KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   26 / 42

75K to 78K   out of 124.3K words

bani da ja yanada mutunci da hankali amma zamana tareda shi a matsayin miji da mata.... Hmmm"" sai kuma tayi shiru takasa karasawa, karshenta dai wannan dare sai bacci barawo shine yasamu nasarar saceta lokacin da take tsaka da tunani tana tambayar kanta wai meye"

dalilin da yasa kowa ke yimata fatan fahad yadawo gareta?.

_FAHAD_

"Tuni fahad yafara zuwa shagon oga Abdul, lokacin da yafara zuwa Abdul din bai wani daukeshi serious ba domin bai zaci cewa ya iya dinki ba sai da yaje wurin sau uku sannan yace yazo yazauna ga keke nan yafara, wata atamfa yabashi da measurement da komai yace ya dinka, ai tunda fahad ya dinka atamfar nan sai Abdul yasoma bashi wani girma na musamman domin koshi fahad yafishi kwarewa afannin dinki expert ne awannan fannin tun daga ranar kasuwar fahad ta bude babu bata lokaci sunanshi ya yadu acikin makarantarsu domin duk wata budurwa mai ji da kanta ta fahad take bawa dinki, bama yan makarantar ba hatta daga cikin garin abuja ana kawo masa dinki, wasu bawai dinkinne damuwarsu ba a'a kawai so suke su kulla alaka dashi sosai oga"

Abdul yayi farin ciki da zuwan fahad shagon domin zuwansa yakawo masa alkhairi masu dinbin

"yawa ga fahad babu mugunta aduk lokacin da zaiyi yankan sabon style zaiyi agaban sauran yan shagon ya koya musu gobe ma wani zai sake kirkira. Sosai yamayar da kanshi mr busy domin har majalissin dare yake zuwa inda magidanta ke daukar karatu shima yadauka dan wayo kam yayiwa su mukhtar wayo,kullum yanada abinyi baya zaman banza shiyasa baida matsalar komai ahalin yanzu kudi suna shigo masa ko ta ina dan idan yayiwa yayan manya dinki sai an nunka masa kudin dinkin nasa sannan abashi koda kuwa yafadi abinda za abashin, husnanshi kuwa kullum suna tare awaya domin tunda yazo kaduna baije kano ba, kullum idan zaiyi girki sai yakirata ta koya masa yauma daga lecture yafito awahale domin tea kadai yasha da safe kuma sai 2 yadawo dakinshi wani tea din yasake sha saida yaji dan dama dama sannan yakira husnah domin ta koya"

"masa yadda zai dafa dan wake dariya yajiyota tanayi tareda fadin,"

"""Ya fahad dan wake kuma? Tabdijam lallai yau dan wake zaisha jifa..."""

"Jin dariyar da takeyi yasashi sakin murmushi,"

"""Kinga idan bazaki koya min ba ni kawai ki fada min kin barni yunwa nata faman damuna..."""

"""Am sorry sweet prince..... Yanzu fara jika kanwa saboda da ita zaka kwaba fulawa din..."""

"Yamutse fuska yayi kamar tana kallonshi,"

"""Gaskiya husnah dan waken nan ba yau ba, bari kawai indafa indomie tunda naji shi nasa hadin"

"yawa gareshi"""

"Kafin tabashi amsa aka bude kofa, bashir ne yashigo mukhtar na biye dashi,"

"""Malam tashi muje gidansu bash.... Wallahi kuma ko baka so sai kaje..."""

Batare da yayiwa husnah sallama ba yakashe wayar yatashi zaune yana kanne ido daya saboda

"yunwa,"

"""Wallahi yunwa nakeji mukhtar kubari muci indomie mana..."""

"""Dallah kazo muje, akwai abinci acan fa..."""

"Baiyi musu ba yakama hannun mukhtar din yamike suka fita, lokacin da sukaje gidansu bashir kanwar bashir din mai suna suwaiba itace keta hidima dasu amma kuma sai kallon fahad take tayi kamar zata cinyeshi shiyasa duk ya takura, suna kokarin barin gidan babansu bashir yadawo Alh Usman mai fitila shahararren attajirin dan kasuwa,afalonsa duk yatara su yana yimusu fada da Nasiha kan su zauna suyi karatu banda wasa sannan su nemi sana'ar yi komai kankantarta ai nan su bash sukayi farat sukace fahad sana'ar dinki yakeyi hakan ba karamin burge Alhaji Usman yayiba nan yarinka saka masa albarka yana cewa yataimaka ya koyawa abokanshi ma domin ko karatun mutum yagama ba lallai yasamu aikin yi akan lokaci ba daga karshe yabaiwa fahad"

kyautar wani hadadden yadi na maza irin mai tsadar nan sky blue da turaren oud wanda shima

"kudinsa akalla zai kai dubu ishirin, bayan sun fito suwaiba ta biyosu tana ta yiwa fahad kwarkwasa da shagwaba shi dai baya iya cewa komai. Tun daga wannan rana suwaiba ta manne masa domin har number dinshi tasamo take damunsa shikuma harga Allah yanzu tsoron mata yake kuma ma banda haka ga husnah agefe, harsu mukhtar saida sukayi masa maganarta amma yace shi baya soyayya dakyar yasamu ya yageta daga jikinsa, ba ita kadai ba duk macen dayaga take takenta na sonshi take fita harkarta yakeyi. A daddafe dai yagama semester dinnan yakoma gida"

dauke da dunbin nasarori sau biyu kacal yaje ganin gida a wannan semester din.

*_Ummi Shatu_*

*Wannan littafin na siyarwane me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

BAYAN SHEKARA D'AYA

"38***Yau garin kano antashi da muku mukun sanyi da tarin hazo wanda ya lullube ko ina shiyasa duk inda ka duba mutane tsilla tsilla kake gani kowa yana yin al'amuransa cikin rashin sakin jiki da takurewa saboda sanyi, a titina kuwa duk motocin dake wucewa da sauran ababan hawa kowa ya kunna fitila saboda nagabansa ko mai tunkaroshi yahangoshi tun daga nesa, fahad yabi sahun mutanen da sanyin yau ke takurawa, dawowarsa kenan daga asibitin koyarwa na malam aminu kano wato (Aminu kano teaching hospital) inda yake gabatar da practical dinsa tun sati uku da suka gabata yafara zuwa, yana dawowa yasa maryam ta dafa masa ruwan zafi yadaure yayi wanka yafito duk sai kakkarwar sanyi yakeyi, agogon wayarshi ya kalla nan yaga karfe biyar"

"da rabi,"

"""Ohh Allah... Ji yanda lokaci yaja amma kai sai kazaci ba afi karfe uku bama. """

"A gaggauce ya shirya cikin riga mai dogon hannu baka sannan yasake dora wata t shirt din mai gajeren hannu ita kuma ja yasaka bakin jeans, sannan yadora rigar sanyi akan rigunan da yasaka wadda takusa kai masa zuwa gwiwarsa, bakar hula yasaka kirar sakar inji ta kamfanin Nike domin ga sunan nan rangadadau agaban hular, har kunnuwansa yarufe da hular sannan yasaka bakar safa mai kauri akafarsa, dan guntun turarenshi da yayi saura shi yadauka yakarar dashi ajikinsa sannan yawuce gaban katifarsa yajawo system dinshi wacce ke kunne muryar sheikh abdurrahman sudais natashi cikin suratul kahfi, kashewa yayi ya ajiyeta kan pillow dinshi sannan yadauki wallet dinshi da bakin glass yafita, cikin gida yashiga gaba daya suma su ayiyah suna falon mamuh suna shan dumi cikin wani katon kasko wanda suka zuba garwashi aciki, su maryama na zagaye da kaskon"

"suna jin wuta,"

"""Wai... Gaskiya dakin nan akwai dumi... Mamuh yau anan zan kwana..."""

"""Kai meyasa baka raboda sakarcine? To kazo ka kwana din ai sai mu kaika inda ranka ko taska muce ga gandamemen saurayi nan amma har gobe bai daina kwana dakin babarshi ba..."" Mamuh"

"tabashi amsa tana gyara lullubin dake kanta,"

"""Ayiyah kina ji fa... Kice wani abu"""

"""Kyaleta autana, yau wannan kaskon wutar adakinka zai kwana"""

"""A'a ai sai dai ku nemo naku ko kibada naki..."""

Dariya sukayi gaba daya yamike daga tsugunnen dayake gaban kaskon wutar kusada su Mariya

"har yana dungure mata kai cikin fada yace,"

"""Ke dalla kirinka kula gashi nan zaki jefa gefen hijabinki cikin wuta... Karki jawa mutane"

"gobara. """

"Mikewa tsaye yayi ya kalli iyayen nashi,"

"""Sweet mamuh zan tafi store.."""

"Sake juyawa yayi ga ayiyah,"

"""Loving momy naje store..."""

"""Kai dai kasani ja'iri, adawo lafiya..."" Inji mamuh, ita kuwa ayiyah dariya tayi tace,"

"""Allah yabada sa'a autanah.."""

"Saka kai yayi yafita yana jin su Mariya na hada baki wurin cewa,"

"""Ya fahad kasiyo mana chocolate..."""

"Yana kokarin fita kawai yakoma dakinsu mask yadauko domin yazama dole yatoshe kofofin hancinsa saboda hazo dan yasan muddin yafita ahaka akwai matsala domin bayan wani bangare na zuciyarsa da ya tabu sakamakon matsanancin hawan jinin dake damunsa harda wata lalurar mai kamada asthma amma kuma ance ba ita bace. Roba roba dinshi yahau yafita daga layin kafin yakarasa gidansu salim yazaro wayarshi daga aljihunshi yasoma kiran salim din, yana dagawa"

"yace,"

"""Kai gwauro.... Dan Allah zo ka rakani store insai turare mana..."""

"Ai salim najin haka yasake tukunkunewa cikin bargo,"

"""Wallahi babu inda zan iya fita a wannan sanyin, kabari gobe da safe ko yamma sai muje mana,"

"""Tab kasan kuwa yanda na matsu da turaren nan? Ni bazan iya rayuwa babu turare ba malam..."""

"""To sai kadawo, nidai babu inda zanje..."""

"Katse wayar fahad yayi yajefe cikin aljihunsa yaci gaba da tukinsa sakamakon yahau babban titi danma daga hancinsa har idonshi duk a rufe suke. Ihsan store yashiga cikin sa'a yasamu dukka turarukan da yake amfani dasu wadanda suka kasance ba masu matsanancin karfiba saboda shi yanzu al'amuransa sai ahankali,suma su ayiyah saida yadauka musu sabulun wanka sinki biyu domin duk wanda zai siya musu abu agidan to guda biyu yake siya, daga karshe yadaukawa su Maryam gidan chocolate yanufi wurinda ake biyan kudi, yana shawo kwana yayi kicibus da"

"maama rikeda jaririn yaronta ahannunta, sam ita bata ganeshi ba domin fuskarshi arufe take,"

"""Hajiya maama. """

"Taso ta dauki muryar amma saita kasa gane ko tawaye, ganin bata ganeshi ba yasashi cire glass"

"din fuskarshi da mask din da yarufe hancinsa, cikeda mamaki maama taware idanuwanta tace,"

"""Ya fahad idonka kenan. Yaushe akasa?"""

"Dariya yayi yamika hannu yakarbi awwab dake hannunta wanda tuni har yafara wayo,"

"""Wallahi hajiya maama ina nan, ina babynki hudah yanzu tagirma ko?"""

"Dariya maama tayi,"

"""Tagirma tana can gida wurin adda labour..."""

"Jin ta ambaci labour yasashi dan runtse idonshi,"

"""Allah sarki... Tana lafiya ko? Yanzu nasan ta haihu ma may be...koda yake bari nayi shiru kar"

"mijinta yasa akamani"""

"""A'a wai baku taba haduwa ba? Ai tana gida, yanzu batada aure..."""

"""Ya salam Sun rabu da mijinne ko kuma rasuwa yayi?"""

"""Wallahi rabuwa sukayi, ai kwata kwata aurenta bai wuce 3 months ba suka rabu. """

"""Ikon Allah... Allah yarufa asiri,wallahi ban saniba nima da yake yanzu nakoma Kaduna da zama"

"can nake karatu, practical yanzuma nazo yi wallahi..."""

"""To Allah yataimaka amma dai yakamata kaida adda labour ku tuna baya, yanada kyau akoma"

"gidan jiya"""

Dariya fahad yayi ya rausayar da kai yana kallon fuskar awwab ganinshi yake kamar bilkisu ce ta

"haifeshi dan tsananin kamarsu kasancewar kamarta daya da maama,"

"""Ai yayar takice miskila ce maama... Tanada wuyar sha'ani """

"Dariya itama mamaa din tayi sannan tace,"

"""To ai zaku daidaita tunda kai kanada saurin fahimta da saukin kai..."""

"""Haka dai kikace, Allah yazabi abinda yafi alkhairi..."""

"Bata kai ga amsawa ba abban hudah yakaraso domin har yagaji da jiranta acikin mota,"

"""Haba nidai nasan tsayawa gaisawa da wata ko wani kikayi saboda naji shirun yayi yawa..."""

"Yafada yana mikawa fahad hannu domin yin musabaha,"

"""Ehh wallahi mijin adda labour nagani shine natsaya muke gaisawa..."" Tafada tana dariya,"

"murmushi fahad yayi,"

"""Ahh kice yayanmu ne, babban yaya yakake?"""

"Dariya abin yabawa fahad jin mijin mamaa na kiransa da wai Yaya bayan kuma yagirme masa ahaife sosai, karbar pampers din dake hannunta fahad yayi bayan yamikawa abban huda awwab, dama pampers kadai tazo siyawa awwab irin babban nan, wurin biyan kudi fahad yaje yahada yabiya har da nasu duk da sunata cewa yabarshi, har zai tafi maama ta dakatar dashi ta karbi number dinshi domin ita dai haka kawai take kaunar fahad shiyasa ba ason ranta aurensu ya mutuba dan dai kawai kaddara tashiga cikine.Lokacin da yakoma gida magrib tayi shiyasa saida yatsaya yayi salla sannan yashiga cikin gida yakaiwa su ayiyah abunda yasiyo musu, sunata saka masa albarka yadauko abincinsa shida Abba yafito domin abban ma yana gari tun watanni biyu da suka wuce yagama service yanzu haka yana zuwa bureau of statistics acan yake dan taba"

"kwadago,"

"Yana zama gefen katifa kamar da tunanin bilkisu yazauna domin gaba daya hirar da sukayi da maama ce tafara dawowa cikin tunaninsa, sama sama yaci abincin yana daf da kammalawa yaji anfara kiran sallar isha kasancewar yanayi yasauya yanzu da wuri ake yinta, tashi yayi yafita masallaci bayan yadawo ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya kwanta da sauran rigunan ajikinsa da safa akafarsa bargo yaja ya lulluba sannan yajawo laptop dinshi yakunna, gaba daya tunanin bilkisu ne ke neman addabar ruhinsa duk da yanata kokarin ganin hakan bai kasanceba. Duk abinda yasan idan yayi zai dauke masa hankali kar yakai ga tuna bilkisu yayi amma abin yafaskara, laptop din ya ajiye agefensa ya kunna wa'azin marigayi sheikh Albani Zaria yana saurara wanda yarage volume din sosai, daga kanshi yayi ya kalli sama kawai yana dulmiya cikin kogin tunani, ji"

"yake kamar zai sake fadawa tafkin kaunarta akaro na biyu duk da bazai so hakanba, yasan kawai"

"yana yaudarar kansa ne wurin kokarin hana zuciyarsa tunaninta domin abinda zuciyar take so ne, kamanninta bazasu taba gushewa daga cikin zuciyarshi ba, to tayaya ma zuciyarshi zata manta da ita alhalin silar sonta ne ya illatata har tasamu rauni daga wani bangare na jikinta, jin anturo kofa za ashigo yasashi maida hankalinsa ga kofar, yaya abba ne yashigo yana rataye da jakar laptop"

"dinshi yana sanye cikin farin yadi,"

"""Amma gaskiya yau kayi over time... Duk cikin aikinne haka?"" Yafada cikin sanyin murya sannan kuma ayanda yayi maganar ahankali yayita irin yadda yakeyi duk lokacin da ciwonshi yatashi"

"hakan yasa Abba karasowa cikin faduwar gaba,"

"""Na dan biya ta gidan Anty asabe ne wai zan yimata register din wani abu nasu na malaman"

"makaranta. Wai amma lafiya kuwa?"""

Murmushi fahad yayi yana gyara kwanciyarshi zuwa barin dama tayadda zai fuskanci Abba

"dakyau,"

"""Lafiya lau nake meka gani?"""

"""Naji maganarka ne ahankali... Amma kasha maganinka kuwa?"""

"""Nasha dazun nan, ka kwantar da hankalinka fa lafiya lau nake Allah"""

"Sai lokacin Abba yajishi yadan samu sukuni, ajiye jakarshi yayi yakalli fahad,"

"""Wannan sandararren abincin fa...?"""

"""Nakane mana..."""

"""Tab, ni ai yanzu ruwan zafi zansha, bari nashiga cikin gida nasa su Mariya su dafa min..."""

"""Su Maryam na aikatuwa hannun samarin gidannan... Idan kowa yayi aure dai sa huta suma"" inji"

"fahad,"

"Daukar flask din abincin abba yayi yanufi hanyar fita yana cewa,"

"""Ni ai ko nayi aure da daya acikinsu zan tafi..."""

"""Katafi da ita tazama yar aikinku ko? Ai ayiyah bazata baka ba dama dai nine..."""

"Baiji abinda Abba yake fada ba sakamakon karar da wayarshi tasoma yi, ganin husnah yasashi jin gabanshi yayi faduwar da har saida yasa hannu ya dafe kirjinsa,cikin sanyin murya yadauki wayar itama najin muryarshi haka yasata jin hankalinta yatashi nan tashiga tambayar ko ciwonshi ke neman tashi amma yace mata a'a saida taji sunjima suna hira baiyi wani abuba sannan hankalinta"

"ya kwanta. Tunda suka gama waya da husnah yake cikin duniyar tunani, idanuwanshi alumshe ga"

wa'azi nayi cikin system dinshi amma azahirin gaskiya ba wa'azin ma yake saurara ba ahaka abba yadawo dakin yayi shirin bacci yadauki laptop din yakashe masa sannan ya kwanta saboda duk azatonshi bacci fahad din keyi bai san tunani yake tayiba tunanin bilkisu wadda yasan har gaban abada bazai taba iya raba zuciyarshi da sonta ba duk da har gobe yana jin zafin abinda tayi masa amma baya danganta hakan da laifinta ko laifinshi yabarshi amatsayin rubutacciyar kaddara wacce

shida ita basu isa guje mata ba.

*_Ummi Shatu_*

BAZATA

*Littafinnan na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

"40***Sam daren ranar fahad bai samu runtsawa ba ko kadan yana ta sake sake cikin zuciyarsa ya kwance ya saka har dare yayi nisa duk da gargadin likita yana yawan fado masa zuciyarsa inda likitan ke cewa yaguji yawaita tunani haka kuma ya rinka samun isasshen bacci arana fiyeda na awa shida. Ganin dai bashida mafita sannan kuma baida guntuwar dabara yasashi fawwalawa Allah dukkan lamuransa dakyar yasamu bacci ya daukeshi wanda sanadiyyar hakan saida ya makara wurin

26 / 42