KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   3 / 42

6K to 9K   out of 124.3K words

bar shago ba sai bayan sallar magrib domin saida yagama yanka kayansu Bilkisu kaf sannan yanufi gida duk da irin tarin yunwa da gajiyar dake baibaye dashi, lokacin da yaje gida bai shiga cikiba dakinsu yafara shiga yayi wanka sannan yashiga cikin gidan, dukkansu suna falon mamu suna kallon wasan kwaikwayo na aku mai labari wanda ake gabatarwa agidan television din ART, daga bakin kofa yatsaya yagaidasu sannan yawuce dakin ayiyah duk da yanajiyo tsokanar da"

mamuh keyi masa bai kula ba domin yunwa yakeji dan rabonshi da abinci tun safe.

"Abincin dare yazuba yaci wato tuwon biskin masara miyar taushe yana ci yana santi har yagama yafito bai koma inda su ayiyah sukeba yafice ya nufi dakinsa, farar jallabiya yasaka yafita sallar isha'i domin daf ake da ashiga. Koda aka idar yadawo kwanciya yayi da niyyar runtsawa amma sam yakasa yin baccin sai juyi da yafara yi, fuskarta kawai yake gani wacce ke dauke da"

"murmushi tana yimasa magana,bashida zabi illa na yabi shawarar zuciyarsa ko zai samu sassauci."

*_Ummi A'isha_*

"11/28, 08:14] Hafsat Rano: © *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_"

*KAMAR DA WASA...!*??

_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*

*4*

"***Kasa nutsuwa yayi sakamakon dukan luguden da zuciyarsa keyi tamkar zata faso kirjinsa tafito waje dan tsananin zafin sonta, ahankali cikin sanyin jiki yatashi ya dauko wayarshi"

"wacce ke ajiye tana charge saboda akwai wutar nepa agari,"

"Komawa yayi ya kwanta ya lalubo contact dinta, _soul mate_ shine sunan da yasaka mata nan yakurawa number tata ido kamar wanda ke son haddaceta har zuwa tsawon wani lokaci, yanke shawarar tura mata da sakon karta kwana zuciyarsa tayi nan ya rubuta mata ya tura mata cikeda shaukin kaunarta har saida yaga sakon ya tafi sannan yaji ya dan samu nutsuwa, ajiye wayar yayi"

akusa dashi kamar wadda ake jira nan tasoma tsuwwa amma bai kulaba domin jikinsa yabashi

husnah ce wadda ba komai zata fada masaba illah ta kara masa damuwa dan haka yashare yaci

gaba da tunanin abar kaunarsa.

***

"Jikinta sanye da yar guntuwar karamar riga kalar ruwan madara wacce take marar nauyi da kauri tana tattara wani report da zata gabatar acikin laptop dinta taji shigowar sako, duk da bata dubaba saida tayi murmushi domin tasan bazai wuce hamood dintaba wanda ko mintuna biyar kwarara basuyi da gama wayaba, saida ta shanye sanyayyen lemon dake gabanta sannan ta janyo wayar bayan ta rufe laptop din. Kwanciya tayi tabude sakon, abin mamaki yabata saboda ganin wata number wadda bata hamood ba, cikin mamaki ta soma karantawa kamar haka, _Salam yake kyakkyawa,hakika kinyiwa zuciyata wani tarko mai wuyar Ketarewa, ganinki sau daya tal yana barazanar kawar da tunanina daga gangar jikina, wallahi ban taba ganin wata halitta wacce tayi daidai da ra'ayina kamarki ba, kece mace tafarko da nafara so tun kafin nayi ido biyu da ita, dan Allah karki ki k'i amsar soyayyata domin idan baki amintaba zan iya rasa rayuwata akan sonki,"

"wallahi ina mutukar sonki, ina sonki bilkisu._"

"Dora wayar tayi akan kirjinta gabanta yana faduwa sannu sannu, aranta tana tunanin to shikuma wannan waye shi? A ina yataba ganinta da har yaji yana sonta? Bata da amsa dan haka tayi watsi da tunanin batare da tabarshi yayi tasiri acikin zuciyarta ba. Addu'ar bacci tayi ta shafa tayi kwanciyarta bayan takashe wayarta, amma me koda gari yawaye tana kunna wayarta sakonshi ne yafara shigowa cikin wayarta inda yake yimata barka da safiya da wasu kalaman soyayya masu sanyaya zuciyar masoya, dan guntun tsaki taja ta ajiye wayar gefe ta kwanta batare da tabi takan"

mai turo sakon ba.

"Aranar ko aiki bataje ba domin sunata soye soye da dafe dafe kasancewar ranar za akawo lefen meenah, itace akan komai gashi gidan ba laifi yayi albarka domin yan uwa na kusa da makota duk anshigo domin karbar kayan, sai misalin karfe uku na yamma aka kawo kayan nan aka shiga tarbar baki da abubuwan da aka tanadar musu basu bar gidanba sai bayan da sukayi sallar la'asar sannan suka tafi nan kuma makota aketa shigowa ganin kaya wadanda suka kasance akwatuna hudu manya sai dan karamin kit na biyar kalar ruwan kasa ita kuma Hindu sai nanda kwana biyu za akawo nata. Ita dai bilkisu yau tunda tatashi kanta adaure yake domin maiyi mata sakon nan ba dainawa yayi ba sau hudu kenan yau yana turo mata sakonni masu dauke da kalaman so da kauna"

tun tana sharewa har ta zauna tana son sanin waye.

***

"Fahad yau tunda yafita shago baiyi aikin kowaba sai nasu bilkisu nata yawuni yana hadawa domin dinki na musamman yayi mata wanda babu irinshi ashagon kuma koda yagama hadawa bai barshi ashagon ba bare har aratayeshi a hangar wurin da suke rataye kayan da suka dinka, shi kansa ya yaba da dinkin da yayi mata shiyasa yake jin zuciyarshi wasai, Abu daya kawai yanzu yake bukata shine yaji muryarta amma yasan hakan ba mai yuyuwa bane. Wata numbershi wadda bai cika amfani da itaba yasa numberta yakirata amma harta tsinke ba adaga ba sai da yasake kira"

"sannan yaji ta dauka cikin sanyayyiyar muryarta wadda kamar tana bacci, sallama tayi amma sai"

yasamu kansa da kasa amsa mata domin wani irin faduwa gabanshi yasoma yi wanda bai san

"daliliba,"

"Sau uku tana fadin ""hello.... Hello. , hello"""

"Jin bai amsaba takatse wayarta, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sai lokacin yaji yasamu kwarin gwiwar yin abinda yake gabansa, tashi yayi ya tattara inasa inasa ya nufi gida lokacin misalin karfe biyar da wurin mintuna ishirin, yana zuwa gida kayan ball dinsa yasaka yafita batare da yashiga koda cikin gidanba acan yasamu ya ragewa kansa damuwa domin sai karfe 6 da wani abu yadawo. Wanka yayi yasha turare kamar wanda zaije zance yafita masallaci can yayi zamansa shida saleem har saida sukayi sallar isha'i sannan suka fito, wani sabon zaman suka sake dasawa akan dakalin simintin dake kofar gidansu saleem wanda wurin yake fuskar mutane ga hasken farin wata wanda ya hadu da hasken lantarkin dake kafe atsakiyar layin wanda ya ratsa ta cikin unguwar tun daga farkon layi har zuwa babban titi can gefe daya kuma yarane dankam masu soya awara"

nayi wasu kuma gyada suke saidawa da dafaffen kwai da sauransu.

"Daga kansa sama yayi yana kallon taurari wadanda suka karawa sararin samaniya ado da kawa,"

"cikin sanyin murya yafurta,"

"""Abokina am in love. """

Juyawa saleem yayi ya kalleshi yana murmushi sannan ga alamun mamaki nan bayyane akan

"fuskarshi,"

"""Yaushe? Kuma wacece?"""

"Lumshe idanuwa fahad yayi yana jin wata sabuwar soyayyarta tana shigarshi,"

"""Wata classic beb ce, kuma wallahi najima dauke da sonta"""

"""Kodai husnah ce?"""

Harararsa fahad yayi kasancewar akwai yalwataccen haske yasanya saleem ganin hararar hakan

"yasashi yin murmushi sannan yadafa kafadarshi,"

"""Bani labarinta abokinah..."""

"Saida yayi murmushin da shi kadai yasan dalilin yinsa sannan yafara fada masa,"

"""Nafara sonta ne tun ban gantaba, tun ranar da nafara jin muryarta a radio tana gabatar da wani shiri naji tashiga raina, kullum da ita nake kwana nake tashi, cikin ikon Allah sai gata jiya a shagonmu ta kawo min dinkunanta..... Amma bana jin zata soni"" Yakare maganar yana cizar lips"

"dinsa cikeda damuwa,"

"""Saboda me kake ganin bazata soka ba? Kanada wani mummunan haline wanda ban saniba?"""

"Saleem yafada yana fuskantarshi,"

"""Sam bahaka bane, saleem ta girmeni fa, jikina yana bani bazata yi accepting dinaba saboda zatace"

"nayi mata yaro dayawa may be ma zata ji kunyar nunani awurin friends dinta da relatives dinta"""

"Dariya saleem yayi yana dafashi,"

"""To kai da waye ya aikeka son wacce ba sa'arka ba?"""

"""Saleem kenan, shi so ba ruwansa da cancanta,shekaru ko duba matsayi, kawai yakan shigane aduk sa'ilin da yaso koda kuwa ba ashiryawa hakanba, saleem wallahi dagaske ina sonta, ni"

"girmemin din da tayi ba damuwa bace zan iya rayuwa da ita mutukar zata yarda ta aureni"""

"Shiru saleem yayi yana kallonsa, ganin yanda yanayin idonshi ya sauya zuwa ja yasashi gasgata"

"aminin nashi,"

"""Abokina ka kwantar da hankalinka, ina kyautata zaton koma wacece zata soka itama domin baka da makusa kuma bakada wani hali ko dabi'a wadda bata kirkiba, kana da zuciyar neman na kanka"

"sannan kana da kyakkyawar mu'amula da kowa, kayi addu'a abokina insha Allah zaka dace"""

"Kalaman saleem sune suka sanyayar mishi da zuciya sannan yasashi jin nutsuwa ta saukar masa, cigaba da kwantar masa da hankali saleem yayi har saida yaji acikin ransa zai samu bilkisu, cikeda"

"farin ciki suka rabu da saleem yana tsokanarsa,"

"""To kai ka isa aurenne?"""

"Girarshi guda daya ya dage masa yana kallonsa cikeda mamaki,"

"""Nine ban isa aureba? Kabari abani matar a lokacin zaka fahimci na isa ko ban isaba"""

Daga haka yamike yakama hanyar gida yana jin saleem har lokacin yana tsokanarsa amma bai

tsayaba.....

© _*HASKE WRITERS ASSO.*_ _(Home of expert & perfect writers)_

*KAMAR DA WASA !*

"***Hannayensa gaba daya ya aza cikin aljihun wandon bakin jeans din dake jikinsa, jar rigace ajikinsa mai rubutu kamar haka, _All the best_,yana tafe yana kallon dukkan jama'ar da kowa hada hadarsa yakeyi, wayarshi ya zaro daga cikin aljihun wandonshi domin duba ko waye"

"ke kiransa sunan Nazifi yagani abokin aikinshi domin shagonsu daya, yana dagawa yaji yace,"

"""Prince ga wasu sun kawo dinki wai nanda next week suke so"""

"""Gaskiya bazasu samuba dunkuna sunyi min yawa"""

"""Hakane but amma naga ka karbi na wasu jiya ai"""

"""Ehh hakane amma ai kadai fi kowa sanin yawan dinkunan dake zaman jirana ko"""

"""Babu damuwa bari nakira hamza naji"""

"Katse wayar fahad yayi aransa yana cewa ""yadai fi domin ita wadda kaga jiyan na karbi nata"

"daban take bazan iya bari wani yayi mata ba shiyasa"""

"Ahaka yakarasa gida direct cikin gidan yawuce domin cin tuwo baba yahango kofar dakin mamuh yana magana dasu maryam wanda baya iya jiyo mai yake fada,durkusawa yayi kasa yagaida shi sannan yawuce dakin ayiyah yana dallawa Mariya harara saboda laifin da tayi masa da sassafe tun kafin tatafi makaranta, zaune ya iske ayiyah tana damawa baba fura acikin kwanon sha na silver"

"da ludai ga sukari agefe cikin wani kofi madaidaici, zama yayi gefenta yana fadin,"

"""Ayiyah kamar kuwa kin san yunwa nake ji"""

"""To ai ga tuwon tsari nan miyar kubewa da mamanku tayi sai ka saka kaci idan kaci sai kasha"

"fura"""

"""Ai kibar tuwon nan kawai ayiyah iya furar kadai zansha"""

"Kafin tayi magana baba yayi sallama yashigo, matsawa fahad yayi yabashi wuri ya zauna kan"

"lallausar dardumar dake shimfide awurin,"

"""Muhammadu wai yaushe dan uwanka zai bullo ne?"""

"Murmushi fahad yayi domin yagane Abba yayansa baba yake nufi, gyara zamansa yayi yana"

"daukar cup din furar da ayiyah ta zuba masa,"

"""Dazu munyi video call dashi baba yace insha Allah cikin karshen satin nan zaizo gida"""

"""To Allah yakawo shi lafiya muna zuba ido, ai saika yanke masa wadancan barun naka ko ko kaji"

"ayi masa sauka"""

Murmushi yayi bayan yazare cup din dake bakinsa ya hadiye furar da ya kurba.

"""A'a baba,zan dai siyo masa akasuwa sai ayiya ta dafe masa su amma wadancan na kiwone bana ci"

"ba"""

"Ayiyah tana mikawa baba furar da ta dama masa ta daga kai ta kalli fahad,"

"""Ni ban taba ganin irin wannan kiwon ba sai awurinka ayita kiwata abubuwa amma baza aciba..."""

"""A'a ai kedai babu ruwanki, barni dashi"" Inji baba,"

"Murmushi fahad yayi yakarasa shanye furar da yake sha,"

"""Baba ayi min hakuri dai har sai sun kara yawa"""

"""Ni ai bance komaiba muhammadu, Allah yasa albarka"""

"""Amin babanmu"""

"Daga haka yatashi yafita,sai da ya leka dakin mamuh ya rarrankwashi mariya sannan yafito yana kunkunin idan tasake zuwa sassafe ta buga masa kofa yana bacci sai ya lakada mata duka. Dakinsa yawace ya rage kayan jikinsa sannan ya kwanta yana nazarin rayuwa, ganin tunanin nasa yana neman yin zurfi yasashi katseshi ta hanyar daukar wayarsa ya fada yanar gizo yana duba labaran"

abubuwan dake faruwa aduniya.

Har karfe goma saura yana haka zuwa can yatuna da bai turawa rabin ransa good night massage ba

dan haka yayi hanzarin tura mata yana lumshe idanu kamar tana kallonshi.

***

"Abangaren bilkisu ganin takasa gano wanda yake turo mata da massages dinnan sai tunaninta yabata cewar ya mudan ne cousin dinta wanda sam jininta bai hadu da nasa ba, wani tsaki taja bayan tagama karanta massage din da yashigo yanzu wanda take sa ran nashine, duk ji tayi kunci ya rufeta har saida takira hamood sukayi hira sannan taji damuwa da bacin ran dake tattare da ita"

sun kau.

Washe gari bayan tataso daga aiki kamar ta biya ta shagon su fahad sai dai tafasa saboda tasan su ammah na can gida suna jiranta saboda gobe za akawo lefen Hindu shiyasa suketa shirye shirye domin bata son lokaci yakure ba ashirya komai ba kuma tasan baza ayi komaiba agidan har sai

anjira zuwanta.

***

Shi kuwa fahad yau tunda yafito shago suke tare da husna duk da ba wai yana son zaman nata bane domin kallo daya zaka yimasa ka fahimci haka sakamakon fuskarsa dake hade babu alamun fara'a ita kuwa husna duk inda yayi sai binsa take da kallon so cikeda burgewa domin sosai yau

"yayi mata kyau,"

Yana dinka kayansu Hindu sai labari take bashi na garinsu shi dai kawai jinta yake amma bawai

yana son labarin bane.

"Yan shagon nasu kuwa kowa sai kallonsu yake yana yiwa fahad dariya kasa kasa,ganin bata da niyyar tafiya shi kuma ta takura masa yasashi fitowa fili yace taje ta tafi da yamma saita dawo, ai tana tafiya babu jimawa yagama abinda zaiyi yabar shagon, shagon su saleem yaje acan suka sha hirarsu wadda kusan rabi ta Bilkisu ce da take can bata san yana yiba. Saida sukayi sallar la'asar sannan suka nufi gida, koda yaje gida abinci kadai yaci daga nan ya kwanta baccin nasa na sabo nan yayishi har na tsawon rabin awa, karfe biyar da wani abu yafarka yayi wanka yafita filin ball duk da yau baya sha'awar buga kwallon amma yana son ya zauna ya kalli masu bugawar, ear piece yasaka acikin kunnenshi yafita yana sauraron wakar fall in love, kamshin oad kawai yake zubawa da haka ya isa filin kwallon yakama katanga yahau ya zauna yabi sahun wadanda ke zaune suna kallo, wayarshi ya ciro yayi dialing number din Bilkisu domin amatse yake da jin muryarta lokacin da ya kirata tana tsakiyar hayaniyar jama'a domin yan kawo lefen basu tafiba suna dai niyyar tafiya matsawa gefe tayi tai sallama cikin muryarta mai mutukar zaki wadda ta saukar masa da kasala mai nauyi cikin sanyin murya ya amsa bayan ya lumshe matsakaitan idanuwanshi"

"sannan yabude su akan masu buga kwallo,"

"""Mai gado i really loves u. """

"Jin abinda yace yabata mamaki duk da bata fahimci wayeba amma tagane itace number din da aketa damunta da turo mata massages dinnan, yanzu kam tagama yarda cewar ba yaya mudan"

bane wani ne daban wanda bata saniba.

"""Uhmmm.kefa? Kina sona?"""

"Jin abinda yace ta dan nisa kadan sannan tace,"

"""Yanzu ina cikin wani uzurine amma idan anjima zan kiraka"""

Kitt ta katse wayar takoma taci gaba da abubuwan dake gabanta yayinda shikuma tabarshi da

faduwar gaba domin bugawa kirjinsa yashiga yi da sauri da sauri......

*_Ummi Shatu_*

© _*HASKE WRITERS ASSO*_

*KAMAR DA WASA !*

_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*

*6*

"***Bilkisu bata samu kanta ba sai dare bayan sallar isha domin har karfe 9 saura na dare mutane basu bar shigowa kallon kayan ba, sai tara da wani abu ta samu tayi wanka tayi shirin bacci domin a mutukar gajiye take jinta yau tsabar busy din da ta shiga sau daya kawai sukayi waya da hamood, yanzunma bata jin zata iya kiranshi shiyasa kawai ta kwanta taja bargo. Tafara"

"bacci sama sama taji karar wayarta,idonta cikeda bacci ta kara wayar a kunnenta,"

"""Love Bacci kikeyi?"""

Jin muryar da bata saniba yasata katse wayar tareda kasheta gaba daya domin bacci take so tayi. Wurin sau biyar fahad yana gwada kiranta sai yaji akashe daga karshe dole sai hakura yayi shima

ya kwanta din yana tunata acikin ransa.

"Washe gari misalin karfe 10 nasafe ta sauka agaban shagonsu ita kadai domin ta baro khulsum a office tana fassara labaran turanci zuwa hausa itama kawai bikin nan

3 / 42