Zayd yace yauwa Ruma ya ma sunan abun nan da kike samun a tea? Me kamshin nan, tace oh kanumfari, yace yauwa shi hajia ki bamu inaso, Hajia babba tace gaskia bandashi, sai dai in kakar ka Aishalle na san tana harka da kayan yajin nan, Hajia Ama da ke zaune ta na kallonsu tace eh akwai Kanumfari guri na, bari na je na kullo muku, Zaid yace ba sai kin tashi ba, a ina kika ajiye muje mu dauko ni da Ruma, ta musu kwatance ya ja hannun matarsa suka fita., Fadila tana ta jin dadi don ta nason tuwo, Jawad yace ina zaaje da wadannan tarkacen? Fadila tace Baby kaduna mana, yace wallahi ba zaa sa min mota yayi ta warin daddawa ba, ta turo bakih tace hajia babba kina jinshi ko? Hajia tace kai dallah chan ka bar dadi, ina ma amfanin wannan cimar da ka ke ci, banda tsotseka ba abunda yake kara ma a jiki, ka dage da cin abincin gargajiya, irinsu tuwon masara ko kayi kumari, amma sai wani abu da sunan ko dadi babu, ya sunan abun ma? Ko guiza yake? Duk suka fashe da daria, yace haba hajia sai ki bamu kunya, pizza ake cewa, tace kai ni rabani da abincin mayu da aljannu, duk suka fashe da daria. Mu'ammar yace indai ta ni ne to gaskia ki bar kayan warinki, ba maso koh Khairi? Islah ta sunkunyar dakai tana daria, Hajia babba tace yan Ingilan burauba, kun ma kanku, Ta kalli su Zayyad da suraj tace Wai ku tsaya ma, idan kunsan ba kwaso ku aje min kayana kar ku je dashi chan ku ajiye min nayi asara. Suraj yace mu muna cin tuwo gidan mu gaskia amma ba sosai ba, sai muna marmari ko honeybunch? Bilkisu tace eh muna so hajia babba, Zayyad yace no ni ina cin tuwo, ban son shinkafar nan, Umma hajja tace ai ni burgeni kakeyi Zayyad ba ruwanka da zaben abinci, kai dan gargajiya ne, yace gaskia ni komai aka dafa ci kakeyi, hajia babba tace kaji dadinka. Nan suka dan taba fira, sukayi sallama kafin suka nufa Sashen Tsoho don yi mai Sallama.
Nasihar ce dai ya qara musu, a karshe ya sa musu Albarka, suka shirya tafia, Mu'ammar da suraj da jawad da Zaid suka dauki hanya daya. Samir ya dauki hanyar bauchi, Zayyad kuma aka kaisu Airport.
*****
Zaria
Tunda ya shigo gidan yake kwala mata kirah, a parlor suka yi kicibus, tace YaAmar lafiya wannan kira haka? Yace close ur eyes, ba ta mai gardama ba, ta rufe idonta, ya sa mata wasu takardu a hannu yace ta bude idonta, ta bude Tickets to Cambridge England ne, ta zaro ido tace yaya? Yace i told u, m ready to sacrifice everything, akwai time zaki koma skool, nd i will apply for masters, still kuma i will find a job, we'll start allover there, we will build our home, nd i will give u the joy and happiness u truly deserve. Dadi ya kashe Islah ba ta san lokavin da ta rungumeshi ba tare da manna mai kiss a baki, tace i love u yaAmar, yace i love u more swrhrt.
Abuja
Time din da ya shigo gidan bata nan ta je skul, ya gaji sosai ya fada dakih, yana si Yayi baccin rana amma ya kasa, giyyarsa ya ciro cikin fridge ya bude zai sha kenan ta shigo da sallama, da sauri ya boye kar ta gani, DonAllah ya daura mai wani irin kunyarta, ba ya so ta ga yana shan giya, shiyasa tunda suka dawo daga Maiduguri yake sha a boye, ta ganshi ta ga me yakeyi. Amma ba ta nuna mai ta gani ba, sai a sannan ta tuno da maganin da tsoho ya bata. Ta qudiri a ranta yaum zatayi amfani da maganin, Allah dai ya as a dace. Yace Yaxayd ina wuni, duk ya bi ya daburce yace lafia lau, banji shigowarki ba, tace ina ta sallama ba amsa ai, ganin ya kasa sakewa da ita ya sa tace bari taje ta rage kayan jikinta, ta fita, tana fita ya kwankwade giyyarsa, daki ta shiga bayan ta cire hijav dinta, ta bude kayan ta, ta ciro ledan maganin da tsoho ya bata, ta shiga kichin ta shiga hada musu lunch, cikin jug din sobo ta juye maganin nan tas, ta kai dinning, zuwa tayi ta shiga kwankwasa mai, sama sama ya ke jinta don har ya fara bacci.Tace yazayd ga lunch na gama, ka fito kaci, cikin magagin bacci yace ki bari sai anjima, ta marairaice tace plss, yace ok lemme dressup, sai da ya fads toilet ya sakar ma kanshi shower kafin ya fito, kan table ya isketa, ta yi serving dinshi, white rice ne and sauce, ya ci kadan, ta zuba mai sobo ya sha sosai sbd yayi dadi, ba a fi 5 mins ba, ya ji zuciyarshi na tashi, Warin giya yake ji, Amai ya zo mai da gudu ya fads toilet ya dinga kwarara Amai ba tsayawa, Maysah sai sannu take mishi, sai da ya kusan minti 20 kafin aman ya tsaya, ya bata tausayi sosai, ta bashi roban ruwa ya sha ya kuskure bakinshi, ta riqoshi ta kaishi daki, ji yayi dakin na warin giya, yace ki kaini dakinki, haka ta miqar dashi ta kaishi dakinta, duk ya galabaita, Sai da yayi kwana 3 kafin Aman ya tsaya, duk ya rame ya qare, sai da wani colleague dinshi yazo Gida ya samai drip, randa Zaid ya warke ya shiga dakinshi ya fiffirto da dukka kwalayen giyan da na fridge yayi waje dasu ya cinna musu wuta, Maysah na kallonshi, dadi ya rufeta, nan take ta kira tsoho ta shaida mai abun da ya faru, shima yaji dadi, yace ai Zaid kuma da Giya har Abada, yanzu ko wani ya gani yana shan giya sai yayi Amai, don kyamar giyya yakeyi yanxu, Mijinki ya daina shan giya da Yardar Allah. Maysah tace Nagode Tsoho Allah ya bar mana kai. Murmushi tsoho Yayi ya kashe wayar..
(3months later)
Mrs Zaid hurry up, zaki sani latti fah, daga ciki tace just a minute Mr Zaid, yace ko na tafi? ta fito tana gyara zaman gyalenta tace ai na ma fito, Zayd ya matso yace u grw more beautiful every morning, murmushi tace ai ban kai ka ba, yace i love everything about u, murmushi tayi ta ce mu tafi kar Ka amsa query gurin Dr James, har zata shiga mota ya riqo hannunta, yace na sa miki ido wato ke ba ki san ido ba ko? Ta zaro ido tace yazayd me nayih? Oh baki san me kikayi ba ko? ta marairaice tace kayi haquri Yazayd, me nayi? Shima ya bi ya marairaice kamar yadda tayi, ya turo baki yace ban taba jin kin ce min i love u ba, waiyo Allah, kunya ta lulluba maysah, ya tsare ta da ido yace ehen ina jinki, ganin kunyanta ya motso ya saketa ya bude mata mota yace na lura akwai sauran kunyana a tare dake, a hankali zan cireshi, da sauri ta kawar da kai tare da yin murmushi.
Karfe 12 ya gama ganin patients a OPD, ya kalleta yace Mrs Zaid kin gaji ko? Ta girgiza kai tace Aa, ina kallon ka ne yanda kake duba patients cikin kwarewa, kaji dadinka Allah Girma, yayi murmushi, yace dadi na da Zabin tsoho akwai Adduoi kamar mutanen da, tayi daria, yace oya ta shi muje muga patients a ward, daga chan sai mu wuce gida, ta miqe ds sauri suka fita daga office hannun su riqe da juna, suna tafia suna birge mutane, wanda Suka sansi sai suce MrAndMrs Zaid, sai su daga musu hannu, a haka har suka isa Ward, Zaid ya shiga ganin patients dinshi, ita kuma tana basu kudi sadaka, ana ta musu godia, su ka fito, daidai wani daki sukaji wata murya na cewa Myzyd, myzyd, sai kuma sukaji wani irin qara daga dakin da gudu suka shiga dakin, Zaid ya kalli wacce ke kan gadon, da alamu rai yayi halinsa, ya tsura ma gawar ido yana so ya gane wacece amma ya kasa, fuskar ta chanza kamanni sosai Fusksrta duk yayi baqi fatarta ta fara kwayewa, kuraje duk sunyi fanchami a jikin, jikinta ba kyan gani, Zaid ya cire baki ya kira nurse, yace haka kuke barin patients? I dont think dis one is Alive now, nurse tace sorry sir, ta mutu, ai mutuwa hutu ne a gareta, patients din HIV+ ce, tunda mamarta ta kawota bata sake dawowa ba, kwanaki sai da mukayi cuffing hanayenta don cizgar gabanta takeyi ta na yagan fatar jikinta, Zaid ya girgiza kai waye likitan patient din? Tace ai Dr Maikudi ne, yazo ya dubata? Tace aa bezo ba, yace haba mana call him, dis patient needs RA, ya kamata a kaita Murtuary before ta koma wani abun, Rumah ki basu sadakan mu tafi, da alamu Zaid be gane ko wacece ba, Maysah da ta ganeta ta fashe da kuka sbd tsoron Duniya, dubeta da yar gayu, yar kwalisa mai iko da kasaita, dubi yanda Allah yayi da ita, tcae Yazayd baka gane ko wacece ba? Yace kinsan ta ne? Tace Badiyya ce, badiyya matarka ta da, wani uban tsaki Zayd ya buga ya ma badiyya wani mugun kallon tsana, yace die, Go to hell and burn to ashes, ya fizgo hannun Maysah yace mu tafi, haba Yazayd, lets help her, she needs us, Zaid yace me zan mata rai zan dawo mata dashi? Uwarta ta ajiyeta ta barta mu sai mu kwasa? Ka yafe mata pls, ta riga da ta mutu, ka yafe mata ko za ta samu wani saukin, yayi tsaki yace ke ya ka mata ki yafe mata sbd ke ta azabtar ni da taso azabtarwa Allah be ba ta iko ba, so sai ki yafe mata tace ni bata min komai ba, Allah bai barin irinsu, tace yazayd a dauketa a mata sallah, Da karfi zaid yace Rumaysah, shige mu tafi, sum sum Maysah ta wuce ta na kallon yadda gawar badiyya ya wulaqance lokaci guda a ranta tace Allah ya gafarta miki, ya ji kanki nidai na yafe miki. Zaid ko wurin be kara kallo ba, ya rufa mata baya, yace u reap wat u sow.
Maiduguri
Karfe 2 na dare, Zuciyarsa ta buga, da sauri ya bude idon sa saboda zafin da yaji, ya sa hannu ya dafe kirjinsa, rabon da yaji ko da ciwon yatsa ne an fi shekara 40, amma yau gashi zuciarsa har ta dara Zafih, tun bayan dawowarsa hajj yake jinsa wani iri, Musbahu Zailani yayi dan gajeran murmushi, a hankali yace wannan Ciwon Ajali ne.
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · 1 hour ago
Gidan6⃣2⃣ Gandu
Gidan Gandu by Biebee Isa Har karfe 4 Tsoho ya zauna zaman jiran mutuwa, ba mutuwa ba alamun shi, har ya far ji ana kiran Assalatu mutuwa ba tazo ba. Ya miqe jiki a sanyayaye ya nufi masallaci, sukayi sallah, ba wanda zai kalleshi yace yana da damuwa, amma shi yasan me ya ke gani. Dawowa yayi ya zauna kan kujerarshi a parlor, yan GIDAN GANDU suka dinga shigowa gaishe
hi kamar ko wacce asuba. Be nuna ma kowa wani abu ba don be son ya tads hankalinshi, kuma be yarda suyi dogon gaisuwa kamar da, da suka fahimci kamar be son magana da sun gaisheshi suke tafia, Hajia Babba ce ta shigo, ta zauna gefenshi, Alhaji barka da Asuba, yace karime ta musbahu, tayi murmushi yace zauna kiji, ta zauna, ya shiga mata fira yana bata labarai masu sanyaya zuciya, cikin dabara yace wai idan na mutu ya zakiyi? Tace chap Alhj ai bana son ma tunanin mutuwarka, na fiso na mutu kafin naga mutuwarka, don na san ina iya zaucewa, yace haba karime, sai kace ba musulma ba, ai kinsan Qaddara koh? Ashe ba so na kikeyi ba tunda mutuwata zata sa ki hauka, ya turo baki, tace Alhaji ni na san ba wanda ya kaini sonka, yace Ahap, ai in kina sona bazaki taba bari wasu suyi man kuka ba balle ki, Addua kadai ce mamaci ke buqata, tace wai tsaya Alhaji, wannan maganganun na meye ne? Yace in banda abinki karime waya san gawar fari? So ake ko da yaushe bawa ya zama cikin shiri, Hajia Ama da Umma Hajja sukayi Sallama, suka amsa musu, suka zo suka gaids Tsoho, suka gaisa da hajia Babba, Duk yanda Hajia Ama taso ta hada Ido da tsoho ta kasa, tsoho ya qi yarda su hada ido, haka kurum taji gabanta na faduwa, ta daure tace Alhaji lafia kake? Murmushi ya fara yace Kalaw nake Aishalle, tace Anya? Hajia Babba tace ke ma kya fada, yanzu ya ke min magana me kama da wasiyya, duk na rasa gane inda maganar tashi ta dosa, Umma Hajja tace Alhaji ko wani abun ke damunka? Ka fada DonAllah, kar kayi nauyin baki, yace ku saurara kuji, shi fa bawa so ake ya zama cikin shirin mutuwa a ko da yaushe, balle mu da mu ka kwana biyu, mun tsufa, ba a sa gawar fari ba, ko ba haka ba? Duk suka gyada kai, to ku kasance masu dangana, ku kasance masu, tsoron Allah, ku kasance masu tuna mutuwa, tsoho ya saba musu irin wannan nasihar, to sai suka share fargaban da ke ransu sai suka dauki wannan nasiha ce kamar wacce ya ke musu kullum. Kuma ina roqon Allah ya hada min Hajjo, Aishalle da karime a matsayin Mataye na na Aljanna, ko a Aljanna baku ba kishiyoyi, ku din kenan duk suka yi murmushi, sukace Amin Alhaji Allah ya hada mu duka a chan, yace Amin Matayena, sanyin idanuna. Ku tashi ku tafi ina so na dan koma bacci, duk jikinsu yayi sanyi, sun san cewa idan tsoho ya farka da Assalatu be koma wa wani baccin sai wani daren, Amma yau yace zai koma, basa son sa abun a ransu ne shiyasa suka fita jiki a sanyaye.
******
Ya kalle su su sha takwas, tara maza tara mata, ya kalli yanuwanshi da ya riqa su biyu tun suna yara, ya juya ya kalli yaran Danuwansa Rabiu, su 5, yan ukku da yan biyu, sannan ya juya ya kalli yaransa. Sai ya saki murmushi, yace Alhamdulilah, duk suka zuba mai idanu, yace kunsan ba abun da ya kai Hadin kai dadi? Hadin kai wani abu ne idan da akwai shi a wuri, to ba abunda ya kaishi dadi, idan anaso a samu hadin kai to dole ku zama rufa ma juna Asiri, Dole ku zama masu yarda akan shawara daya, dole ku bi na gabanku, dole ku so junan ku, dole ku zama daya, dole ku zamo tsintsiya ma daurinki daya. Sai abu na karshe, dole ku tsaya akan junan ku ina nufin masu taimaka ma juna, idan kun hada wannan to kun samu hadin kan junanku. Jikinsu yayi sanyi, Aunty Abida ta fashe da kuka, tace Baba wani abu ya faru? Ko baka da lafia ne? Tambayar da sauran ke son yi kenan, yace bakomai Abida, Nasiha ce da na saba yi muku yau da kullum, Aunty Nuratu tace amma ta yau ta sha bambam, Baba ba ka lafia, ko a kira Dr Munnir? Yayi murmushi yace idan mutuwa ma zanyi Dr Munnir ya isa ya hana? Suka girgiza kai, ba wanda ya san gawar fari, ni dai ku hada min kanku, ko da ace wata ran bana nan, a duk inda nake Zan kasance mai Alfahari da ku, ku bi manyan ku, Mudassir da Labaran, sai yan 3, na baku Girma, na baku shugabbancin wannan Gida, Ku kasance Adalai, ku cire son kai, ku kasance masu son junanku. Baba Hassan da ya gane inda zancenshi ya dosa, ya rarrafo ya kama kafarshi yana kuka, yace Baba, kar ka tafi, ban mu taba kukan rashin mahaifi ba, kaine mahaifin mu, kai ne gatan mu, kaine katangar mu, kar ka tafi baba, idan ka tafi ya zamuyi,? Wa zai ciro mu daga baraka idan mun fada, Tsoho yayi daria sosai, yace kai hassan, wai kai yaro ne? Ka manta kuna da yara masu girman Zayd da Zayyad? Ku zaku kula da kanku, ni na gama nawa, ku ya rage kuyi naku, Hankali na na kwance ne saboda nasan kune manyan gidan nan, ba zaku taba bari Zuriyata ta gaiyara ba, zaku tashi tsaye kamar ina raye. Abunda nake so daga gareku shine Adduarku, da neman gamawa lafia, Aunt Sadiya na kuka tace ai wlh ka ma gama da dunia lafia, don ni na fi sa ka a cikin Shariffai, tsoho ya katseta, yace Aa Halimatuwa, kar kice haka, ba wanda ya san gaibu, ni dai Adduarku nake bukata, kuma bansan yan kuke kuken nan, ba zan ji dadi ku dinga min asarar hawayenku ba, bana son kukan ku, Baba Abbakar, ya fashe da kuka yace baba ka yafe mana, yace kul Abubakar, ba ku taba bata min rai ba, amma duk da haka na yafe muku Allah ya muku Albarka, ku tashi ku tafi, suka tashi jiki ba kwari. Sukayi Gaba, ya kira baba hassan, a hankali yace mai Be Strong Hassan, u are d Man here, kuma banason zaman makoki kaji? baba hassan ya kasa cewa komai sai daga kai da yakeyi kamar kandagare, ya fita da sauri.
Magana ta zagaye Gidan Gandu, duk iyaye sun kira yaransu da ke wajen gari sun sanar dasu, wurin 7am Aunty Abida ta sanar da Zaid, murmushi yayi yace tsoho na son cimma wani abu ne, tace bangane ba, wlh abunda yake bari is more like wasiyya, zaid Tsoho na fama da internal pain, but becoz he loves us dat much ya kasa sanar damu, Zaid m scared to loose him, i love him, gaban zaid ya fadi, yace Mom noone is loosing Anyone, gamu nan zuwa. Hankalinsa ya tashi, ya shiga tada Maysah a hankali yace tashi mu tafi tace ina? Maid, lafia? Yace tsoho ne, wai be lafia, wani tsalle tayi ta fada toilet, donyi wanka, Zaid ya kira Jawad, jawae a rude yake yace ai gashi nan sun dauki hanyar Maiduguri, tun dazu Samir ya kirashi ya gaya mai, Zaid yace nima ga mu