Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   22 / 27

63K to 66K   out of 79.4K words

sai adon dake tsakankanin hakoranta yaji dadi da yaga dariyar Hurriya don yasan yau abinda zai rinkayi mashi yawo kenan har yayi Bacci.saidai yaji dadi sosai da Hurriya ta zamana cikin mata mararsa dariya da kilan sai ya kusa mutuwa inda tayi Dariyarta yaga ana kallonta.











Hurriya ta dade a part dinshi tareda fayrouz sannan ta koma dakinsu tana zuwa tayi sallolinta da batayi ba.





Inna hanne ta iske da wasba aiko da murna wasba ta tarbeta tace tayi missing dinta jiya da daddare daga mata kai kawai Hurriya tayi inna hanne kallonta take da kayan Khalifa har zata tambayeta ta fasa saboda tasan ko wacece Hurriya zata iya bada shedarta







A wurin su inna hanne da wasba ta wuni bintu ma tazo ta zauna Hurriya idan ta kallesu tanajin wani irin nauyi azuciyarta duk da bata cika yadda wani abu yafi karfinta har haka ba don tasan bazata dade ba zata tafi.







Amman hausawa sunyi magana da suke cewa sabo turken wawa tasan cewar zataji ba dadi idan har ta tafi Amman ya zatayi haka rayuwarta tazo mata







Kwanciya Tayi bata wani dade da kwanciya ba bacci ya dauketa mai dadin gaske don ba itace ta tashi ba sai bayan magriba alamar period taji wanda tana fin wata da wattani batayi shi ba dan bata rai tayi sannan ta fita zuwa kitchen wurin inna hanne taje ta amshi ruwan zafi sannan ta nufi toilet ta gasa jikinta da ruwan zafi mai kyau











Saida ta sanya pad dinta sannan ta shirya cikin pink rigarta mai kyau iya gwiwa ta tsaya mata turare ta fesa sosai ta kara shafa ma gashinta mai sannan tayi ma wasba Bankwana wasba kallonta ta rinkayi don kamar ta bita haka takeji Allah ya dora mata soyayyar Hurriya



Tanaji tana gani Hurriya tabar dakinsu ta nufi dakin Khalifa Dukansu suna parlon ta shigo batare da sallama ba Saidai ganin mutum kawai sukayi wani irin kamshin dadi takeyi mai sanyi wanda ba wanda bai shiga hancinshi ba acikin mazan.fayrouz wani irin mugun kishi yakeji yanda take tafiyar catwalk wanda ta dauke ma kowa hankali a wurin banda mutum daya



Harta Khasheem saida ya kalleta ya kasa janye idonshi daga kanta







Kallonsu tayi sannan tace kallon na minene maleek basarwa yayi Khasheem ne yace girl can t lie to you but you re hot fayrouz ne yadan bugi kanshi yace please stop yana bata fuska Khalifa dai yanajin su Amman baice kala ba don tashi yayi ya haye sama ya barsu







Khasheem ne ya kalli Hurriya yace I m Hungry please give us food dan kallonshi tayi tareda daga mashi kai sannan ta shiga kitchen fayrouz ne ya biyota ya rinka yi mata fira.





Koda suka gama suka jera table din Khasheem ya kira Khalifa ta landline yace yazo suyi dinner.







Bai wani dauki lokaci ba yazo da fararen kaya na Loro Piana wanda suka fito mashi da haiba da kyau banda kamshi ba abinda yakeyi don wurin duk ya dauki kamshin shi





Hurriya ita tayi serving kowa acikinsu sannan tayi serving kanta kamar ba yar aiki ba fayrouz kam dadi kasheshi ganin Hurriya ta zauna zataci abinci dasu they ate in silence don kowa yanaji da table manner dinshi









Wani karamin parlo suka shiga Dukansu su ukkun Hurriya kuma ta tattara duk abinda sukaci ta wanke a kitchen saida ta gyara ko ina da komai sannan ta dauki ledarta data sanyo items dinta da zata bukata ta haye sama





Dakin Khalifa kamar dakinta don tana shigowa ta shiga toilet tayi wanka mai dadi tanata wani irin kamshi kayanta ta sanya a washing machine din dake a toilet din ta wanke su tass sannan ta fito daure da bathrobe grey mai kyau







Saida ta shafa mayukanshi tanayi tana bata fuska don everthing there ,is for men nothing feminine raising browse dinta tayi sannan ta bude wardrobe dinshi ta zaro sabuwar jallabiya milk ta sanya wadda ta rinka yimata yawo ajiki turarenshi ta fesa sannan tazo saman kujerarshi ta zauna shiru shiru bai dawo ba ta dade tana zaune don har tafi awa daya ga wani bacci datake bala en ji ga sanyi da yake shiga har cikin kashinta





Dabara ce tazo mata gwara ta kunna tv tayi kallo don tunda tayi wanka nan takejin wani irin bacci.





Kunna smart tv mai matukar kyau da tsada tayi katuwa ganin Netflix account ya sanyata shiga har zatayi logging asalin account dinta na hurain ta tuna kawai sai ta sanya YouTube wakar stability ta ayra star ta sanya kawai



Hurriya tafara enjoying wakar Amman tana cikin jin wakar batasani ba baccin gajiya ya dauketa.





Agajiye yake don sai karfe 1:00 suka gama rapping off na aikin da sukeyi ba abinda yake bukata irin ya kwanta ya Sauke gajiyarshi .



Yana shigowa toilet dinshi ya shiga tareda wanka bai tsaya wani kyale kyale ba kawai kayan bacci ya sanya yazo ya kwanta Saidai yana kwanciya yaji mutum ajikinshi tareda saukar numfashi da yake Khalifa ne ba tareda shakka bare tsoro ba ya bude idonshi tareda sauke matasu ahankali yake binta da kallo sannan yayi tsaki yace stubborn maid ya tashi ya bude screte room dinshi ya kwanta.





Bai wani bacci Sosai ba don karfe 4:00 ya tashi ya gabatar da nafila har asuba sannan yayi wanka ya fita sallahr asuba har ya fito sallahr asuba Hurriya na dukunkune cikin bargo tana baccinta mai dadin gaske.







Karfe 7:00 har yagama shiryawa haka ya fito falo inda duka abokananshi sun shirya kowa sai kamshi yakeyi ba karamin kyau sukayi ba don komai da suka sanya is screaming money don kallo daya zakayi masu ba lallai ka iya dauke idonka ba Saidai kwarjinin su bazai bari a tsura masu ido ba.



Khalifha hannunshi rike da walking stick as usual mai tsananin kyau da tsada haka suka jero su hudu aka bude masu farar limousine convoy dinsu ya dauka sai airpot.







Hurriya kam koda ta tashi mika tayi tana kallon dakin Khalifa mai tsari.

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: M.Qamar



54

Kallon dakin Khalifa mai tsari da kyau tayi sannan ta sauko ahankali ta shiga toilet saida tayi activities dinta sannan ta tara ruwa a bahon wankanshi cike mai kamshi tayi wankanta mai dadi.sannan ta ziro dogayen kafafunta da banda silbi da salki ba abinda sukeyi cikin bathrobe dinshi da suke hang ta dauki sabuwa ta sanya sannan ta fito saida ta bude wardrobe dinshi ta samu kaya masu rashin nauyi kuma da alama zasuyi mata ta sanya





Gyara dakin tayi tass tareda wanke toilet ta sauko kasa sannan ta shiga katon kitchen dinshi tayi yamrita da coconut milk masu dadi har tagama komai tayi arranging ba wanda ya fito shrugging kafadarta tayi irin I don t care ta zauna ta zuba komai kadan kadan kuma dai dai cikinta a hankali ta rinka cin komai har tagama tana gama cin abinci ta shiga kitchen ta wanke kayan data bata sannan ta gyara kitchen din.







Wani takarda ta gani a saman kitchen island ahankali takai hannunta ta dauka note din fayrouz ne yace mata tayi hakuri baiyi mata Bankwana ba they re gone for a business a in Mexico she should take care of herself for him sannan yayi mata kalamai masu nuni da zaiyi missing dinta Hurriya kam cikin dustbin ta sanya takardar.













Saida tayi bacci wanda ya isheta sosai sannan ta fita jikinta sanye da kayan Khalifa wanda duk inda ta gifta kallonta akeyi.







Daidai zata sha kwana taga shaho da kaura suna kallonta kallonsu tayi sannan tayi tafiyarta.



A bakin kofa tagasu Hansa u da su barira da wasila da suwaiba Dukansu dai. Hurriya kam kallo daya tayi masu ta shige daki while su kuma sun kura mata ido tunda ta taho har ta bace masu dagani.





Ahankali ta zauna sannan ta kalli wasba da take kwance tana bacci Hurriya kallon kamanninta takeyi don ko zata tuna dawa take mata kama Saidai hakan ya gagara, gashi gareta wasba sosai kuma baki mai kyau da cika irin na Hurriya

Hurriya batasan ya akayi ba kuma batasan garin ya hakan ta faru ba Amman tanajin tsananin kaunar mutum uku a masarautar Qamar ko kuma mutum biyu saboda ai Bintu tun akauyensu take jin kaunarta har cikin ranta.







Bata shirya ma hakan ba saboda tasan kalubale da sarkakiyar datake cikin rayuwarta kuma tasan cewar itadin ba mazauniya bace ako wani lokaci zata iya canza wuri Saidai ya zatayi itama she got heart like every human being she have feelings and emotions Saidai barrier dasuke dashi ta riga ta dakatar dasu yanda bazasu taba kawo mata cikas ba a rayuwa.





Bintu ce ta shigo ta zauna kusa da Hurriya tana kallonta cike da so da kauna don babu abinda Hurriya batayi mata ba.Tayaya zata fara tunanin cin amanar Hurriya bayan tasan yadda Hurriya take kaunarta duk da bata nunawa idan har taci amanar Hurriya tabbas amanar Allah zata cita ina bazai yiwu ba .







Hurriya kallon Bintu take tanaso ta karanci damuwarta don banda ramewa ba abinda takeyi kuma damuwa tsoro da alamar firgice duka ya nuna a fuskarta. Bintu kam duk ta tsargu sosai da irin kallon da Hurriya takeyi mata ba abinda take tsoro irin Hurriya ta tambayeta miye matsalarta don Hurriya nada matukar kwarjin idan kana kallon idonta bakasan lokacin da zaka fada mata gaskiyar lamarin ba.









Bintu da sauri tace Hurriya bari naje na amshi aikina na kitchen ban karasa ba nazo nan.



Daga mata kai kawai Hurriya tayi don ta lura da ita so take ta tsere mata.shiru Hurriya tayi trying to figure out what was bothering her friend Saidai to no avail ta rasa minene Amman zata gano da kanta.









Bintu na fitowa a firgice kuma a tsoroce Saidai ganin da tayi masu kaura da shaho yafi firgita ta don batayi tsammanin ganinsu ba anan.kallonta Dukansu suka rinkayi irin muna jiran bayaninki ganin Bintu tayi shiru kamar bazata basu amsa ba shaho da baida hakuri yace ke malama kin zuba mata ko baki zuba mata ba.shiru bintu tayi cikin wani irin zafin nama ya wanka mata mari yace magana fa nike maki







Bintu da wani irin rude ta dafe kai tace mashi zan zuba mata à abincin da dare yanzu tana kallona ne shiyasa ban sanya ba kaura ne ya kalleshi alamar ya kyaleta Bintu kam ajiyar zuciya kawai ta saki sannan ta dukar da kanta suna barin wurin ta samu wuri ta zauna





Su barira ne da Hansa u suka zo sukace shawara ta rage taki yarinya ki zuba ko karki zuba munafuka



Barinta sukayi da sakin baki.





Galadima kanshi akasa ya mika mashi farin kyale da zanen wani abu ajikinshi mai martaba Faizan ya kalleshi alamar yanason yaji karin bayani





Allah ya taimake ka yace tana acikin masarautar nan Saidai har yanzu ya kasa ganeta Saidai wannan zanen tabbas ajikinta akwai wannan zanen don ba karamin aiki yayi ba kafin ya samo wannan zanen saboda akwai kariya tattare da ita sarki Faizan kallonshi yayi tareda mika hannunshi ya amshi handkerchief yana kallo wani murmushi yayi na gefen baki tatoo ne na Heral palace dole ake cewa wanda ya sameta zaiyi sarauta kowace iri.



Galadima yace yawwa maganar da kayi man nayi ma jakaddiya magana tace ayi sauri ayi kafin Khalifa ya dawo





Shiru sarki yayi yana nazarin abinda Galadima yace don tabbas a irin wannan lokacin ya kamata ayi abun nan don yadda Khalifa yabar masarautar ,don yanzu yana cikin shakka saboda yadda Khalifa yazo ba tareda ya sanar da kowa ba yasan zai dawo ba tare da ya sanar da kowa ba kuma koda yake sarki yasan Akwai abubuwa da dama da bazai iyayi ba agaban idon Khalifa ba saboda yasan waye Khalifa and what he s capable of doing.



Sarki yace ku samo matan kamar yadda akeyi ita kuma yarinyar ya za ayi mu ganeta inji Sarki Faizan



Galadima yace Saidai a sanya jakadiyya ta duba manah sai asan mi za ace masu a masarautar. sarki na am yayi da hakan sannan Galadima yayi Bankwana ya fita.













Hurriya wayarta ta dauko tana budewa taga alert din 2.5m as promise don tun ranar da Khalifha ya faracin abinci chief of security ya cika alkawarinshi ya tura kudin ajiyar zuciya ta sauke don bazata wani bata lokaci a masarautar nan ba saboda kwata kwata zuciyarta na bata akwai matsala



Kallon kudin dake cikin account dinta tayi 3.5m don su ayyo sun sanya mata kudin Amman batayi aikin ba ita bama wannan ba exist permit din da zata fita masarautar shima kanshi wani Abu ne batasan inda zata samo ba. Da ace chief of security yana anan da tayi mashi magana ya samo mata Saidai sam bata ganshi ba kwana biyu.









Inna hanne tare suka shigo da Bintu bayan isha i lokacin Hurriya har tayi wanka ta kwanta don yau wani irin bacci taji tanaji sosai inna hanne tace Hurriya ma har tayi bacci ashe, ga abincin da na kawo mata kuma,

bintu ce tace ki ajiye abincin nan idan zan tafi sai intada taci. Inna hanne batayi tunanin komaiba ta ajiye abincin ta juya ita kanta wasba tana gama isha i ta kwanta alamar ta gaji don wasba akwai hidima da yake batada aiki kwata kwata daga nan sai tayi nan kullum aikinta kenan ta tsokani fada ba wanda yake biye mata don kusan duk wanda ya kwana ya hantse yasan wurin wadda take zaune a wurinta don Hurriya ta zame mata uwa da uba ba kalar gatan da bata nuna mata duk abinda takeso najin dadi indai tanaso Hurriya bata taba gajiyawa wurin sai mata harta kudi zata zo tace ma Hurriya tana bukata haka Hurriya zata zaro ta bata Saidai wasba ta rinka dariya da murna taje ta kashe kudin





Duk da Hurriya bata wani nuna alamar soyayya ko tayi magana dasu Amman kallo daya idan kayima inna hanne Bintu da wasba zakasan they re very dear to her don yadda take kashe masu kudi take kyautata masu kamar batasan ciwon kudinta ba.





Don ba afi kwana hudu ba saida ta sanya aka dinka ma bintu da inna hanne sabbin hijabai masu kyau haule reza ta bama kudin aka dinko masu na Daidai karfinta harda sabbin takalma don taga Bintu batada wasu takalman kirki sai ta sanya aka siyo masu itada inna hanne gabaki dayansu koda aka kawo haule reza ta sanya ta kai masu aiko sukayi ta murna suna sanya mata albarka hade da addu oi kala kala don sun san ba aikin kowa bane sai na Hurriya duk da tana nuna bata ita bace ba Amman ankare suke da ita acikinsu.







Bintu kallon Hurriya ta rinkayi da take bacci peacefully kamar batada wata damuwa a duniya murmushi bintu tayi wanda yafi kuka ciwo tace ko bacci kike kedin mai kyau ce kuma mai kyawawan halaye duk da cewar kin ki bari muga kyakkawan halinki kin boyesu kota ina kamar yadda kika boye kanki ta ko ina ta yadda ba wanda zai iya fahimtar ki ko ya gane kedin wacece Amman Hurriya ke ta daban ce a rayuwarmu kin taimake mu alokacin da muke bukatar hakan kin kwatar mana yanci a lokacin da rayuwa take barazana a garemu anya zan iya aiwatar da abinda su shaho suka umarce ni ?anya ba kaina na zalunta ba ?don laifin dazan aikata bazan iya yafe ma kaina shi ba.





Kuka ne yaci karfin bintu tana kallon Hurriya data dan sha lips dinta masu kyau da daukar ido long eye lashes dinta da suke kwance kamar ta sanya mascara double eyelid dinta wanda ya taimaka sosai wurin shaping idanunta sai dogon hancinta mai kyau wanda ya tafi kamar an zanashi she s beautiful everything about her is beautiful don mutum ko shine karshen hasadda to sai yayi hakuri ya kyale Hurriya don duk bala en hassadar mutum da kishi sai ya barta





Bintu duk cikin ranta take karanta hakan a hankali ta jawo kular da baba hanne ta kawo mata sannan ta barbada maganin dasu shaho da kaura suka bata,saida ta tabbatar ba a gane mi ta sanya don duk ta dan cakula shi don tasan yadda Hurriya take da kaifin basira da gane abu Hurriya is very smart daga kallo daya takan karanci abinda mutum yake tafe dashi tasha ganin yadda take dealing mutane sosai so she have to be very cautious





A hankali ta fara ambatar sunanta shiru shiru bata amsa ba Bintu kara daga muryarta tayi yadda zatayi ringing cikin kwakwalwarta aïko hakan ta faru don cikin alamar bacci tace Bintu ya akayi ?



Hurriya ki tashi kici abinci tun dazu inna hanne ta kawo kina bacci nace bari na tadaki tunda ta fara maganar Hurriya take binta da wani irin kallo Bintu tsarguwa Tayi tace kodai na kawo maki ruwa ne ki wanke hannunki Hurriya daga mata kai tayi aiko Bintu wadda takejin kamar tana saman kaya saboda irin kallon da Hurriya ta rinka jefo mata mai wuyar fassarawa bata wani dauki lokaci ba sai gata da ruwa da uban yawa a kwano tace gashi





Tashi Hurriya tayi zaune har lokacin idonta bai bar kan Bintu ba saida ta wanke hannunta sannan ta janye idonta ta jawo kular Bintu banda faduwa ba abinda gabanta keyi Bintu Hurriya dagowa tayi ta kalli Bintu da tayi zugum don kamar za ace mata arr ta arce sannan takai 1spoon.

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: Masarautar Qamar



55

Ahankali takai 1spoon Daidai saitin bakin Bintu tana kallonta alamar ta bude bakinta taci abincin a zabure Bintu ta girgiza kanta tareda ja baya tace na koshi Hurriya na koshi fa. Hurriya shiru tayi sannan tace inci?bintu wasu irin kwalla suka rinka zubo mata masu zafi tana kallon Hurriya tace kada ki ci abincin





Hurriya kallon bintu takeyi wanda duk wanda yaga kallon zai tabbatar da cewar she s broken sannan ta girgiza kai .bintu kallon irin disappointing look din da take bata wanda bata taba ganin irinshi a wurinta ba ya sanya da sauri ta durkusa mata hawayenta nakara yawaita kamar an kunna famfo tace na tuba ki yafe mani Hurriya ba yin kaina bane bansan ya zanyi da raina ba kiyi hakuri don Allah tanayin maganar da wani irin tsoro da kuma tunanin irin hukuncin da Hurriyar zata iyayi mata kuka Bintu takeyi mai taba zuciya tareda

22 / 27