Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   12 / 29

33K to 36K   out of 85.7K words

ta rarafa ta kama kafar tsoho, donAllah Grandpa kayi min rai, i love Zaid alot, Tsoho ya kalleta, yace Ke er bariki, bazan aura miki zaid ba, wai Grandpa, zaki zo kina nun karairaye, ni ba yaro bane, ke ga er boko koh? Toh Bature ma yaci ubanshi, hajia karime tazo ta dago badiyya dake ta kuka tace haba Alhaji menene haka? Zaid da jikinsa yayi sanyi ya daure yace Diyyah, ta dago ta kalleshi, ya cire key a aljihunsa ya miqa mata, go home, i got dis okay? Zaid pls help me, dont let him do dis to us, u knw i cant leave wothout u, yace Diyyah kije, i want u to trust me, i will find us a way i promise. Ya kalli mamar yace mom kuje gida zanzo, ta miqe tana hararar tsoho ta ja hannun diyarta, Tsoho yace oho dai agayas akai kasuwa, Zaid ya daure fuska kamar be tava daria ba, fuskar nan daure tamau, tsoho yace ni wannan daure dauren da kakeyi be shigata, kazo ka bugeni sai na san kanayi, in banda rigima irin taka, ina kai ina wannan fyarinyar? Dukaduka yaushe akayi aurenka? Kai a ce kayi shekara 10 da aure ance maka zan yarda ka auri bareh ne?, balle duka ko wata 2 baka rufa ba da aure. To udan mafarko kake ka tashi. Ni Musbahu Zailani ba zan yarda ka auri Bareh ba.

_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
29. Gidan Gandu byBiebee IsaZaid ya juya ya kalli Tsoho yace Ina so ka aura min Badiyya, ina sonta, da ka aura min Wannan yarinyar nayi biyayya na xauna da ita duk da na tsani na bude idanuwa na naganta cikin gidanah, amma saboda biyyaya ko kallon banza ban taba mata ba, ds Su Mu’ammar suke ta kuka suna hadaka da Allah kar a hada auren nan, ban ce komai ba ni, yanxu kuma nazo ina roqonka ka aura min Badiyya kana ce min aa, bakai min adalci ba, tunda na bi umarninka, to nima a bani zabina, tsoho Yayi shiru yana nazarin maganganun zaid, chan yace Zaidu da dai a cikin gida ka ga mace to ina iya aura ma, amma Bareh ne bazan aminta ba, Ba ka taba ganin an auri bareh ba, toh ba kuma zaa fara daga kanka ba, Zaid yayk wani shuumin murmushi, ba a taba auren bareh ba? To kakar yarinyan nan micece? Inace bare ceh? Er wata qasar ma, ko kana zaton bamu da labarin Uncle Abbakar da yaje karatu Russia ya aurota? Naga itama din bareh ce, Tunda har ka yarda ya aurota, nima hakan zaka yarda na aureta, Tsoho ya bude bakih galala, Zaid ni kake gaya ma magana? Hajia babba tace ai ba batun gaya magana sai gaskia, shi Habubakarin finshi yayi da ya auro tubabba? Uncle Abbakar da Maysah da ke tsaye bakin kofa suka qaraso ciki, duk zancen da sukayi a kan kunnenshi, ya kalli hajia babba rai a bace yace Raijana ba tubabba bace, a musulmarta na ganta, ya kalli Zaid yace Zaidu, zaid ya kasa dagowa su hada ido da Uncle Abbakar, don shi Allah ya mishi kwarjini, qaryan tsageri ya kalli baban maysah ya mai tsageranci, Zaid dai ya amsa ba tare da dagowa ba, Uncle Abbakar yace Lokacin da naje karatu russia, sai da nayi shekaru 5 kafin na dawo gida, mu ba mu samu gatan dawowa gida hutu kamarku ba, wanda duk lokcin da kuka so dawowa kuke dawowa, Ganin shekara 5 ba nan kusa bace, gudun kar na fada ga halaka yasa na auri Raijana, mamar matarka, sai da na dawo su baba suka san nayi aure, na sha fada amma da na nusar dashi dabarata tayi aure ya fahimceni, kagane? Zaid da yaji kunyan Uncle Abbakar ya lullubeshi be ce komi ba. Badiyya kake son aure koh? Sunannta kenan? Ya gyada kai, Uncle Abbakar ya durqusa gaban tsoho ya shiga hadashi da Allah, da Magiya kala kala na kan ya bar Zaid ya sake aure, Maysah ma ta durqusa ita ko harda kuka, ganin kukan da takeyi ne ya sa Tsoho cewa sai yaje yayi tayi, ni ba ruwana cikin alamuaaran zaid, na zare hanuna daga duk wani shaani nashi, Zaid ya matso yace ayi mun haquri tsoho, na tuba, na mata Alqawarin aurene, banso ta dauke ni a matsayin mayaudari, Tsoho yace kai dai kasani. Uncle Abbakar yace kace mata ta turo magabanta ni zan tsaya ma, ni zan aura maka ita, Da sauri zaid ya kalli Baban matarshi, yayi saurin sadda kai kunyar uba da ‘yarsa ta lulubeshi, wasu irin mutane ne wannan?Wani uba zai ma diyarsa kishiya? Wata mata zata roqa ayi mata kishiya? Jin muryan Uncle Abbakar yayi inda yake cewa kaji ai, ina so na gana da magabatanta, zaid yace nagode Allah ya qara girma. Wayarsa ya ciro ya sanar da Badiyya ta zo da Magabanta ta yanzu, cikin doki ta sanar da uwarta, cikin rawar jiki sukaje suka kwashi Kawuninta da basu dauke su a bakin komai ba, wani kawunta yace sai yau kuka san damu? Sai da aurenta yazo kuka san amfaninmu? Nan badiyya da uwarta suka shiga bada haquri don basa son abun da zai hana auren nan, sai da suka cikasu da kudih kafin suka bisu, niko nace dama Mace ke tura magabatan ta ba maza ba?
****
Bayan an sanar da yan gida akwai daurin aure a parlon Tsoho, bayan an hallara nan take Uncle Abbakar ya daura Auren Badiyya da Zaidu bisa sadakin Naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba, uncle Abbakar ne waliyyin ango, gaban tsoho akayi komi sai dai tak ce ce musu ba, tausayin Rumarsa yakeyi. Bakin Badiyya kamar gonar auduga, yau ta zama mallakin Zaid, sai yashe haqora take tayi a dakin hajia Ama.

Ita ko Maysah kulle kanta tayi dakin Ammanta tana ta ruzgar kuka, tausayin kanta takeji, anya batayi ganganci ba? Allah gani gareka. Haka ta dauro alwala ta dinga jera nafilfili Allah ya kawo mata sauqi a kan har bacvi ya kwasheta kan dardumanta, bata farka ba sai Assalatu.
Zaid ya shigo dakin badiyya tayi tsalle ta rungumesa, ya dagata ya juya,cikin murna yau gani na zama taka, bantaba tunanin hakan ba, har na cire rai fa, zaid ya ja hancin ta yace i told u i got dis dint i? Yes u did ma hubby, yace kun shirya? Tace ehhh, yace breakfast fa? Ta mai fari tace its too early, yace toh mu tafi, tace mom tace xa mu barta anan, zata biyo mu daga baya, akwai abun da zatayi a nan din, yace ba laifi, ya shiga dakin hajia Babba ya gaidata ya mata sallama yanaso ya iso Abuja da wuri, don yau Monday, ta musu rakiya, suka shiga sashen su Zaid, ya gaida Mamarsa da Babansa, badiyya tana ta jin kunyan qaryar, nan suka musu Sallama, har zasu tafi Zaid yace muje muyi ma Tsoho Sallama Badiyya ta turbune fuska, tace i dont like dat old man, Zaid ya galla mata harara yayi gaba, bata da wani choice din binshi a baya, Da Sallama suka shiga parlorn, yana zaune yana lazimi, Zaid ya durqusa itams hakan tayi, sai da yayi minti 30,kafin ya shafa, Zaid ya ce Barka da Asuba Tsoho, ba laifi Tsoho ya amsa amma ba kamse yadda yake mai da ba, Badiyya da ta gama quluwa da shanya sun da yayi ta gaisheshi tana harareharare, lpy kawai yace mata, Zaid yace Tsoho dama yanzu zamu wuce Abuja, kasancewar yau akwai aiki ban dauki excuse ba, Allah ya Tsare kadai tsoho yace, Zaid ya Amsa da Amin ya miqe har sun kai bakin qofa Tsoho ya cire bakih yace Zaiduu, Zaid ya juyo tare da amsawa, tsoho yace Rumah fa? Zaid ya fara in-ina shi ya mance da wata Maysah, ya shafa qeyarsa yace ita ta na nan, sati me zuwa zan zo na dauketa, Tsoho ya daga kai Alamar toh, Zaid yayi saurin barin parlorn dan kar tsoho ya jaza mai Aiki.. Tsoho kam takaicin Zaid yayi, yana son zaid sosai amma wannan abun da yayi kawai yaji zaid ya sire mai, ya mai ciwo, Duk cikin jikokinsa ba wanda ya ma gata kamar Zaid, don tunda ya aura ma Zaid Maysah yasan ya mishi babban gata, samun Rumah a matsayin mata Alheri ne babba, Amma da yake Zaid sakarai ne, be gano hakan ba, tsoho yace bakomai Duniya ce, Duniya ce zata ladabtar dakai. Yana cikin tunanin zuci Rumah ta shigo da Sallama ya amsa mata cikin sake fuska. Kallo daya ya mata yasan ta sha kuka sosai, tausayinta ya lullubeshi, Nan ta zauna suka shiga hirar yaushe gamo ba tare da ya sanar da its tafian Zaid ba

Abuja
Karfe 5 suka shigo gida, Badiyya ta gaza sukuni burin ta ta samu Zaid a yanzu, tun cikin mota take ta shafa shi, sai da ya dakatar da ita, yace wai so kike muyi accident? An riga an daura auren nan m all yours, i think u can wait har mu isa gida, if not i can find a place park my car nd u suit urself, ganin gatse ya mata ya sa ta shafa mai lafia. Tun a parlor ta fara shafashi tana kissing, haka dai ya biye mata har badiyya ta samu cikar burinta. Zaid ya ga salo salon iskanci, lallai kam badiyya tayi nisa. Sai a yau ne ya tabbatar da ya auri karuwa.

_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · Aug 5
Phatee Lamin
30. Gidan Gandu by Biebee IsaKaii I cant take dis anymore, da sauri ta janyo wayarta ta shiga laluben wayarshi.

Kano
Bilkisu ina abinci nah? Ta kalleshi ta watsar, sai da ya maimaita mata kana ta dago ido ta kallesa, tace ban dafa da kai ba, ya kalleta cikin mamaki yace sabida mey? Sbd ni ba baiwar ka bace, kuma ai naga kana da hannu koh? Zuciyya ta ci Suraj, haqurinsa be kai ta dinga gasa mai magana ba ya qyaleta ba, yau ya lashi takobi sakko mata da wannan rashin kunyar da girman kan nata, Shaqr mata wuya yayi ta sakeh ihuu, ya daga hannu kenan zai mareta wayarsa tayi kara, guntun tsaki yayi ya wulla Bilkis gefe, ya zaro wayarsa, Lil sis screen din ya hasko da hoton lovely K’anwarsa yasa ya dauka da sauri, Hello Islah? Ya kike? Jin muryan yayanta ya sa ta fashe da kuka be tsuma rai, nan da nan Suraj ya rude, Islah? Are you Ok? happened to you? Cikin kuka tace yaya Wlh m not alryt, come get me outta dis hell, ina Mu’ammar? Kinsan i dont have dat ryt to pick u up, tell me is Mu’ammar hurting u? Yaya tinda aka kawo ni so daya na ganshi, rannan ma ko 20 mins beyi ba, kayanshi ya kwasa ya bar gidan, What? Inji Suraj, u mean to say ke kadai ce a gidan for 1month 15days? Ya shiga ciki da sauri yace so sorry sis gani nan zuwa, key kawai ya dauka ya fitow, ya na fadin i promise u duk inda Amar ya shiga a garin zaria sai na binciko shi, he’s going to pay for hurting u. Bilkisu ta fashe da daria, Suraj ya kalleta, goodluck in finding ya Ammar, ba Zaria zaka tsaya ba, ka hada da Kasashen wajeh, dan be K’asar kallonta yayi sosai, zuciyarsa na mai zafih, ransa ya baci sosai, a hankali ya furta me kike nufi? Ko tausayi tace gani yayi ba zai iya zama da ita ba, kuma an fi karfinshi an hana shi sakinta, shisa ya bar Qasar kuma ba zai dawo ba har sai yaji kun raba auren. Idanun Suraj sukayi jaaaa, ya ga bata lokacin shi yake yi nan gun bilkisu ya fita a fusace ya ja motarsa ya bar gidan ya kama hanyar Zaria. Nidai nace Suraj a dai bi a hankali, Allah ya tsare ya kai ka lapya..

Bauchi
Ya Samir pls ka samo min Islamiyya na dinga zuwa, zaman gidan ba dadi, nikadai a ciki, idan ka fita sai dare, pls yasamir, kallonta kawai yayi so daya ya wuce be ce da ita qala ba, haushi ya isheta ta miqe ta nufa dakinsa tajishi a kulle, nan ta fashe da kuka tana ta buga kofa amma yayi biris da ita, abunda samir yake mata ya fara isanata, anya zata cigaba da haqurin nan??

Kaduna
Ko da ta bude K’ofa Fadila ta gank tsaye, Amal ta harareta ta shige ciki, fadila tayi murmushi, tace haba Mummy Bon wai fushin ne haka? Wai ba gashi na zo ba? Amal tace sai da aka kusa wata zaki zo? Tace ai min haquri, ina Irfaan? Tace yana bacci, nan suka zube a parlo suna ta fira, cikin dabara Amal ta tambayi fadila ya zaman ta yake da Jawad, Fadila ta kwashe komai ta gaya mata har sillar auren su,da rashin jituwarsu tun kafin ayi auren, Amal ta nisa ta na tunani, ji labarin nan kamar a fim, tace Fadila listen to me and listen good, Ba zaki biye ma Jawad kuyi ta xaman nan ba, kin dai ji abun da tsoho yace, ba saki cikin auren ku, whch means u guys are stucked together forever u need to learn how to leave with eachoda, nd love eachoda. Fadila ta zaburo, me kike so kice min mummy bon? Ni zan kai kaina gunshi? Na roqe shi ya soni? Kindaiji me ya ce kwanaki koh? Ke ganau ne ba jiyau ba, so ki bar wannan maganar, ba zan taba kwantar da kaina na bishi ya wulaqantanni ba wlh, so bar ma wannan zancen,Amal tayi murmushi, Fadila kenan, ba nufi na kenan ba, namiji sakarai ne, kamar yaro yake sai yanda kikayi da shi, ke fa mace ce, akwai yan dabarun mata da zaisa hankalinsa karkatowa gunki, Fadila ta miqe a fusace tace No thanks, kar Allah ya sa hankalin nasa ya karkato gurina, muyi ta zama haka har dunia ta nade for all i care, Amal ta na mamakin zafin kai irin na fadila, amma she wont give up har sai ta ga ta shirya wadannan maauratan.

Lagos
Riqe take da cikinta tana Murqususu, hawaye na bin kuncinta, ta gama galabaita, ta kawo ma kanta mutuwa, yarda kasan tana ciwon Naquda, ta nayin scramps sosai, amma na wannan month din yayi worst, Waiyo Allahn ta, da qyar ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana jan jiki ta fito daure da towel dafe da cikinta, jiri ya dibeta ta zube a qasa, Shigowar sa kenan ya ganta a K’asa, da gudu Zayyad ya K’arasa gun hanifa, Hanifa hanifa, are you ok? Kamar ta ga wani dodo tayi karfin matsawa, ya sa hannunsa zai dago ta, ta buge mai hannu tana hawaye, Cikin damuwa Zayyad yace pls Hanifa, lemmie help you, ko karfin magana bata da, amma da yake jinin hajia babba na cikin bargonta, tayi qoqarin bude bakih tace I dont need your help…
31. Gidan Ganduby Biebee Isa
tsura mata ido yyi yana kallonta, chan ta cije bakih tare da fadin Waiyo Hajiarmu, da sauri Zayyad ya kira wata nurse a waya ta shaida mai gata nan tafe, Hanifa ta jigata amma taqi yarda Zayyad ya taimaka mata, Har isowan nurse din tana nan kwance da sauri nurse din ta shiga agaza mata, bayan ta gano bakin zaren neh, ta mata Allura, ta rubuts magunguna tare da ce mai kar ya tada hankalinshi, period ne wands ke xuwa ma mata everymonth. Ita nata da hakan yazo, Zayyad ya tausaya mata sosai, har ya na tunanin dama zai iya dauke ciwon ya maida ma kansa da yayi, don shi Allah yayi shi da tausayin mace, Yanzu duk month haka zata kasance? Allah sarki Allah ya baki lpy.

Zaria
Ko da ya iso Zaria, Staright gidan Ammar yayi, yana sakawa da warwarewa, har ya danna horn a gaban gidan, cikin rawar jiki me gadi ya budeh, Islah ta leqo ta window, ganin Yayanta ne ya sa ta fita da gudu, yana parker motan ya fito, Islah ta rungumeshi tare da fashewa da wani irin kuka me tsuma rai Suraj ya rungumi k’anwarsa, yana bubbuga mata baya alamun rarrashi, tayi shiru tana ajiyar zuciya, ya ja hannunta har parlo, Ya kalleta yace Isi meya fadu dake? Nan ta kwashe komai ta gaya mai, Ran Maza ya qara baci, ohh baki san cewa baya ma kasar ba? Ta dago rinannu idanuwanta ta kalleshi, baya kasar? Ina yaje? Suraj ya mike, yace i dont know, nd i dont care, all i knw is dat u wont sleep a day here again, je ki kwaso kayan ki, da gudu ta shuge dakih A gurguje ta hada kayanta cikin Katoton Akwati, ta dauki duk wani abun da zaats amfana, ta qwala mai kirah, yaya i need help here, zuwa yayi ya ja akwatin tare da fadin ragguwa, tayi daria tare da kulle ko ina, suka fita ta ba ma mai gadi key, Mai gadi na son tmby amms ganin ba fuska ya sa shi yin shiru, haka suka dauki hanyar Kano. Ba su rufe Awa 3 suka shigo kano, Bilkisu na nan zaune, Islah ta shigo da Sallama, kallo daya ta musu ta watsar, sai dsi ta amsa sallamar chan ciki, Islah tayi murmushi kisuwa matar yaya, ta kalleta ta harara, Islah dai ta zauna tana jiran suraj ya shigo, Sai ko gashi da Akwati, Bilkisu ta miqe tayi hanyar daki, ya kalleta yace madam a nuna ma Isi dakinki inda zata kwana koh? Harara ta banka mai tace ba shegiar da zata kwana min dakih, Yayi azaman damk’o wuyanta, da sauri Islah tace haba Yaya ka barta mana, ni ko a parlor sai na kwana, Suraj ya ja kayanta Ya tura dakin Bilkisu yace idan har bazaki iya kwana daki daya da ita ba, to u have to choice ko dakina ko parlor, Allah ya sawwaqe na kwana dakin ka, kuma ba zaa zo gidana a sani kwanan parlor ba Wlh ta buga tsoki ta shige dakin, Suraj yayi murmushin takaici yace yau zaki gane baki da wayau, yayi niyyar bin ta daki ya lallasata Islah ta tsaida shi, haba yaya, ai ba a biyewa, Bilkisu qanwarka ce fa, zakaji dadi Yayanta ya duke nih? Ka

12 / 29