Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   8 / 29

21K to 24K   out of 85.7K words

kai, tace Yasuraj wallahi tallahi ina sonka, zan auri Ya Jawad and zaka auri Bilkis, idan muka gudu, mukaje aka daura mana aure me mu kayi kenan? Mu bijire ma iyayen mu? Bakin cikin mu ya kashe tsoho? Gaban ya cigaba da wanzuwa frm generation to generation? If we leave, they will be seperated forever, maybe this f only way to End our Family’s Malice, Ka roki Allah ya sa hakan yafi Alheri, And Allah ya ba mu ikon rungumar wannan Kaddarar, tana kaiwa nan ta ruga da gudu. Tayi sashensu, A hanya ta ci karo da Bilkisu da ta fito daga Sashen Tsoho, taja ta tsaya, Bilkisu na watsa mata harara, tace listen to me Fadila kar ki ga kamar Gobe Zaki zama Mallakin Yajawad kice zaki zake, ki kira kanki matarshi, to bari kiji Yajawad nawa ne, Aurenku suna ne kingane? na dan wani lokaci ne, idan komai ya daidaita zai sakeki ya aureni, so i want u to keep ur distance, ban yarda ayi seducing masoyina ba. Fadila tayi murmushi ta shar hawayenta. Tace Bilkisu bana son Jawad bana kaunarsa toh mesa xanyi tunanin Jan hankalinsa ko ra’ayinsa? Kuma da kike cewa nan ba da jimawa ba zai sakeni, kin ga na miki kama da wadda zata zama bazawara in future? in kinso ki ka she aurenki ki zama bazawara, ki sami wani miji amma badai Jawad ba, i dont love him but i will make sure dat he never ever gets back to u get dis into your thick skull Jawad ya miki nisa. tayi gaba ta barta bakih bude tana mamakin karfin Halin fadila ita da ba sonsa take ba.
*****
Islahulkhiar kwance a green carpet din field din Gidan idonta lumshe, tana tuna moments dinta da Samir, time din da suke kwallo, ko kwallon kwando ko skipping rope, Maganar Hajja Ama ta tuna inda take cewa _kuyi haquri da wa’enda aka zaba muku, ku roki Allah ya sa sune Alheri, ku Maida Soyayyar masoyan ku a kansu, ku maida Soyayyar Masoyanku Soyayyar yanuwantaka don ku Yanuwan juna ne Allah muku Albarka_ islah ta matse hawaye tace Allah kasa Ya Mu’ammar shine Alheri a gareni. Tsaki taji an buga tsuuu Ta na dagowa taga Amira da Hanifa. Amira tace lallai kam kin ma kanki Kiyamul laili, gwanda da kika haqura da Yasamir, don nice matar da aka zaba mai. Gwara da kika dangana Allah hada kanku da Ya Mu’ammar din Islah ta girgiza kanta ta miqe ta kakkabe jikinta tayi gaba don bata son hayaniya. Hanifa da qarfi tace aikin banza, ko me zakiyi Ya Mu’ammar ba zai taba sonki ba, ni yake so ni kadai, jini na ke gudana a zuciyan shi, da komi ya daidaita zai sakeki ya aureni, dan ba zai taba hada iri da dangin mayu da aljanu ba. Chak Islah ta tsaya, kamar ba zata yi magana ba kuma sai ta dawo da baya, ta tsaya Daf da Hanifa tace, Wai tada jijiyoyin wuya na meye ne? Naga dai tsoho ya san dake ya zaba mishi ni? Duk da jinin naki na gudana a jikinshi, ki bari ya sakeni mana yazo ya aureki kafin ki gaya min magana, but as far as m concerned ni zai aura Gobe, nd m d choosed person its not my fault dat m more beautiful and talented dan u, its not my fault dat i’m chosen for him, so Maybe tsoho ya ga rashin dacewar ku ne ya zaba mishi ni, if u have a problem go meet Tsoho, amma idan zaki bi shawara ta, ki koya ma kanki Son YaZayyad don Ya Muammar will never ever come back to u, tana kaiwa nan tayi gaba ta barsu baki sake, chan kuma Amira ta pashe da daria, kaii ashe Islah na da baki haka? Wai its not her fault wato shes more talented nd more beautiful dan u, ooo Islah got attitude, Hanifa takaici goma da ashirin, ashe wannan haka take? Ai bata taba zatan zata tanka mata ba, Ga haushin darian mugunta da Amira ke mata. Ji tayi kamar ta sa Ihu don takaici.
********

A yau Jummaa Wurin Huduba Liman yayi sanarwa za a Daura auren Jikokin me Masallacin nan, ana buqatar kowa ya tsaya bayan an Idar da Sallan Jummah. Haka kuwa akayi, ana Idarwa aka daura Auren ZAYYAD da HANIFA, ZAID da RUMAISAH, JAWAD da FADILA SURAJ da BILKIS, SAMIR da AMIRA da kuma MU’AMMAR da ISLAHULKHAIR bisa Sadaki dubu Hamsin lakadan ba Ajalan ba, aka shafa kuma aka wadata su da Rengem na shinkafa(lol) Tsoho baki har kunne, Angwayen kuwa kadaran kadahan duk da Mu’ammar da Jawad ba su tsaya daurin auren ba. Nidai nace oho dai an riga da an daura. Ko da ku ko baku sai da Tsoho ya Daura muku aure

_Bibilicious Biebee_
Like · 1 · Reply · Report · Aug 4
Phatee Lamin
20. Gidan Gandu by Biebee Isa
Daren da Aka daura Auren abu dunia ya ishe Sabin maauratan, da Angwaye musamman Amaren, daga Zaid sai Amira kadai ne basu da wata damuwa sosai ko wannensu na sashensu jikinsu duk yayi sanyi.
Kuka wiwi Rumaysa keyi, Shikenan me afkuwa ta afku, YaZayyad ya mata nisa, yanxu YaZayd ne mijin ta. Allah ka ba ni ikon Cin wannan Jarabawar. Amma ce ta dafata da sauri ta share hawayenta don bata so Amma taga kukanta hankalinta na iya tashi, Amma ta mata murmushi cikin hausarta da har yau be fita tace Maysah kuka kike yi koh? Tace Aa Amma, Amma tace liar, na ganki kina kuka, kamar jira take ta fashe da kuka, Amma ta rungumeta sai da ta yi me isarta, tace Amma Yazayd Dan iska ne, Mashayi kuma Maz— Amma ta dakatar da ita ta hanyar sa mata hannu a bakih, Sai kuma ta mata murmushi tace Maybe ke xaki kubutar dashi daga sinful acts dinshi, ki nuna masa hanya madaidaiciya, Amma how? I cant, Amma tace shhh, mya Baby i trust u, u can even do more, Have Faith kinji? Ta gyada mata kai. Tace Oya tashi tsoho ya aiko A kiraki nace kina wanka, tashi kijei, jikih ba qwari ta daura dankwali ta fita. Amma ta bi bayan tillon diyarta da ido, tausayinta ya mamayeta, Allah ga Baiwar ka nan, Allah ka shige mata Gaba Amin..
******
Tsoho ya kalleta yace Rumah Nah, ba tare da ta kalle shi ba tace Naam Tsohona, yayi murmushi yace yau ko kallona ba zakiyi ba? Ko har ynz fushin akeyi dani? Ta qaqalo murmushi, haba Tsoho nah, wani irin fushi a na zaune kalau, ya girgiza kai yace Rumah kenan, my favourite among them all. Tayi murmushi, yace A tunanin ki na shiga tsakaninki da farincikin ki na hadaki da baki’n ciki, A Ganinki na hadaki da kunama me zafin Halbi, na san xakice anya Tsoho na sona? Ya hadani da Mashayi kuma Mazinaci? Maysah na san abinda nakeyi. Allah yayi yarinya me hankali, me tunani, me hangen nesa, da sanin ya kamata uwa uba ga ki da Hakuri, kinyo gadon kakarki Aishalle, Auren Zaid Jihadi ne, ke kadai zaki iya hakuri da halayenshi, ke kadai zaki tsaya tsaye a kansa har Allah ya sa ya bar halayensa, kuma nayi istihara tun kafin nayi hadin nan, naga Aurenku Alheri ne, Kece Rufun asirinsa. Rumah kin fahimce ni? Maysah ta daga kai tana kuka, tace eh Tsoho, Allah ya bani iko Allah ya sa hakan yafi zama Alheri tsoho yace Amin Rumah nah, sannan Abu na gaba, munyi magana da Mudassir yace Zaid zai fara housemanship dinshi Nextweek a Abuja a nan National Hospital, Asibiti ta bashi Gida, Amma na baku daya daga cikin gidaje na na Maitama, na yanke hukuncin dake zai tafi, sai ki fara Shirin tafia, gaban Maysah ya bada Hinqim tace Allah kaimu. Yace Amin, Gani yayi sai Kyarma takeyi, hakan yasa yace toh kina iya tafia, sannan Akwai Taron duka Gida Gobe da Safe Misalin Karfe 10 na safeh. Tace toh Tsoho Allah kaimu Goben. Yace Amin Ta miqe guiwa a sake ta bar Dakin tsoho.
******
Wallahi da an san yanda na tsana ganin Fadila da ba a yi gigin hada auren nan balle a daura, wlh na kijininta, Bilkisu tace ni wai ya ma za a aura mun Azzalumi kamar Suraj, ji dai randa ya kamamu ya zane, wlh na tsaneshi, Mu’ammar da yake ganin kamar ya fi su tashin hankali, babban tashin hankalinsa kuwa shine ganin an daura auren Hanifa da wanninsa, Zaid kuwa ba abunda ya damesa, chatting dinsa yake da Diyyan Shagali. Amira kuwa ta maidasu TV sai kallo take wannan yace ka za wannan yace kaza. Aunty Saadiya tace hajiar mu kice wani abu mana, toh dan ubansu sun ishe mutane da surutan banza su saman ido mana suga yanda zan warware alamarin nan, jira nake na ji ta bakin Alhaji, sai na san abunyi, Amma sun tasa ni gaba sai babatu suke tayi, ba sai na sa musu ido ba, Aunty Abida tace ynz dai haquri zamuyi gabaki daya, Sai mu jira muji me baban zaice gobe. Kun gane koh? Duk suka gyada kai, Amar yace hajia me zakiyi ke goben, ni burina a warware auren nan kawai, hajia tace kai dai ka bari sai Goben u shud all trust ur Grandma. Hajia Babba Ta kalli inda zaid ke zaune tace dan gidana Yaya dai banji kace komi bs? Ya kalleta ya watsar yace ban da ta cewa, tace wai ni mesa kake man haka ne? Miqewa yayi yace Jawad ka kirani idan baba ya dawo ya fice daga parlon, hajia babba ta hau masifa ina sonka kana gurxa man, sai wulaqancin tsiya shege me qiran samudawa, kowanensu sai da ya dara..

Gabaki dayan su sun Hallara parlorn tsoho suna zama jiranshi, da sallama ya fito daga dakinsa suka amsa mai, kujerarsa ya zauna aka fara kwasar gaisuwa, sai da aka gama kafin yayi gyaran murya tare da gajeruwar Muqadima, yace Ahhh A jiyan ne aka daura auren Jikokina su 12, Allah sa Alheri, ‘yan dakin hajia Ama da Umma Hajja kadai sukace Amin, Hajia Babba kuwa sai hura hanci take tayi, abu na farko, ya kira Hanifa yace taso nan, ta miqe ta nufeshi ya ciro wata envelop ya miqa mata kamar ba za ta amsa ba ta amsa yace dubu 50 ce sadakin ki ne, jiki ba qwari ta koma mazauninta ta xauna, haka ya kira Bilkisu, Islahulkhair, Amira Fadila da Rumaysah ya danka musu sadakin su a hannu, Sannan yace Ahh gobe lahadi, nasan gobe yan mazan zasu koma bakin aikinsu, to na yanke hukuncin kowannensu zai tafi da matarsa, Jikokin Hajia Babba suka zuba mata ido alamun zasu yi magana hannu ta daga musu alamun suyi shiru, bari taga iya gudun ruwanshi, Tsoho ya cigaba na bada kudadde zaaje Dubai a ma yanmatan kayan daki da na kitchen, da kuma lefe kuma na mallaka ma mazajen Gidaje a duk garin da suke aiki, Sannan kuma na chanza ma kowa mota nd kuma. Toh ina umurni da matan su Shirya, gobe zasu bi mazajensu… Hajia Babba tayi karaf tace kagama? Haba Alhaji? Ran tsoho a. Bace yace Karime menene haka? Tace bangane kowa ya bi mijin shi ba? Sbd me? Daga daurin aure jiya, sai kace an gaji da su,,, ta cigaba da bambami, Tsoho ya fara tarin karya kamar xai shife, tarin da karfi, kuma sai Allah ya kawo mai atishawa me zafi, ai nan hankalin kowa ya tashi, Hajia karime ta rude, sannu Ahaji, Baba hassan ya ruga firij ya dauko ruwa yana fadin Baba sha ruwa, ya ture ya shaqe murya yace ba ruwan da zansha ai haka take so ta ga karshe na koh?toh bazan sha ruwan va, ku barni na mutu kawai tunda ba za a mun yadda nakeso ba, ai nan ta fita hayyacinta, ta fara cewa ya haquri Alhaji, danAllah ka sha ruwa, wlh ko ynz kace su tafi zasu wuce, daman wai naga ba a shirya ba ne, amma yadda kace hakan zaayi, Allah ya huci zuciyarka, danAllah ka sha ruwa, Tsoho ya kurba Ruwan nan taro ya watse bayan an Tsaida maganan gobe kowa xai wuce da matarsa..
*****
Mu’ammar kamar zai yi hauka, fadih yake Hajia wai menene haka? Bangane ba? Ya akayi kika amince masa? Hajia babba tace dan ubanka so kake mijina ya mutu, haquri kawai zakuyi ku tafi dasu din, bayan sati 1ko 2 ku danqara ma shegu saki 3 3, da dadin bakih da jan magana suka amince da tafiar

Hajia Ama da Umma Hajja ne zaune parlorn Umma Hajja su ka tasa Jikokinsu gaba suna musu nasiha me ratsa jiki da ban haquri, tare da jadadda musu haqqin zaman tare da na auratayya, Da kuma ban Haquri, duk wanda yyi haquri zai ci ribar rayuwa a karshe suka samusu Albarka, sannan sukayi umarni da yanmatan suje su hada kayan buqattunsu kafin a aiko musu da wasu, haka suka miqe suna matsar Kwallah kowa yayi sashensu don shirya kaya..

RANAN

_Bibilicious Biebee_
Like · 3 · Reply · Report · Aug 4
Phatee Lamin
21. Gidan Ganduby Biebee
Tsoho ya kalli Aunty Nuratu da Aunty Zainab yace ku zaku raka Rumah Abuja dukda shi Zaid din yace sai Gobe litinin zaiyi reporting so tafianku sai gobe, ke Abida da Hassana zaku raka Islahulkhair gidanta da ke Zaria, Hussaina da Sadiya ku zaku raka Amira gidanta dake Bauchi, Raijana da Maryam ku xaku raka Fadila gidanta dake Kaduna, Yusrah da Rafiyyah kuma zasu kai Bilkisu gidanta dake Kano. Zayyad kuwa zai dauki matarsa Hanifa su tafi chan gun aikinsa a lagos… Ban san tashin hankali, Amare kawai nace a kai gidajensu bance ayi tsegunguma ba, ku tashi ku tafi, Allah ya tsare hanya. Suka amsa da Amin, nan fa aka fara bankwana masu kuka nayih, barin ma Islah, rumah da fadila da suka rungume juna suna kuka, sun ba kowa tausayi, don shaquwarsu ya wuce misali, ko tsoho kansa sai da ya share hawaye. Da qyar aka tura Fadila motar Ya jawad Aunty maryam da Aunty Raijana suka shiga baya, jiki Ba qwari ya Jawad ya zo ya durqusa gaban tsoho Tsoho ya mai Adduan Allah ya tsare, haka ma akayi da Islah Aunty Abida na huran hanci ta shiga motar don bata son tafian nan take ba. Haka Ya Muammar ya shiga motar bayan tsoho ya mai Addua, Yaya Yusrah, da Yaya Rafiyya suka ja Bilkisu zuwa motar Suraj, inda yaje yayi bankwana da kakaninshi kafin ya shiga motar Tsoho yace to ku tunda tafiar ku hanya ce kuna iya tafia. Allah ya bada zaman lafia ya kawo kazantar dakih, ba wanda ya tanka mai, Suraj ne ya fara jan motar sanna Mu’amar ya bi bayanshi sai jawad ke qareshe, Convoy sukayi suka bar gidan mudai sai dai muce safe journey.
******
Baba usman ne ya kebe da samir inda yake cewa Samir kaga kai da na ne, sbd Zainab kanwata ce ita ke bi mun, Akwai shaquwa tsakanina da Mahaifiyarka, ina so ka riqe min Amanar diyata Amira, donAllah kayi haquri da halinta, quruciya ce da sakarci ke dawainiya da ita A sannu zata dawo daidai, Samir ya hadiye miyau me dacih, wato kowa yasan Amira bata da wayau, har ana hada shi da Allah yayi haquri, wato yayi ta haquri shi yana cutuwa, da qyar yace ba komai baba, yace yauwa Samir Allah bada zaman lafia, Anya ba zaku bar tafian nan gobe ba ku bi jirgi? Yace aa bari mu ta tafia ynz, ina da abunyi gobe a office yace toh Allah muku Albarka, Samir yayi bankwana da kakaninshi, ya kwashi Amira da Aunties dinta biyu da zasuyi mata rakiya zuwa Bauchi state.
******
Gudu suke ta shatatawa, ba me cewa juna qala. Balle duk motan ba sa shiri, dama dama motar Suraj Rafiyya da Yusrah Kawayene su kan taba hira. Amma tsohon nan akwai hadin doya da manja. In banda dole me zai hada Aunty Abida da Aunty hassana a mota guda? Haka dai suka daure kowa na kai zuciya nesa har Allah ya kawo su Kano lafiya Unguwar Nassarawa GRA, Gida ne da ya amsa sunansa Gida, a yau ne Tsoho ya mallaka ma Ya suraj gidan nan, ko da suka iso maaikata sun gyara gidan sun kalkale, Fadila da Islah suka fito don kama ruwa, Aunties ma duk suka shigo banda Jawad da Ammar, Yaya Rafiyya tace ku Jawad ba za ku shigo ba? Ya gimtse fuska ganin An kawo bilkisu gidan waninsa be ganin zai iya shiga yace no yaya wadannan ma su fito mu tafi kar maghriba ta mana, yaya yusrah dai ta tabe bakih, tace ina kano ina kaduna? Mu’ammar ne ya yi qoqarin shiga ya dan leqa gidan, auntt tace ku ku muje ko? Kun san tafia mun da nisa, duk suka mimiqe, Islah ta kama hannun Bilkisu ta mata Sallama tace Allah ya hada fuskokin mu da Alheri, Harara bilki ta jefeta dashi, Fadila ko kallo bilkin ba ta isheta ba suka bar dakin, Bilkisu ta rungume Yayanta ta na kuka, Yaya pls kar ka tafih, bana son nan, Muaamar ya share mata hawaye a hankali yace dont cry sis, kin manta abubda Hajia babba tace? Dis is for a short period of time okay? Jus take care of urself Ta gyada kai u too, Suraj na kallonsu ya tabe bakih ya kaufa kai. Mu’ammar ya fita. Haka suka qara daukan hanyan Zaria, in less dan 3hours suka iso Zaria, Cikin gari sukayi Kuyambana Lowcost, inda Tsoho ya ba Mu’ammar gida, haka dai suka shiga gidan suka firfito har yan motansu Jawad, shima dai ya fito, suka nufa ciki, Akwai dan Kurah a gidan suka kakkabe, don shi Mu’ammar ya qiyin waya a zo a gyara. Bayan sun dan huta ne su Jawad suka musu Sallama hardasu Aunty Abida da Hassana don gobe zasu bi flight din maiduguri kuma ta kaduna zasu tashi, Islah ta sha kuka sosai, don ba wanda aka bar mata daga ita sai Muaamar, tana kallonsu suka shige mota suka nufa Kaduna, suna barin gidan shima Mu’ammar ya bar gidan don bejin xai iya kwana under same roof with wata idan ba Hanifa ba. Nidai Bie nace Islahulkhair u are on ur own oo

Gab da Isha’i suka shigo

8 / 29