Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   23 / 27

66K to 69K   out of 79.4K words

narkar da rai tana rokon Hurriya gafara Amman shiru batace komai ba kallonta kawai takeyi





Kiyi hakuri don Allah Hurriya kallonta Hurriya takeyi don ba abinda takeso taji ba so take taji miye dalilinta na cutar da ita saboda tasan Bintu ,wani Abu bazai taba sanyawa tayi tunanin cutar da ita ba indai ba babban Abu bane.





Bintu kamar tasan bayanin da take bukata kenan don haka tace Hurriya lokacin da suka kirani wai zasu biyani har kaura yace yana sona zai aureni haka nace masu babu abinda zasuyi man wanda zaisa na yaudareki ko naci amanar ki sun dade suna bijiro man ta haka Amman naki basu hadin kai sai wani dare da suka tareni a lungu da wuka a hannunsu sukace indan har ban zuba maki maganin ba to idan suka tashi kashe ki zasuyi tareda wasba duka sai sun kasheku sai idan har na zuba maki maganin shine soyayyar da zan iya nuna maki don shine bazasu taba kasheku ba







Kaura ne yace bazai taba bari wani abu ya sameki ba wannan alkawari ne yayi man ba abinda zasuyi maki kawai suna so ne su duba wani abu ne idan kinyi bacci Amman duk da alkawarin da sukayi man na kasa aikatawa share hawayenta tayi zuciyarta na karewa tareda shasheka a muryarta tace ba irin tsoratarwar da ban shiga ba bani iya cin abinci bani iya bacci duk saboda abinda suke fadamani na tsorotarwa







Sai jiya da suka mareni dare nayi sukazo sukayi man gargadi da cewar idan har ban zuba makiba bazanji da dadi ba. Hurriya banda niyyar cutar dake Saidai niyyar kareki don Allah kiyi hakuri.





Hurriya kallon Hawayen dake zuba a idonta take har muryarta ta fara sarkewa Hurriya alama tayi mata da tayi shiru ya isa yanzu ba lokacin kuka bane kinji na hakura inji Hurriya tana sakar mata dan karamin murmushi





Bintu kasa yadda tayi yadda tasan halin Hurriya ya za ayi tayi hakuri har da sauri haka Hurriya daga mata kai tayi alamar ta hakura ai da sauri Bintu tazo ta rungumeta.hurriya bata rai tayi tareda dagata sannan tureta Hurriya ta kura mata idanunta masu matukar haske da kyau tace mata Amman miyasa baki fadamin ba? bintu saddar da kanta kasa tayi don ganin wani kwarjin da Hurriyar ta karayi mata yau.



Bintu tace ina tsoron yadda zan fada maki ne .hurriya wani genuine murmushi tayi mata sannan ta sassauta kallonta zuwa mai sanyi da sauki wanda tana dadewa batayi irinshi ba tace fatma ahankali Bintu ta dago tana kallon idonta wanda har wani maiko suke tsabar kyau da sanyisu abinda bata taba gani ba bintu tunda take da Hurriya shine irin wannan kallon mai kyau da sanyi.







Murmushi tayi ganin mamaki kwance a fuskar bintu sai kuma ta daina murmishin tace kada ki kara haka kinji idan wani Abu ya sameni You re not to be forgiven for the rest of your life koda na yafe maki Hamood bazai taba yafewa ba kinji .Duk abinda zai faru tell me ki fadamin we will face it together and fight it together abinda kike kokarin yi is betrayal koda kinyi shi da ace kinyi shi da niyyar protection don cutar dani sukeso suyi , don t ever try something stupid kinaji.











Bintu ta daga mata kai don wasu maganganun batasan inda ta dosa ba Amman tabbas abinda tayi kokarin aikatawa cin amana ne wanda ba wanda zai taba considering niyyarta da ace wani abu ya sake ya samu Hurriya da yanzu ya zatayi.bintu daga mata kai tayi tareda yin na am sannan tace yanzu abinda zakiyi kije ki fada masu naci abincin zaro ido Bintu tayi tace kada suyi maki wani abu Hurriya tace ba abinda zasuyi man kidai fada masu cewar naci kinji ta ida maganar tare da lumshe idonta masu kyau.bintu daga kai tayi tareda hanyat kofa don isar da sakon Hurriya.









Hurriya tasan abinda ke ranta it s been a while since she played a dirty game wannan karan is not a dirty game she s playing,it s action.



Itadin tayi takwendo lokacin da tana masarautar Heral kuma kakanta ya koya mata tareda cewa self défense ne ko an kawo Mata Hari she will be able to protect herself she always enjoyed the action don ta dade bata taba defeating kankanta ba who s very strong and destructive don ranar da tayi defeating dinshi saida ya bata babbar saraauta wadda akayi shekara da shekaru ba a bama wani sarautar ba saboda irin muhimmancita sai gashi ya bama yar karamar yarinya Hurriya , tareda wata babba chambre à palace dinsu yayi mata kyautar golds da diamonds da dawakai harda gaggarumar dinner ya hada mata damar she was always his favorite granddaughter and she knew that she would forever be his favorite.Hurain Faisait Hamood kenan bestfriend dinshi kuma jikarshi wadda yake jinta kamar shine ya durkusa ya haifeta



Saidai ko a lokacin iyayenta basu san wasan da suke da kakanta saboda haka suke fada mata ita mace ce kuma they believe that nothing will hurt her saboda Akwai security s ko ina a Heral palace don convoy din da take fita dashi a lokacin ko convoy din shugaban wata kasar albarka then why the self defense ?Da mahaifinta da mahaifiyarta sune suka hanata sukace tayi hakuri she s not stubborn sometimes Saidai fa stubbornness dinta irin na kakanta bata cika yi ma mahaifanta ba , Saidai wani lokacin idan ta kafe din ba wanda ya isa ya hanata sai Allah don ko Hamood da iyayenta din Saidai hakuri.







Mahaifiyarta is also from prestigious royal family of <ØòÝ<ØñÝ wadda Hurriya da ace ta dauko irin sarautar mahaifiyarta da ko maganarta ba wanda zai rinka ji saboda tsananin sarauta da iko da mulki nata Hurriya tana iya fin wata shidda bataji maganarta ba Saidai murmushinta wanda kullum yake dauke a fuskarta wanda yake nuni da irin zallah da soyayyar da take ma diyarta bata cewa uhm ko uhm uhm Saidai taita binta da kallo Amman bata cewa uffan idan Hurriya ta shigo har ta gama hidima da bidirinta bata cewa uffan.shiyasa ba wani sabo tsakaninsu Sosai tafi sabawa da kakanta akan iyayenta mahaifinta shima ba mutum bane maisan hayaniyaba saidai yana fira da da ita sosai don haka basu da damuwar komai tunda har mahaifiyarta tace ta daina takwendo itada kakanta ta bari don ranar taji doguwar maganar mahaifiyarta duk da a lokacin ta lura dacewar da kyar takeyin maganar ga dukkan alamu bata saba ba daurewa take don sosai tayi ma Hurriya nasiha tace you should stop doing that my dear you re a girl kinji your father will always protect you and your husband kidaina kinji babanki bayaso kuma bayajin dadi.





Tun daga lokacin Hurriya bata karayi ba ko kokarin yin hakan don har Hamood saida ya tambyeta dalilin da ya sanya ta bari hakanan tace mashi ,yasan halinta na rashin son kutse sosai a rayuwarta don haka ya kyaleta da sai ya sanya an bincika mashi Saidai baisan ya bata mata Daidai da rana daya saboda irin tarin kaunar da yake mata.













Sauke ajiyar zuciya tayi ta kwanta tareda lumshe ido hoton mahaifiyarta da mahaifinta na dawo mata a idonta saidai batasan yawan tunani don haka tayi saurin cire abun aranta ahankali tace forgive me my dear parents Amman today she would show them aininhin Hurriya Faisait Hamood











Bintu kallon shaho tayi dashi da kaura jikinta duk a mace yanda bazasu iya gano wani shirin da sukayi ba gabanta yana faduwa sosai don tana tsoron suyi ma Hurriya wani Abu Saidai she trust Hurriya kaura ne yayi dariya yace ko kefa ai yanzu kinga ba wanda zai cutar da ita kayanta ne kawai zamu bincika sai mu duba abinmu mu tafi ko shaho





Shaho da banda cika da batsewa ba abinda yakeyi don yaune ranar fansar duk abinda ta tabayi mashi.cikin isa yace eh sannan ya kalli Bintu yace ke bace mana dagani ko kuma na fara ta kanki Bintu ai da sauri ta matsa ta nufi dakinsu.









Saida suka samu wuri suka zauna tareda jiran dakin yayi shiru yanda baza a jisu ba.





Sun dade suna jira a wajen sannan suka shiga dakin inda bakajin motsin kowa sai wadanda aka hada baki dasu a mata sai kuma su shaho da kaura da suka shigo.









Hurriya tundaga kafafunta har zuwa wuyanta a rufe yake don cikinsu ba wanda baiyi mamakin shigar kirkin da tayi ba yau don ko dazu sunganta as usual da dan skirt na jeans iya cinya kilan batasan sauro ya cijeta sukayi tunani









Shaho ne ya kalli kaura yace shegiyar yarinyar akwai kyau. kaura kam lumshe ido yayi yace ga gashi ga kamshi don fa inajin kamshinta har a bakina murmushin mugunta yayi shaho yace yau zamu fanshe wulakancin da duk ta tabayi mana karshen jiji dakai da izza yazo.







Shaho yace ban iya jira sannan ya karkato kanshi tareda shinshina gashin Hurriya wanda banda kamshin mayukan Khalifa masu tsada ba abinda suke kamshin na bugun hancin shaho yace jar uba yarinyar nan yar gayu ce kaji wani kamshi da gashinta yakeyi wanda yake barazanar fasa mani kai kaura ne yace dallah ka ishi mutane da surutai muyi sauri muyi abinda ya kawomu mu kama gabanmu.







Shaho yace hakane sannan ya zura hannunshi saitin wuyan Hurriya. wani giggitaciyar kara ya saki don yadda Hurriya ta rike hannun tare da caka mai tsinke kitso mai tsananin tsini da zafi wanda ba zato ba tsammani don baiga tashinta ba Saidai saukar tsinke da yaji.



Cikin tsabar mugunta Hurriya ta murde mashi hannu tareda maida hannun baya sannan ta kai mashi wani duka ta mike tsaye



Dukewa yayi tareda rike cikinshi inda ta kai mashi duka yana gwanjin kukan azaba



Kaura da yayi tsaye yana kallon irin action din da yarinyar tayi tsoki yayi tareda kallon kankantarta



kuma da raina shaho da baiyi ta maza ba kalli fa yarinyar





Kaura bude kafada yayi tareda karya wuyanshi saidai ji kake kass kass sannan ya taimaka ya dago shaho tare da tsaida shi tsaye dayake shima shahon namiji ne ya dake kamar ba abinda ya faru.





Duk iya shegenta bata isa taci galaba akansu tunda su biyu ne Hurriya kam kallonsu tayi zuciyarta na tashi da bacin rai how dared they touch her royal body sunanta fa Hurriya Faisait Hamood the y really have messed with the wrong person nufota sukayi gadan gadan da niyyar dukanta tareda kadata ahankali ta juya ta dauko iccen data boye wanda basu lura dashi ba saida saukarshi da sukaji kowanne acikinsu .kafin su dawo hayyacinsu ta kara masu





Kaura ne yayi ta maza tareda rikota aiko rikon da yayi mata yayi triggering dinta ta caka mashi tsinke dake a hannunta sai jini shaho da yake kokarin guduwa aiko ta buga mashi iccenta a kafa wanda ya durkusa da sauri tareda rike kafar







Dukansu a durkushe kallonsu tayi wanda su kuma suka juya sun kasa kallonta

Kallon hannunta da yake sanye da safa tayi wanda ba abinda take bukata irin tayi wanka ta wanke najasar data taba a jikinta na wadanan jakunan.









Saidai ganin fa ba tabar masu tabon da zasu rinka tunawa da itaba batayi masu wani lahani wanda zata ga jini na fita ba ta tabbata sai taga jini na fita a kowanne daga cikinsu zata iya bacci yau ,daukar iccenta tayi sannan tazo inda suke zazzaune shaho da ya kasa magana alama yake mata da hannu tayi hakuri .har zata buga masu iccen wata idea tazo mata tsinke dake rike da hannunta ta durkusa sannan ta rinka caka ma kowa a gwiwar shi duka biyun aiko nan da nan jini ya fara fitowa saida ta tabbatar ciwon ya shiga jikinsu sosai sannan ta bugama kowanne acikinsu icce ta juya tayi tafiyarta





Ihu kara kururuwa ba wanda basuyi Amman kusan ba wanda yake jinsu saboda baccin da kowa yayi.







Bazata iya kwana hakaba batare da tayi wanka ba don haka kawai ta fito hannunta rike da fitilar wayarta da keys din part din Khalifha wanda aka aje mata saboda tana zuwa tana gyarawa.ba karamar doguwar tafiya bace tasha banda kukan karnuka ba abinda takeji





Har saida ta fara gifto Chambers din princes da princess din ta fara ganin securitys da tsirarrun mutane.









Bude kofar part din tayi tana shigowa ta lumshe ido tana maijin kamshin da parlon yake har cikin kanta, ba inda Hurriya ta tsaya sai dakinshi inda yake tsaff agyare banda kamshi ba abinda part din yake.









Toilet ta shiga sannan ta hada ma kanta ruwa mai dadi da kamshi sannan ta cire kayan jikinta ta sanya su watching Machine ta dade tana gasa jikinta tareda wanka sannan ta fito daure da bathrobe grey gashinta ta wankeshi tayi drying ya zubo a bayanta





Wardrobe dinshi ta bude ta fito da sabbin hoodie brown na bvlgari ta sanya hade da fesa turarenshi tana gamawa ta haye saman gadon Khalifa mai dadi wanda ya zama nata yanzu lumshe idonta tayi kaffn ace wani Abu bacci ya dauketa.

[5/28, 3:33 PM] +234 802 952 0062: Masarautar Qamar

56

Galadima ya kalli jakadiyya yace mata wacece waccan data wuce .



Jakadiya da take bin bayanta da kallo tace bansan taba don ban taba ganin taba galadima yace mata kiyi kokari ki nemota sai a hadata da sauran matan nan .cikin gamsuwa tace shike nan,







Hurriya har ta nufi dakinsu inna hanne na zaune idonta biyu da alama gyangyadi takeyi



Hurriya na shigowa ta mike a zabure ta rinka kallonta Hurriya itama kallonta tayi tace lafiya ?inna hanne sauke ajiyar zuciya tayi tace lafiya lau. Hurriya alama tayi mata ta zauna sannan ta mika mata ruwa saida tasha sannan ta kara sauke ajiyar zuciya don tasan abinda Hurriya take jira taji ayanzu bazai wuce miye ya hanata zuwa ta kwanta sannan damuwar miye a fuskarta





Murmushi inna hanne tayi tace kin tada mana hankali Sosai da bamu ganki ba wasba da kyar na lallasheta taci abinci tana gama cin abincin bacci ya dauketa gatanan kina ganinta ,Bintu ma da kyar na lallabata ta tafi ta kwanta



Hurriya data gaji da tsayuwa don wani irin mugun sarawa kanta yake mata Don har kafafunta karkarwa sukeyi inna hanne da tana kula da ita don tun shigowarta tasan bata lafiya don idonta sunyi wani kalar sanyi tareda canza launi da idonta sukayi







Murmushi inna hanne tayi ganin yadda Hurriya ke kokarin fada da ciwon don kada aga gazawarta don har ta zauna tareda jingina da yar katifarta wanda idan ba sanin Hurriya kayi ba idan ka kalleta zakace lafiyarta lau don yadda take kokari sosai wurin boyewar ciwonta







Ganin inna hanne har yanzu ita take kallo ahankali ta maida jikinta saman katifar tareda lumshe idonta tace bacci ya daukeni a Chamber Khalifha ku daina damuwa da abinda bai kai asa damuwa ba ,maganar ta fito da wani irin huci da zafi don inna hanne saida taji hucin Sosai mai dauke da kamshin mouthwash ya bugi hancinta



Inna hanne ba tareda tace mata komai ba tayima Hurriya saida safe ta fita Hurriya kam ko ida fita batayi ba ta sauke ajiyar zuciya sannan Bacci ya dauketa saidai wani irin nishi da shesheka kawai takeyi cikin baccin





Inna hanne datake labe bata tafi ba ta fito tareda shigowa wurin Hurriya hankalinta tashe data kalli yanayin da take ciki ai inna hanne da sauri ta fita taje ta dauko magunguna da kasko cike da garwashin wuta tazo da sauri ta barbada mata wani magani banda hayaki ba abinda ya turnike wurin





Hurriya kam tana shakar wannan hayakin gayen ta rinka wani uban tari mai sarkewa bude idonta tayi tana kallon inna hanne datake mata sannu amman tana cigaba da zagaye ko ina da hayakin Hurriya alama ta rinkayi mata da hannu ta dakata ta dakata Amman taki



Hurriya numfashinta wani seizure yake yana dawowa saida inna hanne ta tabbatar da hayakin ya shiga ko ina najikinta tareda fita hayyacinta sannan ta sanya wani hayakin wanda ya taimaka ya fara calming Hurriya ahankali Sosai don sala sala hayakin yake fita dayan gayen data zuba



Ahankali numfashinta ya fara daidaituwa sannan Bacci ya dauketa, inna hanne ajiyar zuciya ta sauke tareda godema Allah hade da jinjina ga yayanta.don tun lokacin data ga abubuwa akan Hurriya ta kaaa sukuni sam har saida taje garinsu inda taga yayanta sannan tayi mashi bayanin duk abinda ya faru a lokacin yayanta shiru yayi tareda mamaki hade da tausayin yarinyar da take gaya mashi don haka yace zai dage dayi mata Addu a da sauka da sadaka itama yarinyar sai ta dage da azkar saboda makiyan da kikace shiru inna hanne tayi sannan tace nan fa matsalar take don kwata yarinyar abubuwan addini basu dameta ba don duk wani Abu dake nuni da mutum cikakken musulmi ne bata dashi don ko shigarta irin ta turawa ce don idan ba gani kayi tayi sallah ba zakayi tunanin cewar ba musulma bace sai kuma annurin musulunci da baya boyuwa a fuskarta.







Shiru yayi yanajin bayanin da tayi mashi sannan yayi murmushi mai sanyi tamkar hakan ba abin damuwa bane cewa yayi ki tayata da addu a Allah ya shiryata sannan kina dan nuna mata wasu abubuwan insha Allah zata gyara inna hanne bude baki tayi zatayi mashi bayanin halin Hurriyar murmushi yayi mata tareda yimata alama da hannu da tayi shiru gudun daukar alhaki don akan ce ko alkhairin mutum kafada zai iya zama laifi bare akasin haka Allah dai ya gafarta mana baki daya Ameen Ameen





Inna hanne tayi mashi bayanin ciwon Hurriya ya dade shiru yana nazarin each and every detail sannan ya tashi ya debo magunguna wasu rare herbs ne wanda da kyar ake samo mashi su a daji hade da ganyen da za ayi mata hayaki duka magunguna da ya bata ba wanda baiyi mata bayaninshi ba hade da fatan insha Allah indai aka dage anayi mata zata warke Daidai gwargwado tunda Akwai poison a ciwonta amman ya tabbatar ko bai warkar da ita ba wannan yana fatan zuwa gaba idan har ansamo mashi iccen itaciyar dayake nema shekara da shekaru to Zata iya warkewa har abada yana fatan hakan.







Inna hanne shiru tayi tareda sauke ajiyar zuciya ganin yadda Hurriya take bacci

23 / 27