KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   40 / 42

117K to 120K   out of 124.3K words

nace yayi test sai cemin yayi wai yayi shi"

"bashida matsalar genotype da sauran cutukan zamani dake hana aure..."""

"""To yanzu shi fahad din yasani? Ina nufin yasan matar tasa tanada HIV?"""

"""Wallahi baba yasani, da saninsa kawai boye muku yayi dan karku hanashi zama da ita, kuma"

"kowa yasan mijinta nada shima yanada HIV din amma ahaka ya fahad yace wai sai ya zauna da ita"""

"Shiru dukkaninsu sukayi na wucin gadi shi baba ma gaba daya yarasa abinda zaice sai hada zufa yakeyi lallai kuwa idan hakane fahad kuruciya na yawo dashi, waye yafada masa ana irin wannan"

makauniyar soyayyar akashe kai?

"Su mamuh kuwa har yanzu basu daina salati da sallallami ba, kallon husnah baba yayi sannan"

"yace,"

"""Asma'u abinda nakeso dake kitashi kitafi gidanki kije ki zauna, shikuma zan kirashi zaizo, idan"

"yazo zamu san matakin da zamu dauka"""

"Sunkuyar dakai tayi cikeda ladabin karya tace,"

"""To shikenan baba. Nagode Allah yakara girma"""

"Sallama tayi dasu mamuh suna cemata ta tsaya tatafi da tuwon biski tace a'a bata iya ciba, cikin"

jimami tatafi tabarsu kowa yayi shiru suna tunanin mafita.

Bilkisu na falo sanye da doguwar riga yar kanti tana kallo husnah tashigo tawani dauke kanta bata

"kalli inda bilkisu takeba tawuce daki jimm kadan tafito tashiga kitchen tana cewa,"

"""Su tsohuwar guzuma dai ankusa abar gidan da aketa tunkaho dashi ana huhhura hanci Ashe"

"ana makale da kabari salamu alaikum """

"Ita Bilkisu sam bata gane abinda husnah ke nufi ba shiyasa da taji hayaniyarta na neman damunta tatashi takoma daki ta kwanta taci gaba da kallonta, lokacin kwanciya nayi tai azamar kashe wayarta saboda bata son nacin fahad. Ranar juma'a da yamma saiga fahad yadawo mamaki abin yabawa Bilkisu saboda shi da yayita cewa sai sun nemeshi kafin su ganshi amma shine yakasa hakuri yadawo? Hamdala tarinka yiwa Allah da ba adakinta yake ba yana dakin husnah dan haka suje can su karaci fitinarsu, shi kuma lokacin da yaga Bilkisu mamakin yar kibar da yaga tayi yarinka yi sai taba mata kumatu yake wadanda suka fara luhu luhu gashi ba laifi komai na jikinta ya sake dan bunkasa,wani zumudi yafara yi na son sake kasancewa da ita kawai yana son yasamu dama ne amma ahalin yanzu babu dan ranar husnah ce shiyasa yana fita Bilkisu tatashi tarufe dakinta tayi kwanciyarta. A bangaren husnah kuwa ko da wasa bata nunawa fahad ga abinda wai taje ta shirya ba lafiya lafiya suka kwana amma da safe tun kafin yatashi daga bacci baba yakirashi awaya yace anjima kadan yana son ganinshi shida su bilkisu, tunanin duniya fahad yayishi wai ko zai samu yagano dalilin da yasa baba ke nemansu amma sai yakasa, juyawa yayi yakalli husnah yafada mata cewar ta shirya anjima zasuje gida baba na son ganinsu daga nan yamike yafita, dakin Bilkisu yashiga har lokacin ita bata tashi daga bacci ba tana tunkunkune cikin bargo, zama yayi"

"gefenta yaja kumatunta nan tabude ido ta kalleshi,"

"""Kitashi ki shirya zamuje gida baba na kiranmu..."""

"Gabanta taji yafadi,"

"""Lafiya?"""

"""Ehh to lafiyar kenan dai """

"""Allah yasa..."""

"Sake jan kumatunta yayi sannan yatashi yafita, tashi itama tayi tashiga wanka."

"K'arfe 8 nasafe suka gama shirunsu tsaf a niyyar fahad yasamo musu napep su tafi gaba daya amma sai husnah tace ita kawai suje a machine din fahad inyaso sai tahau napep, wannan dalilinne yasa tafiyar tasu ta bambanta kafin suje tuni husnah taje tasake tsara karya da gaskiya harda su kukanta wai fahad baya adalci yafi son Bilkisu kuma itace take bashi umarni komai sai abinda tace shi zaiyi yanzu ma adakinta yake amma maimakon yasamo musu napep su taho gaba daya sai yaki yace wai Bilkisu zai dauko ita kuma taje tahau napep, kowa dake zaune wurin abin baiyi masa dadiba nan baba yashiga bata hakuri, tana nan zaune tagama kukan munafurcinta sai gasu fahad, su mariya najin Bilkisu suka fito sukaje da gudu suka rungumeta abin yasake baiwa husnah"

"haushi,duk da tahada karya da gaskiya tafada hakan bai hana su ayiyah yiwa Bilkisu kyakkyawar"

"tarba ba. Saida aka gama gaisawa sannan baba yacewa fahad,"

"""Fahad meyasa baka adalci tsakanin matanka? Haka ake zaman aure ko mu haka kataso kaga"

"munayi a wannan gidan?"""

"""Baba menayi?"""

"""Asma'u maimaita abinda kika zo kika fada mana. """

"""Baba tsoronta yakeyi sai abinda tace masa yakeyi, kuma ma ashe tsohon mijinta yanada HIV amma ahaka ya fahad ya aureta shiyasa lokacin bukinmu da nace muje muyi test yaki zuwa yace"

"wai yayi anan. """

"Hangame baki fahad yayi cikeda mamaki ita kuwa Bilkisu har tafara halin nata na saurin kuka,"

"""Bilkisu abinda tafada gaskiya ne wai tsohon mijinki nada HIV"""

"""Ehh gaskiyane baba..."" Bilkisu tafada cikin kuka, kafin baba yayi magana fahad yace,"

"""Amma baba ai ita bata da ita.... Wallahi kawai tada zaune tsaye ne irin na husnah. """

"""Ba tada zaune tsaye bane gaskiyane nidai kawai aje ayi test dan kaima kila kana da ita"" husnah"

"tafada tana hararar fahad,"

"""Ya isa, kai fahad katashi ka debesu gaba daya kuje kuyi test inyaso abinda duk sakamako yanuna"

"ku kawo min. Ku tashi kuje"""

"Sam abinda baba yafada bai yiwa husnah dadiba ita so tayi ace suna zuwa iyayen su rufesu da fada sannan suce fahad sai yarabu da ita, Bilkisu kam sai faman hawaye takeyi tana kukan zuci ahaka"

"suka tashi suka fita, kallon bilkisu yayi cikin fada yace,"

"""Daina yimin kukan nan, kar na kara jinsa """

"Share hawayenta tayi tai shiru husnah na bayansu, juyawa yayi ya kalleta,"

"""Ke kuma tunda kin zama uwar mutane sai ki kaimu asibitin da yadace. "" Tasan gatse yayi mata"

"amma duk da haka sai ta fadawa mai napep asibitin da zai kaisu, lokacin da sukaje asibitin babu mutane dayawa dayake private ne kuma weekend ne, nan aka debi jinin kowa amma bilkisu saida fahad yariketa sannan tabari aka dauki jinin har lokacin kuka takeyi kadan kadan. Sun dan jima suna jiran result sannan aka kawo musu gaba daya suka tafi ko budawa basuyi ba,gidansu fahad suka koma suka kaiwa baba result din shi da kansa yabuda yagani sannan yadago yana kallonsu,"

"""To kamar yadda sakamako dai ya nuna kowannenku lafiya kalau yake. Allah yakara rufa asiri,"

"sannan wannan kar yakawo fitina atsakaninku kubarshi amatsayin kawar da zato"""

"""Baba ni so nake tafada mana a Inda taji ance bilkisu tanada HIV"""

"""Ai zancen duniya baya buya..."" Husnah tafada tana murguda baki,"

"""A'a fahad, abar maganar nan haka kaji, kar Ku kara tada maganar nan..."

"Allah yayi muku albarka"""

"Nasiha sosai su baba suka yimusu sannan suka yi musu sallama suka tafi, tunda suka koma gida fahad ke rarrashin bilkisu sai dakyar yasamu ta hakura tayi shiru ta daina kuka, ita tarasa me ta tarewa husnah agidan nan da bata kaunarta ko lokacin da suke zaune lafiya agaban fahad ne take yimata magana amma idan baya wurin ko kallo bata isheta ba. Tsabar abinda husnah tayi fahad baiji dadinsa ba aranar yabar kano yakoma kaduna ko sallama baiyi mataba shi da titsiyeta yaso yayi sai tafada masa munafukin da yace mata bilkisu nada HIV amma kuma sai baba yace abar maganar. Tunda yakoma kd yadaina daukar wayarta idan tayi masa massage ma baya yimata reply daga karshe kawai sai ta shirya tabishi can kawai sai ganinta yayi da dan akwatinta dama dakinshi shi kadai ne, yanata daddaure mata fuska amma daga karshe dole ya hakura yasakar mata fuska yace ya hakura komai yawuce amma karta kara, duk zuwanta ya takura shi baya samu suyi hirar soyayya da bilkisu kamar yadda yasaba yimata ita kuma batama san husnah na wurinsa ba ita dai taga bata nan kwana biyu. Saida husnah tayi sati daya awurin fahad sannan tadawo gida tana dawowa ta hau yada habaici tana yiwa kawayenta waya tana cewa daga wurin oga take acan taje ta huta sosai abin ya taba zuciyar bilkisu aganinta ai wannan munafurcine fahad yayi shine ko yafada mata husnah na wurinshi nan itama tadau fushi dashi shiyasa lokacin da yazo weekend basu rabu da dadiba saida fada kwata kwata baisan laifinsa ba amma taki sakar masa fuska wannan karon ko yar karar da akeyi masa ake barinsa yayi katobararsa ba abarshi yayi ba bare abarshi yayi abinda ya gadama duk da tasan illar hana kai ga miji wannan karon kam hanashi kanta tayi saboda taji haushin abinda suka yimata shida husnah. Husnah kam tun lokacin da tadawo daga wurin fahad tafara amai da tofe tofen yawu sosai abin ya tayar mata da hankali"

"saboda tana zargin cikine, ai kuwa tana yin test taga shine zancen zuci tafara yi,"

"""Tabdijam ina. Wallahi bazan haihu yanzu ba intsufa ga wahalar karatu,ita matarka ma da take"

"tsohuwa bata yarda tayi ciki ta haihu ba sai ni yar yarinya dani? Wallahi cikin nan zubar dashi za ayi tabdijam """

Abinka da kuruciya duk sai tabi ta yadawa kawayenta wai cikine kuma ita bata so nan suka yita

"zugata suna cewa idan tabari ta haihu yanzu wallahi fahad daina yayinta zaiyi tunda ga matarsa nan ita taki yarda ta haihu sai gayunta take ci,"

"Tana komawa gida da daddare sukayi waya dashi har zasuyi sallama sai tace masa,"

"""Ya fahad.... Tunfa rannan naketa amai da tashin zuciya kuma da nayi test ashe cikine. Nikuma"

"gaskiya ba yanzu ba.... Kawai azubar """

"""Baki da hankali dama? Azubar fa kikace, husnah wai meyake damunki ne?"""

"""To ita anty meyasa ita baka yimata cikinba saboda ita kafi so? Nikuma nice zan wahala kenan..."""

"""Ohhh Allah.... Husnah ki shiga cikin hankalinki, haihuwa bata Allah bace? Ai ba yin kaina bane..."

"Koda wasa karki kuskura ki attempting zubar da cikin nan idan kuma bakiji ba wallahi kika zubar zaki sha mamakina dan sai nadauki mummunan mataki akanki """

Ummi Shatu_*????

"Duk da wannan maganganun da yayi mata bata yarda ba azatonta wai barazana ce yayi mata shiyasa taci gaba da yi masa maganar itafa zubar da cikin nan zatayi ji yayi gaba daya auren yafita akansa daga bilkisun har asma'un fushi yake dasu saboda kowaccensu mai laifice awajensa, ita kuma husnah kishi da rashin wayo yarufe mata ido takasa ganin sudden changes din dake tattare da bilkisu itafa kawai idonta yarufe gani take bilkisu da biyu taki haihuwa saboda karta tsufa irin rashin dabarar da matan yanzu keyi wai aki haihuwa gudun kada atsufa. Ranar laraba yazo kano kuma aranar yake son komawa daga bilkisun har husnah sama sama yagaisa dasu dan ita bilkisu ma ko ganinsa bata yiba tana can wurin aiki sai awaya yakirata, ita kuma husnah tana gida, shi baida dabi'ar binciken wayar mutane amma yau yayi akan husnah saboda yana zargin kamar zugata kawayenta keyi ai kuwa zarginshi yazama gaskiya dan yaga chat dinsu da Fa'iza tana tambayarta wai cikin yazube tace a'a wannan maganin baiyi mata aikiba sai ciwon mara da yasata shine fa'iza ta tura mata sunan wani wai ta gwadashi mana yafi wancan karfi, ranar husnah ta raina kanta domin yi yayi kamar zai dafata yacinye nama danye saboda masifa daga karshe yace wallahi idan ta zubar da cikin nan abakin aurenta kuma kar su Ruky da Fa'iza su kara zuwar masa gida, da bacin rai yakoma kaduna itama bilkisu fushin take yi akan nada wai yazo ko yaje yaganta yayi tafiyarsa, washe gari da rana ya kirata wai dan Allah tayi masa taimako duk ranar da kawayen husnah sukazo ta fada masa da to ta amsa masa amma acikin zuciyarta tace babu ruwanta bazata zama munafuka ba. Bilkisu fa kiba kullum karuwa takeyi ga haske sannan fatarta har wani kyalli da sheki takeyi yanzu duk kayanta dakyar suke shigarta tun bata daukar maganar khulsum dagaske na wai cikine da ita har tafara dauka dan taji period dinta shiru gashi har pad tasiyo guda biyu ta ajiye amma kemadagas yaki zuwa gabanta ne yafara faduwa wanda sam bata San dalili ba, acikin satin fahad yazo nan dinma aranar zai koma fada sukayi kaca kaca da husnah akan cikin nan bilkisu na jinsu kamar zai doki husnah tsabar ransa yabaci bai ko yiwa bilkisu sallama ba yayi tafiyarsa abinda yasake kular da ita kenan, yana tafiya husnah ta aiwatar da kudurinta ta zubar da cikin ai kuwa tasha wuya kamar zata mutu dan azaba, ranar friday sai gashi lokacin husnah bata gama warwarewa ba daga ta'asar da tayi shiyasa yayi saurin ganewa tun kafin ya tambayeta tafara shirya masa karya wai kawai mafarki tayi wata mata mai kamada bilkisu tana dukan cikinta da tabarya tana farkawa taji tana bleeding sai kuma ciwo yasata agaba, fada fahad yashiga surfawa yana cewa kar ta yarda tasaka bilkisu cikin shirmenta ta hada kayanta tatafi gidansu shi yagaji da wannan masifar tata ai dama yafada mata karta zubar da cikin nan amma saida ta zubar. Bilkisu na daki tana jinsu amma bata fitoba saboda ba asata cikiba kar ace munafurci ne, aranar itama tayi gwaji da pt strip din da tasiyo tun kwanaki biyu da suka wuce amma tsoro yahanata yi, tun agwajin farko yanuna mata ciki baro baro, rufe baki tayi tana mamakin to meyasa takasa ganewa tun farko? Yanzu shikenan tayi abun kunya wai itace dauke da cikin fahad ajikinta to ko itama zubarwar zatayi? Masifar da yayita yiwa husnah ce tafado mata nan tsoro yashigeta to ai ko babu"

komai ma lokacine yayi wanda zata nunawa husnah cewa ita ba juya bace sannan babu abinda

yasamu mahaifarta ras take tunda gashi tadau ciki. Duk da cewa husnah ta tafi yaki sakar mata fuska dan tun lokacin da ya bukaceta tahanashi yake fushi ita kuma yanzu tun ranar da tayi pregnancy test dinnan take jin wata matsananciyar bukatarshi kamar me amma ko cikin dakin nata bai kwanaba afalo ya kwana haka yabarta da juye juye da kwalla kun san mai ciki idan taso abu

bata samuba.....

*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

"55****Washe gari da safe tana jinsa afalo yana harkar dake gabansa ahaka ta tashi tayi wanka ta dan shirya sannan tasake kwanciya cikin net,har wurin 9 sannan yashigo cikin dakin kai tsaye bathroom yawuce yaje yayi wanka yafito tana nan dai inda yabarta kwance tana satar kallonshi, ganin bai san tanayi ba yasata maida kallon nata gaba daya kansa, koda wasa ita bata taba zaton zata tsinci kanta cikin wannan yanayin ba wai yau itace ke yiwa fahad kallo na daban lumshe idanuwanta tayi wadanda kasala ta cikasu, tana ganinshi ya kammala shiryawa yasa dogayen kaya"

"kalar ruwan siminti yana kokarin fesa turare yaji atishawar ta, juyawa yayi ya kalleta,"

"""Sannu. Ko mura kikeyi ne?"""

"Jijjiga kai tayi idanuwanta na taruwa da kwalla,"

"""Ayya sorry , idan zan dawo zan taho miki da magani"""

"Batayi magana ba taci gaba da binsa da kallo ji take kamar ta janyoshi amma bazata iyaba, har"

"yakarasa shiryawarsa ya juyo ya kalleta batayi motsi ba,"

"""Ni na fita... Akwai wani abune?"""

"Shiru tayi masa tana matse kwallarta,"

"""Wai meyake faruwa ne? Ke kam sai kace dan ke kadai aka halacci kuka? Haba bakida aiki sai"

"koke koke.... Dan Allah kirage yawan kukan nan. """

"Tashi zaune tayi tana kallonsa amma batayi magana ba,"

"""Bari naje shago.... Nadawo aljihu na babu nauyi ne duk na kashe kudadena wallahi """

Juyawa yayi yafita jin batace komai ba yana fita ta rafka tagumi tana shafar cikinta da hannunta

"guda daya, tunani take yi kila abinda ke cikinta mace ce kila kuma namiji ne, ohh Allah mai iko shi kadai yasani, tashi tayi tafita ta shiga kitchen domin dafaffen kwai take son ci, bayan ta dafa tafito tana kallon dakin husnah kwana biyu duk sai take jin gidan yayi shiru da yawa da husnah bata nan yanzu da ace tana nan tasan tana nan tana aikin yar mata da magana, har zata zauna tajiyo"

"karar wayarta, ciki takoma ta dauko wayar tafito ta daga sannan ta nemi wuri ta zauna,"

"""Labour wai

40 / 42