Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   25 / 29

72K to 75K   out of 85.7K words

bacci yaqi zuwa mai, yanda ya ga dare haka ya ga rana, Maysah kuwa da qyar ta samu bacci ya dauketa a dareb jiya, Yazayd don darajar Allah da manzon sa ka bude, tsaki ya buga, yace ke xabin tsoho kina shiga rayuwata, ki tafi i dont need u, tace naji just open up, ya rarrafo ya bude dakin, Maysah tayi saurin fadawa, duk warin giya ya cika dakin, amma hakan be hanata rungumeshi ba, tana kuka, shima kukan yakeyi, ta ja hannun shi ta wurga shi toilet ta dauko towel ta mika mishi, tace Kayi wanka, ya samu kanshi da bin umarninta, kafin ya fito ta gyara dakin, ta share ta kunna turaren wuta, ta kunna AC, ta ciro mai kayan da zai sa, yana fitowa ya je ya sa wani Jallabiya, tace Yazayd ga kayanka fa a kan gado, ba office zaka ba? Yayi dan tsaki yace ba inda zanje, ya ciro giyarsa ta karshe ya fasa sai sha, tayi tsalle ta fincike, tace shikenan mutum gani yake giya ce maganin matsalolinsa? Kallonta yakeyi yace ke zabin tsoho bani? Tace ba zan bada ba, ko tsoro vata ji ba ta shiga toilet ta tutular da giyan a sink, ya kalleta cikin takaici, ta qaraso gurinsa ta dafa shi sassauta murya tace Ya zayd what happened to u? U look miserable, da karfi ya tureta, what happened to me? I am HIV + dats wat happend to me, What are u even doing here? I tot i told u to leave? Yazayd bazan barka haka ba, nace zan zauna da kai a haka, ya kalleta da sauri, yace ke wai bakin sa meye HIV ba ko? Tace wlh ba sani, cutar da ke karya garkuwar jiki, Yazayd its not d end of d world, u can get treated, please muje Asibiti a rubuta maka magani, idan yaso sai kayi taking preacution nd u'll be alive and healthy, ya kalleta ya watsar yace i dont need any treatments, m dying anyways, tace Yazayd yace kee fita ki kyaleni, da karfi Yace ki fitaaaa, da gudu ta bar dakin sakamakon kukan da ya ci karfinta, ya bi bayanta da kallo, a hankali yace tausayinki nake zabin tsoho, i cannot ruin yourlife, you are still young and innocent, ba zan yarda rayuwarki ta kare kamar yadda tawa zata kare, na so zama dake har karshen rayuwata, don na nuna miki So da Kauna, na nuna ma tsoho Zabin shi Alheri ne, na nuna ma Kowa Cewa Kece Cikon Farincikinah, amma dole zan rabu dake, sabida ina sonki, Ina sonki Ruma, ya sake fashewa da kuka ya fada kan gado yana yi...

3 days Later
Cambridge England
Mamaki ya cikata ganin Ya Suraj a doorstep dinsu, da azama ta rungumeshi Yasuraj, nayi kewanka da yawa shima ya rungumeta, Islahulkhair kinganki haka kika koma? Tayi daria tace Yaya shigo mana ta ja hannu suka shiga, yace Islah ki shirya gove zamu wuce Naija, ta dago kai ta kalleshi, why? Yace Tsoho requests for ur presence, mijinki ya dawo!ta tabe bakih, yace bakiyi mamaki ba, tace yes coz nasan ya na nan, ta kwashe komai ta gaya mai ya jinjina kai, yace toh tsoho yace ba zai shiga hakkin ki va, zabi zai baki, so u choose wisely, tayi murmushi tace i know what i want.

Bayan kwana 2
Maiduguri
Islah durkushe gaban tsoho yace yauwa Islahulkhair, na aika a kira su, ayi komai gaban kowa, kar ace na danne hakkin wani, bazan matsa miki ba, abunda kikeso shi zaayi, idan ba kyason zama da Ammar zan sashi ya sakeki nan take yanke, zaki cigaba da karatunki har na zabi miki wani mijin da na ga ya dace dake, don ba zan yarda da zaman ki haka kurum ba, dole ki sake aure, amma kamar yadda kika sani, ba sauran Samari a gidan nan duk sunyi aure, dole Me aure zan zaba miki a cikin dangi, toh ki Zaba abunda kikeso bayan kinyi tunani, kar ki bari fushi ko daukar fansa ya kaiki ya baroki, Gaban Islah ya fadi, a ranta tace zama da kishiya? Ganin yan cikin gida sun fara shigowa ya sa Tsoho yin shiru.
********
Mu'ammar na so ya hada ido da Islah amma ta dauke kai, ta qi Kallonsa, so yake ya mata fuskar tausayi ko zata ji tausaynsa, cikin kwanan nan ya kasa bacci fargaba ne fal ranshi, ya zaiyi idan ya rasa Islah? Jin Tsoho yace toh Islah, Wani hukunci kika yanke game da Mu'ammar, kin amince zaki zauna dashi a matsayin miji ki koma dakin ki? Ko kin amince a raba aurenku wato ya sakeki? Wannan ba zabina bane, zabin kine, muna sauraronki. Islah ta hau tunani, Amincewarta na nufin ta bar karatunta na Cambridge, karatun da ta ci buri da shi, Baba hassan ya katse mata tunani yace khairi ke muke jira, ta dago kanta a hankali ta fara kallon iyayenta, da kawunninta da gwaggoninta da yayyunta ta kalli tsoho, sannan ta sauko da idanuwanta kan Mu'ammar, a lokacin Mu'ammar idonshi kulle yake, yana karanta duk adduar da ta zo mai bakih. Ta kura mai ido sosai duk abubuwan da ya mata suka shiga dawo mata, tace Tsoho Ina so na koma dakina, ina so na cigaba da zama da mijina, Ina so na samu Aljannata ta sanadiyar YaMuammar, na haqura da karatun, duk dakin a ka dau Alhamdulilah, Mu'ammar da ya daskare zaune, ya kasa tantance me kunnuwansa suka jiye mai, kamar a mafarki ya ke ji, a hankali ya bude idanuwansa fes a kan Islah, ya tabbatar ba mafarki yakeyi ba, Aiko ya takura ya saki Ihuu, yace Waiyoo dadi kasheni. Duk dakin a ka sa Daria har hajia babba sai da ta dara..

_Bibilicious Biebee_
58...Gidan Gandu
Gidan Gandu by Biebee Isa
Mu’ammar be ji kunya kowa ba ya matso kusa da Islah ya riqe hannunta, yace i promise u, ba zakiyi Nadama ba, Ba zakiyi da na sanin zama dani ba, ya kafe ta Idanuwanshi, Islah ma ta kafeshi da nata idanuwan, daman ta dade da yafe mai, so take ta ja ajinta a matsayinta na mace shisa ta dan wahalar dashi kadan, kuma da alamu ta kamu da sonsa sbd yanda ta kafeshi da idanuwanta, da Alamun sun manta inda suke, duk parlorn aka kafesu ds idanuwa, Uncle Abbakar yace kai ku tashi ku bamu guri kun wani tsura ma juna ido, ina basu san tanayi ba, Manyan parlorn sukayi murmushi, Baba hassan yace Mu’ammar kuna iya tafia, nan ma shiru, sai da Hajia babba ta daga murya tace yan soyayyan burauba, to Tsuntsun Soyayyah ma yaci ubanshi. Islah ta miqe a kunyace tafita da sauri, da gudu Mu’ammar ya rufa mata baya duk yan dakin suka hau daria suna yaran Zamani sai abarsu.
Hanyar Sassan Umma hajja tayi, tana sane yana biye da ita, ta share sai da ya sha gabanta tayl daure fuska, shi ko baki har kunne, ya riqo hannunta yace Thanks Angel, sunan da ya kirata dashi ya mata dadi da har bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, ya matso daf da ita ya shafa fuskarta, tare da kai bakinshi kan nata, taso ta dan kara jan ajinta, amma sai ta share don Mu’ammar din ya fara bata tsausayi. Tsoho ya yanke shawaran Mu’ammar ya dauki matarsa ya tafi da ita gidansa na Zaria gobe, Baba Gambo yace tsoho ya maganar karatun ta? Tsoho yace toh wani karatu kuma bayan yarinya ta yarda zata zauna da mijinta, sai dai ya sama mata ABU zaria. Allah ya basu zaman Lafia Amin.
A ranar su Amira suka diro Maiduguri, chan dare kuma sai ga Jawad da Fadila, dangi sai murnar zuwansu sukeyi, Tsoho kuwa yafi murnan ganin jikokinsa, Barin fadila da ta ji sauki sosai,
Yanmatan su biyar, Hanifa Amira, Bilkisu, Fadila da Islah suka kulle kansu cikin dakin hajia Ama, ni banta ba ganinsu karkashin inuwa daya haka ba suna labarin arziki, sun burgeni matuqa da suka hada kansu, ba zaka taba cewa akwai wani sabanin da ya taba shiga tsakanin da ya daga cikinsu ba, Labari sukeyi suna kashewa suna dariya, ko wacce na bada labarin yadda mijinta ke ji da ita, Fadila tace Allah sarki Maysah, shes d only one missed here, bari na latsota ta hau IMO muyi VideoCall, Hanifa tayi daria tace sai kinsa taji haushi, Bilkisu tace kina so ta sa Yazayd kawota cikin daren nan, fadila tayi daria tace wayarta kashe take, Islah tace Allah ya so ta kam, yau da sai kun sa Yazayd tafian dare, duk suka yi daria. Nan Amira take basu labarin honeymoon dinsu na Paris suna ta kyalkyala daria. A gurin yan mazan ma haka suka su 4 suna labari, just like old times, dama sun kasance masu son junansu, sabanin da suka samu ne kwanakin baya ya sa suka bar kula juna, amma yanzu sun fahimci juna sun roqi juna gafara. Jawad ya kalli Suraj yace Wallahi gwanda da tsoho yayi hadin nan duk nafi ku jin dadi, Suraj yace wlh duk na fi ku dacen mata, Samir yace wlh i dont knw wat wud life be like idan ba Lilsismeerana a ciki ba, Mu’ammar yace bari na takaice muku zance Islahulkhairi ne heartbeat dina, duk suka fashe da daria, Zayyad yace wai Ya labarin Dr Zailani? Shiru ya boye, ko Maysah ce ta boyeshi, Jawad yace bari na latso mana shi mu mai tsiya, yace kashh wayar kashe take, Allah ya so ka Bros duk sukayi daria.
Abuja
Zayd ya rame yayi baqih ya jeme, ya fita hayyancinshi, kwananshi 4 kulle cikin daki, kullum Maysah Sai ta kwankwasa tana mai magiyar ya bude amma ko tankata beyi, sai ta jingina jikin kofar tayi ta kuka, yana jin kukan nan amma sai ya share, dama tuni tayi watsi da skuk dinta, Yau Tuesday zayd ya tashi da farar Safiyya ya tashi da wani ir
Inin fever, nishi sama sama kamar zai mutu, hankalin shi yayi matuqar tashi, sanyi yake ji sosai, nishin shi sama sama, Symptoms din kanjamau duk sunyi developing, Maysah ta fito taji yana wani irin tarih hankalinta ya tashi, Ta hau bubbuga kofar kamar zata balla kofar, yazayd ka bude kayi wa Allah ka bude min, ya so bude mata kofar amma bazai iya ba, baida karfin zuwa bude mata, hankalinta ya tashi, da sauni ta wawuri wayarta ta kunna, ta shiga neman layin Yaya Jawad. A lokacin yana tare da babynsa cikin mota, tana zuba mai shagwaba, yace Allah idan ina kiranki kina kin zuwa sai na kwasheki mun koma kaduna yau dinnan, tace Sorry baby, kawai sai mummy ta ga na fita da daddare? Ya murguda baki kamar yanda takeyi yace ba mijinki ya kiraki ba? tace sorry kaki babynah, da mun koma gida kaga daga ni sai kai koh? Da sauri yace to mu tafi gidan mana, tace haba ko 1 week bamuyi ba fa, kafin yayi magana wayarsa yayi kara, ko da ya duba Maysah ya gani, yayi murmushi yace ga matar yaya, ya dauka hello Sis Inlaw, cikin kuka tace YaJawad, yace Maysah me ya sameki? Tace yazayd ne, he’s bin sick, ya kulle kanshi for days, nd yanzu yana nishi sama sama, i can feel his heart beat yanzu haka, i’m afraid he’s dying, YaJawad ka taimaka, Cikin rudu jawad yace ina Maiduguri, but yanzu zan taho as fast as i can, gani nan zuwa, ki kwantar da hankalinki, he’s going to be alryt kinji, ya kashe wayan ya kalli fadila da ta tsura mai ido, yace baby ki koma cikin gida, kice musu na tafi Abuja, tace baby m coming with u, yace noo,tace pls, yace i dont have tym to argue uo staying here nd dats final, ki bari inje kinji? ta turo bakih tace Allah ya kiyaye hanya be safe, yayi murmushi dats my babe, ya bata kiss ta fita a motan tana daga mai hannu, shi kuma ya ja motar ya bar gidan kamar zai tashi sama, Jawad Allah ya tsare hanya.
Abuja
6:45 Jawad ya iso Abuja, sai da yaje ya dauko wanda xasu balla kofan don sunyi waya da Maysah ta shaida mai har ynz be fito ba, ta ma daina jin motsin shi, suna shiga gidan su ka shiga balla kofar, basu sha wahala ba kofar ya balle, rige rigen shiga dakin sukayi, Chan Maysah ta hango shi chan kasan gado duk ya fita hayyacinshi, da alamun rai a jikinsa amma bai motsi, da sauri Jawad yaje ya ciccibi Zayd ya rungume, ya na hawaye don ya tsorata da yanda yaga Zaid, what happened to u brother? Maysah tace i will brief u, buf we hve to take him to a hospital, Jawad ya dago shi, yayi waje dashi, maysah ta rufa mai baya, bayan mota ya sa shi, Ya ciro kudin da be san yawansu ba ya ba masu balle kofa, Maysah ta shiga motar Jawad ya ja motar su ka bar gidan, A hanya Maysah ke ba Jawas labarin abunda ya faru, ran jawad ya baci hankalinshi ya tashi yace wlh dana ga Badiyyar nan, ba abunda zai hanani kasheta. Maysah tace Yajawad ga wani asibiti nan, da alamu private ne,da sauri ya sa trafficator ya shiga asibitin, nan da nan aka karbi Zaid akayi Emergency dashi suka shiga bashi taimakon gaggawa, har sai da zaid ya farfado ya dan dawo hayacinshi, Zaid ya bude idonsa ya ga Maysah da Jawad a tsaye, ya fashe da kuka, Jawad yayi saurin rungumeshi, Zaid yace m dying bro, jawad yace no u are not, Zaid yace ni HIV+, Jawad ya girgiza kai yace i cant believe it, i refuse to believe it, Ya kalli Maysah yace anyi mishi test? ta girgiza kai ta na hawaye, to wa yace yana dashi? Zaid cikin wahala yace kar ka bata lokacinka danuwa na, ina dashi, Jawad ya buga tsaki ya juya yace da Nurse ta kira mai Dr, tace sorry sir, Dr sai 8 yake ganin patients, we can do anythng before he comes, what do u want? cikin daga murya Jawad yace get me The Doctor, nurse jiki na rawa ta fita. Bata jima ba sai gata ta dawo da Dr. jawad ya miqe ya bashi hannu, yace Dr pls help my bro, Dr ya kalli patient din ya zaro ido Dr James yace Dr Zailani? What happened to him? I’ve bin trying to reach him for days, briefly Jawad ya mai bayani, da sauri Dr james ya fita sai gashi ya dawo da wata nurse ture da wani wheelchair yace a daura Zaid suka fita, su jawad suka bisu a baya, wani restricted dakih suka shiga, Dr James ya diba jinin zaid da kanshi ya shiga testing jinin, sannan ya tura Jawad cikin wani Engine da zai tantance duk wani ciwo da cuta da ke jikinshi. Ya kalle su yace dis will take some minutes, Jawad ya rintse ido Maysah ta shiga zuba adduoin da ya zo bakinta, bayan kamar mintuna sha biyar machine din yayi kara, alamun ya gama bincikensa, har printout ya fito, Dr james ya dauki takardan ya ce Dis one is cleared, Everything is fine her, but i can see a minor ulcer, hakan ya faru ne na rashin cin abincinshi nd advisively yadaina shan giya coz zai iya jamishi wani ciwon, ba abunda suke son ji ba kenan, Jawad yace Dr HIV test zaka mai, we careless abt wadannan, Dr James yace just a minute, chan dan qaramin machine din yayi kara, hakan ya sa su duka maida hankalinsu gurin Dr james, Dr James yayi wani murmushi yace Dr Zailani, Congratulations, you are HIV negative,inshort u dont have any blood disease in you. You are all Okay.
_Bibilicious Biebee_
5⃣9⃣ 🏡Gidan Gandu🏠💕Biebee Isa💕 Zaid ya tashi da karfinsa, yace Dr, m HIV free? Dr James yace Yes, you are free frm anytype of Disease. Ihun murna Zaid ya sake, Maysah hawayen farinciki take, Ta na ma Allah Godia, Jawad ma farinciki ya bayyana a fuskarshi, Dr James yace Dr Zailani, m suprised y u dint bother to test ursef, jus bcoz uo wife is + it doesnt mean dat uo are positive too, ya kamata ace kasan hakan, Zaid yace Dr, the moment u told me abt her, i forgot everything, komai dauke ya min akai, kawai ni na sadakas ina da HIV, amma Alhamdulilah, Dr yace dama nasan babu, but to be more sure after l3months za a kara wani test din don tabbatar wa. Yace Ok, dr james ya rubuta mai maganin zazzabi, yace kuma ya kiyaye cin abinci, Ok Dr, can we go now? I have to admit u, no pls, i cant stay here anymore, Dr yayi daria yace ohh, ynx ka gane kan ka har kankamba ake ma Asibiti nah, yayi daria, yace toh ai na ji sauki ba abunda kr min ciwo, kaga gwara mu tafi, Dr james yace toh An sallameku. M expecting to see u at work tomorrow, Zaid ya marairaice yace m sick sir, kuma da na warke i zan zauna a gida kawai don na kula da my Amazing wife ko Zabin tsoho?, Maysah ta kai kanta kasa don kunya, duk sukayi daria, Zaid da kanshi ya kai kanshi kasa gurin da Jawad ya ajiye motarsa, don wani karfi yazo mai, dama fargaba ce ta maida shi haka. Suna isa gidan Jawad ya zube a parlo, Maysah ta yi hanyan kicin tace bari ta hada abinci, Zaid ya shige toilet don ramuwar wankan da baiyi ba na kwana 4...
Indomie ce ta dafa musu, haduwa sukayi kan table duka, zuba ma Zaid ba tare da ta kalleshi ba, tundazun yake son karantar ta, fir taqi yarda su hada ido, Fira sukeyi Jawad na basu labarin dawowan Mu'ammar, Xaid yace muma dai gobe za muje Maiduguri, Maysah ta dago kanta suka hada ido aikuwa idon zaid akanta, da sauri ta kawar da kanta tana murmushi. Wayar Jawad tayi qara, yace ohh god, ya dauka, yace hello baby, m so sorry, fadila tace shine kaki nemana koh? Jawad ya shiga bata haquri, yana wani narkewa yana shagwaba, yana fada mata how much he missed her, baki bude Zaid da Maysah suke kallonshi, ji yanda yake magana kamar mace,

25 / 29