Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   15 / 27

42K to 45K   out of 79.4K words

and poisonous don aura dinshi ta cika ko ina





Ba inda ya tsaya sai inda wurin da taron manya mutane suke zazzaune kallon kujerar da yayanshi yake zaune yayi



While yayan shima idonshi akan Khalifha murmushi Khalifha Qamar yayi wanda mutane suka fi bama irin murmushin suna Devil smirk



Girmamashi ake ana gaishe shi duk inda ya wuce wata kujera akazo aka ajiye mashi ya zauna suna kallon polon





Kusan kowa a wurin a ranshi yake tambayar mai ya kawo Khalifha Qamar nan wurin miyake yi yana makaho wanda bai gani saidai ba wanda ya bari maganar ta fito







Murmushi Khalifha yayi don haka yayi ma chief of security dake gefenshi alama aikam da sauri ya matso





Chief of security yana gama magana da Khalifha ya nufi wurin wani wanda ke rike da usur magana yayi mashi a kunne.









Manage this please ba yawa pagae din yau. Very busy



Share ,comment and like



Love you all

[5/28, 3:32 PM] +234 802 952 0062: <Masarautar Qamar

The mysterious palace



By Khadija (KMU)



39&40



Announcement din da akaji coach din nayi ne ya sanya hankalin kowa ya karkata ya koma wurin shi fargaba ce ta mamaye mai martaba sarki Faizan wanda yake zaune kan kujerar mulki







Wurin shiru ya dauka kamar babu kowa a wurin cikin karfin da Allah ya bashi ya mike zuwa filin polo din hannunshi rike da sandar shi



Wani kosasshen doki ne aka fito dashi fari Mai wani irin kyau da daukar ido chief of security ya mika ma sandar shi sannan ya haye dokin





Wanda yaci wasan polon daga masarautar kano ya fito don haka idonshi akan Khalifha Qamar wanda yake makaho mizaiyi yanzu kuma bayan angama wasa kuma ya za ayi ayi wasa tsakananin mai gani da makaho gaskiya kilan barcin rashin ido to yana da tabin hankali na musamman don ba wanda ya taba cinshi a fagena wasan polo bare kuma makaho



Gaskiya an mutunci shi da kuma kimarshi saboda a rasa dawa za a hadashi wasan sai makaho





Tun kafin aje ko ina zaiyi maganin shi,

Khalifha kallonshi yayi sai kuma ya maida hankalinshi wurin dokin



Tambayar su akayi sun gama shiryawa dayan yaron ya bada amsa while Khalifha Qamar yayi shiru





Ganin kallon da Khalifha yayi ma chief of security aiko nan da nan chief of security din yace yerima ya shirya da wani irin zafin nama Khalifha ya fara gyara dokin shi





Mabusa aka hura masu wanda yasanya acikinsu kowa ya fara buga wasanshi





Ba wanda hankalinshi bai karkata wurin wasan ba saboda abun da mamaki makaho da buga wasan polo



Fargaba da tsoro ya cika zuciyoyin mutane da dama wanda aciki harda Danuwanshi wato Sarki Faizan Qamar







Zuciyoyin mutane da yawa sun buga jin ana announcement na cewar Khalifha yaci wannan wasan



Rabonshi da irin wannan wasan shekara Goma kenan kuma ko a shekara gomar da suka wuce Khalifha Qamar bai taba faduwa wasan polo ba don duk inda yayi sai yaci







Yanayin sarki Faizan ya canza Sosai ba abinda fuskarshi ke nunawa irin zallar bacin Rai da damuwa Anya Khalifha bai warke ba abinda ya tambayi kanshi kenan





Ya akayi yaci wasan?to ai Khalifha Qamar da zuciyar shi yake gani bada ido ba don ba abinda bayayi duk da baida ido polo ne kawai ya Daina wannan kuma ba wanda yasan dalilin hakan

Sarki Faizan tausar zuciyar shi ya farayi a hankali yace haba dai kadaina irin wannan tunanin Khalifha shida ya gani kilan har abada amman ina







Galadima ne yadan karkato yayi mashi rada wanda a wani irin duniyance launin fuskarshi ta canza ta dawo mai dauke da murna





Saukowa yayi daga kan dokinshi sunanshi kawai ake kira wato Khalifha Qamar Dan sarki Qamar yadda yake tafiya zai tabbatar maka dacewar shi din sarki ne don kwarjinin shi bugun xuciyar makiya da yadda yake tafiya kamar yanajin tsoron taka kasa Amman acikin tafiyarshi zaka hango karfi kuma da jarumtar da Allah yayi mashi









Sarki Faizan ne ya sauko daga kan kujerar mulkin shi yana mai jin faduwar gabar haduwar shi da Khalifha dan Karamin kaninshi kuma da ya zamar mashi babban kalubale a rayuwarshi





Gardawan Guard din Khalifha ne suka zo da sauri suka tarbe saitin da sarki Faizan yazo tare da kareshi suna fitoda manya idanunsu waje da bindugu





Shiru wurin ya dauka kowa idanunshi bude suna kallon ikon Allah sarki fa dakanshi





Black Americans ne Guard dinshi Giant Kamarshi wanda daga gani they are loyal kuma sun san aikinsu





Ba wani alama ta girma da suka bama sarki Faizan abu daya suka Sani cewar bai isa ya gifta layin da suka ja ba kuma tabbas idan ba Khalifha ko chief of security yayi masu magana ba bazasu taba barin shi ya wuce ba





Da sanda Khalifha yayi ma chief of security alama da subar shi yazo aiko yana masu magana Dukansu suka matsa





Murmushi sarki Faizan yayi tare da zuwa wurin Khalifha ba wani bata lokaci ya rungumeshi Khalifha shima rungumeshi yayi back tare da cewa it s being a long time brother I miss you inji sarki Faizan Qamar





Khalifha Qamar wani Devil smirk yayi tare da cewa nazo na amshe sarautar masarautar Qamar Rest assured kaga bazaka kara missing dina ba tunda muna cikin masarautar Qamar



A hankali yayi maganar yanda ba wanda ya isa yaji face sarki Faizan Qamar



Murmushi sarki Faizan yayi sannan yace banda abun Khalifha ka taba ganin inda makaho ya sarauci Al-umma





Ko kallo Khalifha bai kara bin sarki Faizan dashi ba bare yayi tunani amsa ya nufi hanyar motar shi don shikam ya gama magana idan kuma yariga ya gama magana to ba wanda ya isa ya sanya shi ya maimaita miskili ne sosai



Manya manya mutane ne sukazo wurin Khalifha da niyyar yi mashi magana amman security s dinshi suka dakatar dasu ta hanyar daga masu hannu da nuna masu bindgogi







Tashin kurar mota kawai kakeji a wajen wanda hakan ya sanya mutane dayawa cikin alhini da fargaba







Sarki Faizan Qamar har baya Ganin gabanshi saboda tsananin bacin ran da yake ciki da kyar ya samu ya lalubo murmushi a fuskarshi yayi ma manya mutanen dake wurin sallama





Khalifha Qamar cikin motane ya saki wani murmushin mugunta sannan ya kwanta akan kujera tare da lumshe ido.





Wanda sukayi polo da Khalifha kam ya raina kanshi sosai don daga baya ya gane cewar Khalifha jarumi ne.







Hurriya kam Al-Amarin zinariya yanzu ta rasa mi zatace saboda kullum akwai abubuwan da take badawa akai mata na duniya duk abinda ta bada kuma haka zata sanya a maidashi ba tare da ta kallah bare kuma har ya burgeta





Wasba kam ta samu wuri don ba karamin son Hurriya take ba kuma dawowa datayi a wurin shine babban abu najin dadi data samu a masarautar Qamar Don tunda ta dawo wurin Hurriya komi za a kawo ma Hurriya indai na ci ne tohm sai ta rage tukunna Hurriya ke cin abinci koda Hurriya kam bataci komai ba Allah ya sanya mata kaunarHurriya don tanajinta kamar wani bangare na jikinta







Kullum sai ta nuna ma Hurriya tayi Bacci don haka Hurriya na kwanciya zata matso gefenta ta kwanta sannan tayi mata addu a da taga ta fara motsi sai ta koma katifarta ta kwanta





Hurriya kallon abubuwan da zinariya ta sanya a kawo mata da safe tayi shrugging kafadar ta tayi tare da tafiya inda take wanki don yanzu aikinta daya a masarautar don kwata kwata ta daina zuwa shashen zinariya aiki



Wankinta takeyi tare da zura earpiece a kunnenta tanajin wakarta mai dadi tana cikin yin wankin uwar bayi tazo tare dayi ma kowa magana Dukansu suka matso wurinta domin jin mai zatace



Yawwa Zamuje sashen Gimbiya subira da kuma yerima Khalifha saboda suna da bukatar masu aiki Don haka ku kiyaye nan ta fara gaya masu irin Dokokin na Subira da Khalifha duka Dokokin are strict Amman ya zasuyi dolensu ne tunda abinda ya kawosu masarautar kenan.







Acikin duka mutanen data tara ba wanda bai shiga cikin damuwaba da tashin hankali ba saboda inda zasuje aikin





Hurriya kam duk da earpieces ne a kunnenta tanajin duk abinda suke cewa



Uwar bayi bata ce mata komai ba don tasan gaba da gabanta aljani ya taka wuta tasan very soon zata shiga hankalinta ta daina wannan jiji da kai din da izzar don mutum biyu mararsa sauki a masarautar sun dawo.







Uwar bayi tayi gaba a hankali suka bi bayanta har zuwa sashe magajiya Zama wato subira tafiyace mai nisa Amman kwata kwata Hurriya yanzu ta daina ganin tafiya saboda har ta saba





Bayan sun iso kowa ta nemi wuri ta tsaya domin jiran Gimbiya subira don ta fito taga idan sunyi mata







Zaune take a wata matsiyaciyar kujera mai kyau sanyi da kamshin turaren wuta mai dadi da tsada sai kafafunta acikin wani ruwan mai kumfa mai matukar kyau da daukar ido



Idonta sanye da wani haddaden designer glasses mai matukar kyau da tsada itadin kyakkawace ta ajin farko don wani irin luminous skin gareta wanda yake brightening kamar sunshine skin dinta kam flawless ga smooth skin dake fidda wani uban glow tanada wani irin dogon gashi wanda yake bude anyi mata gyaran ponytail gashinta brown hair ne mai matukar kyau wanda kallo daya zakasan ana kashe mashi kudi wurin gyaranshi





Tana da dogon hanci mai kyau wanda ya fito kamar biro idonta sun hadu don wani irin double eyelid gareta wanda suka fita sosai eyeballs dinta wani kalan dark brown ne mai shining Itadin mai kyau ce kuma tasan da haka





Kallo daya idan kayi mata zakasan bratty ce ta ajin karshe don yadda take wani yamutsa fuska kamar kashi pedicure akeyi mata wanda har angama soaking kafar gyaran kafar za a fara







Gyaran nails akeyi mata nails dinta masu bala en kyau very cautions matar takeyi mata saidai subira da wayarta na a hannunta tana dariya sai kam hannun matar ya goce tare da yankarta kadan





Duk abinda ke wurin tsayawa yayi domin sun san rashin mutuncinta





Saukar kyakkawan marin da sukaji ne wanda ya sanya kowa shan jinin jikinshi



Dukar da kanta matar tayi wani irin matsiyacin kallo subira take aikawa matar da ta kusa haihuwarta shiru wurin ya dauka



Tashi subira tayi tsaye anan naga komai nata itadin doguwace saidai ba Sosai ba don baza a sakota cikin jerin gajeru ba tanada wani irin figure mai daukar hankali don everything about her is screaming perfection





Ture matar tayi sannan ta takata bayan takawar da tayi mata jawo kanta tayi baki daya ta sanya shi cikin ruwan kumfar da aka wanke mata kafar sannan ta fito da kan tana watsa mata kallon banza





Numfashin matar yana kawowa yana daukewa Amman batausayi bare tausayawa

Ta kalleta shekeke sannan tace ke kidahumar inace da sauri ta dukar da kanta tace don Allah kiyi hakuri Allah ya taimake Gimbiya kiyi hakuri don Allah





Wani uban tsaki taja sannan ta haye sama kuyangunta na bayanta



Ruwan wanka mai dumi aka hada mata fitowa kuyangar tayi tareda cewar Allah ya taimake ki nagama sannan ta fita subira batace komai ba don wayarta ke a hannunta cire bakin glass dinta tayi ta aje tareda shiga toilet din





Saidai tana taba ruwan da aka zuba mata a komin wanka ta fara kwala ma kuyangar ta kira da sauri saro tazo tana durkusawa ruwan komin ta diba sannan ta watsa mata a fuska saro bata ida dawo hayyacinta ba ta kara watsa mata ruwa mai zafin gaske a fuska wani irin ihu ta kwalla tadiyeta subira tayi da tsantsar mugunta da gadara saida ta fadi akasan tiles din









Saro yau taga bala i a rayuwarta Sosai don saida ta hada mata ruwa ya kai sau ashirin tukunna akasamu yayi ba irin zagin da batayi mata ba yau ,zagin na cin mutunci ma da wulakanci kuka Saro ta rinkayi data fito duk wanda ya ganta kawai hakuri yake bata.







Hurriya suna tsaye kusan awa dinsu ta uku kenan ga sanyi ita kadaice ma ta samu wuri ta zauna tanajin wakarta hankali kwance ta riga da tace idan har aka kara minti biyar ba a fito ba to tafiyarta zatayi



Kallon agogon wayarta tayi tareda tashi tsaye ganin lokacin da ta bada har yayi







Saida ko fara tafiya batayi ba aka farayi ma magajiya zama wato subira iso



Ba wanda bai shiga taitayinshi ba don kowa da hanzari ya tashi aka hau layi Hurriya kam da already akan layi take













Sanye take cikin wata Long slip miu miu dress kalar grey melange kasan rigar kusan an tsagashi sai wasu matsiyatan heels 5inches Gashin kanta ya zubo har bayanta idonta cikin bakin glasses dinta mai kyau tayi kyau na daukar hankali don zaka dade kana kallonta ba tare da ka gano makusarta ba.



Kamshin ta ya cika ko ina a wurin



Kuyangu kusan guda bakwai abayanta









Uwar bayi ce taje wurinta tare dayi mata bayani



Cikin yanga da jiji da kai da tsantsar sarauta kuma da mulki ta fara bin ma aikatan



Duk wurin wacce tazo saita daga mata fuska tareda kallonta sannan ta sharrance mutum tsabb da sunayen dabobbi sannan ta sanya maka sunan dabba kuma ta kiraka da akuya ko tunkiya ka amsa.

Ta rufe hancin ta tsaff don tace warin bunsurai sukeyi





Marin da ta sauke ma yarinyar dake kusa da Hurriya shine ya sanya Hurriya tayi mata kallo daya sannan subira ta kara da take ma yarinyar kafa wanda kararta ya karade ko ina Amman ba wanda yake da tacewa bayan tagama zagin yarinyar hade dayi mata wulakanci da cin fuska ta karkato wurin Hurriya







Subira kallon Hurriya ta farayi tunda ga sama har kasa fuskar nan ta Hurriya neutral batada wata damuwa don earpiece ne sagale a kunnenta

Uniform dinta ne ajikinta don ta kwana biyu bata sanya normal kayanta ba yanzu tana yawaita sanya uniforms



Subira kallon tsantsar kyau da aji take na hallitar Hurriya don tunda tazo wurin ko kallon inda take batayi ba kuma har lokacin bata fara kyarma ba yadda akeyi idan akaji takunta

Tabb kawai subira take cewa don ita ba makauniya bace don ko makaho ya laluba su da ita da Hurriya yasan Hurriya ta fita kyau



Tabb first in history



Subira gyara tsayuwarta tayi cike da gadara kuma da mulki da isa tace ke gorilla >؍ ta bugama Hurriya tsawa



Hurriya tsaff tanajinta amman bata ko kalli inda take ba ta kalli gabas Saukar kyakkawan marin da taji wanda ya sanya tayi saurin dafe kuncinta ba tare da ta kalli saitin da marin ya fitoba a har yanzu



Ke wacca irin kidahumar dabba ce inji subira

Hurriya saida ta dan mari kanta don taji dagaske ba bacci take ba



Don tunda take rayuwarta ba wanda ya taba sanya hannunshi a fuskarta da sunan mari sunanta fa Hurriya Faisait Hamood diyar babanta kuma jikar sarki Hamood tabb Hurriya bata ida dawowa daga duniyar tunanin data shigaba taji saukar tsinin takalmin subira a kafarta



Runtse idonta Hurriya tayi tanajin zafin har cikin kwakwalwarta



Subira tace Ke waca irin jahila kucaka tunkiyace Hurriya wadda idan ka kalli idonta idan kasan mi kakeyi dole ka ruga kayi ta kanka



Kallon subira tayi sannan ta tsotsi bakinta tace da mamanki da babanki sune manya jahilai kucakai kuma dabbobi



Da wani irin zafi nama subira ta daga hannu zata mareta wanda Hurriya itama da sauri ta rike hannuta





Tana rikewa ta sakin hannun kamar kashi tare shammacarta ta wanka mata wani wawan mari kafin ta ankara ta kara mata wani

Mari Hurriya ta rinka bata wanda baida iyaka subira banda ihu ba abinda takeyi



Hurriya kam kwatakwata marinta datake yaki calming anger dinta don haka ta daina marinta ta shiga jamata gashinta cikin azaba da muguwar keta how dared she slapped a royal princess Hurriya fa Faisait Hamood mari fa tunda take a rayuwarta ba wanda ya taba marinta kuma ta takata da heels masu tsini ta fito da jini a jikinta she will never let this slip





Kara jan gashin Hurriya take saidai hakan shima bayi mata ba banda ihu ba abinda subira takeyi



Cikin zafin nama ta cire dogayen takalman subira inda subira ta ta fadi warwas tana kuka



Da takalman duka biyu Hurriya ta rinka kwada ma subira duka kuma kota ina dukanta Hurriya take ihunta kawai ake ji







Mutane sun taru sai salati suke amman ba wanda yayi yunkurin hana Hurriya.







Hurriya saida ta tabbatar ta ji mata ciwo don idan bataga jini jikinta ba tohm sam bata iya Bacci







Bata ko kalli kowa ba cikin mutanen ta sanya earpiece dinta ta koma dakinsu don tana bukatar wanka duk duniya ba abinda ta tsana irin ace ta taba wani she need a bath.

<Masarautar Qamar

The mysterious palace



41&42



Saida mutane suka tabbatar Hurriya tagama cin uban subira tukuna sukazo suka fara riketa suna sallati don duk Hurriya taji mata ciwo wanda da kyar aka dauketa aka shigar da ita Chamber dinta





Jakadiyya suka nemo wadda tana Ganin halin da subira take ciki ta hau salati Tana sanar da ubangiji kallon kuyangun tayi tace garin yaya hakan ta faru





Nan aka kwashe labarin tass aka gayamata shiru jakadiya tayi tana jin jina abun a ranta saidai wani ihu da subira tayi ya sanya tayi sauri tazo inda take tana tambayarta lafiya



Idon subira kwalla da hawaye kawai suke fiddawa na azaba ta nuna mata wani wuri a bayanta tace zafi







Jakadiya sannu tayi mata sannan ta shiga toilet da kanta ta hada mata ruwa masu dumi

Sannan suka kamata aka shiga da ita





Gashi akayi mata wanda duk wanda yake a sashenta saida yaji ihunta ko ina na jikinta zafin ciwo ne ga rauni







Saida jakadiya ta tabbatar da ta gasu sannan ta fito ta shiryata lokacin har Doctor ya iso yana jiran subira domin ya dubata.









Tun kafin aje ko ina magana ta karade ko ina abinda Hurriya tayi wasu kam ta burge su sosai don ba kowa yakeda confindence din bugun diyar sarki ba Amman ita ta zane tass saidai da yawa wasu sunji tausayin Hurriya saboda sanin halin subira bazata taba kara barin Hurriya tayi bacci mai d adi ba acikin masarautar don azaba ce zata rinka sanyawa anayi mata.







Hurriya kam ba inda ta tsaya sai babban kitchen

15 / 27