Page 1
GIDAN GANDU by Biebee Isa
Tsaki Haneefa ta qara bugawa a karo na biyu, yanzu mu kullum haka zata dinga samu latti? Bilqeesu tace Aifah, inda sabo ai ya ci ace mun saba, ta cika nawa, Hanifa tace wlh baxa ta sabu ba, bari mu dawo daga makaranta wlh mu samu Tsoho mu gaya mishi, Islahulkhair da ke gefen su ba ta tanka musu ba, cikin damuwa Fadila tace Mallam Audi donAllah ka qara mata horn, kafin Mallam Audi ya qara Horn suka hangota tana sauri cikin yanayinta na sayih ta fada cikin mota qirar bus, Mallam Audi Ina kwana, ya amsa mata cikin murmushi, tace kayi haquri wlh banga Socks dina bane, yace ba komai shigo muyi ta tafia kar mu bata wani lokacin. Ya ja mota ya bar haraban wakeken gidan da ke qunshe sashe sashe..
Kusa da Islahulkhair ta zauna gefenta Fadila ce riqe da keypoint tana karatu, Ta ce hey Sisters, sorry i kept u waiting, Fadila ta dago ta kalleta, cike da zolaya tace Allah ya nuna mana ranar da zamu daina jiran Maysah, kin cika nawa, tace wlh banga safata bane ta kalli Islah tace yadai sisi? Murmushi ta mata tace lafya u will never change will u? Daria ta mata ta kama kunnenta tace sorry, ta kalli su Hanifa da bilkis a gefe tace duk ina kwananku, a tare suka buga tsaki tare da hararta, ba ta damu ba don idan da sabo ta saba. Mazan da ke zaune su hudu a chan baya tace Whatsapp bro, daya kawai ya amsata sauran 3 hararata sukayih. Ta kalli Na’imah da bakinta ke sake tana jalalar da miyau tace Nimcy a rufe bakin mana, kar ki bata gaban hijabinki, cikin tsiwa nimcy tace anqi a rufe din, sa’idawa masu bacci da ido daya, tace Allah baki haquri ta ciro littafinta ta shiga dubawa don yau suke fara NECO exams…
Jikokin Alhaji Musbahu Zailani kenan masu rubuta Jarabbawar qarshe ta makarantar Sakwandire na TopOnwards Science College Maiduguri, Su 10 cif zasuyi graduation bana…
***************
Assalam Alaikum tsoho me ran qarfe, Tsohon da ke zaune kan Sofa kyakyawan gaske ne, kadan ya rage ya cika shekaru chasa’in cif a duniya, tsufansa me kyau ne, gyara zaman gilashisa yayi yace Hanifa ce da Balki? Eh mune, amma bilkisu nake ba balki ba, yayi daria yace ja’ira, ya jarabawar? Suka ce toh Alhamdulilahi, duk suka yi shiru, Tsoho yace me bakin shan qwai menene? Naga magana a bakin ki, Hanifa ta zumburo baki, tace kaga dai tsoho ka bar ce man me bakin shan qwai, yace toh ai naga kun kasa magana, ku fada matsalarku a magance maku ita, Ke Me Gadon zinare menene? Bilkisu tace daman Tsoho qara muka kawo ma, Haneefa tayi charaf tace tsoho mu dai mun gaji, wao kullum sai Maysah ta samu latti, gashi mun fara jarabawa, wlh idan bamu bi a sannu ba wata rana sai an hana mu zana harabawa saboda latti, Mu gaskia da sakel, a san yadda zaayi damu, ko a sama mata me kaita ta qarata chan da lattin ta, Tsoho yayi jimm yace kuyi haquri, kunsanta da Nawar tsiya, zan mata fada, amma maganar raba tafiya duk bata taso ba, tun lokacin yayyunku da sukayi aure tare ake kaisu makaranta kunga lokaci guda ba za a bar wannan qaidar ba, Hmm ai daman munsan baka san laifinta ka fi sonta cikin jikoki, da sauri yace haba yan jikoki na, wlh duk daya na dauke ku, ku bari zanyi shawara da iyayenku, ku saurareni kunji? Sukayi godia suka mai Sallama.
*******
Ta kalleshi tace Tsoho tunda nagama karanta ma Jaridar bari naje nayi karatu dukda bamu da paper Gobe sai Jibi, yace RUMAISA’U Meyasa kike sa ‘yan uwanki latti? Kullum ke kadai suke jira, ko so kuke a hanaku shiga makarantar! Duk cikin lallabi yake mata magana, ta yi raurau da fuska tace, kayi haquri InshaAllah zan daina, yauma don safata ta shige wani gurin ne ai da bansamu latti ba, yacr donAllah ki daina kinji? Tace InshaAllah, yace yauwa idan kin shiga cikin gida ki kiramin Hajia Babba, tace toh Tsoho ta miqe ta fita, a ranta tace InshaAllah sai na riga kowa shirin makaranta jibi, ba za a qara jirana ba sai dai na jira…Tayi Sassan Matan tsoho domin kiran Hajia Babba, da Sallama ta shiga dakin Hajia babba ce da Abida (Maman Hanifa) a dakin, suna ganinta sun ka bata fuska, ta gaida su ba wanda ya amsata, tace Hajia Babba tsoho na kiranki, ba ta jira ta ce komai ba, ta fice don bata son jin zagin da za a jefi kakar ta dashi ba. Anty Abida ta buga tsaki tace jikar Mayu kawai. Hajia Babba taja tsaki tace wanda suka gaji tsiya game da miqewa don ansa kiran mijinta Tsoho.
*******
Gidan Alhaji Musbahu Zailani, wanda yan unguwa da sauran mutane ke ma laqabi da GIDAN YAWA, gida ne katon gaske gari guda ne, me qunshe da sashe sashe, su biyu kachal mahaifan su suka haifa, shida Qaninshi me suna Rabi’u iyayensu asalin yan qasar Chadi ne yan Shuwa Arab, Shekara 2 kachal ya ba qanenshi. İyayensa sunyi hijira zuwa qasar Nigeria garin Maiduguri inda suke sana’ar sirfani da dinki,Bayan Rasuwan Mahaifansu Musbahu ya rungunmi qaninsa suka cigaba da wannan sanaar dinki, har Allah ya buda musu, sun samu İlimi me inganci na arabi da boko. Kafin suka fara habaka Sanoin su ta wani sigar.. Har suka zama matasan Attajirai.
A kasuwan da suke Sanaarsu, Akwai Wata yarinya Karime da ke kawo musu tallan fura fura, yau da gobe ya sa suka saba da Musbahu har suka fara Soyayyah, ba ayi wata wata ba ya kai gaisuwa gun iyayenta, yace ba su da kowa a Qasar nan sai qaninshi. Mahaifin karime yace bakomi an bashi karime, ana haka ne diyar kishiyar Maman karime ta shigo daga tallan Goro, ta gaidasu, Baban yace sannu Hajjo kin sha rana shiga kan kabad ki dauko samira na nan da abinci kici tace to, Rabiu ya bi bayanta da kallo chan yace Baba wannan fa? Yace hajara kenan, qanwar Karime ce, amma ba uwarsu daya ba, uwarta ta rasu, sukace Allah ya ji qanta, Baban ya miqe yace ina zuwa, ya shige ciki, Musbahu ya lura Akwai magana bakin qanenshi, yace yaya dai Rabiu? Yace Yaya wannan yarinyan ta man, bansan ko babanta ze ban ita ba, Musbahu yace bari yazo a kwatanta daman gwara kayi auten kaima, ko da baban ya dawo Musbahu ya sanar dashi buqatar qaninsa, Mallam yayi shiru yace baqi taku ba, amma Hajjo bata da kowa sai Allaj sai ni, Hajjo tasha wahalar kishiyar uwa, ta na kan sha, Zan baka hajjo amma sai kayi man Alqawarin cewa zaka riqe man ita da amana, da sauri Rabiu yace wallahi na amince baba, zan riqe maka ita da amana. Yace toh shikenan na baka ita bayan Sati 2 kuzo a daura aure. Sunyi murna gaba ki dayan su…
*******
Da daddare Mallam ke gayama maman karime yadda sukayi da meson Karime, murna fal ranta, Allahu Akabar, ashe zan ga Auren Karime nah, kai madalla madallah, yace ai ba auren karime kadai zaki gani ba, harda na hajjo, take Annurin fuskarta ya dauje dif, tace bangane ba, yace Qanin Musbahu ke son Hajjo kuma har na bashi ita, maman karime ta daka tsalle ta re da riqe qugu tace Kam babban balaeen chan….
Page 2
GIDAN GANDU by Biebee Isa
Sai kuma ta fashe da kuka, yanzu mallam ni zaka tona wa asiri? Eyi? Yace bangane tona miki asiri ba, dan ka ga ba ni na haifi hajjo ba shine zaka aurar da ita ko neman shawara bakayi? Ynx idan tayi aure wazai na kai mun talla? Ko ni kakeso na fita tallan da kaina? Takaici ya hana mallam magana sai kawai ya fice ya bar dakin…
*****
Tadihn su sukeyi irin ta masoyan da, Hajjo ta shigo da Sallama a fuskarta, Musbahu ya amsa da murmushi, yace Amaryarmu, nan da nan karime ta hada gabas da yamma, tace wato Rabiu ba xai janye ba koh? Me zaayi da wanda ba a san asalinsu ba? Hajjo ta shige cikin gidan da sauri tana matsar qwallah, Musbahu ya bata rai yace haba karime me yasa kike haka neh? Sai kace ba Mahaifinku daya ba? Charrr uban, Allah ya sawwaqe, daman wayace ma baban mu daya? To tsaya kajih yanda abun yake, da ita kishiyar maman mu ta shigo gidan nan, Agola ce, kuma da ta rasu, shine babana ya riqeta, ni kadai ral mahaifana suka haifa, Musbahu yace najih dai, be kamata kina nuna qyamarki gareta a fili ba, ko kina kishi ne don ta fiko kyau, wani mugun ashar ta lalayo ta dinga zage zage da qyar ya lallabata tayi shiru. Ya shaida mata gobe zasu je Chadi don sanar da kawunninsu auren su, ta mai Allah ya kiyaye
******
Ko da Su Musbahu suka isa qasar Chadi suka tarar da Kanin Mahaifinsu Ya rasu me dakinshi batafi wata 2 ba itama ta rasu, Musbahu ya kalli Rabiu yace kaga Rabiu inaga mu tafi da su Mudassir da labaran Nigeria, yara ne ba su fi shekaru 10 ba su da kowa yanzu sai mu, yace Yaya duk yanda kace hakan zaayi…
Haka kuwa akayi Washegari suka kama hanyar Nigeria. bayan kwana 2 aka daura auren Musbahu da Karime, da kuma Rabiu da Hajjo. Dan madaidaicin Gida ya kama musu, suka zauna tare da yanuwansu Labaran da Mudassiru, Musbahu yace Karime ta riqe su, fir taqi ita bazatayi bautan yara ba tun kafin ta fara samun nata, haka Rabiu ya kwashe su ya kaima Hajjo su, ta amshe su hannu bibiyu.
*****
Bayan Shekara daya.
A daddafe ta szuwa ta kai kanta bangaren Karime, kuka takeyi tana kiran Yaya ki taimakeni, bayana zai balle, Karime da ke zaune tana tamnar cingam ko kallo bata isheta ba, nan Hajjo ta xube tana murqususu, amma karime bata ce mata ci kanki ba, Tunda Hajjo ta samu ciki Karime ta ji wani tsanarta ya shigeta, jin haushinta daya ya zaayi hajjo ta samu ciki? Ita bata samu ba? Ta sha kai ma cikin hari tun yana qarami amma bata samu nasara ba, Kishinta takeyi Sai kace kishiyoyi, ta dinga juyi a qasa amma ko kallo bata samu ba daga karime, maqociyarsu ce Umm Afeef ta shigo gidan da Sallama, ganin hajjo a qasa yasa ta qarasa gunta tana sallami, me ya sameki haka? Ko naqudar ce? Sannu, ta kalli karime tace kedai bakiji dadin rayuwarki ba, wai shin mini daya kuke aure da zaki nuna mata wannan halin ko in kula? Karime tace Maman Afeef wlh ki fita idona zamu kwashi yan kallo dake. Cikin wahalaliyar muryan hajjo tace umm afeef marata, bayana, ta fita da gudu tana fadin ina zuwa Bata tsaya ko ina ba sai gidan Unguwan zoman garin Ummu Anisa, ta ce ki temaka haihuwa tazo ma hajjo, ai ko da gudu suka fito suka nufa gidan, har ynx hajjo na qasa ta na mutsu mutsu, maman Anisa tace kamata mukaita ciki, Karime tace Waaa? Ai wlh ba zaa shiha da najasa dakina ba, ummu Afeef ta buga tsaki tace in fitsari banza ne, kaza ma tayi, Ummu anisa tace rabu da marar tausayin nan kamata mu kaita bangarenta, nan suka bar karime na ta zazaga masifa. Suna ko shiga daki Hajjo tayi wani yunkuri ta santalo danta, Kai Masha.. Maman afeef ba ta rufe baki ba sai ga wani dan ya fito, cikin murna tace Yan biyu– sai ga wani dan ya kuma fitowa, Guda maman afeef ta sake da qarfih, ummu aneesa sai sannu take ma hajjo, kafin aka gyara hajjo. Da yaranta maza kyawawa kamar babansu. Ummu Afeef ta fita waje da sauri taga karime na labe tana leqe, ummu afeef tayi shewa tace samun Yan uku sai ‘yar baiwa, Karime ta dafe qirji tace na shiga uku, Yan uku? Maman afeef na fita ta samu almajiri kayi maza kaje kasuwa kace ma malam Rabiu hajjo ta haihu ta samu yan uku. Da gudu almajiri ya ruga.
Karime kuwa kamar tayi hauka, sai sambatu take tayi, Hajjo ta haihu? Ta samu yan uku? Kuma maza? Jar ubanchan, wlh bazata sabu ba. Da balaee nima sai na haihu cikin watan nan hka ta dinga haukanta…
Da gudu Rabiu da Musbahu suka shigo gidan, kallo daya zaka musu zaka san suna dauke da tsantsar farin ciki, Hajjo har tayi wanka tayi kyau abunta, Rabiu ya kwaso yayan ya rungume, ya miqa ma yayanshi, Musbahu ya amshesu tare da musu addua, Allah shi rayaku.. Nan ummu aneesa tace a bar hajjo ta samu bacci, Yan gidan kuwa Labaran da mudassiru sai murna suke tayi Nene Hajjo ta haihu.
Musbahu ya shiga cikin Gidanshi jiki na rawa yake ta qwalawa Karime kira yana Karime karime, Hajjo ta haihu har daki ya bita yana gaya mata, Yan uku ta samu, kuma duka maza, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, shi be ma lura da yanayinta ba, yace wai baki san hajjo ta haihu bane ba? Cikin tsawa da masifa tace Tou Sai Me? Ya dan kallota, karime lafiya? Ta miqe tace ita ta kawo hakan, ta sabi zaninta ta bar gidan, shiko Musbahu tunani yake me yayi zafi haka?
***Rannan suna Yara sukaci suna Hassan Hussaini da Gambo, Yaran nan abun so ne gurin Jamaa, har yau Karime bata leqo ta gansu ba, Rabiu wani kuka ta musamman yake ba matarshi, Hajjo na shan wahaln yan ukun nan, ba wanda ke tayata da rainonsu, sai Mudassiru da Labaran, ganin hakan ne Karime ta sami Rabiu da kuka wai ita dai a bata mudassir da labaran, ita tana cikin kadaici, waye waye, Rabiu be ce komi ba yace su koma gun karimen, Musbahu ya so tambayar ba a si kawai sai ya share. Karime ta cigaba da riqonsu don kawai kar Hajjo ta moresu, a hankali a hankali ta dinga chusa masu tsanar Hajjo.
*******
Abu na Allah cikin Shekaru yaran hajjo 6 har da yanuku kasancewar duk shekara take haihuwa wani abun Allah yaranta duka maxa, Bayan Yan uku ta samu Ahmad da Ibrahim, sai auta Hafiz har yau Karime ko batan wata ba ta taba yi ba, an bi Malaman anbi yan tsibbu da bokaye amma a banza. Musbahu na san Yaran Yanuwansa sosai, ya sa yan uku da Amad makaranta Islamiya..
***
A bakin kogi me kallon boader ya hango er yarinya na kuka gashin kanta ya rufe mata fuskarta da sauri ya qarasa yace ke me akayi maki? Dago kanta tayi Ya Salam!! Aljana ce ko mutun? Cikin hausarta da be fita tace wlh mutun ce ni, ya sunanki? Sunana Aishalle daga ina kike? Masu kamen bayih ne suka kamo mu shine ni na gudo nayo nan, ke er wace qasa ce? Tace kamaru, yace ina iyayenki? Ta matse qwallah tace sun rasu da dadewa, yace ta shi na siya miki abinci, na saki kwalekwalen da zai kaiki har kamaru, da sauri ta girgiza mai kai,Tace wlh ba zanje ba, banda kowa a chan, bauta mukeyi a gidan sarki, kuma na gudu da na koma zaa fille mun kai. Ka barni a nan kawai, Musbahu ya tausaya mata qwarai, yace zakije gidana? Da sauri ta daga mai kai, yace toh biyo ni, ba gaddama ta bishi, sunyi tafiya kadan kafin suka isa gida, tun daga soro yake qwala ma karime kira, ta fito, kai mallam ya kake kwala man kira kamar wani watan ramadana– turus ta tsaya ganin Alajana da gudu tayi daki ta na fadin bayanka Musbahu bayanka Aljana, yayi daria yace keee mutum ce, ta dan leqo tace daga ina? Ya kwashe komai ya gaya mata, shine nace ta zo ta xauna a gidan nan, Ashar ta saki, Wannan Alajanar zata zauna dani? Wannan Mayyar? A gidan nan? Wlh ba dai gidan nan ba, Musbahu ya fusata yace Gidan ki ne ko nawa? Toh sai ki hanata xama gidan nan idan kin isa.. Zuciya ta ci karime ta daka tsalle ta damqo gashin Aishalle
Page 3
GIDAN GANDU Biebee Isa
Aishalle ta sake ihun wahala, Musbahu ya chapko karime ya hadata da bango, ya ja hannun Aishalle yayi waje da ita, karime na kwance kasa amma bakinta be daina furta zagih da batanci ga Musbahu ba, Wurin Hajjo ya kaita, tayi sauri fa lullube jikinta da zanih, yace hajjo ga yarinya nan danAllah aba ta abinci kuma tayi wanka a bata kaya, Hjjo tace toh Yaya, Yace Aishalle ki saki jikin ki, ba abunda xai sameki anan, ga qanwata na zata kula da ke kinji? Aishalle ta gyada fuska,usbahu ya sakai ya fice,Hajjo tace zonan kinji qanwata? Aishalle ta matsa kusa da hajjo tana dari Dari don ta tsorata da alamarin karime, Jan hannunta tayi ta kaita har daki, ta zubo mata faten doya ta bata, sosai taci abincin nan. Sannan ta bata kaya ta sata tai wanka.
Kwanan Aishalle 5, ta sake da hajjo da yaranta, ita ke kula da Hafiz auta, wanka da wanki, haka kuma zata tasa su Hassan gaba tayi ta basu tatsunniya, kullum Musbahu Sai ya shigo ya ga ya take, Duk zaton karime Aishalle bata gidan, don ba shiga sassan hajjo takeyi ba balle ta ganta. Kuma ta hana su mudassir shiga balle su kawo mata rahoton gulma.
Wasa wasa har Aishalle ta samu wata 2 a gidan Rabiu, tayi clean ta qara wani irin kyau me firgitarwa. Kuma tana son yaran Hajjo har ranta, da taimakon Hajjo Aishalle ta iya abinci da wasu gyaran da ya kamata ace mace ta iya. Haka suke zaman su cikin aminci da yarda da juna..
******
Yaya kana ganin karime baza ta bamu matsala ba? Musbahu yace Rabiu ni ba raggon maza bane, na isa da gidana, Kuma bawai zan auri Aisha bane don na ci mutuncin karime sbd bata haihuwa ko wani abu, aa zan auri Aishalle ne don ina matuqar sonta kuma dan raya sunnan manzo. Rabiu yace toh shkn Allah shi sa a dace..
Hajjo ce ta ma Aishalle bayani, tace Mamman Hassan ba wai zan muku musu bane, amma wallahi ina tsoron matarshi, hajjo itama cikin damuwa tace kar ki damu kowa da halinsa zai zauna. Allah dai ya sa mu dace..
Yau ana sallahn jumaa aka daura auren Musbahu Zailani da