KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   34 / 42

99K to 102K   out of 124.3K words

tafi sannan ta sauka itama tatafi. Bilkisu kam wani irin bakin ciki takeji wanda batasan dalili ba, ganin da tayiwa su fahad manne da juna yaki ya bace daga cikin idanuwanta da zuciyarta gaba daya, ji take kamar ta shakeshi tayita"

"dukansa ko zata huce, har sukaje gida bataji bacin ranta ya ragu ba,"

"""Kenan Allah kadai yasan abinda sukeyi idan su biyune kadai "" Tafada acikin zuciyarta saboda"

"yanzuma sukayi haka agabanta inaga su biyune kacal ashagon, tsaki taja tasake ja akaro nabiyu"

"tana kokarin rage kayan jikinta, falo tafita ta hado tea tazauna tana sha sai faman jan tsaki takeyi saboda bacin rai,"

"Duk tsakin da take ja fahad na jinta amma bai yi maganaba kuma yasan dashi take,"

"""Ita ta dazun da kaketa hada jiki da ita, ita kuma wacece?"""

"Yaji tafada cikin murya mai dauke da fushi,"

"""Husnah ce fa matar da zan aura, har sadakina yana gidansu..."""

"Banza tayi dashi saboda ita ba wannan ta tambayeshi ba, wani tsakin takuma ja sai yanzu tagane"

"dalilin yarinyar na kin yimata magana dan ko sallamarta bata amsaba tana ankare da ita,"

"""Mtswwww wato kishi kenan zatayi dani? Ni ai ba sa'ar kishinta bace..."" Tafada cikin fushi sannan ta dangwarar da cup din hannunta ta mike tawuce cikin daki taje ta kwanta saboda taji ciwon kanta yafara tsananta. Har yaci weekend dinshi yakoma bata dawo daidai ba koda yaushe cikin fushi take,shidai tunda yasamu yakoma school bai waiwayo gidaba sai after 2 weeks. Ranar da yadawo da daddare yaje gidan anty asabe ya debo lefen Bilkisu yakawo mata, tana kwance adaki tana aiki acikin system dinta, zama yayi agefen gadon yana kallonta itama kallonshi takeyi tun lokacin da"

"yafara shigowa da kayan har lokacin da ya kammala yazauna dan nesa da ita kadan,"

"""Bilkisu ga wannan. Kayanki ne"""

"Kallonshi tayi ta kalli kayan,"

"""Kayan menene? Kayan fadar kishiya ne ko me?"""

"""A'a ba kayan fadar kishiya bane, kayan lefenki ne, ai kinga lokacin da mukayi aure banyi miki"

"ba..."""

"""Ehh hakane..."" Tafada tana jin zuciyarta na wani irin tafarfasa, itafa gaba daya haka kawai take jin haushin auren da zaiyi batare da wani daliliba,ganin bazatace komai ba yasashi tashi yafita, harga Allah da yace mata kayan fadar kishiyane babu abinda zai sata karba amma tunda yace mata"

"lefantane shikenan, tashi tayi da kanta ta jera akwatunan gefen wardrobe dinta."

"Tunda biki ya karato fahad yazama busy Bilkisu kawai kallonshi take tana jin mugun haushinsa musamman ma ranar da yazo mata da maganar wai ta gyara kayanta na falo tasasu a side daya saboda itama husnah tasamu wurin saka nata duk inda yabi da harara take rakashi, babu abinda ya shalleta da aurenshi sha'anin gabanta kawai takeyi da fita aikinta acan take rage tunani da damuwa wadda bata san musabbabinta ba, duk cikin yan uwanta da gidansu babu wanda ta fadawa saboda aganinta wannan ai be abinda zata zauna tana fada bane, ko khulsum saida tafara ganota sannan ta"

"sanar da ita wai fahad ne zaiyi aure,"

"""Yanzu ke mijinki zaiyi aure amma kike zaune ahaka? Shine bazaki tashi ki gyara kanki ba..."""

"""Khulsum nifa banida lokacin su wallahi, basune agabana ba suje can su karata..."""

"Cikeda jin haushi khulsum ta kalleta tana harararta,"

"""Maza dai kibari kiyi saken da zaki dade kina cizon yatsa bare gashi kince karamar yarinya zai"

"auro..., wallahi ina tausaya miki mutukar baki zage dantse ba kina ji kina gani zata kwaceshi """

"""Ni dama ban rikeshi ba ai, taje ta kwadashi ta cinye..."""

"""Hmmmmm labour kenan, kina son guy dinnan fa kawai kin kasa ganewa ne saboda zafin kishin"

"dake damunki da shegen son girman tsiya. """

"""Ni kar kiyi min sharri malama. , kinga tafiyata sai gobe"""

"Bata jira cewar khulsum ba ta yi tafiyarta,tana zuwa gida ta tarar anfitar da kayanta duka waje an fente gidan da sabon fenti 2 colours wanda zai shiga da kowanne kalar furnitures, duk sai kuma takara jin babu dadi damma dai falon yanada girma sosai haka bedrooms dinma sannan ba lallai wanda ke daya dakin yajiyo motsin wanda ke cikin dayan ba wannan shine saukinta iya falo da"

"kitchen da store kawai zasuyi shearing, da damuwa makale saman fuskarta tayi wanka tashirya"

"sannan ta dora girki, dan wake tayi tana tsamewa daga cikin tukunya fahad yashigo,sanye yake da kananan kaya yaje ya amso kayansa wadanda zaisa ranar daurin aure da ranar dinner, kitchen din yabita dan ganin me takeyi ganin dan wakene yasashi zubawa acikin flate yawuce bedroom dinta yazauna yaci acan, har yaci yagama yafita maganarsu batafi guda uku ba, shiyasa lokuta da dama yakance Bilkisu miskila ce koda acikin ranshi ne domin tanada wani murdadden hali mai wuyar fahimta cikin sauki. Tunda aka fara hidimar bikin nan ta tsame kanta daga sabgar kowa su maama ma da sukace mata zasuje bikin hanasu tayi tace indai saboda ita zasuje to suyi zamansu, daren ranar abba yakirata yayiyyi mata nasiha sannan yace me take bukata yanzu na gyaran daki ko falo ko na kayan kitchen tace babu komai saboda itama gaba daya kayanta sabbine fil babu abinda take bukata kuma kitchen dinta cike yake da kayan amfani duk da haka saida Abba yasaka mata kudi cikin account dinta. Tun ana saura kwana biyu masu jeren husnah suzo fahad yacewa Bilkisu ta matsar da kayanta na kitchen tasaka a side daya hakama na falo amma duk tayi mirsisi da yayi magana kuma tafara yimasa masifa bai kulataba saboda ya fuskanci kwana biyun nan fada takeji shi kuma yanzu ba wannan ne agabanshi ma in fact ma bayaso husnah tazo ta iakesu cikin wannan halin, bayan yafita daga gidan maama yakira yafada mata abinda ke faruwa yace da Bilkisu ta gyara kayanta ta mayar side daya amma taki, washe gari saiga maama shiyasa ranar ko aiki Bilkisu bata jeba sake kuluwa tayi lokacin da taji dalilin zuwan maama wai dan kawai ta tayata gyara kayanta abarwa husnah space shikenan tahau fada kamar dama jira take ita dai maama bata kula ba itace ta zage ta gyara kitchen din ta sakawa Bilkisu nata abangaren dama ta barwa husna daya ban garen, falo ma haka tayi ta jerawa Bilkisu kujerunta suna kallon dakinta ta raba falon biyu,har dare suna tare da maama saida ta gama komai sannan tatafi, ita dai Bilkisu sai kunkuni"

take tana cewa fahad zai san ita yakai kara wurin kanwarta.

"Washe gari yan jere sukazo ita dai tayi tafiyarta office shiyasa kafin ma tadawo har sun gama sun tafi ranta ne yabaci saboda ganin yanda falon ya matse babu space sosai, kayan husnah dukka milk colour ne tun daga kujeru har su cuttens da sauransu, dakinta kawai tawuce kai tsaye taje ta zauna"

"tanata zancen zuci cikin bacin rai,"

"""Haka kawai za awani zo atakura min. mtswwww"""

"Sam bata son fita falo saboda bata kaunar ganin kayan husnah, bakin cikin ganin wadannan kayan shine yahanata bacci adaren yau, shi kuwa gogan tana jinsa sai kaiwa da kawowa yakeyi shi alalle ango, rashin baccin da bata yiba shine ya haifar mata da matsanancin ciwon kai da safe dan dashi ma ta tashi, jin tace bata da lafiya yasa fahad kawo mata magani amma taki sha saboda haushinsa takeji bata san daliliba gashi tsabar wulakanci tunda yafita daga gidan bai dawo ba har yamma,tambayar kanta tashiga yi kenan nuna mata yake son yi bai damu da lafiyarta ba? Ko kuwa so yake yanuna mata wulakancinsu na maza alokacin da giyar aure ke dibar su? Da wannan takaicin ta wuni zuwa yamma tasamu ta tashi tayi wanka ta shirya, kitchen tashiga dan samarwa cikinta abinda zata saka masa tana yi tana mita saboda ada gaba daya kitchen dinnan natane sai inda takeso zata ajiye abu amma yanzu aikin banza anwani zo an kakaba kayan wata aciki, indomie ta dafa ta soya kwai guda biyu takoma falo tana hararar kayan husnah tasamu wuri tazauna, saida tagama cin abincinta tayi salla sai ga khulsum, tsayawa khulsum tayi tana karewa"

"falon kallo hannunta kan habarta,"

"""Tirkashi...hajji fahad dai yadage sai yayi mana kishiya. Har anzo anzuba jere?"""

"Ita dai bilkisu tana jinta batace komai ba ita kuwa khulsum saida taje ta leka ko ina har bedroom da kitchen duk saida ta duba sannan tazo ta nemi wuri ta zauna tana bawa Bilkisu shawarwari, bayan tafiyar khulsum kawai jin hawaye tayi wadanda bata san dalilin zubowarsu ba, gaba daya tayi sanyi kalau tayi sukuku da ita, shi kuwa uban gayyar taga kamar adokance yake da wannan auren saboda ko zama baya samu yanzu idan yafita tun safe baya dawowa sai dare ita dai tasan wannan bai dameta ba amma kawai bata cikin walwala da farin ciki,yan gidansu kuwa da sukace mata zasuzo tayata zama kin yarda tayi amma duk da haka saida suka zo, ana igobe daurin aure har gida su ayiyah sukazo suka yi mata nasiha akan tayi hakuri sannan kuma azauna lafiya idan husnah tazo ta riketa kamar kanwarta, ita dama tasan su ayiyah na sonta bata da case dasu. Washe gari takama ranar daurin auren husnah da fahad sai Abba da nusaiba kanwarsu salim amma shi fahad nashi auren a Kaduna za adauroshi gidan da ake rikon husnah, Bilkisu na can dakinta tana aikin da babu gaira babu dalili dan kawai ta debewa kanta kewa tarage damuwar dake ranta wacce bata san ko ta mecece ba fahad yashigo cikin shirinsa tsaf na tafiya daurin aure, farar shadda mai"

"tsada yasaka sai jar hula da farin takalmi wato dai kwankwasiyya atakaice sai zuba kamshi yakeyi,"

"""Ranki yadade ni nafito, sai Allah yadawo dani... Insha Allah tare da amarya zamu taho..."""

Banza tayi dashi saboda aganinta wannan ma ai rainin wayo ne wato saima yanzu zai sakaya

"sunanta da yake maganar aurenshi zai fada mata,"

"""Mai gado bakiji ni bane. ?"" Yafada yana tsuke fuska,"

"""Idan najika me zanyi maka? Ko daukarka zanyi akaina inkaika har wurin daurin auren?"" Tafada"

"cikin masifa,"

"""A'a nidai yau ba ranar fada bace ranar farin cikina ce ranar da bazan manta da ita ba, ki nemi"

"abokin fadanki amma ba Muhammad fahad ba. """

"Daga haka yajuya yafita hakanne yasake kular da ita har taji kwalla tafara zubo mata, wurin karfe"

"10:30 khulsum tazo lokacin tagama kukanta amma idanuwanta jajur suke,"

"""Labour kuka kikayi ko? Haba ke kuwa sai kace karamar yarinya?"" Khulsum tafada tana kallonta,"

"""Hmm khulsum ba zaki gane bane yaron nan ya iya bakar magana kamar rainon gwauro..."" Tafada"

"acikin ranta amma afili sai tacewa khulsum,"

"""Nifa babu kukan da nayi uwar son jin tsurku.... Zaki fara sa idon naki da kika saba..."""

"""Allah ya shiryeki kawata, kina wahalar da zuciyarki wallahi Tab inama nice fahad"""

"""Da kece me zakiyi?"" Bilkisu ta tambayeta tana harararta,"

"""Da Allah kadai yasani """

"""Kya dai ji dashi"""

"""Allah dai yabar kawata uwar gida agidan fahad wallahi ko amarya tazo kece star "" Khulsum ta"

"fada tana rangada guda, tun Bilkisu bata biyeta har ta biye mata suka yita yarawa zuwa can saiga meenah da maama amma banda Hindu wai bata jin dadi kuma da yake cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe, sune suka raya mata gidan har tasamu damar manta damuwarta. Har dare suna gidan dan acewarsu sai ankawo amarya akan idonsu hakan kuwa akayi bayan sallar magrib sai ga yan kawo amarya damma sun tsaya agidansu fahad anyi budar kai amma tun yamma suka iso, duk da su maama suna taya Bilkisu kishi amma hakan bai hanasu tarbar yan kawo amarya da fara'a ba, ita dai Bilkisu tana daki ita da meenah, tana ji yan kawo amaryar wasu daga cikinsu na cewa su dai baza suje dinner ba sun gaji, tabe baki tayi tabi lafiyar gado ta kwanta, fahad kuwa tun safe lokacin da yayi mata sallama yafita bata kara sakashi cikin idanuwanta ba, shikam yana can gidansu dakinsu na da shida ya abba tun bayan dawowarsu daga Kaduna yake cikin ruguntsumi bai samu kansa ba yanzu ma haka shirin tafiya dinner suke yi shida abokansa dan hatta su mukhtar"

duk sun zazzo suna dakin salim ansaukesu acan.

"Bilkisu na kwance tana jin hayaniyar dake tashi ta yan kawo amarya ga kawayen amarya sai ihu da shewa sukeyi bata samu taji gariba har saida suka tafi dinner dinnan nan su khulsum suma sukayi mata sallama suka tafi da sauran yan uwan su fahad, bayan kowa yatafi amma tana jiyo yar hayaniya adakin husna ta shiga wanka tayi shirin bacci ta kwanta duk da tasan yaudarar kanta kawai takeyi dan ba yi zatayi awannan lokacin ba, 12 saura aka dawo daga dinner din nan sabuwar hayaniya ta tashi hakan yasake kona mata rai bayan kamar mintuna talatin taji karar tashin motoci zuwa can kuma taji tsitt alamun kowa ya tafi, ita dai tana kwance daga inda take bata ko motsa ba, 12 da wani abu taji motsin shigowar fahad, kai tsaye dakinta yafara shiga yana rike da leda a hannunshi na dama hannunshi na hagun kuma yana rike da wayarshi da babbar rigarshi, kai daga gani kasan a mutukar gajiye yake domin hakan ya bayyana akan fuskarshi karara, langabe kai yayi"

"yana kallonta cikin shagwaba yace,"

"""Shine ko nemana ma ba ayi?. """

"Wata harara ta dalla masa amma sai yayi murmushi, ya karasa gaban gadonta ya ajiye mata ledar,"

"kallonshi tayi afakaice yana sanye da dark purple din shadda dinkin half jamfa da hula babbar rigar kuma na rike hannunshi,"

"""Ga kayan kwalam da makulashenki..."""

"""Bana so ka kaiwa amaryarka. """

"""Karki damu tare na siyo muku nata yana falo, yanzu zanje na kai mata. """

"Bata tanka ba ta dauke kanta taja duvet ta dan jiyo kadan ta kalleshi,"

"""Zanyi bacci dan kashe min hasken idan zaka fita..."""

"Murmushi yayi maimakon yafita saima ya zauna kan stool din dake gaban mirror,"

"""Basai fa kin koreni ba zan tafi, bari na dan huta..."""

"Bata kulashiba taja duvet ta rufe har kanta tana sauraron ajiyar zuciyar da yake saukewa ahankali zuwa can kamar bayan mintuna 15 taji yatashi yakashe mata wutar yafita, tofah kamar amafarki sai taji kuka ya subuce mata wanda bata san musabbabinsa ba,ni kaina Ummi A'isha so nake naji"

dalilin kukan Bilkisu........

"_jiya yar dakina asked me wai sis ummy wacce irin kamace da yan Jami'a? I laugh over and over and over again then nace mata, yan gayu masu class kuma wayayyu saboda seriously duk wadda tayi jami'a zaki sameta komai nata is different tun daga mu'amalarta da mutane and so on, hatta a dressing dinta ma wallahi zaki fuskanci mai class ce babu baragada da yawan hayaniya shiyasa kukaji na siffanta husnah da haka, da nace kana ganinta zaka gane yar Jami'a ce what i mean is da zarar ka ganta kaga mace mai class kuma abar burgewa, and da nace tayi hudar kunne guda uku bawai fa ina nufin hakan baida kyau ba a'a kawai inaso innuna irin ta kure kwalliya da gayu mai yawa so dan Allah kar ayi min mummunar fahimta wallahi duk abinda nafada da kyakkyawar"

"niyya nafada, tnx for ur love and support._"

*_Ummi Shatu_*

*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

"50***Kuka take yi harda shessheka gaba daya ta jike pillow din da take kai, ga wani matsanancin ciwon kai wanda yafara damunta har tsawon karfe daya da kusan rabi takai tana wannan kukan, Dai dai wannan lokaci shi kuma fahad na can tare da husna, lokacin da yashiga kishingide ya isketa ta dan fara bacci, tashinta yayi ta hanyar kama yan kafarta wadanda sukasha jan lalle da"

"baki yana jansu ahankali, bude ido tayi tana kallonshi cikeda gajiya da tarin bacci,"

"""Ya fahad... Sai yanzu kadawo?"""

"""Wai har kin fara bacci asma'u? Oya tashi kici abinci sai ki kwanta..."""

"Yafada yana janyo hannunta, kafada ta noke tamaida kanta ta kwantar saman pillow,"

"""Ni bana jin yunwa, kaci kayanka..."""

"Murmushi yayi ya matsa jikinta, ahankali yace,"

"""Ko kema kina jin tsorone?"""

"""Name?"" Tafada tana bata rai,"

"""Kar kici min kazata kuma nace sai kin biyani !"""

Daga shi har ita dariya ce ta subuce musu ta harareshi sannan ta gyara kwanciyarta izuwa

"rigingine,"

"""U kid yourself sweetheart Good news da zan baka yanzu shine am off, soo allow me to sleep"

"pls. """

"Murmushi yayi yana shafar lallen hannunta,"

"""To kinga dadinma zagewa kici kaza kenan tunda ba biyana zakiyi ba, wake up pls"""

"Girgiza kai tayi tana lumshe idanuwanta,"

"""Na koshi wallahi, sai da safe zanci """

"""Ok, sleep tight my love, good night """

"Bata amsaba ta gyara kwanciyarta ta hanyar juyawa daya bangaren, shikam yunwa yakeji sosai saboda yau da yunwa yawuni throughout shiyasa ya zauna yaci rabin kaza yasha madara, tashi yayi yashiga bathroom yayi wanka

34 / 42