Masarautar Qamar Sirrin Fadar Sarauta by Khadija KMU

Author :  Khadija KMU Category :  Romance

Chapter   14 / 27

39K to 42K   out of 79.4K words

what is different about him that no other human being has.





He s intact kamar kowani mutum mai lafiya saidai his aura,peril and danger that always follow him behind wanda ba kowa yake da hakanba. a business world ana kiranshi da cobra blind snake saboda poisonous dinshi da danger dinshi a masarautar su kuma ana kiranshi da Khalifha Qamar



Tafiya yakeyi rike da sandar shi sai glasses din dake a fuskar shi wanda dan mutum bai isa ya hasko idonshi ba saboda makantar dake tattare dasu





Wucewa yake ta mutane kusan kowa yana durkusawa yana gaisheshi amman a wurin tamkar baisan dasu ba don ko kallo basu isheshi ba wani acikin security dinshi yazo wanda da alama kamar hakan dokace a wurin shi a hankali kallonshi yayi sannan ya kalli security s din yace they re all fired chief of security din ya sara mashi tara da bowing yace okay sir ya tafi







Chief of security din ya dawo yana kallonshi tareda tunanin hali irin na Khalifha Qamar chief of security yace a zuciyarshi ko miyake expecting daga Khalifha Qamar a reptile without any emotion.







Duk masarautar ta dauka Khalifa Qamar ya dawo Khalifha Qamar lmakaho ya dawo.







Gafa Khalifha Qamar kam ya fans kunajin dadin labarin namu ko kuma dai da sauki tohm gafa wani shi kuma wai Khalifha Qamar shima kamar baida kirki Amman ku biyoni domin muji labarin Khalifha Qamar din.





Anan na kawo karshen free page na wannan

Littafin ya Koma na kudi saboda wani dalili na daban









[5/28, 3:32 PM] +234 802 952 0062: <ØßMasarautar Qamar

The mysterious palace



By Khadija KMU



Page 35&36



Shiru shaho da kaura sukayi suna sauraren abinda zubaida take fada wanda kamar ba gaskiya ba don basuyi tsammanin haka ba kuma sun sa rai sosai da kyar shaho ya sauke ajiyar zuciya sannan yace mata shi kenan wani lokacin kada ki damu muna tare murmushi tayi sannan tayi fari da ido tace nagode ta wuce abinta



Shaho kallon kaura yayi sannan yace mashi to yanzu miye abun yi?Rada ce yayi mashi sannan suka kyalkyace da dariya suka tafa kamar wasu mata suka bar wajen





Hurriya har yanzu idonta a lumshe yake tanajin waka inna hanne ce ta shigo ta kalleta sannan tace Hurriya kitashi kici abinci kada ulcer ta kamaki







A hankali Hurriya ta bude idanunta masu masifar kyau ta zubama inna hanne su wadda fuskar ta ke nuna alama da tausayi da damuwa



Cizon bakinta tayi ta kara kallon inna hanne domin tabbatar da irin kallon da take mata wanda tafi tsanar irinshi a rayuwarta ta tsani irin wannan kallon wanda ke cike da tausayi saboda itadin ba abar tausayi bace bata bukatar tausayin kowa a rayuwarta she s all alone in this battle of life don haka bata bukatar wani sympathy daga wurin kowa she will win the battle all by herself





Kallon inna hanne tayi cikin idonta aiko ba shiri inna hanne ta sauke idonta kasa



Hurriya zama tayi tareda bude kular da tayi mata spaghetti taji kifi sosai plate ta amsa ta zuba batasan mi yasanya Allah ke hadata da mutanen kirki masu sonta ba duk da cewar bata cancan ci hakan ba

Kallon plate din tayi inna hanne tace ki samu kici abincin da zafi batace mata komai ba kuma bata fara ci ba har saida inna hanne ta fita sannan ta fara ci



Taci taliyar Sosai saboda yau tadan ji yunwa saboda bataci abinci ba bayan tagama cin abincin wani bacci ya kwasheta.





Karfe 8:00 ta tashi na safe don haka agurguje tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka ta sanya uniform sannan ta nufi bangaren gimbiya



Shiga tayi kitchen dama iyakarta kitchen tunda ta fara zuwa sashen aikin bata taba wuce kofar kitchen din ba kuma bata taba yima kowa magana ba kullum tanajinsu suna kananun maganganu da munafucin irin na gidan sarauta Amman bata taba cewa kala ba



Kallonta kowa yakeyi don ta saba da irin kallon amman na yau ya bambamta kallon kowa tayi sannan tace munafukai bunch of useless sannan tazo ta fara aikinta sakin baki sukayi suna kallonta don akwai iyaye manya wanda sun haifeta amman ba ruwanta ta zagesu





Saida ta tabbatar tagama duk abinda ya dace sannan ta nufi kofar fita kiran sunanta akayi tareda cewa zinariya na kiranta batace komai ba ta bude kofa tafita abinta shiru sukayi kowa yana ayyana abubuwa cikin ranshi saidai sun san cewar ta debo ruwan dafa kanta.





Hurriya ba inda ta tsaya sai inda ta saba wanki ba tareda bata lokaci ba ta fara aikinta as usual ta dade tana wanki saidai tanayi tana kallonn inda wasba ke zama tana zuba mata labari kullum kasa janye idonta tayi don haka tana gama dauraya tayi shanya sannan ta nufi hanyar da taga wasba na yawan fitowa akwai yar tafiya don saida ta shanye titin sannan ta fara hango wurin kamar unguwa shiga tayi cikin unguwar wasu yara tagani suna wasa magana tayi masu wanda ya sanya su daina wasan suna kallon tsantsar kyaun hallita da gashin da Allah yayi mata



Dukansu ba wanda ba kallonta yake ba dage gira tayi tareda kallon idanunsu wanda ya sanya sukaji ta cika masu idanu tambayar su tayi gidansu wasba aiko kamar jira suke ta tamabayesu cike da murna suka rakata har kofar gidan dari biyu ta basu tace su raba sannan ta shiga cikin gidan wanda baida girma amman dai ginaun Bulo da bulo ne

Murna yaran sukai i tayi sunajin dadin kudin da tabasu suna mata godiya da addu a



Babu ko sallama ta kutsa kai ta shiga daga ciki inda takejin ihun yarinyar da shasheka







Dukan wasba kawai takeyi wanda kamar Allah ya aikota wasba kuma shimfide a kasa bata lpy sai tazuba mata ruwan randa mai sanyi gaske tukuna take zuba mata dorina tana don ubanki karya kike ba wata rashin lafiya da kikeyi sai kin wanke kayan can shegiya mayya tsintarciyar mage bata mage dukanta kawai takeyi tana zagin iyayenta





Hurriya kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah ranta na kara baci bata cika shiga rayuwar mutane ba ita haka Allah yayita kuma batasan ana shiga rayuwarta saida mi bazata iya zama tana kallon ana Neman kashe Wasba





Shiga cikin gidan tayi sannan tazo saitin matar tana watsa mata wani kallo da idanunta masu kwarjini cikin tsiwa da gadara matar tace ke kuma daga ina shegiya la anarna halan kema zuwa kikayi domin ceton ta Tau bari kiji inagaya maki wanda suka fiki ma sun barni don ba wanda ya isa ya kwaci wannan tsintarciyar magen cikin gidan nan tana rike kugu tana watsa ma Hurriya wani kallon banza



Hurriya batace kala ba tana kallonta har tagama kumfar bakinta





A hankali Hurriya tazo saitin wasba tana kallonta duk ta rame ta fita hayyacinta Hurriya sam bazaka iya karantar abinda ke fuskar taba



Dagota tayi sannan tace sannu kinji bata gama fadar sannu ba taji anja mata gashi abinda kam tafi tsana arayuwarta kenan wani ya tabata hakan yana triggering dinta wanda har monster in her mutum zai iya gani A hankali ta juyo domin kallon isasshen saidai ko mamaki babu uwar rikon wasba ce kallon hannunta Hurriya takeyi wanda yake rike da gashinta tana mamaki is she kidding her dayan gashin Hurriya ta fara ja wanda ya sanya Hurriya Tayi saurin janyewa tareda dauketa da kyakyawan mari rike tana watsa mata wani kallo me ma anoni



Rike kuncinta tayi tana lailayo wani ashar ai bata ida kai aya ba Hurriya ta kara wanka mata mari





Kallon bukitin da ta cika da ruwa Hurriya tayi aiko ta dauko ta sheka mata shi duka wanda ya sanya ta faduwa tana shesheka





Hurriya bulalar da ta yadda ta dauka ta fara zabga mata ita ko ina ajinkinta da tsantsar mugunta da keta ihu takeyi kota ina tana Neman taimako acece ta Amman shiru ba wanda ya lekota saida Hurriya ta tabbata tayi mata blue and black sannan taje wurin wasba har zata tada wasba wata roba ta dauki hankalinta



Robar yaji ta hango aiko ta nufi yajin sannan tazo saitin fuskarta ta zazzage mata shi ihu take tana kiran sunan makwabtan ta Amman ba wanda yayi yunkurin taimaka mata





Hurriya riko wasba tayi wanda zata iya cewa abinda bata taba ba all her life kenan wasba kam murmushi tayi tana kallon Hurriya tanajin kamar taga mahaifiyarta har sunzo zaure Hurriya ta tuna da har yanzu bataga jini na fita a jikin matar nan ba anya zata iya bacci yau batare da taga jini na fitowa ba cewa tayi dan zauna sannan ta koma ciki



Hurriya Kallonta tayi ko motsi batayi alamar ta suma Amman a haka Hurriya taje ta take mata hannu tare da murzawa yadda ko bata kare ba tasan akwai gocewar kashi ko babu gocewar kashi akwai targade tafison tayi jinya kamar yadda ta sanya wasba jinya







Ba inda ta tsaya sai dakinsu sannan ta kalli wasba tace ta kwanta ta huta zata samo mata abinda zataci wasba murmushi kawai take tana binta da kallon kauna



Kitchen Hurriya ta shiga bata iske inna hanne a kitchen din ba saidai haule reza don haka Hurriya wurinta ta nufa tace mata ta zuba mata abinci ba bata lokaci haule reza ta zuba ma Hurriya abinci da yake tana yinta sosai amsa Hurriya tayi batare da tace ta gode ba ta nufi dakin ta kalli wasba tace tashi kici ahankali wasba ta tashi sannan ta karbi abincin a hannun Hurriya tayi bismillah ta faraci taci abinci sosai Hurriya cikin kayanta ta lalubo wani magani da aka bata farkon zuwanta masarautar Qamar ta mika mata tace ta sha .amsa tayi tana yamutsa fuska alamar batasan magani Ganin irin kallon da Hurriya takeyi mata ne ya sanya ta hadiye maganin hade da ruwa.









A hankali yake saukowa daga saman bene ba abinda bai Ganin ba ta CCTV caméra inda akayi mashi barbade yana kallonsu da duk abinda suke cewa jin takunshi da isowarsa ya sanya kowa ya shiga taitayinshi



Takunshi wanda yake bayyanar da kamala kuma da taurin kai sai kuma aura dinsh da take zagaye dashi



Tunda suka ji takunshi kowa ya shiga tsananin fargaba da shakku don ya cika ko ina a parlon da kwarjini da girman shi fuskar shi babu alamun sassafci ko sauki idon shi rufe da glasses mai kyau da tsada sai walking stick dinshi wadda ta kara fito da dressing dinshi





Dukansu dukawa sukayi har yazo katon dining dinshi kallonsu Dukansu ya shigayi yana karantarsu bude kulolin yayi na different varieties na abinci sannan ya tsaya a dake ya dage table din baki dayanshi banda karar fashewar Abu ba abinda kakeji a wurin plate da abincin suna tararatsewa komai yana zubewa kasa cikin tsananin bacin rai yake kallon duka munafukan fuskokin su da suke kallon kasaa ya buga masu wata muguwar tsawa yace how dared you ba wanda acikinsu hanjin cikinshi bai kada ba saboda tsawar da ta ratsa ko ina na falon ida juye komai yayi kara kawai kakeji wani abu ya danna aiko nan da nan sai ga cheif of security ya shigo kallonshi yayi sannan yace they re all fired kuma kayi punishing dinsu according to my rules how dared they messed with their future king .chief of security ya dukar da kanshi yace yess your league cikin bacin rai ya koma kasa don ko abinci bai bi takanshi ba







Kuyangin suka biyo chief of security din banda kyarma ba abinda sukeyi don sun san kashinsu ya bushe don Allah ya taimakesu ba Khalifha Qamar dakanshi yayi masu hukunci ba





Ba inda suka tsaya sai babban prison din dake cikin palace din chief of security sai kamewa akeyi duk inda ya gifta don shima kamar boss din nashi yake fuskar nan tashi kullum babu dariya anan aka watsa su sannan ya bada dokokin yadda Khalifha Qamar yakeson ayi masu azaba .





Hurriya kam tsayawa tayi tana kallon wasba wadda tana gama shan magani bacci ya dauketa kallon yadda take sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta fita wurin Bintu ta nufa inda take zaune tayi uban tagumi kallonta Hurriya tayi sannan tace mike damunki a firgice ta juyo ta kalleta sannan ta turo baki fashewa Bintu tayi da kuka tana kallon hurriya zama Hurriya tayi kusa da ita tana sauraren kukan da takeyi har saida tagama sann Hurriya ta kalleta da ayar tamabayar miye ya sanyata kuka





Bintu kallon Hurriya tayi tace ina cikin damuwa ina tsoron kada wani abu ya sameki Hurriya har yanzu banda sukuni tun ranar da naga kina kokowa da numfashin ki. Hurriya shafa kanta tayi sau daya wanda kamar ta shafa kashi don tana shafawa ta sauke hannunta murmushinta mai sanyi wanda ke fiddo mata da aininhin kyau da kuma wata boyayyiyar charisma da kwarjini tayi hakoranta farare tass da kuma Gold dinta dake tsakankanin hakoranta gefe da gefe





Bintu kallonta kawai takeyi tana fatar Hurriya ta kasance a irin wannan yanayin a har abada ba irin yanayin da zata rinka daure fuskaba



Murmushin daga zuciyarta ya fito wanda ya kasance har cikin ranta kuma zata iya kirga murmushin da ya fito daga zuciyarta irin wannan tunda ta baro masarautar Heral wannan shine na biyu ko kuma







Kallon Bintu kawai takeyi Bintu har ta bude baki zatayi magana saiga wasu kuyangu biyu sunzo wai Gimbiya zinariya na kiran Hurriya .

[5/28, 3:32 PM] +234 802 952 0062: <ØßMasarautar Qamar

The mysterious palace



By Khadija (KMU)



37&38



Hurriya kallon wasba tayi wadda har ta fara warwarewa inna hanne ta samo masu aron katifa inda Hurriya ta kwana jiya da yau kwana biyu da suka wuce taje kiran da zinariya tayi mata

saidai yadda matar ta rinka kallonta kamar zata cinyeta ne ya bama Hurriya haushi Sosai don har saida ya zamana cewar Hurriyar ta gaji da kallon da take mata tayi tafiyarta zinariya kam abinda ya bata haushi sosai itadin wacece face kaskantatciya wadda bata da gata









Hurriya kam tafiyarta tayi don bata ga amfanin tsayawa inda akeyi mata irin wannan lusful look din ba



Don kawai bata bukatar wani ya kara tabata a masarautar nan da sunan duka da ba abinda zai hanata ta buge idon zinariya yadda idan ance ta kara kallonta haka gobe bazata

Kara ba saidai tasan girman abun da take tunanin aikatawa ne don as a maid how could she messed with someone like her shiyasa don haka duk hukuncin da akayi mata bazata iya retaliating ba bata cikin yanayin buge idon kawai ma shiyasae don this is not an excuse to her because she doesn t give a damn at all yaushe ta fara tunanin abinda zaije ma ya dawo saidai idan bata ga damar yin abun ba sunanta fa Hurriya Faisait Hamood murmushi tayi kadan sannan ta cigaba da kallon wasba wadda dan kwalinta yadan zame





Kallon cikakiyar sumarta Hurriya tayi wadda take da yawan gaske da cika saidai gashin yayi dukun dukun ga dukkan alamu ba a kula dashi



Ahankali ta taba gashinta wanda itama takejin ya takura ma rayuwarta don tana bukatar aski idan ta aske nata sai taba ma wasba itama ta aske nata don gashin yayi masu yawa









Khalifha Qamar zaune yana kallon masu aikin da ake shigowa dasu yanzu kusan batch na bakwai kenan Amman har yanzu ba wadanda sukayi mashi



Don idan ankawo sai ya tashi yayi analyzing kowacce acikinsu saidai Dukansu ji suke suna cikin wani bala i da masifa saidai kwata kwata baya saukakawa kowanne acikinsu don duk wanda aka kawoshi chamber din Khalifha Qamar to ba ason shi ba a kaunar shi fitinar shi da izzarshi ta ishi kowa





Cheif of security wanda ya shigo da kuyangu kusan guda goma kallonshi yayi yana jiran command daga wurin oganshi kuma uban gidanshi saidai baice kala ba ya tashi ya hau sama



Yasan nufin shi har yanzu basuyi ba cikin rashin gajiyawa da halin yarima ya korasu sannan ya fita zuwa nemen wasu







Khalifha Walking stick dinshi ya canza da wasu kaya masu matukar kyau sannan ya fito yana takunshi mai girgiza makiya har ya iso inda convoy dinshi suke kallon security s dinshi da suna Ganinshi suka fara dukar dakai alamar gaisuwa yayi ya dade yana kallonsu





Alama yayi da sandar shi da abude mashi mota da sauri aka bude mashi farar limousine dinshi ya shiga da tsantsar mulki hade da lumshe ido yanajin kamshin da ya mamaye ko ina a motar sannan suka fara tafiya







Da wani irin mugun gudu suke tafiya kowa basu wuri yake don a yadda suke tafiya basu keda asara ba sai wanda ya haye masu







Wani katon fili ne inda wurin yake dauke da manya manya mutane daga masarautoci daban daban zaune ana kallon polo din da ake bugawa wanda a shekara sau daya akeyinshi





Jiniya ce wadda sarki kawai akeyi ma irinta tohm irinta tawagar Khalifha Qamar sukeyi don wata irin kara jiniyar takeyi wadda saida hankalin kowa ya dawo kansu





Kowa ya saki baki da kunnuwa yana jiran yaga wani issashen ne haka



Mai martaba sarki Faizan Qamar wanda yake zaune akan kujerar girma ta mulki ya kalli motocin da suke shigowa wurin da wani irin mugun gudu murmushi yayi yana kara gyara zama The Devil is back Don basai an fada mashi kowaye ba makahon Kaninshi ne ya dawo wanda hakan bai bashi mamaki ba ko kadan don an sanar dashi zuwanshi don yana sane da duk abinda ke faruwa a chamber dinshi murmushi yayi na kasaita

Saidai abinda ya bashi mamaki mi ya kawo Khalifha a filin polo don tunda ya fara makanta shekara goma bai taba zuwa ba sai yau



Akwai kallo kenan koma miye a hannun rigarshi yana jiran yagani







Bude mashi kofa akayi sannan ya sauko da kafafunshi.

girman hallitar shi da kuma annurin sallahr fuskarshi ya fito sosai wanda ya sanya ma masu kallonshi shakkar shi



Brass Nautical folding stickc ce rike ahannunshi na dama yana dogarata cike da mulki



Ba wanda zai kalleshi yace mashi makahone don ko lokacin da yayi makanta ba lallai Kagane cewar shidin makaho bane saboda yadda ba wanda yake taimaka mashi da hanya kuma da alamari na Rayuwa



Ya fito a cobra dinshi dangerous

14 / 27