KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   31 / 42

90K to 93K   out of 124.3K words

min da ita... Idan tana bukatar wani abu akirani.. "" yakarashe maganar yana kallon maama wacce ke"

"dariya,"

"""Insha Allah zamu kula da ita kamar kana wurin..."" Inji meenah,"

"""Yawaa nagode, bari naje..."""

"Juyawa yayi yatafi suna sake yimasa sannu, shi sai yanzu yafara jin dan ciwon kai kadan kadan da"

"dan jiri jiri yasan bawai dan andebi jinin bane may be saboda ciwon dake tare dashi ne, tunda yabar wurin su meenah ke gulmar abinda suka gani,"

"""Ya fahad dinnan kamar wani salihi ashe shima number 1 ne..."" Hindu tafada tana dariya,"

"""Ai kibari kawai adda labour fa tahuta amma takasa ganewa.."" Mamaa tabata amsa,"

"""Gentle dashi wallahi..."" Inji meenah, hirar dai suka bata lokaci sunayi kasan idan kaga mai son"

wanda ya shafeka kaima sonshi kakeyi watakila dalilin kenan da yasa suke kaunar fahad.

"Daurewa yayi yakai kanshi gida duk da jirin da yakeji, yana shiga yawuce ciki baiko kalli dakinsu"

"ba dake soro,"

Falon ayiyah yashiga yawuceta zaune gaban murhu tana karasa daka kuli kulin da zata yiwa baba

"kwadon zogale wanda idan yadawo daga masallaci zai ci, ita kuma mamuh tafita zuwa gidansu salim,"

"Anan tsakar falon ya kwanta yayi pillow da damtsen hannunshi, ahaka yaji motsin shigowarsu"

"mariya daga makaranta,"

"""Sai yanzu kuke dawowa daga makaranta ko? Kun tsaya wasa ahanya ko?"""

"""Allah ya fahad sai yanzu muka samu napep..."" Maryam tafada tana cire sandal din dake kafarta,"

"""Bari natashi nakamaku zama ku fadi gaskiya..."""

"Sun fara rantse rantse kenan ayiyah tashigo dauke da kwanukan zogalen da ta dafa,"

"""Kai da naga kamarma bakada lafiya amma shine zakazo kafada yara da fada ko fahad?"""

"Murmushi yayi sannan yatashi zaune,"

"""Ayiyah lafiyata kalau fa kawai dai jinina aka dan diba..."""

"""Jini? Meya faru?"" Ayiyah tafada tana mikewa tsaye daga durkushen da tayi tana ajiye kwanuka,"

"""Babu komaifa... Bata da lafiya ne wai kuma ana bukatar jini shine aka debi nawa"""

"Yana fadar haka ayiyah tagane Bilkisu yake nufi,"

"""To Allah ya sawwake yabata lafiya. A asibiti take kenan?"""

"""Ehhhh, ayiyah taimaka kibani zogalen nima inci..."""

"""Allah ya sawwake, gashi ai dama babanku na dafawa..."""

"Hado mishi tayi cikin plate harda su tumatur da sauran kayan lambu, zama yayi sosai yaci sannan yakoma ya kwanta babu jimawa bacci yayi gaba dashi bai farkaba sai daf da la'asar, yafito tsakar gida domin yin alwala,zama yayi yasa maryam takawo masa ruwan alwala, yana yin alwalar mamuh tazo tana tambayarsa awanne asibitin su Bilkisu suke domin suna son suje dubata yanzu fada mata yayi yakoma falon ayiyah, yana salla yaji tafiyarsu suna yimasa sallama shi kadai aka bari agidan domin harda su maryama aka tafi. Bayan ya idar da salla yasake kwanciya sai lokacin yamika hannu yadauko wayarshi yana dubawa text din husnah na barka da friday yagani sai kuma miss called dinta da nasu bashir, daya bayan daya yarinka bin miss called din yana kira bayan"

yagama yatashi ya yafita kofar gida yazauna yana jiran dawowarsu ayiyah.

"Yafi mintuna talatin zaune awurin sannan suka dawo, maryam na rikeda babban warmer mai kyau,"

"""Maryam me kika samomin?"" Yafada yana kokarin tashi tsaye,"

"""Surukarka ce tabayar akawo maka wai kaci ka maida jinin jikinka. """

"Jin abinda mamuh tafada yasashi yin dariya saboda yazaci wasan da tasaba yimasa yauma tayi, binsu yayi suka shiga cikin gida,ga mamakinsa kuwa sai yaga ashe dagaske ne domin agabansa"

"maryam ta ajiye warmer din tana cewa,"

"""Ya fahad wai gashi..."""

"Budewa yayi nan kamshi ya bugeshi mai dadi, farfesun hanta ne cikin warmer din yaji kayan"

"kamshi sai kamshi ne ketashi,"

"Kallonsu mamuh yayi sannan yakalli maryam yace,"

"""To kuma ni zaki kawowa ki ajiyewa? Mika musu..."""

"Dauka tayi takai gabansu mamuh ta ajiye, cikin plate mamuh ta zuba masa ta mika masa,"

"""Wallahi mamuh wannan yayi yawa... Rage"""

"""Ba ragewar da za ayi, kaida kabada jini har leda daya da rabi ai dole kaci abubuwan da zasu kara"

"maka jini dannan. """

"""Mamuh dazufa da bakya nan wallahi naci zogale dayawa..."""

"""Saifa ka cinye fahad, dauki maza ina kallonka..."""

"Dauka yayi yafara ci ita kuma taci gaba da raba nasu, yana ci yana hadawa da ruwa har ya cinye saboda ita hanta akwai cikawa mutum ciki shiyasa yajishi yakoshi over, tashi yayi yafita bayan ya gama yakoma dakinsu, salim yaturawa text yana sanar dashi anjima zai rakashi su dubo Bilkisu,"

wanka yashiga domin yanzu ya danji karfin jikinsa.

"Bayan sallar magrib suka tafi asibitin su uku saboda harda ya abba,dukkaninsu sunsha dogayen kaya, babu kowa adakin sai iya Bilkisu da meenah suna zaune kan gadon Bilkisu na shan tea har lokacin tana sanye da hijabinta, jin sallamarsu yasata sake kasa da kanta bata ko dagoba saboda bata son ganin sun hada ido da fahad saboda tasan yanzu bata da wata martaba a idonsa tunda ashe sadaka aka aura masa ita tasan ba kowane yakitsa wannan abunba sai iyallo saboda dama itace ke"

"cewa zata aurar da ita sadaka, yanzu gashi anja mata reni da wulakanci a idon yaro,"

"Tana ji su Abba na tambayar yamai jiki suna yimata sannu dakyar ta iya amsawa sakamakon kukan da ke kokarin taho mata, lokacin da taji meenah na gaisawa itada fahad sai taji kamar da biyu yake yin gaisuwar nan ta shareshi bata ko dago ba daga karshe su Abba suka fita suna yimata"

"fatan samun sauki haka itama meenah sai ta tashi tafita yarage su biyu kadai cikin dakin,"

"""Sannu... Yajikin? Ke daga fada miki gaskiya shine zaki kwanta ciwo...?"""

Jin abinda yace yasata dagowa ta zuba masa harara saboda ta tsani ke dinnan kafin ta dauke idonta

"yarama,"

"""Ni ai ka kira da matar sadaka ko?"""

"""To da matar meye? Sadaka aka bani kuma nakarba..."""

"""Wallahi karya kake yi..."""

"Nuna kanshi yayi da yatsa,"

"""Ni kike cewa ina yimiki karya?"""

"""Ehh din. """

"Kafin yayi magana meenah tashigo rikeda waya nan ta mikawa Bilkisu tana cemata,"

"""Adda labour gashi su elmustapha ne..."""

"Karba tayi suka fara gaisawa dasu elameen suna yimata ya jiki, bata saurari fahad ba wanda"

"ahankali yace,"

"""Yarinya kuma sai kin biyani jinina da na baki dan ba kyauta nabayar ba..."""

Shima bai sake bi ta kanta ba yayi waje abinshi yabarta da kunar zuciya domin maganganunshi

"sosai yanzu suke bata mata rai,wayar nan kawai tanayi ne bawai dan tana fuskantar abinda take cewa ba......"

*_Ummi Shatu_*

*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

"46****Daren ranar ma haka ta kwana batayi bacciba saboda tsabar bacin rai da damuwa da zarar ta tuno maganganun da ya yayyaba mata sai taji kwalla ta ciko idonta. Washe gari dasafe aka sallameta suka koma gida, suna zuwa tasamu tashiga wanka tafito domin shiryawa kamar tasaka hannu aka tayi ihu haka takeji idan har tatuno da maganganun fahad, ahaka ta daure tashirya tana cikeda damuwa tana gamawa Hindu takawo mata abin karyawa nan ta zauna tasoma dan kurbar ruwan zafi bawai dan tanaso ba amma sauran kayan karyawar ko tabasu batayi ba ahaka Hindu"

"tadawo ta sameta tana rikeda sultan a hannunta,"

"""Adda mai gado yabaki ci abincin ba? Saifa kin dan daure..."""

"Jin abinda Hindu tace yasata dagowa ta kalleta da kodaddun idanuwanta wadanda ko kwalli babu,"

"""Hindu banida apatite abakina wallahi, sam bana jin dadin komai..."""

"""Duk da haka ki dan daure mana, sannan dan Allah ki gyara fuskarki kisaka koda powder ne da"

"kwalli... Amma ya fahad yazo yaganki ahakan nan ai akwai matsala..."""

Harara ta watsawa hindu sannan tamaida kallonta kan sultan wanda ke miko mata hannu yana

"yimata gwaranci, mika hannu tayi zata karbeshi amma Hindu taki sakinshi tana cewa,"

"""Kai bari kar kaje ka karasa mana addarmu kaga dazun nan tadawo daga gadon asibiti..."""

"Murmushi Bilkisu tayi ta karbeshi sakamakon kukan da yafara yi, ita kuma haka Allah ya dorawa"

"yaran kannenta kaunarta duk sun shaku dasu babu wanda yake yimata kiywa,"

"""Dan Allah adda labour ki daure kici abincin nan kar yayi sanyi sannan ki gyara fuskarki saboda"

"tsaro..."""

"""Ke hindu idanma fa akan fahad kiketa wannan damun nawa bazan yiba..."""

"""A'a wallahi Adda labour ni basaboda shi bane kawai dai ai kinga idan kika saka kwallin fuskarki"

"zatafi fitowa amma yanzu Allah baki ganki ba duk kin canja kin sake fadawa..."""

"Bata sake yin magana ba ta jawo abincin gabanta ta bude tafara ci tanayi tana bawa sultan, saida"

"tagama tsaf ta zauna gaban mirror tana shafa powder sai tajiyo sallamar khulsum, tana jiyosu sunayi itada hindu atsakar gida hindu nacewa bazasu amshi uzurinta ba tunda bataje asibiti ba"

"saida suka dawo gida. Anan gaban mirrior din khulsum tashigo ta sameta tana zizira kwalli,"

"""Labour patient har an warke anfara coda ado za atari oga?"""

"Harararta Bilkisu tayi ta taso daga gaban mirror din tadawo gefen gado kusa da khulsum,"

"""Zaki fara ko? Allah yakawo ki ai kuma..."""

"""Ah to ai gaskiya ce anwarke mana me kuma yayi saura banda akoma bakin daga..."""

"""Sai kiyi kuma..."""

"""Yawwa wai ke yaushe zaki tare ne? Allah kinga labour ki tare tun kafin abinnan ya bayyana dan"

"wallahi ni harga Allah ban yarda da wannan ciwo ciwon nakiba. Laulayi kika fara ko?"""

"""Wai ke meyasa ba a abun arziki dake ne? Ni dan Allah kinga karki bata min rai..."""

"""To yi hakuri, sorry kinga jiya banzo asibiti na dubaki ba ko? Wallahi khalifa ne nima baida"

"lafiya... Amma yaji sauki yau"""

"""Babu komai ai da kinyi zamanki ma kin kula dashi"""

"""Ai yaji sauki yana can tare da babanshi"""

"""Allah yakara masa lafiya..."""

"""Amin... Yawwa wai mutuniyar kin kuwa taba gwada hadin nan dana turo miki rannan?"""

"Dariya Bilkisu tayi saboda ita wallahi ma sai yanzu tatuna da sakon da khulsum din ta turo mata,"

"""Madam kedai kije kiyi tayi amma ni wallahi bazan yiba..."""

"Kallonta khulsum tayi cikin jin haushi,"

"""Allah yashiryeki labour maza dai ki tsaya kallon ruwa kwado yayi miki kafa wallahi idan baki"

"kama mijinki a hannunba... Hmmm zaki ganene"""

"""Toh Anty..."""

"Dariya khulsum tayi sannan tayi kasa da murya tace,"

"""Wai dan Allah laulayinne da gaske?"""

"""Ban saniba..."""

Kafin khulsum tasake magana suka jiyo sallamar fahad atsakar gida amma ahankali kamar wani

"marar gaskiya, mikewa khulsum tayi tana cewa,"

"""Bari na kwashi yanmatan kafafuwana inbarku kusha morning show dinku, ga wata gumba idan"

"kinaso sharp sharp ce wallahi """

"""Banaso akai gaba..."""

"""Kedai kika sani wallahi, ni sai anjima"""

"Mikewa tayi ta kwanta bayan fitar khulsum tana jiyo lokacin da khulsum din suke gaisawa da fahad atsakar gida mintuna kadan tsakani taji shigowarsa ta hanyar bude kofa da yayi bata ko motsa ba ayadda take bare ta dago ta kalleshi, daga dan nesa yatsaya yana kallonta, riga da skirt na leshi tasaka wanda aka yiwa simple style yayi dass ajikinta, dakin gaba dayanshi sanyayyen"

"kamshine ke tashi cikinsa,"

"""Yajiki ?"" Yafada yana murmushin da bazata ganeba,"

"""Da sauki"" ta amsa kamar bataso domin badan shi din mai jin magana ce komai kankantarta ba"

"da bazai jiba,"

"""Dama nazo dubaki ne, hope kinji dadin jinina dake jikinki?"""

"Juyowa tayi afusace ta harareshi,"

"""Dadinta ma dai banice nanemi da kabani jinin ba, badanma lokacin da aka saka min bana cikin"

"hayyacina ba da me zanyi da jininka.... Wa yasani ma ko guntun sikila ne..."""

Murmushi yayi yana kallonta yasan dai maganar dayace wannan matar sadakar da yakirata dashi

"ne yaketa sosa mata zuciya har take neman hanyar mayar masa da martani,"

"""Kiyi hakuri bani na kar zomon ba rataya aka bani, kuma ratayar ma ban karba ba """

"""Idanma ka karba idanma baka karba ba ruwanka, sannan da kake cewa sadaka aka aura maka ni"

"ai yanzu ma kanada damar da zakace kafasa... Tunda ba adole"""

"""Akan me zance nafasa? Ai narigada na karba"""

"""Duk da ka karba ai kasan hanya mafi sauki wacce tadace da zakabi ka mayar da sadakar """

"Tabe baki yayi yasamu kan bedside drewar yazauna yadora kafa daya akan daya,"

"""Ni yanzu ba wannan ne yakawo ni ba inada abin yi dubiyace ta kawo ni..."""

Wani kallo tayi masa yana sanye da kananan kaya amma yadora lab coat asama kafarshi rufe cikin

"bakar safa, takula akwai shi da saka safa akafa sai kace wani marar lafiya,"

"""Yanda kake da abinyi haka nima nake dashi, nidai kawai ka datse igiyar auren nan kowa ya"

"huta..."""

"""Ban ganeba.... Wai kina nufin ni fahad na sakeki? Idan hakan kikeso zan yimiki amma abisa"

"sharadi guda daya..."""

Mikewa yayi daga kan bedside drewar yaje yatsaya mata aka dukkan hannahensa yasaka su cikin

"aljihu,"

"""Kifara sanar dasu Abba irin zaman da mukayi dake dafarko da irin gangancin da kika sakani nayi harna sakeki lokacin da wannan shedanin tsohon dan duniyar yake tsaka da hure miki kunne, sannan sai kisake fada musu abinda ke faruwa ayanzu idan har kikayi haka to wallahi zan yimiki"

"yadda kike so. """

"Sosai kalamansa suka bata haushi ta lura yanzu baida magana saita hamood magana daya sai ya jefo hamood aciki, takasa gane tsakanin shi da hamood waye yafi wani tsanar dan uwansa saboda shima hamood din lokacin da tana gidansa baida magana sai ta ya kira fahad da karamin yaron nan marar kunya, shi kuma fahad yanzu magana kadan zaice tsohon dan duniya,tana can duniyar"

"tunani har fahad yawuce yabar mata dakin yayi tafiyarshi kawai sai bude ido tayi taga baya nan,"

"Tagumi ta rafka tana tunani, ai ko giyar wake takesha bazata taba gigin aikata wannan abun da fahad yafada ba, ai idan ta kuskura abba yaji cewar itace ta kashe aurenta karo nafarko dan ta auri"

"hamood wallahi kashinta yabushe,"

"""Ai yanzu bakida mafita banda wacce tawuce kiyi hakuri ki zubawa sarautar Allah ido. """

"Zuciyarta tafada mata, shiru tayi kawai tana tunani, yanzu ita shikenan haka zatayi rayuwarta da yaro karami wanda baya ganin girmanta? Tunfa daga yanzu ya rainata to inaga wani abu ya hadasu ai sunanta sorry kawai, tsaki taja takoma ta kwanta tana istigfari acikin zuciyarta."

"Tun daga ranar har takarasa warwarewa takoma aiki fahad bai sake zuwa gidanba ita anata bangaren hakanma yafi mata kwanciyar hankali saboda baizo inda takeba bare yafada mata bakar maganar da zata hanata bacci kamar yadda yasaba, kokari ma take tayi tasamu ta yakice matsalarshi daga zuciyarta. Shi dinma yayi hakanne domin yabarta ta sarara kuma ta huta sannan"

"shima aiki yasakoshi gaba koda yaushe cikin aiki suke mutum baida lokacin kansa,"

"Ana saura kwana uku abbanta zai dawo daga tafiyar da yayi masu hayar gidan fahad suka tashi wato wadannan turawan da suka karbi gidanshi dama already sun gyara gidan sai dan gyare gyaren da baza arasa ba. Ranar laraba da daddare Abba yasauka wanda da tunima yajima da dawowa dan dai kawai yabiya ta wurinsu elmustapha ne yagansu, dawowarsa da kwana biyu"

fahad yarako babansu domin yiwa Abba sannu da zuwa dama awurin maama yake jin komai

"yanzunma itace tasanar dashi dawowar Abba,"

"Tunda fahad yagaida Abba yakoma gefe ya zauna yana saurarensu suna tattaunawa cikin fahimtar juna da mutuntawa, ahaka ammah tazo ta samesu suka gaisa ta fita, babu jimawa saiga Bilkisu itama tasha dogon hijabi har kasa,durkusawa tayi ta gaida baba sannan tamike zata fita, hada ido sukayi da fahad ta harareshi wannan karon bai ramaba amaimakon hakama sai yayi murmushi kawai, bayan fitarta ya maida hankalinsa kan maganar da su Abba sukeyi inda abban yake cewa tunda yadawo ai sai ayi maganar tarewar Bilkisu agidanta, dan haka idan har babu matsala nanda sati biyu sai ta tare agidanta nan baba yace babu kuma anyi abu akan gaba saboda dama mutanen da suke zaune agidan fahad din sun fita dan haka ko gobe ake son tariyar babu damuwa, anan dai aka bar zancen azuwan nanda sati biyu zata tare saboda abata dama ta gabatar da dan shirye"

shiryenta da take son gudanarwa.

"Fahad sun bar gidansu Bilkisu cikeda karramawa ga uban kayan tsaraba da Abba yabawa baba, washe gari fahad yasoma gyara gidansa gashi a lissafinsa bazaifi sati daya da tariyar ba zai koma"

"makaranta, haka dai yake ta kaiwa da kawowa danma yayunshi na taimaka masa."

"Bilkisu kuwa tun lokacin da abba yasanar da ita maganar tariyar nan take cikin kunci, kullum cikin fushi take hatta khulsum saida ta fahimta har saida ta tambayeta meke faruwa nan ta sanar da"

"ita wai

31 / 42