KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   42 / 42

123K to 124.3K   out of 124.3K words

binsa dakin nashi tayi ta samesu kwance yadora hanfan akan kirjinsa, ture"

"hanfa tayi ta maye wurin tana turo baki,"

"""Ai wurinane. """

"Dariya yayi ya daga hanfa sama yana cewa,"

"""Baby kinji momynki na kishi """

"""Ni ba momy bace..."""

"""Oh sorry baby i mean..."""

"Sake rukunkumeshi tayi,"

"""Nima sai ka dagani..."""

Kwantar da hanfa yayi ya dauki bilkisu yana dagata. Kallonta yayi yana murmushi ita kuma tana

"feeding din hanfa,"

"""Kema fa harija ce baby..."""

"Harararsa tayi, ""kamanta..."""

"""Dagaske kinfini jaraba ni kawai juriya nafiki, ke kinada son abun amma bakida juriyarshi,da"

"kanki zaki nema amma mintuna kadan zaki fara yiwa mutum raki kina kukan kin gaji """

"""Ni garama da ka tuna min, planning nak. """

"Bata karasa ba taga yawani zabura kamar ta caka masa allura,"

"""Baby p me? Lallai sai yau nayarda kema karamar yarinya ce. , gaskiya koda wasa ban amince"

"ba soo karma kifara"""

"""To sai muyi na musulunci ai..."""

"Kallo yakafe ta dashi zuwa can yace,"

"""So kike ki kasheni ne? Bazan iya wannan wahalar ba dan zan iya mutuwa, wannan ai"

"muguntace. """

"Duk ta yadda ta bullo masa sai ya bulle dan dole ta hakura, idan kagansu da yar yarsu kuwa abin gwanin ban sha'awa ammafa kowa acikinsu kishi yakeda ita, shi bazai ga ana feeding dinta yayi shiruba sai yace ai nashine ita kuma wai bazai kira daughter dinshi da baby ba sai ita, cikeda begen juna yakoma makaranta dama semester din karshe ne, ranar da yakoma da daddare yakirasu"

"video call yana kwance adakinsa kan katifarsa sukuma suna kan gado bilkisu rungume da ita,"

"""Hy daughter "" Yafada yana murmushi,"

"""Hy Daddy "" Bilkisu ta amsa tana dariya,"

"""My daughter how are u?"""

"""Am fine Daddy "" Bilkisu tasake amsawa tana dariya, hira yaci gaba da yiwa hanfa ita kuma"

"bilkisu na amsa masa daga karshe yabata fuska ganin bilkisu ta sauya mata maman da take bata zuwa dayan,"

"""Baby kuma yaza abata nawa?"""

"""We are sorry Daddy... Kadan zaka sammata kagafa kwarewa tayi..."""

"Haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikeda kaunar juna da tattalin juna, har fahad yakammala karatu lokacin da zai gama bilkisu hutu ta dauka a office tabishi kaduna cikeda jin dadi da farin ciki yarinka nunasu awurin friends dinshi da abokan arziki yana cewa ga familynshi idan badan shine yafada ba da tabbas dayawa bazasu yarda ba saboda ko da wasa baiyi kamada"

mai iyali ba.

BAYAN WASU SHEKARU.

"Wata matashiyar mata nahango kyakkyawa wacce ke cikin kwalliya ta alfarma tsaye tana rarraba idanuwa a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu kano, tana sanye da jar atamfa ta yafa jan mayafi sannan komai nata ja tayi amfani dashi tana ta faman duban agogon dake daure hannunta,sake daga idonta tayi akaro na biyu nan tahangosu suna saukowa daga matattakalar jirgi, murmushi tasaki yayinda nima na waiga domin kallon wadanda take yiwa murmushin, wani kyakkyawan saurayi nagani rikeda hannun wasu yara guda hudu, biyu maza biyu mata, biyu kansu"

"daya suma biyun kansu daya, dagudu yaran sukazo suka rungumeta suna kiran ""oyoyo mommy"""

"Kallon matashin saurayin tayi ta dan bata fuska,"

"""Daddy kai wallahi tafiya dakai jidaline... Duk kunbi kun sakani doguwar tsaiwa wurin nan"""

"Ido ya kanne mata guda daya sannan yace,"

"""Wai ai duk acikin so ne..."""

Da key din hannunta tayi amfani wurin bude musu motar nan yaran suka kwasa dagudu suka

"shige,"

"""Dadina dakai yarinta, har yau baka girma ba"""

"""Waye yaron? Kibari muje gida zan kamaki"""

"Dariya tayi takama kunne guda daya,"

"""Am sorry ya fahad"""

"Wata dariyar yasake yi cikeda farin ciki, hannunta yakama suka nufi cikin mota yana bata labarin dinner din da zata rakashi yau da daddare ta wani friend dinshi, sau dayawa idan yace ta rakashi party ko dinner sai tace a'a ita bataso suje tare ayi masa dariya kowa yana tafiya da yar karamar"

yarinya yar kasa da 25 amma shi yadebi tsohuwa duk lokacin da tafadi haka sai yayi dariya yace

"Shifa har yanzu yakasa ganin girman da taketa kurin tana dashi saboda kallon mitsitsiyar yarinya yake yimata her age is just a number, kuma ako ina baya kunyar nunata amatsayin matarshi duk inda zaije tare da ita yake zuwa, ko wannan umarar ma da sukaje da yara har ita yaso sutafi duk da last time iya su biyu sukaje sukasha soyayyarsu suka barwa ammah yaran,to wannan zuwan amma aiki ya hanata kasancewar tazama babbar jami'ar gwamnati mai kulada harkokin yada labarai shikuma ma'aikacine a asibitin koyarwa na mal Aminu maganar dinki kuwa tun shekarun baya yadaina domin bilkisu takafa ta tsare ita kadai yake yiwa dinki ahalin yanzu amma yanada babban shago da yabude yazuba ma'aikata sukeyi. Kowa yasan irin shakuwa da soyayyar dake tsakanin ma'auratan, lokuta da dama su maama na gulmarsu idan suka hadu suce sun rasa wannan irin kauna ta adda labour da ya fahad duk sunbi sun bata junansu da shagwaba kullum cikin yiwa juna shagwaba suke kuma duk fahad ne ya koya ma Bilkisu, ita dai Bilkisu babu abinda zata cewa fahad sai fatan alkhairi domin ya zame mata wani babban jigo acikin rayuwarta, guy din yayine tako ina yanada yakana da kunya da kawaici ga iya soyayya shiyasa baya taba gundurarta sannan yana respecting dinta takowanne bangare baya taba treating dinta kamar karamar yarinya sai ta bangaren love, itafa yanzu da zataga wacce karamin yaro da babba zasu fito neman aurenta da zata bata shawarar ta auri yaron domin sai yafi kulawa da ita, abangaren fahad shima hakane kwata kwata baya sha'awar auren karamar yarinya acewarsa wacce ta girmeka tafi kula dakai zatayi treating dinka kamar baby amma kananan yaran nan babu abinda suka ajiye sai rashin kunya, ahalin yanzu dai yaransu hudu da bilkisu hanfa da Muhammad fahad sai Mimi da Awwab, to muna"

addu'ar Allah yaraya su amin.

"Alhamdulillah anan labarin kamar da wasa ya kammala ina addu'ar ubangiji Allah ya taramu cikin ladan nidaku yakuma yafe mana a inda nayi kuskure. Hakika ban taba sanin inada dunbin masoya har hakaba wallahi sai yanzu, tabbas kun nuna min kauna da kuma soyayya, da yawa daga cikinku wadanda suka siyi book dinnnan ban sanku ba banma taba tunanin kun san da niba, ina mutukar godiya hakika soyayyarku wallahi itace abar dubawa agareni bawai kudin da kuka siyaba domin mai sonka shi zaiso kayanka nagode Allah yabar zumunci,sai mun hadu cikin kundin haske wato gamayyar alkaluman marubutan haske gaba daya, zanzo muku da wani labari mai salo daban akan darajar malami da amfaninsa cikin alumma, sai mun hadu da yardar Allah taku ahar kullum Ummi"

A'isha.

*_

*_Ummi Shatu_*

42 / 42