta kalli Dinning, kulolin dazu ne, ba ta yi qasa a guuwa ba ta qarasa ta bude kular, jollof rice din da Maysah ta girka ne, tayi tsaki ta nufa kicin, ba alamun an fera doya balle an daka, ta gama dube dubenta bata ga wani abu me kama da sakwara ba, ran ta yayi mutuqar baci, ta fita kamar zata tashi sama, ta banka dakin Maysah, Amira ta gani kwance ta na sharar bacci, ta matsa gadon ta daka ma mata duka a baya ke don kutumar ubanki waye tsaranki?ni zakiyi wa bariki, Amira ta tashi a firgice tana mustsutsuka ido, tace lafiya? Nace don ubanki ina sakwarar da kika ce zaki man? Ke bakiyi min ba kin hana a yi min, idon amira ya qeqeshe, ta kalli Maman badiyya tace ke dai banza ce wlh, harbkin yarda xan miki sakwara? Yo uban waye bawanki da zakisa aiki? In ba zaki ci abin da aka girka ba ki barshi, ke in banda abun kunya kinzo ki tare gidan diyarki har kina sa Matar gida aiki, wallahi Maysah kika samu, Ki gode ma Ubangiji da ba nice matar Zaid ba, da sai na shayar dake madarar mamaki. Baki bude maman diyya take kallon Amira, ba ta taba zaton zata iya gaya mata magana haka ba, ta zata itama kamar Maysar take, ta ma tsorata da alamuran Amira, yarinya qarama ta ke gaya mata magana haka? Ai ko yau zataci uban yarinyar nan, sai ta saukar mata da duk abunda ke kanta, tace ke yau sai naci Uban Babanki, amira ta kalleta tace Uban babana? Tsoho kenan? Maman diyya tace shifa shege Maye, ai muna da labarin Musbahu Zailani bokan zaure ne, shege tsohon banza, yau sai naga uban da ya tsaya miki, Don uban-- ba ta qarashe ashar din ba Amira ta daddage ta kamtse maman badiyya da mari, bata gama tunanin ko marinta akayi bat ta qara jin wani marin, ta dago kai ta kalli Amira, kika mareni? Ta ko qara mata wanih, ta dafe kuncinta ta sake ihu waiyo na shiga uku tace jamaa ku taimakeni jikan Mayu sun kamani, jikar Zailani, Amira ta daga hannu zata qara mata wani marin Maysah ta shigo da gudu...
3 hrs · Public
More
4⃣7⃣ 🏡Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕
Ganin Maysah be hana Amira kara ma maman badiyya wani marin ba tare da nuna ta da yatsa, tace ki ka qara cewa tak sai na lakada miki dukan tsiya, da sauri maman Badiyya ta riqe bakinta don ta fi danganta Amira da wadda ke aiki da Aljannu, amma in banda Aljannu wacece zata kalli girmanta ta daga hannu ta mara har kala 5? Maysah da sauri ta janye Amira tace Haba Amira me-- shut d hell up amira ta katseta, tace ba a haifi uban da zai zagih tsoho gabana ban mareshi ba wlh, duk tsufan ka, ko da gemun ka na jan kasa ina iya kamtse ka da marih, ko waye, ni gwara a zage baba da a zage tsohonmu, sum sum maman maysah ta ja tsamin jikinta ta bar dakin kar ta qara jin wasu yatsu biyar a kumatunta, Maysah tace yau na bonu! Amira kin san me kika ja min? Allah kadai ya san me zai faru idan diyarta ta dawo, amma Meerah be kamata ba-- Amira tace Maysah i told u to shutup dint i? Wai ke me ke damunki? Kina gidan mijinki amma baki da maraba da er aiki, ke baiwarsu ce? kin tsaya suna juya ki, toh wlh idan zaki kwatar ma kanki 'yanci ki kwatar, in ko ba haka ba, duk sharar da suka dibo kanki zasu zubar tana kaiwa nan ta shige toilet don watsa ruwa.
Tare suke da Alh. Haladu a wani hotel sun gama aikata sabo, qarar wayarta taji, ganin mamarta ne ya sa ta sake tsaki ta dauka, hello mama, ya akayi ne? Ji tayi maman na kuka, Badiyya ba lafiya, yanzu na sha tagwayen mari kala 3, badiyya ta zaburo, wani dan abun uban ya mareh ki? Nidai ki dawo, ko nayi tafiata, Badoyya ta miqe a gurguje tace ma Alhaji haladu zata je gida Emergency ne, be bi baasi ba ya ciro bandir din 1000 yace zasu yi waya.
A sittin ta shigo gidan, tayi dakin mamar, Zaune ta sameta zaune kan gado Fuska ya suntume ya kumbura, fuskar tayi jaaa, Mama me ya sameki? Waya miki rauni a fuska? Tace Wata ce ta zo gurin Rumaisah, Badiyya ta shirga uban ashar tare da kwabe dankwalin kanta ta ci dan mara, tayi hanyar fita, tace kul badiyyah, Wlh yarinyar nan ba ita kadai bace, Tare take da Aljannu, mama ba Aljannu ba Allah ya sa Almatsutsai ne sai na ga uban da ya tsaya musu a gari Abuja, ta fita tayi dakin Maysah, Amira na zaune tana shafa, Maysah na Sallah, ta sa kai tana sujjada Badiyya ta fincikota, ta maqureta, Amira tace ke karuwa, bakisan darajar Sallah bane da ba zaki iya bari ta idar ba ki mata ko me zaki mata? Au na manta fa ke jahila ce, Badiyya ta juyo ta kalli Amira da bata fasa shafar hodan da takeyi ba, tsaf ta ganeta, yarinyar da ta taba mata rashin kunya ne wata rana da taje neman Zaid a Maid. Amira ta rufe powdern ta ajiye, tace ni kike nema, ba Maysah ba don kamar nice na mari uwarkih kamae so 5 ne ko 6 i cany remember dai? Ta kalli maman Badiyya da ta labe a bakin kofah ta kasa shigowa tace, Mummy mari nawa ma na miki? Badiyya ta sake Maysah, tace Amira kike ko uban wa? Karon mu na farko na qyaleki, wannan kuwa zan nuna miki ni ba saar ki bace balle kuwa uwata, ta matso gadan gadan ta nufi Amirah, Maysah tayi saurin riketa Aunty Badiyya kiyi haquri, laifina ne, wlh laifina neh, ni zaki hukunta, Amira cikin fushi tace Maysah kinci ubanki, ki kyaleta muga abun da zata yi mana? Da alamu tsautsauyi yake niyyar kawota kusa danih, jin haka yasa maman badiyya zuwa ta kama diyyarta, badiyya ya isa, na gaya miki yarinyar nan ba ita kadai bace, ni wlh na yafe, Allah kadai yasan abun da zata miki, Nan Badiyya ta tirje ta shiga bambami da ihu da masifa, mamar ta riqeta gam.
Tunda suka shigo gidan suka san cewa va lafia, da sauri Zayd yayi parking ya fito, Samir din ma parking din yayi suka shiga da sauri, Dakihn Maysah suka nufa, ganin maman Badiyya riqe da ita ta na tirjejen a barta ta bige Amira ya sa Zaid zuwa ya janye Badiyya, Shima Samir ya janye Amira tare da rungumeta, a hankali take sakar da ajiyar zuciya, Maysah kuwa sai kuka take tayi, Zaid ya ce Sam matarka is unstable, ka kwasheta ku tafi, kaga yanda ta maida min gida? Samir ya kalli zayd ya wurga mai Harara, yace ka dai san waye unstable not my wife, ya dago Amira dake kwance a kan kirjinsa yace meerah na me ya faru? Ta dago ta kalli Zaid tace Kalli fuskar sirikar ka, ba gardama ya juya ya kalli fuskan maman Badiyya da ya kumbure, yace subhanAllah Mummy me ya sameki? Badiyya tayi caraf tace marinta fa tayi Zaid, Zaid yace Mari?? Amira tace ba daya ba, marirrika ta sha, kuma ko yanzu ta sake yin abun da tayi zata samu fiye da haka, Ran Zaid ya baci, ya kalli Maysah cikin tsawa yace ke kika sata koh? Kuka ta keyi ta kasa cewa komai, ya kalli Samir yace Sam ka ga abun da nake ce ma ko? Ka hukunta matarka ko ni wlh na hukunta ta, ba zan dauki raini , ba zan yarda a rai na min Iyalina ba, don rashin kunya ki daga hannu ki mari someone that is old enuf to b ur mother? Samir yace Easy mana zaid, ai ba mu ji meye dalilinta ba, ya fuskanci Amira yace lilsis tell me what happened? Cikin rashin tsoro ta warware musu komai tun bayan tafian samir har zuwa yanzu. Ran Zaid yayi mumunan baci, fita yayi daga dakin ya fada dakinshi, Ran Samir ya baci ya kalli Maman Badiyya yace ki gode ma Allah ba a gabana kika zage tsoho ba, wlh da yanzu kina kwance gadon Asibiti ya kalli matarshi yace lets go ya fita shima. Amira ta kalli maman badiyya tace dis is wat happens wen u mess with Musbahu Zailani ta suri jakkarta ba tare da ta kalli Maysah ba tace mun wuce. Badiyya ta fice daga dakin maman ta bita a baya. Maysah ta zuve kan gadi tana kuka a hankali..
******
Mama me kike tunani da kika zagen musu kaka haka? Kinsan me kikayi kuwa yanzu? Kinsan yanda suke son wannan tsohon? Ai ko mahaifansu ba sa son su kamar yanda sukeson tsohonsu, yanzu shikenan kin ja min, Zaid yayi fushi, Mamar Badiyya ta kalli diyarta tace kiyi haquri, ban ta ba tsammanin abun nan zai juye ya koma haka ba, indai Zaid ne ba matsala yanzun nan ba sai anjima ba zai sauko, ta miqe ta dauko wani turare ta bata tace ta shi ki shafa kije gunsa, ina tabbatar miki da cewa sai yadda kikayi dashi. Badiyya tayi shewa tace woo mummyna shisa nake sonki, ta miqe ta fada toilet don gyara jikinta kafin ta nufa dakin Zaid..
****
Tunda daga kofar dakin ta ke cin karo da kwalba da gwangwanin giya, Hakan ya tabbatar mata da gogan nata ya sha giyarsa yayi tatul, don ta san fushin da ya dauka giya kadai ce zata kwantar mai da hankali, chan kusurwa ta hango shi yana baje, idonshi lumshe amma ba bacci yakeyi ba, tun kan ta qarasa gunsa yaji wani qamshin turare, da sauri ya bude idonsa, Giya ce ta fara gaya mai karya, ganin badiyya yayi ta rikide ta koma mai Maysah, da sauri ya fincikota ta fada jikinshi, ya shiga sarrafata, badiyya abin nema ya samu ta biye mai suka lulu duniyar maaurata.
What?? Alhaji Haladu yace cikin kidima, Jawad aka ba contract din da nake expecting? PA dinsa yace eh yallabai, yanzu ma yazo refinery yayi signing contract din, yace zai tafi in 10days time, Zufa ya shiga tsatsafo ma Alhaji Haladu, Yaron nan na so ya shige gaba na? PA yace ai Alhaji daga sama ne abun, ni ya kamata naje Amsterdan, aka ce na barshi ya za a ban contract din Niger-Delta na barshi ya tafi don na san zan fi samu a na Niger Delta din, yanzu kuma sai ace shi zaije to wlh ba zai rayu ya ga wannan ranar tafian nashi ba, wlh ba zan barshi ya dakushe min tauraruwata ba, yaro kankani ya shige gabana ba. Wayar sa ya lalubo Gambo Kisa Gayu, ringing biyu ya dauka hello ya Alhaj, be tsaya sauraron kirarin da ya saba mai ba yace kana ina Kisa Gayu? Wlh gani Damaturu ina wani operation ne, kayi maza ka zo kaduna Gobe Goben nan, kaii Alhaj anya zan iya zuwa? Gaskia ina wani dan aiki ne zuwa jibi ko gata zan diro,Ni ka dawo gobe ko nawa ne zan biya ka, yace Alhaj kayi haquri ka bari har na dawo, idan kuwa emergency ne sai na turo ma yarana, Aa Kisa gayu na fi yarda da aikinka, na baka nan da kwana 3, yace lafia lao lokacin na gama komai anan, me kakeso ayi ne? Yace Akwai wani yaro da ya shige hancina ya qudundune, yaron da ya hanani rawan gaban hantsi, wai shi Jawad Zailani so nake a min maganinshi, Yallabai me kake so a mai me? Yace so nake a kasheshi..
3 hrs · Public
4⃣8⃣ Gidan Gandu by 💕Biebee Isa💕
Tohm zanyi qoqarin dawowa da wuri, idan ban samu damar dawowa ba, zan turo ma yarana, suma kwararru ne, Alhaji Haladu yace banso a samu matsala, yace Kar Ka damu Alhaji, sai dai kaji daga gareni, a haka sukayi Sallama, Alhaji Haladu ya tattara kayanshi ya wuce Kaduna..
Lagos
Zuciyarta ta amince da Shawarar da ta ba kanta, inda zuciyar k ce mata, ta manta komai da ya faru a baya, ta rungumi mijinta, tunda be da wani aibu, hasalima shi ke biye da ita, ita kuma na wulaqantashi, ya kamata ta zage damtse wurin kyautata wa mijinta, tunda har ya kai ga shaawar sake wani auren, kuma har ga Allah kyautata mata da yakeyi zuciyarta ta kamu da sonshi, son da ba ta tunanin ta taba ma wani mahaluki irinshi. A yau tayi niyyar faranta Ran Mijinta Zayyad, Yau zata Roke shi gafarar abubuwan da ta mishi a baya, da sauri ta tashi ta shiga kicin don daura abinci, Watanni takwas kenan da zuwanta legas ba ta taba yin abinci don Zayyad ba, yau kuwa gashi ta shiga shirya mai kayan dadi, sai da ta gama fried rice dinta da fried plantain, kafin ta yi pepper chicken dinta, wurin karfe 1:30 ta shirya komai kan dining, da sauri ta fada toilet don yin wanka, ba jimawa ta fito, ta shirya cikin wasu riga da skirt na atamfar hollan da ya yi matuqar yi mata kyau, rabon da ta shafa kwalli a idonta har ta manta, yau ko Hanifa har da kwalliya, ta feshe jikinta da turarruka masu kamshi, ta kashe daurinta, hanifa tayi kyau har ta gaji, kallo daya zaka mata kasan tana cikin nishadi. Karfe 2:30 taji horn din shi, da sauri ta leqa window, shi din ne, sai yanzu ta qare mai kallo, Zayyad kyakyawa ne gashi da kyan zuciya, ita kanta ta san YaZayyad yayi haquri da ita, shisa yau takeson faranta mai, don runtse ido zatayi ta rungumeshi, da sauri ta fita daga dakin, ta zo fitowa kenan santsin tiles ya kwasheta da sulbe ta fadi ta gurde kafa, Azaba ya hana ta sake ihu, amma hawaye tuni ya fara sunturi. Shigowa yayi da Sallama, idonsa ya sauka kan hanifa, da sauri ya qarisa gunta ya na tambayan lafia? Kasa magana tayi, hawaye kawai take iya, fadiwa kikayi? Sannu kinji tashi, ya danyi yunqurin ta da ta, ta saki ihu me qarfi, Yaya kafana, Me ya samu kafan? Ya kalli Kafar ya ga ya dan jirkice, nan ya fara salati ya rude iya rudewa, sabarta yayi kamar wata baby ya kaita daki ya shimfide kan gado, yace sannu, bari najeh na siyo Robb ko Deep heat na shafa miki kinji? Ta kasa cewa komai, da gudu ya fita, ba ayi minti 15 ba sai gashi ya dawo, da Magunguba cikin leda, Ya dibo maganin zafin ya shiga shafa mata a qafa a hankali, ita kuwa sai ihun kuka takeyi don Zafin da takeji, sai da ya shafe mata kafa da robb kafin ya ballo Ibrufen pain killer da wani sleeping pills, ya bata ta sha, sannan ya shiga shafa mata kai yana cewa sannu kinji, try nd have some sleep, cikin kuka take cewa Yaya Abincin kan Dinning, da sauri ya kalleta, mamaki ya rufeshi, amma har a ranshi ya ji dadi, yau shine da abinci?Lallai kam Allah na gode ma, yace karki damu Hanee, zanci but sai kinyi bacci, bata tsaida kukanta ba har bacci ya kwasheta..
Kano
Tunda ta gano gaskia game da YaSuraj ta kulle kanta ta shiga tunani, ta fuskanci son da yake mata gaskia ne, ita kuma ta aminta da zuwa yanzu ta kamu da sonshi, Toh meyasa ba xata yafe mishi dab qaramin laifin da ya mata ba? Ta rungumi mijinta wanda take ma Zazzafan So ba tare da saninta ba? Toh dai lokaci yayi da bygones will be bygones, zata rungumi mijinta zabin Allah a gareta, fatan ta Allah ya kara Hada kansu, ta tashi ta bude kofar ta ta fita, karfe 12 da rabi, ta san Yasuraj ya dade gurin aiki, da ya kan dawo cin Abinci, amma tun bayan abin da ya faru ya daina dawowa, don ya san ko ya dawo ba zai ganta ba saboda kulle qofarta da tayi, shikuma be son ya takura mata, ya fi so ta sauko don kanta. Bilkisu ta shiga kichin ta hada abincinta mai rai da lafiya, ta dawo ta ta sake wanka ta yi kwalliya ta dawo parlo ta kunna tv, binibini sai ta kalli agogo. Kamar daga sama sai gashi ya dawo daukan wasu files da yake da buqatansu a gurin aiki emeegency, yayi mamakin ganinta zaune a parlor, suna hada ido ta kauda kanta, Tace Sannu da Zuwa, murmushi Yayi zuciyarshi cike da jin dadi yace Yauwa Billy nah, erhm daman na yi mantuwa ne, bari nashiga na dauko, be jira amsarta ba ya shiga daki dauko files din, sai gashi ya fito, Billy bari na tafi sai na dawo, ta dago kai ta kalleshi, tare da marairaicewa tace ga fa abincinka nan fa? Wani dadi ya mamaye zuciyar Suraj, yace tohm sakko min dashi nan, ta miqe a yangace ta nufa dinning din ta kwaso kayan ta zo ta zube gabanshi, ta shiga zuba mishi fried spagetti da vegies sauce, ta tsiyaya mai lemu a cup, ta miqe zata tafi yayi saurin riqo hannunta, ta zuba mai idanuwanta, ya ce sorry i cant eat alone, ta ce sorry m not hungry, yace ai baki isa ba, ya zaunar da ita kasa kusa dashi, yace cikin ki beyi kama da wanda yaci abinci ba, bata sonyi mai musu sai tyi shiru, haka ya dinga ci ya na bata a bakih, tun tana kunya har ta daina ta xage tana ci, sai da suka ci plate 2suka sha lemunsu ta tashi ta kwashe kayan, binta yayi kicin, ya

19 / 29