Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   20 / 27

57K to 60K   out of 79.4K words

ayyo sannan ta amshi magungunan ayyo ta kalleta tace daya ki barbada mashi a abinci safe rana dare,Daya kuma a inda yake kwana daya kuma sai ki samo mana gashin kanshi Hurriya shiru tayi tana kallon ayyo saida ta dauki kusan mintin biyar batace kala ba kuma bata tashiba ahankali tace kudina fa? Ayyo rike kanta tayi alamar damuwa tace idan aiki ya kammalu Za a tura maki wani dan iskan kallo Hurriya tayi matw tareda yadda magungunan kasa sannan ta juya tayi hanyar kofa ai aguje ayyo ta biyota tace yi hakuri yar nan yi hakuri kudi dai kikeso ko yanzu zanyi maki transfer yi hakuri dauka Hurriya ko waigowa batayi ba bare ayyo tayi tunanin zata dauki magungunan





Takaicin iskanci da yarinyar nan ya ishi ayyo haba mi take takama dashi cikin masarautar shegiyar yarinya mai mugun wuyar sha ani tayi tsoki ta cigaba da maganganunta ita kadai.









Hurriya kado ta shigo part din Khalifha ba kowa wani irin sanyi kamshi parlon yakeyi lumshe idonta tayi aranta tace he s a neatness freak ta dade tana enjoying ita kadai don batasan miyasa ba she s in love with each and everything in his part ko saboda bata saba Ganin an kawata wuri da dull color bane sai a wurin shi



Don tafi ganema bright color don haka heral palace komai nata was bright Amman dull color ya shiga ranta sosai don har ta fara tunanin itama ta koma dull color irin na Khalifha kamar wata mysterious girl tace a ranta sannan ta shiga kitchen kallon komai na kitchen din tayi intact don ko wood din dake kitchen din shima dark colorne cikin ranta tace blind man and his dark color





Harkar abinci ta fara don yau jinta kawai take kamar a kitchen dinta na Heral palace she surely misses alot don aiki ta farayi tana waka tana rawa kadan cikin kwarewa da kuma aji da zallar miskilanci a rawar.





Abubuwa tayi Sosai banda main dish da tayi harda su appetizer side dish dasu desert sai guava juice data hada



Bayan tagama komai ta gyara kitchen din tass don kamar yanda takeyi lokacin da tana Heral palace haka tayi komai sannan ta jerasu a babban dining table din.





Kwata kwata batasan baya nan ba don kawai aikinta tayi



Sannan ta samu wata yar kujera tadan zauna.







Kamshin turarenshi da kuma aura dinshi da taji shine ya tabbatar mata da isowar shi a parlon fuskarshi a hade as usual a hankali Hurriya ta taso sannan ta kalleshi cikin yanayi na girmamawa tace welcome back sir,trying all her very best to be a good maid shiru yayi batare da ya kalli ko gefen da take ba da wani irin sauri ta kara cewa your food is ready sir .



Shiru yayi mata sannan ya haye sama Hurriya kam all her life ba a taba rainata irin na yau ba she s Hurriya Faisait hamood fa how dared him tana mashi magana zaiyi banza da ita.





Zuciyarta ta rinka cewa caim down Hurain calm down you re his maid kuma he don t wanna talk right now then leave the fucking idiot abinda zuciyarta ta rinka ce mata kenan don haka ta nufi dining cikin natsuwa da miskilanci ta zauna

Bude dishes din tayi sannan ta ciji lebenta ta lumshe ido it s been a while bataci abincinta haka ba don haka ta zuba komai a plate dinta accordingly with the best table manner take komai Daidai cikinta ta zuba komai







Bismillah tayi ta faraci abincin tana lumshe ido yanda take cin abinci kamar wata American royalty saboda table manners dinta.









Khalifha tun daga kan shigowarta ya fara kallo har shigarta kitchen da yanda ta rinka waka da rawa tabe bakinshi yayi yace arrogant fool sannan ya cigaba da kallo dariya yayi kadan Ganin yadda take aikin cike da kwarewa kuma da sauri takeyi tana magana cikin wani British accent wanda bai tabajin wani dashi ba tunda yake wani irin fluently.English din kuma British who is she??







Kallon yadda take cin abinci yake da mamaki don tunda yake bai taba coming across mutum mai table manner dinta ba kamar wata royalty ta America kamar kuma ta russia wani irin masifar kyau tayi wanda tana tauna lasagna din da tayi murmushi yayi escaping a bakinta Khalifha he almost freeze by just looking at her wasu dimples ne both suka lotsa harta gold din dake tsakiyar hakoranta biyu saida suka fito



Who is she?what did she want from me itama tazone ta illata ni?saidai abinda yafi bashi mamaki wanda har yanzu bai ganeba ba abinda ta barbada mashi kilan ita nata abun sai nan gaba.







Takun shi Hurriya kawai taji tissue ta dauka ta goge bakinta wanda bai baci ba kwata kwata



Bazaka taba cewa taci abinci a wurin ba saboda table din da plate dinta very tidy



Khalifha cikin muryarshi yace jack ai da sauri jack ya shigo yana I m here sir cikin yanayi na miskilanci yace feed all this trash to my dogs .





Abincin da ta dafa shine za a bama karnuka itafa ce Hurain wato Hurriya Faisait Hamood.

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: Masarautar Qamar



51



Shiru Hurriya tayi tana kallon jack wanda ya dauki duka abincin da ta dafa



Khalifha kam ko second glance bai karayi mata ba ya nufi kofar fita.



Hurriya shiru tayi tareda bin bayanshi da kallo .









A kwana à tashi ba wuya wurin Allah yau har tayi kwana hudu da farayi ma Khalifha aiki duk yanda tayi tunanin saukin abun baizo mata da sauki ba.Duk abincin data dafa mashi bai taba kallonshi ba bare har ma yaci ita kadai take wahalarta don zata dafa ne taci ta koshi sannan ya sanya abama karnu kanshi ba yadda ta iya.



Fannin ayyo saida Hurriya taji saukar miliyan daya a account dinta na Nigeria sannan ta amshi aikin da suka bata don ta amshi maganin saidai har yanzu bata zuba mashi ba









Ta riga ta yanke hukuncin aikin wata biyu zatayi a Part din Khalifha bazata bari shekara ta zagayo mata ba tana cikin masarautar Qamar kudin da zata hada zasu kai 7m dana part dinshi dana ayyo don haka tana gama umara sai ta wuce canada





Bintu ce ta shigo duk ta rame kwana biyu sam basu hadu da Hurriya ba don Bintu naganin Hurriyar kamar ta juya kallon tuhuma Hurriya ta rinka binta dashi. Bintu kallon kasan siminti tayi Hurriya a hankali cikin zakin muryarta tace miye ya sameki ahankali Bintu tace ba komai shiru Hurriya tayi sannan ta rinka bin ko ina na jikinta da kallo sannan ta fita ba inda ta tsaya sai wurin inna hanne saida suka gaisa tace mata tanason ta bincika mata abinda ke damun Bintu.inna hanne ta bata assurance din insha Allah zata duba mata







Hurriya ta nufi part din Khalifha abayace jikinta fara tayi mata masifar kyau don banda annuri ba abinda takeyi



Part din yayi wani irin shiru karar Ac kawai kakeji bedroom dinshi taje ta gyara mashi fess hade da wanke toilet kwata kwata bataji motsin shi ba don haka tayi sauri tagama ta fito parlon



Cikin sauri take komai don gyaran parlon ta cigaba dayi saida ta share ko ina tass tareda gogewa sannan ta hado ruwan mopping ta farayi goge parlon mai tsananin girma



Mopping din ba kadan tayi ba saidai karar tafiyar da taji da kamshin da taji ya sanya tasan sunyi Baki kwata kwata bata juya ba don abinda takeyi shine ta cigaba dayi





Prince maleek da fayroz sai Khasheem ne suke takunsu na sun isa duk cikinsu babu wanda ba wani bane don arziki ta ko ina ya bayyana ajikinsu sun hadu sosai don suma wasu irin manya ne gasu yan gayu cikin izzarsu suma da mulki suke tafiya har suka shigo da tsaddadun takalmansu cikinsu ba wanda bai taka mata mopping ba da tsaddadun takalmansu





Juyowa tayi domin wucewa saidai abinda tagani ne ya sanyata tsayawa duk sun bata mata mopping din da tayi da takalmansu masu tsada kuma suna kokarin ida wucewa ta inda tagama mopping yanzu







Zuwa tayi Daidai inda suke neman wucewa ta tarbe wurin tareda zuba masu idonta masu masifar kyau ba wanda acikinsu bai kalleta ba ba kamar prince maleek wanda izzarshi take yanayi data Khalifha







Kallon kallo Dukansu suke ma juna Hurriya in a mocking way tayi raising brows dinta tace ina zaku?







Kallonta sukeyi saidai cikinsu ba wanda ya santa a matsayin yar uwar Khalifha ko wata cikin yan matan gidan irinsu liya da neela don haka tabbas mai aikicyar shi ce saidai kuma shigar da tayi ba irinta masu aiki bace







Prince maleek langabar da kanshi yayi yana zuba mata idanunshi masu kashe yan mata, fayrouz shine yayi magana yace wacece ke?







Shiru tayi batare da tace mashi kala ba Amman bata fasa kallonshi ba.



Move from here inji Khasheem kallon kafafunsu tayi tace har sai kun cire wannan kazaman takalman naku





Kallonta suka rinkayi irin did you know what you just said kazaman takalma fa takalmansu duk guda daya zai iya siyanta daga masu kai tayi saboda ba product din da bata Sani ba acikin takalmin kuma tasan duka kudinsu maleek sanya yake da bakin takalmin Nicholas Kirkwood babban designer kuma kayansu a extremely expensive and Are not common ko acikin designers product don idan baka kai shege ba ma duk girman ka duk kudin ka bazaka taba sanin companyn din ba amman isassu wadanda sun isa kuma masu manya manya kudi to tabbas zasu san mi ya sanya







Daya acikinsu kuma ya sanya wani farin takalmi na Marcelo Burlon shima babban expensive designer ne worthing alot of millions Khasheem kuma ya sanya shima bakin takalma na Vera wanga Dukansu manya manya takalma ne daga designers company don ba irinsu fendi Versace ko Gucci bane wanda kowa ya sani Aa wannan sai ka kai da nisa sannan zaka iya sanin su







Hurriya kallon maleek tayi tace Nicholas Kirkwood shoes fayrouz tace marcelo Burlon Khasheem kuma vera wang interesting tace tareda rike mopper tana kallonsu





Dukansu kallonta suke in awe suna jinjina mata wani irin miskilin kallon maleek yake bin Hurriya dashi wanda shi kanshi baisan yana haka dinba fayrouz shima kallonta kawai yakeyi tareda washe baki ya matso kusa da ita hannunshi ya kai zai taba mata gashi aiko a take ta buga mashi mopper din dake hannunta a gwiwarshi rike wurin yayi yana ouch wash dariya Khasheem ya fashe da ita yana kallon Hurriya dake tsaye da mopper a hannunta da alamar idan ya kara zatayi abinda yafii haka wani silent murmushi maleek yayi tareda cewa ta basu wuri





Hurriya kin matsawa tayi hannuta rike da mopper shiru sukayi suna kallonta ahankali cikin miskilanci da kuma aji tace appointment Dukansu kallonta sukeyi wai bataga shigarsu bane kodai bata ganewa ne? Gaskiya wannan yarinya ta gama rainasu fayrouz daya kasa rike Maganarshi ya juya kamar wani mace kalleni da kyau nayi kama da wanda saida appointment zai shigo nan



Hurriya yanda ya juya ya sanya ta dage girarta tana mai kallonta mai dauke da raini kuma da kwarjini bude bakin da Khasheem yayi da niyyar magana ne bai kaiga yin maganar ba sai ga turaren Khalifha da ya cika ko ina da aura dinshi da ta canza Atmosphere din shiru duka wurin ya dauka





Khalifha yana screat room dinshi tunda ta shigo part dinshi yake kallonta harta zuwansu fayrouz tunda yake bai taba ganin mutum mai confidence dinta ba kuma sosai yayi dariya ganin yadda ta buge kafar fayrouz yadda ta karanto takalman dake kafarsu ya bashi matukar mamaki who s she?



Wacece ita mi tazoyi Chamber dinshi yana yawan tambayar kanshi Akwai wani boyayyen abu tattare da ita she also look like someone from prestigious royal family





Bai yarda da ita ba very soon yasan zai kamata red handed after all he s Khalifha Qamar.





Walking stick dinshi sai kyali take jikinshi wata grey rigar chloe ce sai dogon wando baki na Michael kors yayi kyau na fitar hankali don wani haske kawai fuskarshi take fiddawa ga kamshin shi da ya mamaye ko ina



Fayrouz ne ya fara rungume Khalifha Khalifha shima rungumeshi yayi back sannan Khasheem da maleek sukayi joining hug din Hurriya tabe bako tayi tace Disgusting tabar wajen





Khalifha yanajinta kuma yana kallon yadda ta mela baki irin tana kyankyamin rungumar da sukayi.









Cike da kaunar juna suke kallon amininsu childhood friend nasu wato Khalifha Qamar ba karamin kewarsu sukayi ba don sun dade basu hadu dashi ba don baya barinsu suna zuwa fayrouz ne ya kasa rike maganar zuciyarshi yace Kayl who s that rudr girl ahankali Khalifha yace my maid ba Khasheem ba hatta maleek saida réaction ya fito daga fuskarshi. Irin mai aikin ka Mad inji fayrouz yace but the girl is fucking beautiful and rude



Maleek ne ya kalli Khalifha yace kayl I m hungry

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: Masarautar Qamar

52

Hurriya duk zuwan bakin Khalifha ya isheta don fayrouz kamar bindinta haka yake indai har ta shigo part din to yanan makale da ita yana zuba mata surutu





Hurriya kala batace mashi don aikinta kawai takeyi ba tareda tasan dashi ba a duk lokacin da yake.



She s not liking anyone of them don duk ta takura kamar yau basu nan don tunda ta shigo aiki bataji motsin kowanne acikinsu ba she wondered where are they don haka tayi aikinta cikin kwanciyar hankali tana gamawa ta nufi inda take wanki .



Tana wankinta saiga wasba tazo tana haki kallonta Hurriya tayi tareda tambayarta lafiya wasba tace kizo ana nemanki Hurriya kallonta tayi tace wake nemana?wasba shiru tayi tana kallon Hurriya don batasanshi ba murmushi tayi sannan ta farayi mata kwatancen shi nan take Hurriya tagane chief of security ne dauraye hannunta tayi tamike sannan suka jera itada wasba suka tafi hanyar da yake suna zuwa wasba ta shiga daki







Kallon Hurriya chief of security yayi tareda cewa kamar fa har yanzu yerima bai ci abinci ki ba and the deal is 3weeks and yau saura 1week idan bai cin abinci gaskiya I will not give the salary as you demanded ki sanya ya rinka cin abinci and bedtime story is a must.





Hurriya kallonshi take ba tareda tace komai ba and she believes duk abinda ya fada na cewar bazai bata kudin ba to zai aikata





Cewa tayi i will make him eat the food in good three days by then idan baici ba you should fire me kallonta cheif of security yakeyi irin kinsan mi kike fada kuwa Hurriya daga mashi kai tayi da wani irin confidence



Murmushi yayi ganin yadda ta dage don shi yasan halin ogan nashi amman yarinyar akwai confidence











Hurriya koda ta koma tunanin abinyi ta fara all of them are stressing her gasu ayyo da suka tura mata kudi batasan ya zatayi ba she doesn t want to affect any innocent soul tasan hypocrisy na masarauta shiyasa har yanzu ta kasa yin abinda su ayyo suka sakata







Convoy ne wanda suke zaune a baya cikin bakar mota Khalifha hannunshi rike da glass cup wanda yake dauke da non-alcoholic wine red a hankali yake sipping shida prince maleek sun kame wuri daya fayrouz ne ya kalli Khasheem yace i think I m in love yanayi yana lumshe ido Khasheem yace with whom murmushi yayi yace with that mysterious girl I think i like her Khasheem yace wai wacece kake magana a hankali yace Hurriya prince maleek kam sauran kadan ya kware saboda yanda yaji maganar kamar saukar aradu



Khasheem dariya yayi yace wannan yarinyar mai kama da kurame sannan

Yayi wata dariya yace zanga yadda zata kula ka





Fayrouz yace nine fa fayrouz ajuji yayi wani murmushi mai kyau









Prince maleek tunda fayrouz ya furta maganar yanason Hurriya mood dinshi duka ya canza Khalifha kuma mutum bai isa yace ga mood dinshi ba har suka iso





Bakar limousine dinsu ce aka bude masu suka fito su hudu ba karamin kyau sukayi ba

Dukansu hudun babu na yardawa acikinsu kowa yana ji da kanshi kuma kowa ya hadu





Suna dawowa Dukansu ba wanda bai gaji ba saboda wani aiki ne sukayi ma Khalifha yunwa ce ke nukurkusar kowa acikinsu don basu wani cin abinci kirki tunda sukazo palace din saboda rashin yardar Khalifha cookies kawai da fruits suke ci sai drinks Khalifha yama saba donshi kamar ba mutum ba don ko baici komai ba Lapia lau sukam they re not liking rashin cin abincin nan.









Tun daga bakin kofa suka farajin kamshin abincinta wanda ta kokarta sosai don different varieties of food ne tayi saboda Khalifha ko zayaci abincinta





Fayrouz ne da Khasheem suka lumshe idonsu tareda saurin shigewa ciki sai Khalifha da prince maleek suka biyo daga baya





Fayrouz sakin baki yayi tareda mutuwar tsaye yana kallon hurriya don zai iya cewa tunda yake yawo kasashe bai taba ganin mace mai kyaunta ba riga ce yar baka mai shara shara yar karama wadda bata ko rufe mata adon dake cikinta ba gyaran gashinta very matured yau saboda ba kitso bane kawai ta daureshi a bayanta ne sannan ta saki gashin







Prince maleek kallonta yakeyi wanda shikanshi bai Sani ba don kwata kwata ya kasa dauke idonshi a kanta parlon shiru ya dauka Hurriya kam kallonsu tayi sau daya ta dauke kanta batasan wainar da ake toyawa ba jin shirun yayi yawa ya sanyata juyo kallon fayrouz tayi tareda dage gira daya tace lafiya kodai kana bina bashi ne?





Murmushi yayi yace mata you look so breathtaking a hankali tace T for thanks don har ta juya sai kuma wani tunanin yazo mata wani irin dadi fayrouz yaji saboda kula shi da tayi Khasheem ne ya nufi dining table tareda budewa yace wow zamuci dadi

fayrouz ne yace Hurry let me eat your food nasan it will taste delicious.





Prince maleek shima a hankali yazo ya zauna Khalifha Qamar wanda yana shigowa kallo daya yayi mata tareda shigewa sama duk abinda ke faruwa yana kallo ta CCTV camera yana kallon yanda duka abokanshi ke bin Hurriya da kallo akai kaice ba kamar fayrouz da duk inda tayi idonshi na nan akanta







Hurriya da kanta tazo tayi serving dinsu Because she knows

20 / 27