Gidan Gandu Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  BieBie Category :  Romance

Chapter   6 / 29

15K to 18K   out of 85.7K words

a qasa, ya nuna ta da yatsa dont even think abt dis. Yayi cikin daki ya barta yashe a qasa, side smile Badiyya tayi tace muje zuwa. Daki ta bishi ta ganshi yashe kan gado, gyara mai kwanciya tayi ta zo ta baya ta runguneshi, suka yi bacci, assalatu ya tada Zaid, ganin Badiyya yayi rungume dashi tana sharar bacci, komi da ya faru jiya ya dawo mai, ya qare ma Badiyya kallo, kyakyauwa ce, daman akwai masu kyan nan a Naija, well haka yake son mace wayayya, ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da dauro alwala, be tada ta ba ko da yayi sallah, ya shiga kicin dan hado musu brk fst, 8am ta fito Tana wannan yauqi tana kwarkwasa ta zube jikinshi,ta bashi peck G’mrn My Zaid, be hanta abunda take mai ba, m so hungry, yace i cooked u brkfast, tayi farrr rwly? Show me, Yace i will if u let me, ta gane me yake nufi ta daga shi da sauri, ya riqo hannunta ya kaita har kichin, suka zauna suka ci tare, harda feeding juna, cikin kwana 3 badiyya ta siye zuciyar zaid, haka yake son Matan Naija su kasance a waye, kullum suna maqale da juna. Badiyya ta fahimci Zaid, iyakanshi Romance. Sai ta daina zaqewa tana biye mai yanda yakeso.
*******
Ta kalleshi cike da qauna tace My jawad, wats troubling u dis days? Yayi faking smile yace bakomai baby, tace me ya sa ka tafi ba tare da kamin bankwana ba lst 3weeks? Kuma da kazo last week ba mu samu munyi magana ba, me ya faru? Yace bakomi kissu na, tace har ka fara boye mun abu ko ya jawad? Noo baby ba haka bne toh menene? Nan ya kwashe komai ya gaya mata game da abunda ya hadasu da fadila, bilkisu ta tashi tana huci kam balaee, Shine ka qyaleta? Yace hey babe chill mana, ya wuce, tace wlh be wuce ba, ya kamo hannunta duka biyu yace nace ya wuce ko? Ta ce naji, ta miqe ta barshi zaune.Dakin Aj ta shiga ta na huci ke lpya? Tace kinji kinji, ta kwashe komai ta gaya mata ita ma tace balaee, harda Ya’amar dina aka ma rashin kunya, tashi muje sassan su.suka fita gabaki daya.
*****
Hajia Ama zaune tana bare gyada, su Bilkisu suka shigo, sai da gaban hajia ama ya fadi don ba zata iya tuna ranar qarshen da suka shigo sassanta ba, Ba su da niyar gaisheta, tace mai gado lapya? Bilkisu ta watsa mata harara hanifa tace ina maras kunyan jikarki? Fadila nake nufi Hajia Ama tace ba sa nan suna chan gidan Yayanku hafiz dukkansu 3, yayansu dai ba yayanmu bq, don mu ba hada jini da mayu da aljanu ba, hajia Ama tace kuyi hqri, Bilkis tace idan bamuyi hqr ba hauka zamuyi? Suraj da Zayyad da suna cikin dakin Ama, tun shigowar su sukejin su, Suraj yace yaran nan basu da kunya, ya fita Zayyad ya bi bayanshi, ke uban wa kuke ma magana haka? Hanifa ta kalleshi galala ta watsar, dan ubanki nikike ma wannan kallon? Tace an kalla din, bilkis tace ke kika tsaya kulashi, ni ai idan na raina bola ko shara ba zubawa cikinta, tass kakeji ya kamtseta da marih, ya juya ya ba hanifa nata Allah ya isa mugu azzalumi shege daniska, charr ran maxa ya baci, belt ya ciro ya fara shauda musu, Zayyad ya qwace su yace ku gudu, yaja shi yana haba, meyasa ka biye musu, hajia Ama ma fadan biye musu da yayi takeyi. Da gudu suka yi sassan Hajia Babba suna kuka, hankalinga ya tashi, da qarfi ta fito, wai waye, uban me kuke ma kuka? Nan suka shirga mata qarya da gaskia, wai Zayyad da Suraj ne suka kullesu suka musu dan banzan duka, ko dankwali bata sa ba tayi sassan Hajia Ama da sauri masifa na cinta, Aishalle yau sai kin ci buhun ubanki, kika sa jikokin ki suka ma bayin Allah duka ko? Nima yau sai munyi na mu, Ama ta fito, suraj da Zayyad na bayanta, tana kar ku sake kuce komai, kuna jina? Ama ta kalleta tace kiyi hqr yaya karime, ba haqurin da zanyi, shegu mayyu wanda suka gaji maita, sai na daka ki yau cikin gidan nan, tayo kanta gadan gadan ta maqure nata wuya, Suraj ya finciko hajia babba ya watsar a qasa, wani irin Ihuuu hajia babba ta sake kamar an sa Lasfika, daidai nan Jawad ya iso, yana zuwa ya sakar ma Suraj nushi a hanci, suraj beyi watawata ba, ya rama nan dambe ya kaure, Zayyad yazo da niyyar rabasu, Jawad ya kaimai nashi nushi a baki, nan zayyad ya zuciya ya rama, sai abun ya koma 2in1, Ihu su hanifa keyi hajia babba nayi, Hajia Ama tayi saurin shiga sassan Umma hajja don ta ga ko su baba Abbakar na nan, fadan qarfi akeyi anan fadila, Maysah da Islah suka shigo gidan, ganin fadan maza yasasu sakin kuka duka, Maysah tayi sassan Tsoho da gudu, bawanda ya iya shiga fadan sbd duk mata ne, Islah tayi boys qrts don neman Yasamir. Har jawad ya far habo ga jini ta baki.
*****
Shigowan shi gidan kenan, daga nesa ya hango su suna dambe, hango jawad yayi yana firda jini, danuwanshi uwa daya uba daya aka ma wannan taron dangi? Balaeee, yarda trollynsa yayi ya cire er whyt top dinsa yayi wurgi da ita, ya ruga da gudu, wani tsalle yayi ya chafko zayyad ya hadashi da bango, ya finciko Suraj ya dinga kaimai nushi, abunka da wanda ke gym’n Jawad ya dago kai ya kalleshi ya sakar da murmushi suka tarar ma Suraj, suna duka, daidai nan Tsoho ya iso gurin Ba kasafai yake fitowa daga parlornsa ba, amma yau shine har sassa, Su hanifa sai kuka akeyi, hajia babba na ganin tsoho ta qara fashewa da kuka, Samir ya rugo da gudu tare da Mu’ammar zasu shiga filin dagan Tsoho ya musu alamu su tsaya, tsoho yace ku bar fadan nan, Ku bari nace, Jawad ya bar dukan Suraj, shi ko wannan cigabawa yayi da kilar suraj kamar Allah ya aikoshi, tsoho ya qara cewa nace ka bari ko? Ai da alamu be jin tsoho, da qarfi Tsoho Yace ZAIDU

15. GIDAN GANDU byBiebee Isa
Ture Suraj yayi tare da zuwa ya dauko rigarsa ya nufi sassan su, duk suka bishi da kallo, Tsoho ya kalli Samir tare da miqa mai wayarsa ya ce kiramin Dr Munnir, hannu na rawaSamir yayi dialling no din, ringing daya ya dauka ya miqa ma tsoho, Allah ya qara ma tsoho tsawon rai, Dr muna lpy? Ya amsa, yauwa danAllah kazo ka duba min yara na nan, yace toh gani nan zuwa, Tsoho yace kowa ya tafi sashensa. Zayyad ya kama suraj ya kaishi dakin Ama, aka watse. Ba a jima ba Dr yazo, a duba Suraj, ya bashi pain reliver Tsoho yace aje a duba Jawad, ko da Dr yaje sashen hajia Babba korarsa tayi tace ba sa buqatar likita munufukan banza..
******
Har kwana 2 shiru kakeji, kowa yayi zaton Tsoho zaiyi magana akan fadan shekaran jiya qala be ce ma kowa ba, kamar baayi ba, Be qullaci kowa ba, ko da Zaid yazo gaisheshi be nuna mai komai ba faramfaram, yana mai wasan kaka da jika, har suna sa ran Tsoho zai masu magana amma be ce komai ba.
Hajia Babba ji take da Zaid, duk cikin jikoki ta fi yi dashi, amma gurza mata RM yakeyi, mamanshi Abida ma tafi sonsa.
*****
Lamarin Gidan ya qara tuburewa sabon Gaba ya qara qulluwa, Samarin Gidan kuwa zumuncin su ya baci, dama suke zumunci a gidan amma tin bayan fadan nan ba me cewa dan uwansa qala, Gaba me qarfih suka dauka da junansu. Duk wa’annan abubuwan da suke Tsoho na sane da su.
Ya samu su Ido, yana tunanin shikuma haka Qaddararsa take? Gaban da Iyalansa keyi na matuqar damunsa. Amma InshaAllah komi yazo qarshe, yasan abinyi..
****
Haka ne bigbrosamir abubuwan gidan nan ya rinchabe, kowa gaba yakeyi, ni ba abunda ya damen da gaba kowa nawa ne, yace shiya sa kike burgeni ba ruwan ki da ‘yan ubanci,tace kaima ai haka bigbrosamir shisa nake sonka, yayi daria, yanzu ka fa da mun wannan shigar zai burge Yazayd? Samir yace sis na fiso ki bar mgnr Zaid, tayi rau rau da fuska zatayi kuka, ba zan mishi ba ko yasamir? Ba zaiso ni ba? Duk ta bashi tausayi don yasan ta na son zaid, yace kar ki damu zai soki, bana so kikai kanki ne, na fiso ya zo gunki tace toh shkn bigbrosamir, zan kama kaina.
*****
Ta shigo Gidan da motarta, Taci gayu sosai, ta fito ta na taku daidai, fitowar Amira daga sassan Umma hajja kenan taga baquwar fuska, Amirah ta nufeta da murmushi sannu da zuwa, Badiyya tace yauwa, Amirah tace gun Hajja Ama kika zo ko umma Hajja? Badiyya tayi far da ido, ko daya, gun Zaid nazo da fatan yana nan, Nan da nan fuskar Amira tayi dif, tace bashi kike binshi ko tara? Diyya tayi dan murmushi yan dunia tace ko daya naxo ansar zuciyata ne da ya sace min, da fatan kinsan inda ya ajiye shi, in ran amira yayi dubu ya baci, tace ke shegia eriska me bin maza har gidansu, ki bar gurin nan ko wlh na miki tunbur kuma na lalada miki dan banzan duka Badiyya tayi daria, ke yarinya, kinsan dai ni ba tsarar ki bace ko? A banza zan baki shekaru 5 ko 6, zan miki uzuri daya dan naga kina kama da myzayd, nd kamar kina hauka da sai kinyi nadamar furucin nan, Amirah tace na rantse da Allah ina iyawa, idan kin san mutuncin kanki ki bar gidan nan ynz, in ko ba haka ba, zaki ga Haukana don mugun bugu zan miki, na kareraya ki, na kaiki asibiti na kuma yi jinyarki, Daria sosai badiyya keyi, Amira ta kwnace dankwali au daria ma na baki ko? Tayi dammara, daidai nan Maysah ya qaraso gun da gudu ta sha gaban Amira, Haba Amira me ya hadaki da baquwa? Wannan er iskar zata shigo mana gida tai mana karuwanci, wai her Zaid, ko uban wa yabata yazaid din, haba Amira kiyi hqr mana, ke dalla matsa matsoraciya, tsayuwar rin wannan cikin gidan nan balaee ne, Ji gashin doki, ji man kanti ji matsatsun kaya, wlh kamar jikar bokan tudun qarfe, ai wlh sai ta bar gidan nan ynz ba anjima ba, kafin Allah ya jarrabe mu da Kwarantsa cikin Gida, Maysah tace haba Amira, ita ko diyya daria kawai take, Maysah ta juya ta kalli diyyah haka kurum taji gabanta ya fadi, ko me ya sata faduwar Gaba oho? Ta dai daure tace baiwarAllah kiyi haquri danAllah, Yazayd kike nema? Bari a dubo maki shi, ta ja hannun Amira, daga nesa suka hango Yazayd din na jogging, ita ko badiyya ta qarasa gun shi, shikuma ya daga ta sama suka rungume juna, Haka kurum Maysah taji gabanta ya tsananta bugawa, Amira kuwa baki ta bude galala, kaiii Rumguma? Tsanar Yazayd da karuwa(sunan da ta samata)ya shigeta, meye haka, gabansu suke iskanci? Bata ga komai ba sai da taji badiyya nacewa haba Zayd kai da kace zaka nemeni har kwana 5 shiru? Nayi missing dinka, ina tunanin ko ka mance ni? Cikin sigar lallashi yace so sorry my diyyah, wlh i was busy ne, har yau ban siya sim ba shisa ban nemeki ba, but its a good thing u came over, i’m glad to see u, ya akayi kika gane gidan? Ta mai far da ido, kasan familyn Zailani ba boyayye bane, yace haka ne, Sai sannan Zaid ya lura da Meerah da ke tsaye wata a gefenta ba tare da ya kalli Maysah ba, ya kalli Amira yace ke ya ma sunanki?? Amirah ta watsa mai wani mugun harara, Badiyya tace kai honeybunch ur sis is hilarious, ya danyi gyatsine yace haka take bata da hankali, ya qara kallon Amira yace Zo ki kai Badiyya gurin Hajia Babba kice mata baquwa tace, Badiyya tace Oh no dear, ba yau ba, i jus came to check on u, but next time musamman zanzo gaida Inlaw’s na, yayi dariar jin dadi yace yauwa sweety, ya ja hannunta ya rakata har mota, Amirah da Maysa suka bisu da ido, Maysah na tir da wannan hali nasu, Ameerah kuwa takaici da baqin ciki kamar tayi kuka, Maysah ta ja hannunta ta fizge tayi dakin Yasamir,Yana ganinta ya miqe tsaye yace lilsismeerah menene waya tabaki? Ta na huci, bigbrosamir daman Yazayd dan iska ne? Ynz wata tazo gidan nan nemanshi kaga yanda ya rungumeta? Ta kwashe komai ta gaya mai, Samir yace toufa, shima Zaid da rigima yake, yasandai ba wanda zai aura mishi bare, kar ki damu kece matarshi, na auri wannan? Allah shi kyauta na aureshi, kai kaga abunda sukeyi? Ai wlh bazan aureshi ba, shi gashi wayayye. Yayi karatu turai ya zama chris tucker, toh wayewa ma ya ci ubanshi, Samir daria ya fara, isit funny bigbrosamir? Ni ynz wa zai aureni? Kowannen ku is in lov? Kuma ni ba zan auri daniska ba wlh, kar kuma Tsoho yace zai zaban mun daga cikin yayyinmu wanda sukayi aure. Shidai Samir har yagaji da surutan Amira, ya daiyi shiru yana jinta, wani Lokaci tabashi daria wani Lokaci ta bashi takaici, shidai yace Allah ya shirya Amira nikuma biebee nace Amin
16. GIDAN GANDU by Biebee Isa
Hajia Babba, Hajia Ama da Umma Hajja zaune a parlor, Tsoho ya kalli Ama yace Aishalle me ya faru sati 2 da suka wuce? Aishalle tayi murmushi don ta san ko ba dade ko ba jima sai yayi maganar, nan ta kwashe komai ta fadi mai tun daga shigowan su Hanifa har fadan, Tsoho ya jinjina kai, Charaf hajia babba ta chafe, baka da labarin rashin ta idon da Fadila ta ma Jawad, rashin kunya da zage zage, amma be ko kalleta ba balle ya duketa, toh shi suraj ya hade bilkin da hanifan ya zane, shi ko zaid ya zo ya lakada mai na jaki ai dan’uwa befi danuwa ba. Tsoho yace shikenan, Allah shi kyauta, ku tashi ku tafi, ya kalli Umma hajja, yace ki turo mun Hassan Hussaini da Gambo tace to Mallam hajia babba ta buga tsoki, M.Zailani ya gyada kai Allah ka shirya.
*******
Baba Hassan, B.Hussaini da B.Gambo zaune a kasa kan carpet, Tsoho yace toh kunji hukuncin da na yanke ya kuka gani? Baba hussaini ya nisa yace anya Baba wannan abu xai yiwu, kasan gaban nan me qarfi ne tun kafin a haife mu akeyinshi, sai nake ganin kamar wuta za a qara ma lamarin, tunda duk basu jituwa bane, maganin kar a fara kar ayi, Baba Hassan ya girgiza kai yace aa ina ga hakan ne maslaha a cikin wannan gaban, dole muke kawo qarshen wannan Gaban kuma inaga wannan ce hanyar da zai sa a samu sulhu, So ina ga Baba hakan daidai ne, Baba Gambo yace Hakan daidai ne kuwa baba, sai dai a roqa Allah ya daidaita tsakanin mu duka, M.Zailani yace Hussaini ka fahimci abun da Yayanka yace? Baba Hussaini ya gyada kai, yace wannan gaskia ne, daman bawai naqa bane ina gani kamar ba za a daidaita ba, baba hassan yace always pray for d best broda. Yace toh Allah ya sa mu ga da kyau. M.Zailani yace toh shkn tunda har kun amince da Raayina. Hakan zaayi (ni nace me zaayi tsoho? Harara ya wurgo ni da ita)
********
Maysah da Tsoho suna zagaya gida, ya na bata labarin Soyayyar shi da Aishalle, tana ta daria yace muje mu kaima Yayanki Ziyara, Tace wanne daga ciki? Yace muje dai, rabon da Tsoho yazo bangaren samari Har mantuwa ta manta, kai tsaye dakin farko ya qwanqwasa ya shiga, Zayd ne kwance da fara singileti ba bacci yakeyi ba amma daga ganinshi buge yake, ga kwalbar giya ta Gulder da Star ya shanye, Gefenshi Diyya ce kwance tana bacci, Tsoho firgici Maysah firgici, tsaf tagane wanda tayi fada da amira ce shekaran jiya, lallai Abun Yazayd ya girmama, har gadon baccinshi yake kawaota, Allah ya shirya! A hankali Tsoho yace Giyah? Ga mace Kwance a cikin Gidana? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Zayd ya miqe duk da ya dan tsorata amma da yake dan dunia yace me ran qarfe lafia ka shigo Sassan mu? Ko nema na kakeyi? Tsoho ya share yace ziyara kawai na kawo ma, Amma bari muje kafin ya ce komai Maysah ta riga tsoho fita, jikinta rawa yakeyi, har suka koma Sassan tsoho basu tanka wa Juna ba, Duk Zuri’ata Zaidu kaine Daban Allah ya shiryaka Dole na muku Aure, dole nake aurar daku duka, Ya Allah kai mana da kyau.
******
Fadila da Suraj a dakin hajia Ama suna Soyewa, tana zuba mai shagwaba Wai gaskia ba zai tafi kano week din nan ba, yace baby kiyi hqr so kike a koreni a wajen aiki? Tace ba sai a maka transfer ba? Yace ina kike so mu zauna idan munyi aure? Ta daga kai sama tana tunani tace Kaduna, yace daman tunanin mu daya, kar ki damu da hannuna na zana gida a kaduna har an fara gini fadila tayi ihun murna tace thank u mysuraj, Sarkin Gida ne ya shigo da Sallama yace Tsoho na kiran ku, suraj yace mu suwa? Yace dukkan ku na cikin dakin nan, har da Hajia Ama, taro ne na gaggawa, suraj yace toufa Allah ya sa lapya, fadila gaya ma su hajia a ciki da su Islah, aka sanar dasu duka. Kowa ya Hallara abun mamaki harda yayyinsu da matansu da sukayi aure na nesa ne kawai babu to lapya inji Islah?duk suka zazzauna, One by One tsoho ke kallonsu, daga matayensa zuwa yaransa zuwa jikoki harda masu musu Abincin GANDU, Tsoho ya gyara Murya Ina Zaidu?? Jawad yayi qarfin halin cewa yana Dakih, be ji aikena bane? Jawad ya miqe bari na kirashi, yace kai Jawad Zauna, Ya kalli inda mata suke yace RUMAH jeki kira yayanki Zaid, gabanta ya fadi haka ta miqe tayi Sassan Samari, ta kusa minti 5 tana tunannin yanda zata shiga dakin, sai

6 / 29