Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   25 / 27

72K to 75K   out of 79.4K words

ta shafa mai kadan ta shirya cikin grey maxi dress ba karamin kyau tayi mata ba don bata wani cika sanya maxi dress ba rayuwartaba sosai.









Saida ta shirya tsaff wanda kallo daya zakayi mata ka kara kallonta tsantsar kyau ilimi da wayewa da jinin sarauta su kadai ke magana a ko ina ,a hankali take saukowa daga part din inda banda ihu da kauyanci ba abinda ke tashi matane masu kyau a wurin kowa taci ado acikinsu mai kyau da daukar hankali suna mai cin abinci sunajin dadi kallo daya zakayi kasan suna cikin murna da farin ciki .



Hurriya kusan duka a tare suke kallonta saboda karar takalmin 5inches dake kafarta they were all in awe wannan kuma fa kallo daya tayi masu wanda kusan duk sun hadu a sunacin abinci a dining,



table din shake yake da different varieties of food and drinks desserts fruits ne appetizer babu dai tsiyar da babu sai lemuka masu kyau a ido da kuma dadi a baki masu tsananin tsada wanda daman ire irensu saidai à masarautar zaka gansu.









Bata zauna cikinsu ba don haka ta nufi kitchen domin dafa ma kanta wani Abu don ita she wasn t interested with all these ahankali take Neman kitchen din wanda har Allah ya bata sa a tazo wani daki a hankali ta bude don irin kofar nan ce marar kara tana Ganin ba kitchen bane ta jawo kofar saidai bata ida rufewa ba taji ana cewa ehh duk sun saki jikinsu yanzu zan hada ma kowacce acikinsu shayi bata ida jin sauran maganar ba ta koma neman kitchen







Saidai kuma taji bata bukatar komai maganar matar nan take dawo mata tanason ta cire ma anar maganar ko kuma abinda take nufi Amman ta kasa don haka tayi shiru tana kallon ceiling din dakin da aka kaita.





Knocking akayi mata saida ta dauki mintoci sannan ta tashi ta bude kofar tana bude kofar taga jakadiya cikin adonta na bakin lace mai kyau tana murmushi Hurriya dage girarta tayi irin ina jiran naji miye ya kawo ki Amman shiru batace komai ba banda murmushi ba abinda takeyi tace kinci abinci dai ko Hurriya kallonta take tanason ta karanci wani abu a fuskarta Amman taki the woman look fake don wannan dariyar da takeyi ba daga har cikin zuciyarta takeyi ba da alamar caring,cema Hurriya tayi ya kamata muje kici abinci saboda kada yunwa ta kama ki Hurriya dai sai kallonta take da fararen idonta jakadiya na juyawa tayi wani dariyar mugunta Hurriya najin sound din dariyar matar don haka ta rinka binta abaya







Har dining din sukaje ta jawo mata kujera yanmatan sai binta suke da kallo tareda alamar burgewa Hurriya zama tayi jakadiya zata fara zuba mata abinci tace no i will serve myself ahankali ta ajiye plate din jakadiya tana cursing dinta acikin ranta don tasan karshenta ya kusa zuwa yau bada dadewa ba suna a wurin aka rinka kawo masu ice tea mai wani irin kyau da kankara harda Hurriya aka kawo ma tea din







Saidai acikin yan matan jikinsu na rawa suka amshi ice tea din kowa ta kai bakinta, Hurriya kallon ice tea din tayi wanda shine taji ana magana akai kenan smirk tayi ta cigaba da cin abincinta cikin natsuwa ,kallonta jakadiya kawai takeyi, kasa daurewa jakadiya tayi tace Hurriya ga ice tea nan kisha shiru Hurriya tayi batare da tace mata komai ba ta cigaba da cin abincinta jakadiya kam tayi tunanin bataji ba duk da tafi tunanin ma taji rainin wayonta ne don ta kula yarinyar muguwar yar rainin wayau ce ,cewa nayi ga ice tea kisha Hurriya batace komai ba ta cigaba da cin abincinta har saida ta gama sannan ta amsa sai a lokacin jakadiya tagane taji kawai magana ce bataga damar yi ba tsoki tayi tareda kallon Hurriya data daga lemun zatasha wani dadi ne ya kamata ta juya da sauri zataje ta gayama Galadima good story din don yace sai ta kula Sosai Because daga ganin yarinya she s smart tun kallon farko da yayi mata ya gane hakan don haka yace mata she have to be very cautious akanta she wasn t expecting Hurriya zatasha shayin koda yake sune kadai suka san mi suka zuba ashayin kawai idan baka da gaskiya sai kaita kawo abubuwa a ranka haka ta kasance wurin jakadiya











Hurriya kam tana tafiya tayi tsoki tace bad bitch sannan ta tungular da ice tea din daman ance idan baka iya kama barawo ba to shi tsaff sai ya kama ka toh abinda ya faru kenan ta tashi tsaye tana tafiyarta tana kallon sauran yan matan da ba abinda suka tasa irin son duniya because how would they not notice their motives perhaps they aren t smart at all saboda ya za ayi ka yadda da mutane su dauko ku dayawa sannan akawo ku building mai kyau a baku kaya na sanyawa masu tsada sannan kuma abaku abinci irin wanda suke ci and sai kuyi trusting dinsu a wannan  duniyar masu kudin da zasuyi haka batare da cimma wata manufarsu ba suyi don Allah kadan ne she believe they knew everything from the start using dinsu akeyi they re just feeding their greeds while that s the most dangerous thing da tasani sabado tasan too much greed can take one to his grave tsoki tayi tana kallon hadamar da suke tace bunch of ignorant people sannan ta haye sama tareda shiga dakin ta sanya makulli ta rufe sannan tabar makullin ajiki saboda she doesn t trust them at all don kalar mutanen ne da they ll go at any length su samu abinda suke so don taga haka Sosai a idanun jakadiya .









Saida ta karayin wanka sannan tayi alwalar isha i ta fito mai ta shafa sannan ta sanya wata farar silk night gown da aka kawo mata







Banda kamshi ba abinda take don saida ta feshe kusan ko wani turare da aka kawo mata sannan ta zumbula doguwar hijab tayi sallarh isha i sannan ta kwanta bata wani dade da kwanciya ba bacci ya dauketa Mai dadin gaske .













Jakadiya kallon parlon takeyi duk yan mata ne Amman babu Hurriya babu alamunta kusan Dukansu bacci sukeyi da mamaki take bin kowa da kallo saidai ba gifcinta ko kadan shiru tayi tana tunanin inda taje don tunda har tasha shayin ya kamata ace tana kwance tana bacci jeka kadawo kawai takeyi tundaga katon parlon har zuwa dining Amman babu alamar ta ganin rashin Hurriya yayi yawa sai Zuciyarta tace taje ta duba ko tana daki cikin hanzari ta nufi dakin Hurriya ta shiga kwankwasawa kamar zata balla kofar Hurriya cikin bacci taji bugun kofa she hissed sannan tace who s that







Jakadiya sauke ajiyar zuciya tayi tace ki bude kofar Hurriya cewa tayi na fara bacci saida safe





Wani abu zan baki kada ya lalace ki bude ki amsa Hurriya shiru tayi ta koma ta kwanta abinta lallai wannan matar batasan wacece Hurriya Faisait Hamood she s the smartest girl in their palace and she believes that no one can outsmart her





Tanajinta tana knocking amman tayi shiru ta gyara duvet din tareda rage ac ta cigaba da baccinta.









Galadima ne yazo da wasu irin kyawawa mata kusan guda ashirin har part din sarki faizan wanda yake zaune cikin shigar shi ta alfamar fuskarshi sai annuri yake fiddawa na hutu da jin dadi





Galadima ya durkusa ya gaishe dashi amsawa yayi tareda kallon shi ahankali cewa yayi an daura? galadima da sauri ya durkusa yace eh an daura murmushi yayi sannan ya tashi ya kallesu kyawawa ne na ajin karshe don wasu farare ne







Mardiya aka kai mashi a daki sannan yayi ma Galadima murmushi ya shiga sarki Faizan kallon mardiya yakeyi tareda takaicin lalata rayuwar yara kanana da sukeyi Allah ya Sani bayasan kalar rayuwar nan wannan wace irin masifa ce ta gidan sarauta shi duk idan hakan ta faru yana mai dadewa yana shiga cikin damuwa ahakan yana ganin duk abinda yake sawa ayi masu gani yake bazai iya biyansu ba.





So dayawa yakan tsaya yayi tunanin cewar dolene sarautar ?abubuwa da dama zaka sadaukar dasu saboda sarautar ya kan tambayi kanshi yayi hakuri yabarma Khalifha sarautar ya nemi yafiya , Saidai duk lokacin da yayi wannan tunanin sai yayi saurin kawar da tunanin don bayaso zuciyar shi tayi sanyi but guiltness din ina zai kaishi kananan yara yake sanya a daura masu aure wanda auren ko awa 48hrs bayayi wanda ma anar auren kawai suyi consummating marriage din shikenan manufar auren ana gamawa kuma zai bada kudi Sosai ace a nisantasu da masarautar abasu gida da kudin sana a da duk abinda ake tunanin zasu bukata.





Abinda sarki faizan bai Sani ba duka basuyin abinda yake sanya su don ko auren ba a daurawa don hakanan ake kawo mashi matan a wulakance suke fitar dasu a masarautar babu wanda yasan abinda yake faruwa sai su sai Allah, ko reward din da yake badawa ba wadda ake ba mawa acikinsu Allah dai ya kyauta







Kallonta yake so innocent and beautiful ahankali fuskar Hurriya ta rinka dawo mashi tunda yake bai taba ganin mace mai kyaunta ba saidai yayi mamaki da bai ganta ba a masarautar saurin kawar da maganar yayi tareda kara kallon farar yarinyar dake kwance saman lallausan gadonshi.









Hurriya kam yau da wuri ta tashi don tun ana kiraye kirayen sallahr asuba ta tashi don haka ta samu sallahr asuba da wuri don koda tagama sallah saida tayi wanka sannan ta samu ta koma baccinta mai dadi.









Galadima banda bala i ba abinda yake ma jakadiya na rashin Hurriya itakam jakadiya tsaye tayi tana mamaki don bataga abun tada hankali anan ba saida ma anar data karanta a duk maganganu Hurriya wanda a bayyane komai yake ,shine yafi bukatar Hurriya may be when he s done sleeping with her sai ya aika ma sarki ita hakane duk ya nuna a fadan da yakeyi don kamar zaiyi hauka.





Karfe 11:00 ta tashi saida tayi bedding gadon data kwanta cikin tsari sannan ta gyara komai ta shiga toilet tayi brush hade da tsala wanka tareda wanke gashinta da shampoo mai kamshi na cantu da conditioners masu sanyi dadin kamshi a toilet din tayi drying kanta ya bushe Sosai sannan ta fito





Zama tayi saman vanity table tana kallon kanta a mirror gashinta sai salki yakeyi mai ta fara shafama gashin sannan ta shiga combing dinshi yana sauka har abayanta hair style ta farayi ma kanta masu kyau duk wanda tayi sai taga baiyi mata yanda takeso ba don wanda ta kwance yanzu sai ya maida ta kamar wata baby ita kuma tafi bukatar abinda zai sanyata tayi looking matured don haka kawai ta daure duka gashinta ta nadeshi can tsakiya sannan ta sanya deodorant da sprays kallon kayan da aka kawo mata tayi wani wandone designer yayi capturing dinta wanda duk a farfashe yake ko ina ba kamar ma cinya shiryawa tayi cikin blue wandon crazy da farar riga







Banda kamshi ba abinda takeyi fuskarta fayau sosai skin dinta Sai shining da glowing kawai yakeyi kallon kanta tayi a madubi ttaga she s okay don haka ta sauko kasa







Galadima da yake zaune a falon sumar zaune yayi yana kallon yanda take tafiya kamar dagangan takeyi kamshinta ya bade ko ina a parlon gashin kanta sai wani daukar ido yake a she s natural ,everything about her is natural she s almost perfect not just perfect she s beyond perfection don ba wani abu da aka bar mata a hallita wanda za ace ya zama abun kushe ga mutane babushi sai dai halaye Amman hallita kam babu kushe





She s beautiful and perfect beyond words don kalamai baza su iya rubutawa ba dogayen kyawawan hannuwanta wanda basu da komai amman suna da matukar tsari da daukar hankali don kamar bata daukar ko tsinke







Ko wanne a wurin saida yasha jikinshi don harta yan matan dalala suka saki baki suna kallonta confidence dinta kam har yayi yawa Because all eyes on her Amman kamar ma kara gyara tafiyar ta takeyi kamar ma she s looking down on all of them haka tazo ta ratsa su babu ko kallon arziki bare har suyi tunanin zatayi masu magana duk tabar kamshinta da kwarjininta da uwa uba mulki da sarauta





Dining ta zauna tareda zama ta zuba komai accordingly yanda ta saba cin abinci ta faraci





Duka idanun akanta yanmatan were all in awe don yadda take cin abinci cikin tsari tareda maida hankali abun burgewa ne sosai Galadima kam shan majina ya fara yana marmar da ido don gani yake duk abinda takeyi saboda shine she s trying to seduce him she s also a harlot don yanda take cin abinci kamar dagangan gani take. she is cautious saboda kawai ta burgeshi





Cikin jiji da kai tareda baza babbar riga ya tashi yaje wurinta saida ya gama kalleta tsaff sannan yace Hurriya yan mata an tashi lafiya Allah ya sanya dai wurin yayi maki idan baiyi ba ma sai na sanya a canza maki







Hurriya kamar batasan Allah yayi hallita a wurin ba ta cigaba da cin abincinta maganar duniya yayi mata tayi banza dashi shikam Galadima dizigin nan ya shige shi don ba a taba ci mashi fuska ba irin wannan da mutunci shi da kimarshi wanda ba wanda baya respecting dinshi a masarautar dubannin mutane wanda idan yayi magana ake rububin amsa mashi don sunajin kamar sarki yayi maganar.







Who s she what did she think of herself maganar da yake niyyar yi mata kenan kafin ya furta mata maganar har ta tafi batare data san akwai mutum ba bare har tasan ita ake jira







Galadima shiru yayi jakadiya kam da sauran yanmatan kasa gimtse dariyarsu sukayi suka fara kyalkyata ta irinta ban haushi. Galadima fuu ya fito yana Nema Hurriya don ya wulakanta ta saidai ba inda bai dubata ba kamar aljannah babu ita.











Hurriya kam tana fitowa daga Chamber wani garden ta fara hangowa wanda babu abinda babu tunda ga nesa wurin yayi capturing dinta.







Ahankali cikin natsuwarta take tafiya har tazo wurin tunda daga nesa yake kallonta har dariya yayi ganin yanda tayi twitching bakinta tareda frowning face dinta





Garden din tazo sannan taje ta zauna saman swing tana kallon yanda bishiyoyi ke kadawa wani solace ne ya fara shigarta don har wani lumshe ido takeyi kamar kuma an tsikareta ta tashi Daidai iccan Ruman ta tsaya sannan ta katso guda daya akwai ruwa akusa da wurin yana ta zuba saida ta daureye ruman din sannan ta fara kokarin barewa





Wani irin sligh murmushi tayi mai sanyi alamar it s her favorite fruits kuma ta dade batasha shi ba saidai har ta dauki daya Because she can t wait to taste it sai tunawa tayi a tsaye take, bata fara tafiya ba taji saukar muryar sarki faizan yace duk abinda kika dauka nan kamar sata kikayi saboda bana ki bane Hurriya juyowa tayi tare da zuba mashi idanunta masu kyau da kaifi saidai batace komai ba har ta koma wurin swing din ta zauna sannan ta fara shan ruman ahankali kallon yanda takesha cikin natsuwa da burgewa yayi don har wani lumshe ido takeyi alamar abun nayi mata dadi murmushi yayi ya cigaba da kallonta kamar ya samu tv har tagama







Saida tagama tace mashi i will repay you in the future kallonta yayi yace ya za ayi Na yadda saidai ki biyani yanzu shiru tayi tana kallonshi murmushi yayi mata mai kyau don shima badao kyau ba don a wurin shi subira ta dauko kyau



Yace mata you can pay me now Hurriya tsotsar bakinta tayi sannan tace I don t have anything to pay for now sarki Faizan cewa yayi just promise me with anything i ask daga mashi kai kawai tayi cewa yayi be my friend kallonshi tayi mamaki fal a fuskarta amman babban mutum zai zama friend dinta girgiza mashi kai tayi alamar aa sai yace mata you already promised me,so you can t take back your words







Zama yayi a swing din dake opposite dinta sannan yace mata kada ki damu I can be a father and also a friend at the same time daga mashi kai tayi Because he doesn t look like someone da zai iya cutar da ita saidai batasan cewar sarkine zaune da kanshi





Fira ya rinka janta dashi saidai abun mamaki bai taba ganin miskilin mutum irinta ba ta bashi duka attention dinta Amman hardly yaji tayi magana amman tabbas hankalita na akanshi kuma tanajin duk abinda yake fada saida bata cika magana ba,







Saida firan yazo karshe tukuna ya farajin maganarta jefi jefi ta fahimce shi sosai ta magana ,kamar yana fama da damuwowi dayawa she knew alot of people like them they just need a shoulder to cry and a friend to rely on,she understands all the pain that he s going through ,ta conversation dinsu shiyasa ta rinka kokari wurin tana taya shi magana.









Sun dade suna magana saida call ya rinka shigowa wayar sarki Faizan non stop saidai yaki dauka Hurriya tace ya dauki wayar sai yaki ganin haka tayi mashi Bankwana may be he needs his privacy but trying to be kind itakam ina ruwanta





Koda tabar garden din ba inda ta nufa sai dakinsu don duk yau bataje ba kada hankalisu ya tashi don tasan halinsu da sanya ma rai abu hada wasba kullum Hurriya takan zauna tayi tunanin yanda ta canza sosai kamar ba ita ba she réa do change alot don da bata barin damuwar kowa ya dameta ba abinda ta Sani irin kanta amman yanzu komai ya canza ba kamar da ba











Galadima ne yake kiran sarki Faizan wanda baijin dadin hakan ba don ya kashe mashi firar da yake da his little fairy cikin tashin hankali Galadima yace aikin wuka yayi aike yace muyi sauri mu gano wannan yarinyar saboda masu nemanta sun yawaita gab wani abu yake da niyyar faruwa sannan kuma ya bada sako a fada maka Khalifa yana gani





Sarki faizan wani irin fargaba da zullumi da tsoro kawai ya shiga abubuwa sunyi mashi yawo damuwa itace kullum abinda

25 / 27