Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   21 / 27

60K to 63K   out of 79.4K words

it was her duty to do that accordingly ta zuba ma kowa abincin da tsari tayi serving dinsu Khasheem banda santi da lumshe ido ba abinda yakeyi









Maleek abinci yanayi mashi dadi kuma yanajin dadin kallon yarinyar baisan miyasa ba fayrouz kam sai washe baki yake yanacin abinci Khasheem ne yace Amman wallahi Kyal ya gama damu yanzu akwai mai dafa irin wannan abincin a gidanan shine yake wahalar damu da cin cookies da fruit gaskiya it s unfair duk tare suka rinka maganar





Khalifha kallonsu kawai yake yana mamakin yadda suke cin abincin don kamar basu taba cin abinci ba.









Hurriya saida ta dade zaune a kitchen tana tunanin ta inda zata fara don Khalifha kwata kwata baici abincin ba she desperately needs money don she have to work hard indai tanason ta hada kudin





Kiran sallahr magrib da taji ya sanyata tashi ta nufi dakinsu saida ta kwanta ta huta sannan tayi alwala tayi sallah Bintu da wasba tare suka shigo Dukansu ba wanda baiyi murna da Ganin Hurriya ba don aiki na dan shige mata kwana biyu suna wuya bata zauna dasu ba.Ba kamar Bintu don inna hanne da wasba kullum suna ganinta







Inna hanne ce tazo da tuwon masara mai dadin gaske don ko yadda yake turiri mutum ya isa ya gane ga man shanu data kwalala masu a saman tuwon kallon Hurriya tayi tace Hurriya kin shigo? daga mata kai Hurriya tayi





Inna hanne tace bari na samo maki wani Abu da zaki dan ci don nasan baki san tuwo Hurriya cewa tayi na koshi a hankali cikin natsuwarta da miskilanci.wasba lumshe ido tayi tareda cewa kai wannan tuwon zaiyi dadi tareda kai hannunta Hurriya ce tace wasba don t eat this food without washing your hands kada ki sake kici abinci nan ba tareda kin wanke hannun ki ba daga mata kai wasba tayi tareda fita domin wanko hannun bintu dariya tayi mata hade da gwalo turo baki tayi inna hanne dai murmushi tayi tace wasba sarkin rigima







Bintu ta kalli Hurriya tace ya aiki a wurin makaho?kinajin dadi shiru tayi Bintu bata fuska tayi tace ki gaya mani don Allah Hurriya wani dan karamin murmushi tayi tace eh tareda daga mata kai har zata ce wani Abu sai tayi shiru ta kalli Hurriya tace bari na wanko hannuna.





Saida suka wanko hannu tareda wasba suka dawo suka zauna inna hanne itama ta zauna inna hanne saida ta kalli kowa Acikinsu tace suyi bismillah atare sukayi sannan suka sanya hannu suka faraci a hankali .daga gani tuwon na kai masu karo



Bintu ce ta bude baki zatayi magana Hurriya girgiza mata kai tayi tareda nuna mata da hannu tayi shiru.they all ate in silence saida suka gama ci bayan sun wanke hannu sun dawo Hurriya tace mata ba a cin abinci ana magana ki bari daga mata kai Bintu tareda jin dadin correction din da Bintu tayi mata sannan tayu masu inna hanne Bankwana





Hurriya wayarta ta dauka tareda sanya earpiece inna hanne kallonta tayi tace aikin zaki koma daga mata kai Hurriya kawai tayi inna hanne shiru tayi don batasan aikin dare sam bare aikin dare a masarautar Qamar yanada matukar hadarin gaske cikin sanyi murya tace ki kula kinji Allah ya tsare ya taimaka Daga mata kai kawai Hurriya tayi ta tafi.















A parlo ta iske Khasheem da fayrouz suna kallon ball ai fayrouz yana jin motsinta ya tashi yazo wurinta biyota yayi har kitchen din da ta shiga sannan ta dora ruwan zafi ta zauna saman kujerun kitchen island shima jan kujerar yayi ya zauna yace miss world banza Hurriya tayi dashi ba tareda ta kalli inda yake ba .





Oats dinta ta dama sannan ta zuba madara tareda zuba brown sugar ta dawo ta zauna a hankali take shan oats dinta shi kuma fayrouz ya kura mata ido yana kallonta tareda admiring dinta ko kyaftawa bayayi yanda take shan oats din kadai abun kallo ne don da wata irin natsuwa sosai take Shan oats din.









Saida tagama shan oats din yace please I need a favor from you kallonshi tayi favor kuma daga mata kai kawai yayi haka yace mata please can we be friends Hurriya kallonshi kawai tayi ba tareda tace komai ba ta fita da dan sauri ya biyota yace mata bazan daina binki ba har sai kin amince man Hurriya kallon rashin sanin abinda yake kawai tayi ta hau sama.









Tun daga parlon sama ta fara lumshe ido saboda wani kalar bacci da takeji a hankali ta bude dakinshi wanda yake ko ina duhu don wutar dakin kashe take Saidai sanyin dake ratsa sakin har ya fita hankali.





Kunna wutar dakin tayi inda ta hango shi kwance idonshi sanye da glasses a rufe cikin natsuwa da kuma catwalk ta nufo inda yake a hankali ta dan leko fuskarshi tace sir nazo zan karanta maka bedtime story shiru yayi ba tareda yace komai ba Hurriya zuwa tayi ta jawo drawer bedside dinshi books ne masu dadi kuma favorite dinta ko acikin books din murmushi tayi tare da daukar littafin ta fara karantawa cikin muryarta mai dadi kuma da zallar British accent









Khalifha kam tundaga saman kanshi har tafukan kafafumshi yakejin muryarta cikin wani irin yanayin natsuwa da dadi take karantawa.





Shiru Khalifa yayi yana tunanin minene identity dinta ina ta iya turanci turancin ma na yan america





Hurriya batayi aune ba tana karatu kawai sai ji tayi an rike mata hannu da wani irin tsorata da fargaba don batayi tunanin idonshi biyu ba kuma hankalinta gabaki daya yana akan littafin da take karantawa.kallon idonta masu kyau da matukar kaifi yayi wanda ta fito dasu waje haskensu na haska nashi idanun riko waist dinta yayi tare da hawa gadon don har ta kusa rungumeshi kallonta yake tundaga kananun gashinta da ya zubo gaba ya kwanta mata da baya a hankali cikin wata murya yace who send you?miye ya kawo ki.

Masarautar Qamar



53

Hurriya ranta banda baci ba abinda yakeyi don wannan Khalifar mai ya dauke tane who give him the audacity to touch her duk lokacin da yaga dama abinda wani bai taba ba kallonshi takeyi ta cikin glashin shi Saidai bata iya ganin idanunshi shi kuma yana ganin komai





She doesn t want to cause any trouble saboda tanason ta amshi kudinsu tabar kasan cikin muryarta mai dadi tace ka sakeni please yana jinta sarai don wani kara lumshe ido yayi saida ya dauki mintuna sosai sannan yace sai kin fadamin wanda ya aiko ki Chamber dina Hurriya ganin bai gane yaren da takeyi mashi aiko ta manna mashi cizo mai zafin gaske a hannunshi da sauri Khalifa ya saketa yana mai kallonta





Kallonshi tayi ta harareshi tareda cewa bastard can kasan muryarta lips dinta kawai suka motsa ba tareda saninta ba Khalifa yana kallonta ta cikin madubin idonshi.



Juyawa tayi tareda sakin littafin zata nufi dakinsu bata kai bakin kofa ba Khalifa yace You re not done with your work





Juyowa tayi tareda hararshi tace sakarai Khalifa duka yana kallonta shi abun har mamaki yake bashi yadda batajin tsoronshi take zaginshi zaiyi lokacinta.



Devil smirk yayi ya kara lumshe idonshi Hurriya haka ta dawo ta zauna ta cigaba da karanta mashi littafin tanajin numfashin shi ya fara canzawa ta tashi Saidai jin muryarshi tayi yana cewa where are you going ? Hurriya zama tayi ta cigaba da karanta littafin cikin gajiya don cikin ranta tana ayyana randa zai kaita karshe tasan ba hakuri zatayi ba idan ya cigaba da haka ta tsani bossy attitude dinan nashi Amman zatayi maganinshi very soon









Bacci dukansu ya kwashesu duk basu sani ba Hurriya zaune a saman kujera kusa da gado shikuma kwance akan gado





Kiran sallahr asubar farko ya tada Khalifa kallon Hurriya yayi data makure saman kujera wuri daya yayi gashin kanta ya sauka skin dinta banda glowing ba abinda yake kamar ba bacci take ba.

Daga ganin yadda ta makure yasan sanyi ke gasata a hankali yace mata you deserve it my arrogant maid ya shiga katon toilet dinshi yayi wanka hade da alwala ya fito saida ya shirya ma masallaci yayi nafilfilolin shi sannan ya tafi masallaci.







Baiyi tsammanin abinda ya gani ba don koda ya dawo saman gadonshi ya ganta ta kudundune tana bacci ga dukkan alama batayi sallah ba har yayi yunkurin tadata kuma ya share ya bude secret room dinshi ya shiga .







Kwanciya yayi wani bacci mai dadi ya daukeshi.







Hurriya bata tashi ba har kusan sha daya don mafarkai ta rinkayi masu dadi baccin yayi mata dadi sosai.hamma tayi sannan ta bude idonta masu kyau ta kalli dakin







Hurriya tace aranta yaushe rabon data samu peaceful sleep haka gadonshi very cozy Saidai kamshin Khalifa ne ke dawainiya da ko ina na jikinta kamar tare suka kwanta ko tayi wanka da turarenshi don wani irin kamshin shi takeyi ko ina tsoki tayi ta gyara dakin tsaff sannan ta shiga toilet dinshi Saida ta wanke toilet din sannan tayi nazarin yin wanka kilan ta rage kamshin turarenshi da takeyi







Saida ta zuba ruwa masu dumi a cikin bahon wanka sannan ta cire kayanta ta shiga tana shiga ta lumshe idonta don wani irin missing din toilet dinta ya taso mata ta dade cikin ruwan zafin bata fara wanka ba sannan ta kara fitowa ta hada ruwan wanka mai foam da kamshi ta shiga wani irin lumshe ido tayi jin kamshin shower gel din Khalifha it smells nice and dangerous don bata taba jin kamshin shower gel haka ba don baya sanyi kamshi kamar irin wanda take using Saida yana da dadi Saidai kamshin shi yanada karfi









Wani silbi jikinta yake fiddawa kamar jikin tarwada kamar kada ta gama wankan haka Hurriya takeji don ta dade bata samu irin haka ba kawai ta sanya a ranta she will enjoyed more of this bath in the future don bazata iya kilan yadda tayi wanka a toilet dinsu ba this toilet will be hers daga yau and she will keep sleeping in his cozy bed tanason ta kara enjoying life dinta kadan kafin tabar nigéria Because she doesn t know what is awaiting for her there.





Dogon gashinta mai kyau da tsawo ta wanke shi tass irin wanki da rabonta dashi shekara da shekaru saida ta tabbatar ya fita sannan ta dauki hand dryer dake a toilet din ta busar da kanta tsaff ta rinka shafa designers man gashin shi mai tsada sannan ta fito taji dadi sosai kayanta sun danyi datti bazata iya barinsu ajikinta ba.





Bude wadrop dinshi tayi sannan ta kalli kayan dake shake acikinta .latest branded designers ne komai a wurin dark colors sunfi yawa a kayanshi ta dade tana kallo kafin ta bude wata wardrobe din wanda girmanta kusan daki guda kayane sabbi dal wanda ba a taba sasu ba Hurriya kallon komai take sannan tace extravagance abun kuma sai yadan bata dariya she just called someone extravaganza while lokacin da tana Hurain haka take akwai kayan da idan ta siyesu har ta bayar dasu bata taba sawa ba she loves shopping kuma everyyear ana canza mata komai na dakinta tun daga furnitures har zuwa kan clothing zata iya cewa all her life bata taba saka kayan da ba designer ba kuma babban designers brands wanda clothe din are worthing thousands and millions of dollars.





Kuma zata iya tayi barnar kudi ta siye kaya da mahaukatan kudi Amman bazata taba sawa ba suna ajiye kuma kullum hakan bazai hanata fasa fita ta siye wasu kayan ba.





Extravagance life kenan wasu bakaken hoodie ne tagani sabbi bakake ahankali tazaro su ta bude hermès tagani cikin natsuwarta ta kalli kayan tana fatar Allah ya sanya zasuyi mata don taganshi giant ne.



Cikin yanayin natsuwarta ta fara sanya rigar sadai rigar har kusan gwiwowinta saida suka rufe mata wandon ta sanya shikuma inda Allah ya taimaketa baiyi mata yawa ba sama da kasan wandon rubber ne sai yadan kama kafarta she looks so cute and breathtaking ba karamin kyau na daukar hankali tayi ba don kayan sunyi mata kyau sosai





Kayanta ta fito dasu sannan ta sauko kasa ta baya inda take ganin washing machine ta zuba kayanta da morning fresh din da take wanke wanke



Washing machine nagama wanke mata kayan ta shanyasu tareda shigowa kitchen tunanin abinda zatayi ta fara mai sauki





Dankali ta debo ta fere sannan ta ciro fresh liver dinta saida ta daura manta sannan ta wanke liver lokacin data gama wankewa har man yayi zafi ta zuba dankalinta



Wani kyawawan hadi tayima sauce din kamshi sai tashi yake.



Fayrouz ne ya shigo kitchen din cikin gayunshi sai kamshi yakeyi fuskarshi sai wani salkin kyau takeyi kallo daya zakayi mashi kasan cewar shidin dan gayu ne kuma dan kwalisa mai kudi



Kallon gashin Hurriya yake wanda da ace zata bashi dama da ya taba yaji ko nata ne saida bashi da wannan damar har sai ya mallaketa he will look forward into mallakar wannan yarinyar komin wuya insha Allah .





Tunda ya shigo tasan da shigowar shi duk da tabama kofa baya saboda Allah ya bata ji Sosai cikin muryarshi mai dadi yace mata hurry babe Hurriya banza tayi dashi ta cigaba da aiki fayrouz kam zama yayi saman kujera Saidai Hurriya ta rinka jin sheshekar kuka saida ta gama kwashe dankalinta tazo ta kura mashi ido irin namiji kana kuka ?



Daga mata kai yayi yace i don t need anything from you fa just a simple friend minene abun kin yadda I swear duk randa nayi misbehaving kar ki kara kulani please Hurain please Hurain gaban Hurriya banda faduwa ba abinda yakeyi don murya Al-Amr kawai takeji please Hurain ahankali tace mashi yayi shiru da hannunta tana kallonshi so cute and full of spirit why don t her befriend him atleast ko ta koma there will be so much memories of the palace kuma he seems carefree and simple ga yanada barkwanci da shiga rai why not tayi keeping dinshi as only male friend din da tayi tunda tazo Nigeria duk a ranta take tunanin





Muryarshi mai dadin sauraro yace mata please Hurain kallonshi tayi cikin natsuwa tace stop calling me Hurain sunana Hurriya dan durkusa kai yayi yace yess your royal highness daga mashi kai kawai tayi can we be friends please ? A hankali ta daga mashi kai wani irin ihu ya buga don yasan first step in a relationship shine friendship daganan sai a zama best friends daga best friends kuma sai azama lovers yasan wannan tactics din and he s very sure it will work.



Zuwa yayi ya rinka tayata aiki don pancake din kusan tare suka kwaba yana mata fira Hurriya bazatayi karya ba Amman gaskiya she s enjoying his company don duk da bata cewa komai a firan to ta maida hankalinta da komai a kanshi



Maleek ne ya shigo kitchen saboda yanasan yasha magani da ruwa marar sanyi tunda ya bude kofa yagansu duk da fayrouz shike maganar yana nuna mata yanda abin ya faru da hannu



Ita kuma tana kallonshi da duk wani attention dinta wani irin bang bang yaji zuciyarshi nayi a hankali ya dafe zuciyarshi yana kara kallonsu Khasheem ne yazo tareda wani dariya yace miye nike gani haka





Maleek fita yayi Hurriya taci gaba da aikinta kusan fayrouz ne ya taimaka mata wurin shirya table din sukayi setting komai tare





Khasheem ya kalli maleek yace ka taho muci abinci a wani miskilance ya taso ya zauna saman table din Hurriya ita tayi serving dinsu ta sanya ma kowa Daidai sannan ta mika mashi har zata juya fayrouz yace Hurriya please i need a favor juyowa tayi tareda alamar miye please join us Hurriya bata wani bata lokaci ba ta zauna cikinsu don yunwa takeji daman.





Khalifha ba abinda bai gani ba ta dakinshi yana mamakin audacity da zeal dinta har ta sanya mashi kaya .



kamshin turarenshi mai matukar dadi ya daki kowa cikin kasaita da natsuwa sai kuma walking stick dinshi dake rike à hannunshi ahankali yazo ya zauna kallon su duka yakeyi ba kamar fayrouz da hankalinshi gabaki daya yana akan Hurriya





Maleek ne cikin miskikanci yace Kayl join us for breakfast your maid is surely a genius Dukansu juyowa sukayi a mamakance did they heard right anya abinda sukaji Daidai ne a compliment from prince maleek fa dashi da Khalifha kusan halinsu daya na miskilanci don mutum zai iya kwana baiji a daga bakinsu ba to gwara Khalifa yanada zafi da fada don anajin fadanshi Time to time shi kuma maleek ba ruwanshi da shiga hidimar kowa





Khasheem Dariya yayi maleek did you just compliment her daga masu kai kawai yayi



Hurriya kam batace komai ba don Komi za ayi a wurin ba zatace uffan ba indai ba gamacin abincinta tayi ba.





Khasheem ya kalli Khalifa yace Kayl join us I m sure you will like the food haka shima fayrouz yace cmon gee join the food da dadi saida suka rinka magiya sosai sannan ya zauna yayi bismillah ya faraci.



Kallonshi suka rinkayi da mamaki don basuyi tunani zaici so easily haka ba.



Hurriya wani irin dadi taji they really did help her in this battle don batasan ta yanda zata fara a cewa yaci abincinta ba, yau za a sanya mata 2.5m ta riga tayi deciding tabar kasar with 3.5m tasan cewar kudin zasu kaita saudiyya.

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: M.Qamar



Short page



Tunda Khalifa ya fara cin abinci wurin ya dauki shiru Sosai





Ba wanda ya kara cewa uffan har saida suka gama Hurriya ce ta fara tashi kallonta Khalifa yakeyi cikin kayanshi data sanya a ranshi yace gaskiya batada kunya ba izini yar aiki ta bude maka wardrobe ta sanya kayanka kuma kamar batayi laifin komai ba





Bayan sun gama cin abinci Khalifa da maleek suka fita.hurriya saida ta tabbatar kowa acikinsu ya gama cin abinci tazo ta kwashe duka kayan datti fayrouz ya biyota ya rinka tayata komai yanayi yana mata labarai masu tsananin ban Dariyar duk yanda Hurriya take daurewa saida fayrouz ya kawo zance data kasa rikewa saida tayi dariya kadan a lokacin Fayrouz kam sumar tsaye yayi yana kallonta don wani irin kyau kawai yake gani dimples dinta hakoranta masu kyau wanda bai taba ganin irinsu ba

21 / 27