Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   2 / 29

3K to 6K   out of 85.7K words

Aishalle, bisa sadakin silallan zinari 5, Hajjo ta gyara Aishalle, da daddare Musbahu ya shigo Sashen qaninshi yace ma Hajjo ta shigo da Aishalle sashen karime zai hada su, sai da gaban hajjo ya fadi kafin tace toh Yaya ga mu nan zuwa. Wuce wa yayi sashen karime, tana xaune ta na shan rake ko Isha’i ba tayi ba. Mallam sannu da zuwa, tace yauwa karime rake ake sha, e wlh zaqin tsiya kana sha? Yace aa, yo daga ina kake haka sai uban qamshi kake zubawa, rabon da na ganka tun safe? Kafin yace komai su hajjo suka shigo da sallama ya amsa, karime tace wai meye? Da daddaren ma ba za a barka ka zanta da mijinka ba? Hajjo dai bata ce komi ba, Aishalle kuwa gabanta ya tsanta bugu, hajjo wace ce wnnan sai noqe noqe take kamar manahuka? Musbahu yace Karime, tace naam mallam, zaki tuna fuskar nan? Hajjo bude mata fuska, Hajjo ta bude mata fuska, karime tayi zumbur ta miqe, oh Allah Musbahu wai kai ina kake samo aljanai masu tsigar mayu! Haka kwanaki ka kawo wata mayyar, ai gwara wanchan akan wannan! Wannan ai kynta ya shahara, danAllah kiyi haquri baiwarAllah, ai kuma Allah ya hallice ku Duk da bansan me mijin nawa ya miki ba amma kiyi haquri, ta ba musbahu daria sai da ya dan dara, yace Karime wannan ce na kawo miki ita kwanaki sunanta Aishalle, kuma a yau ta zama matana saboda na aureta, Karime ta daka tsalle ta chakumo wuyanshi,/Ni zaka munafurta ni zaka ci ma amana? Idan ka isa Allah ya tsinen, babban balaeen chan, sai ta sakeshi ta wawuro sandan rake ta maula wa hajjo a baya, hajjo ta gantsare baya, ta yo kan Aishalle, yau sai na daddaki kashin babba buraubaki, Cikin zafin nama musbahu ya damqota ya jefar ya nuna ta da yatsa, karime ki kiyayeni karime ki fita idona, ta yo kanshi ta chakume shi, na rantse yau sai ka sakeni idan baka sake niba ba ka haifu ba, wlh sai ka saken, yace karime na sake ki saki daya, ihu ta sake da qarfih tace na shiga uku, daman basona kqke ba? Shege tsinanne laananne, ta figi zanenta ta bar gidan da gudu ko tsoron dare bata yi.
Ya kalli Hajjo tace Hajars kiyi haquri ni na jamaki ko? Tace bakomai Yaya, yace nagode ki jeki wanke fuskanki kar ki sa su hassan damuwa tace to yaya nagode sai da safe, Aishalle Allah ya tashe mu lafiya.
Like · 1 · Reply · Report · Aug 3
Phatee Lamin
****
Bayan Wata Biyar
Zama suke cikin so da qaunar juna, abu na Allah Aisha na dauke da cikin Wata 4, Hajjo na kula da ita sosai, su Hassan na sonta Goggo Amarya suke ce mata, Hafiz na ce mata Goggo Ama sbd shi yana da tsamin baki, haka kuwa kowa ke ce mata Goggo Ama, su Mudassir kullum suna gidansu karime suna kai mata rahoton abun da ke wakana cikin gidan, ta dau alwashin raba Aishalle da gidan nan amma bokanta ya shaida mata Aishalle ba zata taba barin gidan nan ba, kuma ya hango yaranta da jikokinta cikin wannan gidan, kuma duk wanda Musbahu zai aura a bayan Aishalle yake don sonta a cikin jininshi yake, Hankalin ta ya tashi ainun, babban baqin cikinta be wuce yanda Musbahu yayi watsi da ita, a tunanin ta zaizo yace a maida aurensu amma shiru, gashi uwarta ta rasu, abinci ma gagaranta yakeyi, haka ta samu babanta tana kuka tace sai dai yaje ya ba Musbahu haquri a maidota, yace shifa ba inda zaije, ba zata maidashi tsohon banza ba Nan ta fashe da kuka tana tirje tirje, don yaga uwarta ta rasu shisa be damu da ita ba, ya fi son hajjo, duk da Hajjon ba diyarsa bace, tsakanin da da mahaifi sai Allah, zuciyarsa ta karaya, yace zai ma Musbahu magana. Da kanshi yaje kasuwa gurin Musbahu, Musbahu yace haba baba ai da ka aika an kirani yace bkmi, nan ya gaya mai abunda ke tafe dashi, ya danyi jimm baba yace idan baka so dole ta haqura bawai ina maka dole bane, yace lahh bakomi wlh ni ko ynx a shirye nake a maida auren mu.
Haka kuwa akayi ba a jima ba aka maida auren, bayan ya samu Aishalle ya mata bayani ta nuna mai bakomi, amma ta shige dakih ta ci kukanta hajjo na lallashi,. Daga bangare a ka fidda ma Karime dakih ciki da parlo, rananr da tare su Mudassir dadi kamar ya kashe su uwar dakinsu ta dawo, nan ta rada musu wanih abu kunne suka hau shewa…
******
A yau Aishalle ta suntulo danta kyakyawa me kama da babanshi da taimakon hajjo da na umm aneesa, ko kallo basu ishe karime ba, amma hauka ne kadai batayi ba, takaicinta ya akayi Ama ta riga ta haihuwa kuma namiji? Musbahu baki har wuya yau ya gudan jininshi, Rannan suna da yaci suna Aliyu. A rannan ne karime ta tashi da wani kitifi wai ita ba ta san qanshin ragon da ake soyawa, maqota basu bi kanta ba don sun san halinta sai da suka ga tana amai suka temaka mata, a ka kira ummu aneesa don ta dubata, gwajin farko ta gane karime na da juna biyu. Aifah tun lokacin karime aka fara salon iyayi da kankamba, ba ta san wannan ba ta san wanchan. Har Allah ya sauketa lafiya, amma tayi baqin cikin ganin mace ta haifa, Musbahu ya nuna farincikin shi ranar suna diya ta ci suna Abida. To daga nan Aishalle da karime suka fara gasan haihuwa, duk shekara sai sun haihu, sai da Karime tayi mata 2 Sadiya da Zainab kafin tayi namiji daya Usman, ita kuwa Aishalle bayan Aliyu ta haifi Umar da Abubuakar sai mace daya Maryam tun daga maryam Ba su sake haihuwa ba. Maryam din Ama na da shekara 7 Hajjo ta qara haifan Yan biyu mata, Hassana da Hussaina, Aishalle kam kamar ita aka ma haihuwan nan murna kamar mene, tace wlh Yaya Hajjo ke er baiwa ce, daga yan uku sai yan biyu dama ni, tace kema Allah xai baki….
*****
Hannun hajjo saqale da nashi, kuka take tayi jin abun da ke fita daga bakin mijinta, Hajjo na so na zame miki Gata har qarshen rayuwarki, amma da alamu kwanana yana gab da qarewa, tace wai rabiu me kake cewa haka? Cuta ba mutuwa ba fa? Hajjo kenan sati biyu kenan ina fama da ciwon cikin nan, nidai dan Allah kayi shiru, Hassan ne da qanenshi suka shigo dakin ganin mahaifansu na kuka yasa suma suka fara kuka, Da qyar rabiu yace hassan Allah muku Albarka, jeka kira mun babanka, da gudu ya fita sai gashi ya dawo da Musbahu da Aishalle a rude, Asha Rabiu ciwon ne haka? Sannu yace yaya ka yafe man idan na taba bata maka, Yaya ga Amanar iyalai na, na san zaka kula mun dasu, Kafin Musbahu yace wani abu rabiu ya cika yace ga garin ku nan, Tashin hankali.
4. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, shi ne abunda Musbahu ke maimaitawa, Hajjo kuwa don rudu kasa kuka tayi, Musbahu yayi qrfin halin fita kiran maqota don a suturceshi cikin awa da be wuce daya aka kai Rabiu gidanshi na gaskia, kafin aka zo zaman makoki, Karime ta dan rude da farko amma daga baya sai ta gyagije wai Allah ke kama maqiyanta ta hanyar kashesu.
******
Bayan Arbain; Musbahu ya rungumi iyalan marigayi qaninshi, dukkansu ba wanda be zuwa makaranta banda Hassana da Hussaina.
********
Bayan wata 5
Aishalle kince kina son muyi wata magana? Tace eh Mallam, daman wani abu na hango, yace me ke nan? Tace Me zai hana tunda Yaya Hajjo tagama Takaba me zai hana ka aureta? Ina ganin ta hakan ne zaka fi kula da ita kuma ka riqe amanar da qaninka ya bar ma, ya tsura mata ido, dama chan yayi wannan tunanin amma yana tsoron abun da zaije ya dawo shisa ve gaya ma kowa ba, kaii amma Allah yayi ma Aishalle albarka Akwai da kaifin tunani, yace Aishalle kin tabbata wannan shawarar taki har ranki? Don ni bana so nayi abunda zai bata ranki, tayi murmushi Maigidana kenan, kamanta hallacin Hajjo a gareni? Ko kirkinta da kular da ta bani ka mance wlh wannan abu har raina, don a qasar nan banda kamarku. Yace toh shkn, na amince, tace ka taso muje mu kai qoqon barar mu, yayi daria yace Aishalle baki da dama.
Karime dake labe bakin kofa ta na jinsu idonta ya rufe tsabagen tashin hankali, kishi da Hajjo? Aiko zaayi yaqin basasa na biyu a gidan nan, keji wannan hegiyar mayyar, dan taga na barta ta zauna shine har da gayyato hajjo, ganin sun kusa fitowa ne yasa ta shige dakinta da gudu.
******
Hajjo jin maganar tayi bambamraqwai, ya zaayi ta auri yayan mijinta? Kuma Mijin Yaya karime? Aishalle tayi sauri tace donAllah yaya hajjo kar ki baza mun qasa a ido, kinsan duk wnda zaki aura a bayan mijina yake, kuma so kike kiyi aure wani gurin ya rabaki da yaranki? Auren mijina ne mafita gareki, hajjo ta harareta, hussain da ya shigo yace Umma danAllah ki auri babanmu, shiru tayi sai chan tace Allah ya hada kawunnan mu. Suka amsa da Amin. Ji sukayi ance idan ka isa Allah ya tsinen, ni zaka ci wa mutumci? Hajjon zaka aura? Qanwata? Yayi murmushin takaici, yace ynzun kika san cewa qanwarki ce? Ai aure be haramta tsakaninmu ba, kuma kamar anyi angama, ta chakumo wuyanshi, tace kuran sai ka saken, ya ce so kike na sakeki? Wani dan guntun tunani tayi tace da sauri aa kar ka saken danAllah, amma yasin da sake ba zata sabu ba. Daria yayi ya ja hannu Aishalle sukayi qofa ta juyo ta fara zagin Hajjo, Musbahu ya leqo yace qara ce mata uffan a bakin Aurenki wlh kuna kika tafi kin tafi kenan. Dif kakeji kamar an dauke wuta, sai murgude murgude da harare hararen da takeyi, ba halin magana. Oh su karime ashe ana san auren… Ana idar da Sallahn jummaa aka daure Auren Hajjo da Musbahu…..
******
Bayan Shekara 15.
A halin yanzu
Hajia Babba(karime) Haihuwan ta 10 Shida sun rasu saura Abida, Sadiya, Zainab, sai Usman haushinta daya yaranta maza duk sun rasu daya kawai ya rage mata. Hajiya Ama(Aishalle) yaranta Aliyu, Umar Abubakar, Maryam, Rabi’u sai Auta Nuratu. Tun Da aka yi Auren Hajjo da Musbahu ko batan wata bata taba yi ba, Yaranta da Rabiu basu da bambanci da yaran Musbahu a cikin Gidan.
******
Dalilin da ya sa na tara ku anan shine; Na yanke hukuncin hada aurenku duka, kasancewar ku Maza duk kun gama makaranta ga Sanaar ku kunayi, ya kalle Mudassiru da Labaran yace matsayin qannai na kuke, amma aure be haramta tsakanin ku da ‘yayana ba, saboda haka kai Mudassir kaine babba, na baka Abida, kai Labaran Sadiya ce matarka, karime sai faraa take tayi, don tasan sai yanda tayi dasu mudassir din Musbahu Zailani ya cigaba da cewa, Hassan Maryam ce taka Hussaini kuma Nuratu, Gambo kuma na baka Zainab. Aliyu kuma zaka auri Hassana, Umar kuma Hussaina, Abubakar kuma akwai diyar Alhaji Mai dala’ilu Hafsat, yace ya baka ita charaf Karime tace Wa?? Ai kuran baku isa ba, Hafsatun da ke son Usman? Kuma mun gama magana da mahaifiyar yarinya tace ta ba usman Hafsatu, Wlh ba wani Habuvakar, karime sanin dukian Alhj me dalailu ne yasa ta ke son hada danta da diyarshi, Shi dama Abubakar ya fita daban cikin gidan, yace Baba a bar ma Usman din, duk daya ne, don be son Auren yanzu musamman na zumunci, ya cigaba da cewa ni dama ina son na qaro ilimi, , yace toh shkn da kai da Usman din duk daya ne, Allah ya ba da xaman lahya. Suka amsa da Amin gabaki daya, Karime tace yauwa Alhaji maganan Zainab da Gambo, ya xaayi ka hadata da gambo? Bayan kasan hajjo bata qawnar jinina? Wani kallo da ya watsa mata ya sata nustuwa lokaci guda..
*****
Sunyi qoqarin fahimtar junansu, kowa yayi naam da hadin da aka mai, Zainab kuwa tana son Gambo qwarai da gaske amma Karime tana laantar wannan hadin, Gambo ma yana danne zuciyar sa, don duk dakin Hajia babba ita kadai ce ta fita daban, Hajia Hajjo(mama hajja)da Goggo Ama suka lallasheshi kan yayi haquri yama babansu biyayya, Haka dai yayi haquri ya chusa ma kanshi son Zainab don ya lura tana sonshi.
A haka akayi aurensu, nan cikin gidan aka fidda ma kowa gidansa ciki da parlo, aka aje amare anan. Abubakar har ya tafi qasar Rasha(Russia) don karatu.
A qasar Russia ya hadu da Yarinya me suna Raijana, course mate dinshi ce, yau da gobe suka shaqu, har suka qullah soyayyah tsakankinsu, har Abakar ya yanke hukuncin aurenta, Raijana ta gabatar da Abbakar ga mahaifinta, dayake mamanta ta dade da rasuwa, fir babanta yaqi wai bazai aura ma dan Africa diya ba, ta dage ta nace tace wlh sai ta aureshi, yace shiko idan ta nace sai ta aureshi, to ba ruwanshi da ita, ya yafeta, da yake sun yan chan sun dauki soyayyah da mahimmanci ta tsallake mahaifinta ta ja hannun Abbakar, Haka sukaje wani massalaci aka daura aurensu.Haka suka gama karatunsu, sukayi shirin dawowa NIGERIA, yace su zo suyi ma babanta sallama, suka nufa gidanshi amma yana ganin su ya musu korar kare, yace beson qara ganin Raijana, haka suka wuto Nigeria guiwa a sage.
*******
Zaune suke a parlorn M.Zailani gabaki daya ana cin Abincin Gandu, yayi sallama hannunshi riqe dana Raijana, duka suka zubo musu idanu, Umma Hajja ta fara ganeshi da sauri ta miqe tana tafa hannu ga Abbakar ga Abbakar, gunta ya nufa don tun kafin ya girma ita yafi sani don tana sonshi kamar ita ta haifeshi, ya rungumeta ta shafa sumar kanshi, ya nufa M.Zailani ya zube ya na kwasar gaisuwa, kafin ya nufi Hajia Ama yana gaidata farinciki ya mamayeta amma kawaici ya hana ta nuna, ta amsa, sannnn ya Gaida Hajia Babba ta amsa cikin yatsina. Ya gaida yanuwanshi, Idon M.Zailani kan Raijana da take tsaye bakin qofa, yace Abbakar wacece wanchan, yayi murmushi ya kamo hannunta ya kawo ta gab da baban nashi, cikin turancinta tace Good Afternoon Papa, cikin turancin yan da yace hawwayu? Tace fine papa, Yace Abubakar wacece wannan? Abbakar ya murmusa yace Matata ce, Duka dakin suka hada bikin wurin cewa MATARKA?
5. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Hjia babba ta fara tafe hannayenta biyu tana salati, Abbakar kafira ka auro ka kawo ta cikin gidan nan?wani mugun harara ya jefeta dashi, Hajia Ama tace yanzu daman baka da wayau, Abbakar ya dafe kanshi, Umma hajja tayi saurin miqewa ta ja hannun Raijana tayi waje da ita, sassan ta ta kaita ta shigar da ita dakih, ta debo mata abinci ta mata alamun ta ci sbd ba ta iya turanci ba, Raijana tayi murmushi tace thank u, Umma hajja ta komo cikin babban parlo, Abbakar xube gaban babanshi, yace Baba ka yafe mun, bana son aikata sabo ne yasa na aureta, kuma musulma ce, ta rabu da mahaufanta saboda ni, baba idan na rabu da ita ban mata hallaci ba, na kuma ci amana, shiru ya gifta na wasu yan lokkuta M. Zailani yace shikenan Allah ya maka Albarka, na yafe maka, amma daga yau ba wanda zai qara auren bare, kuma ni zan zaba ma kowannenku mataye da mazaje, yace nagode baba, Abbakar ya matsa gun mahaifiyansa Hajia Ama, yace Ama danAllah ki yafe mun, tace bakomi Abbakar Allah ya bada saman lfy. Yace Umma hajja ina raijana? Tace tana chan daka, ya nufe dakin tana ganinshi ta fashe da kuka, Abbakar ur family is against our marriage ryt? Ya rungumeta yace dont cry, dy are not like dat, i explained evrything to dem, and dy understood me, u have nothin to worry abt.
*****
30 years later..
Baba Mudassir da Aunty Abida(first daughtern karime) na da yara 7, Tahir, Fatima, Noorayne, Zayd, Farida, Haneefa sai auta Ahmad, Baba Labaran da Aunty Sadiya na da yara 5, Yusuf, Khamis, Mu’ammar, Yusra , Bilkisu. Yaran Aunty zainab(diyar karime) da baba Gambo(dan Hajjo) 2, Samir, Samar. Baba Usman kuwa da Aunty hafsat diyarsu daya Ni’ima sai da suka shekara 15 da aure suka haifeta. Baba Hassan (dan Hajjo)da Aunty Maryam(diyar Aishalle) na da yara 4, Imran, Faisal, Munira, sai auta Nasir, Baba Hussaini da Aunty Nur yaransu 3,Irfaan, Zayyad da Raffiyah, Baba Aliyu(dan Aishalle) da Aunty Hassana (diyar hajjo) nada Yara 3, Aisha, Nabila sai fadila, Baba Umar da Aunty Hussaina na da yara 2 daga Suraj sai Islahulkhair. Uncle Abbakar da Aunty Raijana(er mutanen Russia) diyarsu daya tilo Rumaysa’u….*********
Yawancin jikokin M.Zailani sunyi aure, shike hada auren jikokinsa, Be hada auren jikan dakin Hajjo da jikan karime ko jikan karime da na Aishalle, hada yan daki yakeyi (misali dan baba hassan da diyar baba Hussaini) ko kuma diyar (Baba labaran da dan baba mudassir) shi a ganinshi hada auren jikokin Karime da jikokin hajjo ko na Aishalle matsala zai haifar don yana sane da gaban dake qulle tun kafin a haifi yaransu, amma ya kan hada jikokin Aishalle da Jikokin hajjo aure don su yasan Akwai yarda da amincin junansu. A qaidar gidan M.Zailani namiji daya gama karatun degree dinshi zaa mai aure, sai ya dauki matarshi ya tafi da ita duk inda zai kaita, mace kuwa da ta gama sakandire ake mata aure ta qarasa gidan mijinta. Jikokin gidan kama sukeyi don da wuya ka tsame wannan kace yana da kyau wannan be dashi, duk kakansu su ka dauko wurin kyau da haske, Sai dai kowa da halinsa, suna gaban da suka ga kakkaninsu sunayi, yan dakin Umma hajja da hajia Ama kadai ke zaman lafiya, Amma baka ra’ban yan dakin hajia babba, don da kun wuce sai ta zagi kakarku.

Maza 7 zasu kammala degree dinsu ko wa da fannin karatunshi, gabaki dayansu suna Oxford University, Mata 6 kuma ke jarabawar qarshe, kuma da sun gama za a hadasu Aure, matsalar gidan baka soyayyah don baka san da wa zaa hadaka ba, amma ba zaa rasa wanda kake burin a hadaku dashi ba.. Wannan kenan.
Kowa da halinsa, Islahulkhair ba ruwanta

2 / 29