Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   16 / 27

45K to 48K   out of 79.4K words

tana yamutsa fuska kamar ta taba kashi







Tana zuwa cikin sa a ta samu inna hanne a kitchen din aiko tana Ganin Hurriya ta taso sannan ta kalleta ta sadda kai ,Hurriya tace ruwan zafi inna hanne ta daga mata kai ta samo bucket ta zuba mata sannan ta dawo ta kalli Hurriya tace naji abinda kika aikata Hurriya meyasa baki tausayin kanki damu da muke tareda ke baki tunanin duk abinda ya sameki a masarautar nan kamar mu ya taba ne?Aaqv. Q





Hurriya daukar bokitin ruwan wanka tayi batare ta bata second glance ba ta nufi toilet cikin sa a taga wasba Aikenta tayi ta dauko mata kayan wankanta





Hurriya wanke jikinta tayi sosai sannan ta fito ta daura Alwala duk inda ta gifta nunata kawai akeyi ana kananun maganganu Hurriya kam ko ajikinta wasba kam tsalle kawai take tana kallon Hurriya har suka iso daki





Wasba bata shiga ba saboda tasan Hurriya zata shirya yanzu. kuma batasan ana kallonta don haka ta tsaya waje gashinta Hurriya ta gyara sannan ta sanya kaya marar sa nauyi









Yau kwana uku kenan da faruwar dukan da Hurriya tayi ma subira don mutane dayawa suna jiran tsammanin ganin yadda zata kaya Saidai shiru.







Hurriya bata da damuwar komai don tanazuwa tayi aikinta kullum na wanki







Subira jikin ya samu dama Sosai Amman tasha wuya Sosai don wani ciwon jiki ta rinka fama dashi sosai ko ina na jikinta ciwo yake mata idonta idon Hurriya abinda tayi mata sai tayi matashi tenfold don ba a taba wulakanta kamar haka ba tunda take rayuwarta kuma wulakanci ma daga filthy maid dole ne ta dauki hukunci













Sarki Faizan Qamar a wani katon parlo wanda yake da matukar girma da daukar ido babu abinda parlon baiji ba na more rayuwa don wasu expensive chandeliers da suke bada haske kota ina expensive sets of royal chairs da aka shimfida a parlon komai na parlo is perfect don wani sanyi da kamshi dake busowa a kota ina



Kallo Daya idan kayi ma parlon zakasan an zuba dukiya ba yar kadan ba don parlon Saidai ace end of Discussion







Kaida kawo kawai yake a parlon fuskarshi dauke da damuwa da fargaba







Wayoyi ne kusan Guda uku a saman side table s23ultra sai iphone 14pro max guda biyu s23ultra din ya dauka tare da dannah number Galadima in a very commanding voice sarki Faizan Qamar yace yana bukatar ganinshi yanzu









Ba a dauki lokaci mai tsayi ba saiga galadima yazo yana durkusawa yana gaishe da sarki Faizan cikin wani yanayi yace tashi



Tashi yayi sarki Faizan yace kaje wurin Aikin wuka kace yayi mani Duba akan Khalifha Da sauri galadima yace to angama ranka ya dade yayi kirari sannan ya fita.









Zinariya cikin tafiyarta ta takama da isa taje part din subira inda take kwance ana mata massage isowa akayi ma zinariya har cikin part din subirar kallon subira tayi from head to toe sannan tayi murmushi tace you re indeed beautiful subira





Shiru subira tayi batace kala ba zinariya data riga daman tasan halin subirar bazata taba ce mata kala ba





Murmushi zinariya tayi tace tunda kika dawo masarautar Qamar baki zo kin gaisheni ba ta ida maganar a wani irin gadarance i don t care ko ki gaishe ni ko akasin haka nazo ne nabaki warning





Subira idonta akankance ta dago tana kallon zinariya da mamakin warning din da take magana don tasan tunda tadawo gari nan bata hada hanya da ko wani ma aikacinta ba don tasan wacece zinariya tasan kaidinta da sharrinta don ita ba ko wace kazanta take tabawa a masarautar Qamar ba kuma akwai abubuwa da dama idan akace bazata iya ba



Zinariya ita idan ana sallah ba a magana kallon subira zinariya tayi sannan tace ba komai ya kawo ni wurin ki ba sai dalilin Hurriya naji abinda ya hadaki da ita don haka kada ki kuskura kiyi mata wani Abu idan kuma baki dauki abinda na fada maki yanzu ba tohm kinsan sauran





Kinfi kowa sanin zinariya a masarautar nan basai na fada maki sauran ba tana gama maganar ta kakkabe alkyabbar ta tabar subira da sakin baki







Shiru subira tayi tana cizon yatsa don tasan zinariya tasan mi zata iya da wanda bazata iya ba saidai duk abinda Hurriya tayi mata sai ace ta tashi a banza gaskiya bazai yiwuba



Shiru tayi tana tunanin tasan halin zinariya tunda har tazo tayi warning dinta haka she s capable of doing everything to protect the girl murmushi tayi don wani tunani yazo mata a hankali tace idan kinsan wata bakisan wata ba







Sanyawa tayi a kira mata uwar bayi ba bata lokaci uwar bayi tazo tana durkusa ma subira cikin yanayi na jiji da kai tace tana bukatar Hurriya ta dawo aiki a shiyarta uwar bayi da mamaki a fuskarta saidai bata isa jin ba asi ba don haka ta amsa mata da angama ranki ya dade









Hurriya kwananta biyu kenan da fara zuwa sashen subira aiki don tunda akace zata koma da aiki a wurin bata musa ba Bintu hada kukansu itada wasba Hurriya kam bata ga abun damuwa ba saboda tasan abinda ya kaita shine zatayi tadawo





Itama subira bata wani damuw da al-amuran Hurriya don kowa yayi mamakin hali na ko in kula da take nunawa don kwata kwata ba kyara bare zagi bare hantara babu ko daya tun mutane na jiran suji abinda subira zatayi ma Hurriya har sun hakura





Yau watan Hurriya daya gam a part din subira aikinta takeyi tsakaninta ga Allah don ita Bata da kwiyu sam sam





Karfe 8:00 ta tashi ba yadda wasba batayi tashinta tayi sallahr asuba ba kiri kiri takiyi ta koma bacci saida takwas tayi mata sannan ta tashi tayi sallahrta bayan tagama sallah ta tattara kayanta da sukayi datti ta wanke su tasss





Tana shigowa taga inna hanne kallon Hurriya tayi sannan tace Hurriya rigima saida nace ki bari in wanke maki shine kika wanke da kanki a hankali Hurriya tace ki huta





Kallon wasba wadda wayar Hurriya take rike a hannunta tayi tace wasba yar gidan Hurriya muje ki amso mata ruwan wanka da murna tace to inna hanne .Bintu ce ta shigo ta kalli Hurriya tace Hurriya kinsan ashe har yanzu su Hansa u basuyi hankali ba sunce idan suka warke sai sun sabauta ki don Allah kibi a hankali kinji



Hurriya kallon Bintu tayi sannan ta daga mata kai alamar taji inna hanne suka fita itada wasba



Hurriya brush dinta ta dauka da kayan wankanta ta fita





Wasba ta kawo mata ruwan wanka saida tayi brush sannan ta bama wasba brush din ta shigar mata dashi ciki ita kuma ta shiga wanka





Lokacin data fito har lokacin wasba na wurin na jiranta tana ganin fitowar Hurriya tayi murmushi tazo suka jera suna zuwa wurin dakin tababama Hurriya brush dinta ta ruga ta nufi wurin Bintu.





Hurriya murmushi tayi Ganin yadda take tsallatsalle sannan ta shiga ciki madubi ta kalla sannan ta kalli sumarta da kullum kara cika mata kai takeyi wanda batasan haka samm





Tsoki tayi sannan ta dauki comb ta sharce gashin tare da shafa mashi mai raba gashin hudu tayi gida hudu sannan tayi ma kanta kalaba manya guda hudu



Kalabar ba karamin kyau tayi mata ba don kamar wata yar baby ta maidata ta sauka har tsakiyar bayanta



Mai ta shafa sannan ta bude kayanta tana kallo ta dade bata sanya normal wears ba yanzu ta saba da sanya uniform dinta don tanafin wata yanzu bata sanya kayanta ba face uniform kullum saita wankensu kuma



Tsoki tayi ta fitoda wata farar riga mai matukar hasken gaske ta sanya inner wears ta sanya rigar



CropTop ce rigar wanda ta fito mata flat stomach dinta wanda yake da adon zinari a cibinta sannan ta sanya blue jeans trouser mai fadi



Ta murza turarenta mai saukin kudi ba karamin kyau tayi ba jinta take Daidai yau sosai kilan saboda tafi ganema wannan shigar sosai frowning face dinta tayi sannan tace it s been a while sannan ta nufi part din subira





Wani irin kyau na fitar hankali tayi don kamar wata baby haka ta koma tafiya take cike da izza da mulki har ta iso part din subira subira kam daga stairs taga shigowarta wanda saida taji gabanta ya fadi



Ba abinda ya dauki hankalinta irin adon dake cikinta wanda tana hango siririn Gold din dake tsakiyar cikinta

Kin janye idonta tayi daga kallon da take mata wanda cikin sa a Hurriya tayi mata wani kallo aiko da sauri subira ta basar







Kitchen ta shiga ta fara wanke wankenta hade dora breakfast.





Subira kam ta kasa goge zinarin da tagani ajikin Hurriya da kuma irin shigar da tayi don tunda tazo bata taba ganinta ba uniform ba tsoki tayi tareda cewa yaune dai karshen ki acikin masarautar nan mayya



Suna cikin aiki ne aka fara shela cewar subira na bukatar kowa acikin ma aikatan ta awaje anyi mata sata



Bude baki kowa acikinsu ya farayi ana jimamin waye yayi wannan satar Hurriya ajiye wukar da take yanka albasa tayi tareda wanke hannuta ta sake nade gashinta sannan ta fita





Ma aikata kuyangu hadimai bayi ne masu matukar yawa kowa ya jera layi saboda za a cajesu hade da caje kayansu



Hurriya kam ko ajikinta tana kallon yanda kowa ke kyarma shiru wurin ya dauka Sosai saiga subira ankawo mata kujera

Zama tayi cike da yauki da takama tana kallon duka mutanen dake wurin kallon Hurriya tayi sai kuma ta saki murmushin mugunta.

[5/28, 3:32 PM] +234 802 952 0062: <ØßMasarautar Qamar

The mysterious palace





43&44







Wata irin chajewar wulakanci ake masu don ko ina ake caje mutum har akazo kan Hurriya





Kallon matar da take chaje yan uwanta tayi da niyyar zata fara caje Hurriya



Hurriya kam wani irin kallo ta aika mata dashi mai cike da kashedi da kuma gargadi matar ahankali tabar wurin Hurriya tana sosa kanta don ba inda labarin Hurriya baije ba a masarautar wadda zata iya dukan kamar Gimbiya subira kuma gatanan tana zaune lafiya a masarautar ita wacece da zata yima Hurriya laifi gaskiya ba ruwanta



Don haka sub sub tabar wurin ,subira da take zaune akan kujera murmushi kawai tayi don tana kallon komai daga inda take don har yanzu ba a fara wasan ba







Ba wanda ba a fito mashi da kayanshi ba don duk wadda take tsaye a wurin saida aka fito mata da jakar kayanta ko kullin kayanta haka akazo ana warwatse kayan mutane





Jakkar Hurriyace aka juye kayanta wanda kamar nata ne karshe salatin da aka farayi ne ana nunata shine ya maido hankalinta daga inda take kallon tantabarun da suke soyayya wanda alama ya nuna basu da wata damuwar duniya a rayuwarsu





Sunanta kawai ake kira ana nunata cikin natsuwarta da calmness nata ta juya tana kallon mutanen da suka zuba mata ido suna barauniya ce ashe banda sarkar Gimbiya subira hada wasu sarkoki da kudade acikin kayanta





Hurriya kallon saitin zubaida tayi inda take rike da sarkoki biyu mafi muhimmanci kuma da hadari a rayuwarta sai kuma wani pendant shima a hannun zubaida



Kallon kowa takeyi a wurin tunda take rayuwarta bata taba shiga bacin rai irin bacin ran da take ciki yanzu ba kuma ba saboda satar da aka laqa mata ba aa saboda sarkokin da ba wanda ya kamata yasan da zamansu face ita saidai mi anyi mata abinda bazata taba yafewa ba don ko taso ta yafe ba lallai ta iya hakan ba



Inda sunsan daraja da kimar sarkokin da kuma hadarin su da basuyi gigin fiddo su ba



Ba wanda zai iya gane yanayin da take ciki saboda Allah yayi mata baiwar boye duk hali da zata shiga ko ace tana cikin wani yanayi



Ranta a matukar bace yake batasan ta aikata abinda bashi ba a wurin don yadda ranta yake bace ba abinda bazata iya ba





Wata irin mahaukaciyar dariya akayi tareda jefo mata kalmar daman ashe barauniya muke zaune da ita bamu Saniba ba kama ba alama ashe abun kunyar da mutum ma yake aikatawa kenan sai kuma yazo yana hura mana hanci yana cika yana batsewa inji karime wadda take kusa da zubaida



Subira na zaune akan kujera tana kallon expression din Hurriya wanda ta kasa karantar ta sam Amman yanda abun yake tafiya yana sanyata nishadi sosai



Zubaida ce tace kuna son kusan wacece barauniyar tamu kowa daga kai yayi dariyar mugunta tayi sannan ta nuna saitin Hurriya inda take a tsaye tana kallon kowanne acikin su Amman baka iya gane yanayinta



Kunga abinda ta sata ta daga sarkar subira mai matukar kyau da tsada wata dariya tayi tace ashe na manta barauniyace ta dade tana sata bamu sani ba kunga abinda ta sata





Hurriya da wani irin zafin nama ta iso wurin Zubaida ta wanka mata mari tareda amshe sarkokinta guda biyu wanda bata kaiga dagasu ba tana watsa mata wani irin kallo





Kallonta subira tayi sannan ta taso har inda Hurriyar take Daidai kuma da wasu manya manya Dogarawa suka zo kowanne hannunshi rike da zabgegiyar dorina





Subira na ganinsu tayi murmushin nasara sannan ta kalli Hurriya tace ashe daman kedin ballagarazar barauniya ce kaskantarciya halan gadon satar kikayi daga tsaffi ta fashe da dariya sannan tace talaka haka kuke a ko yaushe sai kun nuna halin ku na kudin cizo banda halin kudin cizo ashe hada sata ma kike tohm Alhamdulillah yau anyi walkiya ashe banda sarkata hada wasu sarkokin tayi maganar cike da tsantsar wulakanci da rainin wayayu





Hurriya kallonta tayi tanajin cewar kilan idan batayi wasaba wannan yarinyar kilan saita fidda mata yatsa daga jikinta shiru wurin ya dauka subira dariya tayi tace ba tare da wani bata lokaci ba ki durkusa har kasa bisa gwiwowin ki kibani hakuri kawai sannan ki kawo sarkokin hannunki





Wani dan iskan kallo Hurriya ta bita dashi sannan tace hakuri zan baki ko tace subira ta daga kanta tana jijiga jiki tsotsar bakinta tayi sannan tace my Ass over my dead body ta juya tana mai kara damke sarkokinta a hannunta da niyyar barin wurin saidai wata irin azababbiyar dorina data shiga a jikinta saida ta dafe kanta murmushi subira tayi tace ina jiran crowling dinki sannan kizo har inda nike ki bani hakuri filthy maid ta juya tana kada jikinta wadda tasha maxi dress dinta mai masifar tsada sai heels dinta ta koma saman kujera tana kallon show din da ta hada





Alamu tayi ma dogarawan da su cigaba da aikinsu wanda daman su jiran haka sukeyi da wata irin kyata suke zuba ma Hurriya bulala wadda har saida ta kai kasa jin bugun take har cikin kanta don har wani gigita dukan yake wata tsawa suka buga mata tareda cewa ki durkusa kije ki bata hakuri matsiyaciya yar dangin matsiyata kallon dukansu tayi da bloodshot eyes dinta a wulakance tadauki lokaci Sosai don kamar bazata ce koma ba ta tsirtar da miyau tace over my death body Ko sarki ban iya duka mawa bare kaskantarciyar diyarshi ta sannan tace kune sakarkaru bayi wadanda suka gaji tsiya ta ida maganar da tabbatar masu haka





Don ko zasu kasheta a wurin nan bazata durkusawa ko sarkin garinba bare sakarar diyarshi saboda a masarautar su babban laifine ace descendant din royalty na Heral palace ya durkusa ma wani babu wanda yakai suyi ma hakan kuma har yanzu ba a haifeshi ba.







Dukanta suke kota ina tareda cewa ta basu sauran sarkokin dake wurinta amman ina After all her name is Hurriya Faisait Hamood babanta baida kafiya amman kakantane yake da wata irin kafiya babanta sanyi gareshi kankanta ne yakeda wani irin zafi idan ka taboshi kusan komai na kakanta ne ta dauko sarauta kafiya zurfin ciki kamewa duk na kakanta ne



Basu ji basu gani don tace a amsar mata sarkokin Hurriya kuma dole ta durkusa ta bata hakuri



Hurriya idonta jawur ta kafe don wani irin zafi zuciyarta takeyi mata kallon subira kawai takeyi subira kam dariya kawai takeyi





Dawowarsu kenan daga spain yaje wani boardmeeting a matukar gajiye yake don ba abinda yake bukata irin hutuwa don yanzu suka shigo masarautar Qamar idonshi a lumshe suke yana cikin farar Lamborghini yayi relaxing kanshi.





Bude idonshi yayi ta saitin inda dandazon mutanen suke a hankali ya lumshe idonshi don bai cika shiga hidimar da batashi ba



Chief of security shine yake tukashi tsoki yayi ganin yanda mata sukayi blocking way din kwata kwata ba inda zasu gifta da sauri yayi connecting ya kira sauran convoys din yace su dakata ayi clearing hanyar



Yasan halinsu sarai banna zasuyi don ba ruwansu da duk wanda zai gifta masu chief of security yayi ma Khalifha magana zaiyi clearing hanyar daga mashi kai kawai Khalifha yayi





Chief of security wanda ya fito yana kallon mutane yana mamakim mai ke faruwa ba inda ya nufa sai wurin da yaga mutane sunfi yawa ya kutsa kai saidai cikin tashin hankali yazo wurin dogarawan da suke dukan Hurriya yace su bari dukanta Dukansu shiru sukayi mashi





Kallon subira yayi don yagane ga dukkan alama abinda tace shine suke bi don haka yace zaku kasheta ki sanya su daina dukanta wata dariyar rainin hankali tayi tace kai asuwa tayi mashi rashin kunya ta zageshi tasss





Ku tabbatar da ko zatayi yawo tsirara sai kun amsar min abinda ke hannunta sannan ta durkusa ta bani hakuri







Shaho wanda zuwanshi kenan duk baiji dadi ba saboda badashi akayi show din ba yarinyar yana da alhakinta sosai don haka da zabgegiyar dorinarshi a hannunshi yazo da ita kallon dogarawan yayi sannan yace ku matsa Hurriya da duk ta jigata ta fita hayyacinta don ba kadan suka duketa ba ko ina na jikinta a farfashe yake saidai batajin ko zasu kasheta zata basu sarkarta sannan ta durkusa ma wannan wawiyar saidai she made a vow duk wanda ya sanya hannunshi sai ta sanya shi ya biyata ba tenfold ba thousands fold they will pay with biggest price Dukansu dake wurin nan



Duk jininta da ya fita saita sanya nasu ya fita dubun nata wannan is a promise ko batayi promising ba tasan bata iya bacci idan har bata

16 / 27