KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   25 / 42

72K to 75K   out of 124.3K words

yadaure fuska kamar bai taba dariya ba,"

"""Macuci.... Azzalumi..... Mugu to Allah ya toni asirinka. yanzu dama hamood kasan kana dauke"

"da kwayar cutar HIV amma shine ka aureni ahaka har kake burin hada shimfida dani?"""

"Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yazare farin tabaran dake sanye cikin idonsa, zama yayi"

"kan kujera ya dora daya kan daya yana watsa mata kallon dake kara tafarfasa ranta,"

"""To sai me dan na aureki ina dauke da HIV? Bake kika manne min kika like min akan dole sai na"

"aureki ba? Karfa ki manta har aurenki kika kashe dan kawai in aureki in zauna dake """

"""Ya isa haka malam Ai duk wadannan abhbuwan dakake ikararin cewar na aikata na aikatane"

"acikin rashin sani Kuma ina nadamar hakan ahalin yanzu, wallahi hamood kaci amanata kuma"

ka zalunceni wanda bazan taba yafe maka ba har abada Sannan ka gaggauta sallamata domin

"gidan ubana zan tafi insha Allah nagama zama dakai """

Wata shakiyiyar dariya yasaki irin wacce ke dauke da mugunta tsantsa aciki sannan yayi mata

"kallon uku ahu,"

"""U are such an idiot mai gado, sai yanzu nasan bakida tunani sam.... Hmmmm to idan ke shashasha ce ni mai hankaline... Bazan taba sakinki ba koda kuwa za amaimaita yakin duniya akaro na uku. And lastly abinda zan fada miki shine u should mind ur tongue kisan irin maganar"

"da zaki rinka fada min idan bahaka ba jikinki zai rinka gaya miki """

"Yana kokarin mikewa taje tasha gabansa cikeda masifa da tashin hankali,"

"""Wallahi hamood koda baka sakeni ta dadin rai ba to yazama wajibi ka sakeni ta dolen dole koda kuwa agaban kotu ne domin nagama zama da macuci,mayaudari, mashayi kuma mazinaci... Ko kana tsammanin har yanzu ban san irin kazamar rayuwar da kuke yi kaida waccan karuwar ba? To Allah yagama tonar asirinku dan haka kasakeni kuma kabani kudina naira dubu dari biyar wanda"

"abbana yabani kai kuma ka lallabani ka kwace. """

"Tafa hannaye wasila tashiga yi wacce fitowarta kenan daga cikin daki,"

"""My dear yanzu kana tsaye kanajin abinda wannan mahaukaciyar take fada maka amma shine"

"bazaka dauki mataki ba?"""

Tun kafin wise tarufe baki hamood ya dauke bilkisu da wani gigitaccen mari wanda yayi

"barazanar makantar da ita, zafin marin yasa bilkisu sake daga murya tana furta,"

"""Allah ya isana macuci azzalumi kuma wlhi sai ka bani kudina sannan dolenka ka sakeni """

"""Banza yar gidan matsiyata ni zaki yiwa sharrin na karbar miki kudinki? Uban me uban naki yake dashi da har zan karba? Saki kuma bazan yiba ko kin zaci nima irin wannan sakaran yaronne da zan sakeki aduk lokacin da kikaso? Koda zan sake ki yazama dole inmore sadakina dan haka sai"

"kishirya daukar kwayar cutar HIV """

"Tun kafin yakarasa bilkisu ta dadimeshi tana kuka,"

"""Ni ba yar matsiyata bace sai dai idan kaine dan matsiyata kuma wallahi daga yau nagama zama"

"dakai """

"Wani marin yasake bata sannan yashiga dukanta babu ji ba gani har saida takai kasa lokacin ne yafara ball da ita yana nausa mata kafa aciki, kuka bilkisu takeyi tana ihun neman dauki ganin yana kokarin kasheta yasa wise zuwa tana kokarin hanashi amma yahaukace kwata kwata bayaji"

"bare gani,"

"""Nashiga uku hamood ka kusa kasheta... Kar kayi kisan kai kaga yanda takeyi fa... Kabarta haka"""

Shine abinda wise keta fada amma hamood yaki saurararta ganin haka yasata sulalewa daga gidan

tagudu tun kafin hamood yakashe bilkisu azo tafiya dashi ahada harda ita.

"Bilkisu kam tajima da fita daga cikin hayyacinta sakamakon na jakin da hamood ya lakada mata abu na karshe da zata iya tunawa shine taji hamood ya gwarata da kujera ta fadi akan hannunta na hagu wanda take awurin wani azababben zafi ya ziyarceta, cikin azababben ciwon kai take bude"

"idanuwanta ahankali wadanda suka kumbura suntum sakamakon uban bugun da suka sha,"

Ammah ce da meenah zaune acikin dakin wanda ko ba afada mata ba tasan asibitine domin ga

"alamu nan sun nuna hakan, ga ruwa nan ana kara mata a hannunta na dama sannan hannun hagun ta kuma an daddaureshi dasu bandeji alamun dori,"

"Wasu hawayen nadama ne suka zubo daga cikin idanuwanta, ganin ta dan motsa yasa ammah da"

"meenah azamar tasowa dukkaninsu Wanda har bakinsu na haduwa wurin yimata sannu,"

"""Sannu mai gado..."" Inji ammah,"

Kai ta dan daga cikin azabar ciwo ta rinka binsu ammah daya bayan daya da kallo kamar yau tafara ganinsu. Bata iya cewa komai ba sai ciccije baki da takeyi sakamakon ciwon da dukkanin

"jikinta keyi mata musamman ma hannunta na hagu,"

"""Sannu adda labour Allah yatashi kafadunki"""

"Dagawa meenah kai tayi tana cije baki hawaye na kwaranya daga cikin idanuwanta ahaka su maama suka shigo itada Hindu,maama na dauke da sultan ita kuma Hindu tana goye da meenal abayanta sai hudah wadda hannunta ke rike da nata, cikin zuciyarta take wani irin kuka mai tsuma rai saboda ganinsu mama da 'yayayensu yasake fama mata raunin da take fama dashi, su gasu da yaransu agidan mazajensu cikin walwala da kwanciyar hankali amma ita tanata shiga cikin runtsin"

"rayuwa,"

"""Allah ka gafarta min... Allah natuba... Astagfirullah..."" Shine abinda taketa fada cikin zuciyarta,"

"jinta take ta tsani hamood ta tsani duk wani namiji mai irin halinsa ahalin yanzu,"

"""Allah ya isa..."" Shine abinda lebanta suka furta amma babu wanda yaji, cikin tausayawa da"

"jimami maama da hindu suka karaso gaban gadon su dinma kamar zasuyi kuka,"

"""Sannu Adda.... Sannu... Sai Allah yasaka miki insha Allah"" inji mamaa,"

"""Kuma inbanda zurfin ciki irin na Adda labour bata fa taba fadar irin zaman da sukeyi ba bare"

"tafadi cewar yana dukanta..."" Hindu tafada tana kokarin zama agefen gadon,"

"""Ni dama tun jimawa wallahi na fuskanci akwai matsala kugafa irin ramar da tayi har iyallo ke"

"cewa ciki ne..."" Meenah itama dake tsaye kusa da amma ta tofa nata,"

"""Ai Dr yace babu wani ciki yanzu... Yace bata da komai, gara ma da Allah bai bata ba domin hada zuri'a da irinsu wannan hamood din hatsarine... Allah yabata masu albarka nan gaba"" maama tafada tana kokarin mayar da kwallar da take kokarin cikowa idanunta, ammah dai har akayi aka gama bata tofa tata ba suna nan zaune sunata yimata sannu har Abba yazo yadubata yatafi hakama mazajensu duk sunzo sun dubata, khulsum amarya itama daren ranar sai gata, kowa yaga bilkisu sai yaji tausayinta sakamakon kumburar da fuskarta tayi tsabar duka. Lokacin da dare yayi meenah ce tace zata kwana da ita amma ammah tace a'a kowa yatafi gidansa inyaso Rabi mai aikinta sai tazauna su kwana tare hakan kuwa akayi, ita dai bilkisu kasa baccinma tayi sakamakon"

"suyar da zuciyarta keyi motsi kadan zata furta,"

"""Allah ya isa..."" Acikin zuciyarta kokuma afili. Saida tayi kwana uku agadon asibiti sannan tafara tashi har ta zauna kuma an danyi sa'a kumburin fuskar tata ya dan ragu, har ranar babu wanda yayi mata maganar hamood may be suna son abar asibitinne tukunna sai asanar mata abinda yafaru, aranar tana zaune maama na kusa da ita agefen gadon tana bare mata ayaba tana ci sai ga hajiya"

"iyallo ita da yakumbo mai gado, tunda iyallo tashiga dakin take tsinewa hamood,"

"""Ni dama wallahi wannan yaron ban yarda dashiba... Yaro sai kace dan dambe wani murgujeje dashi... Wallahi tsohon mijinki shine miji mai gado... Yaro mai kunya ko gaisheka yakeyi idanuwansa akasa bazai taba yarda ya hada ido dakaiba amma shi wannan idonsa atsakar ka yake sai yasaka idonsa cikin naka sannan zaiyi maka magana....Allah yasawwake,Allah ya kwashe"

"masa albarka macuci"""

"Tun abun na bawa su maama haushi har yadawo yana sakasu dariya, iyallo nata faman hamuki ya"

"mudan yashigo wanda dama shine yakawo su,yana yiwa bilkisu yajiki iyallo tahau cewa,"

"""Ai shikenan yanzu sai acika min burina ayi hadin nan.. Ni dama tun farko mudansiru naso abawa"

"aka ki..."""

"""Dan Allah iyallo mu ki kyalemu muji da abinda muke ji..."" Maama tafada tana hararar gefe,"

"""To fitsararriya dadinta ma dai bake naceba balle kiyimin rashin arziki... Fitsararriya kawai.."""

Shi dai ya mudan ficewa yayi daga dakin da alama shima baiji dadin maganar iyallo ba ko meye

dalili? Bilkisu kuwa jin iyallo ta ambaci fahad har tana yabonsa yasata dulmiya kogin tunani.....

*Wannan littafin na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

*_Ummi Shatu_*

*Wannan littafin na siyarwane me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma

08030811300*

_BILKISU_

"37 ***Har iyallo ta karici bambaminta tagama bilkisu batace uffan ba kusanma gaba daya yanzu tadaina fahimtar abinda suke cewa domin tadade da yin nisa acikin kogin tunani tabbas maganar iyallo gaskiya ce fahad yarone mai kunya kuma nagartaccen namiji domin ita kanta ta shaida hakan duk da har yanzu bata jin zata iya zaman aure dashi domin yayi mata kankanta shekarunta sunfi nasa, to tayaya zatayi rayuwar aure dashi? Tayaya zai rabeta amatsayin matarsa? Haba ai da kunya,jikinta yanzu yafara bata cewar wannan abunda yafaru da ita harda hakkin fahad kila Allah ne yayi masa sakayyar cutarwar da tayi masa itada hamood shiyasa ya hanasu jin dadi da farin ciki a lokacin zaman aurensu, ita kanta sai yanzu take ganin wautarta da rashin wayon da ta aikata gaskiya hamood ya shammaceta ya cutar da ita, wasu hawaye masu zafi taci gaba da zubarwa ganin haka yasa iyallo sake dagewa wurin tsinewa hamood ita kuwa bilkisu ita kadai tasan dalilin kukanta gashi kukan zuci takeyi marar sauti sai dai kawai aga hawaye na zuba alhali likita yace irin wannan kukan yafi illa dan haka ta nisanceshi amma ita kanta tasan bazata taba iya"

hana wadannan hawayen zubaba domin direct suke tahowa daga can cikin zuciyarta.

"""Adda labour dan Allah kiyi hakuri kidaina kukan nan haka.... Maganin me kukan zaiyi ne?"""

"Mama tafada cikin rakwarkwabewar fuska,"

"""Mamaa yazama dole inyi kuka... Barni in koka ko zuciyata zatayi sanyi """

"""Kidai yi hakuri kuma ki daure dan Allah. """

"""Maama..... Bazan.... Baz. """

"Ai bata kai ga karasawa ba kirjinta ya sarke idanuwanta suka kakkafe, wata gigitacciyar kara maama tasaka yayinda su iyallo kuma suka hau zuba salati, karar da maama tafasa itace ta janyo hankalin ya mudan yashigo cikin dakin cikin tashin hankali ganin abinda ke faruwa yasa shi fita da sauri zuwa office din likita, maama na rike da ita tana gunjin kuka likita yashigo yafitar dasu ta hanyar basu umarnin su fice daga dakin, yajima akanta sannan yafita har lokacin jikin maama bai daina rawaba da nasu iyallo domin su duk atunaninsu mutuwa bilkisu tayi amma sai likita yace musu bahaka bane su kwantar da hankalinsu da ranta kuma insha Allah zata samu lafiya, ita dai bilkisu na can bata san abinda ke faruwa ba domin tadade da rabuwa da hankalinta, lokacin da su ammah sukazo ma baccinta take tasha sai ruwa da ake kara mata, tsaki meenah taja tasamu wuri ta"

"zauna kusa da Hindu bayan tadawo daga leken bilkisu ta window din dakin da take ciki,"

"""Wai dan Allah sai yaushe za abar baiwar Allahn nan tahuta ne? Haba jama'a Karin ruwa yaki"

"karewa """

"""To ya za ayi Ameenah... Allah dai yabata lafiya..."" Inji ammah, zama sukayi jugum jugum har sai"

"da likita yakira ammah nan suka rankaya gaba daya suka tafi, dan takaitaccen bayani yayi musu"

"dangane da matsalar da bilkisu tasamu amma yace yanzu sun samu nasarar shawo kan matsalar sai dai yanada kyau ta guji tunani da shiga bacin rai domin maganar gaskiya zuciyarta na daf da bugawa saboda damuwa, duk cikinsu babu wanda bai kokaba sai Ammah kadai itace ke basu hakuri, zuwa dare bilkisu ta farfado hakan ya dan kwantar musu da hankali musamman ma da sukaga duk wuraren da yataru jini ajikinta ya barbaje, babu laifi taji sauki sosai sannan ta samu lafiya matsalar kawai dorin hannunta ba akunce ba likita yace sai nan da sati biyu haka suka yita faman kaiwa da komowa har zuwa lokacin da aka kunce dorin aka sallamesu, duk bilkisu tabi tasake kekashewa kamar wadda tayi shekara akwance. Lokacin da suka koma gida ba karamin mamaki tashiga ba domin ganin kayanta gaba daya nasawa andebosu da duk wani abu wanda yake mallakinta ne, ita dai har ta kwana ta yini tasake kwana babu wanda yayi mata maganar hamood ko wata magana mai kama da haka, shi kansa abba baiyi mata maganar ba iyakaci idan taje ta gaisheshi suka gaisa shikenan amma bai yimata maganar hamood ba haka itama ammah duk da suna zama suna yin hira, sai akwana na biyarne maama tasake dawowa gidan domin dubata itada hudah harda farfesun kaji da dambunshi wanda ta iyowa bilkisu, cikeda sha'awa bilkisu ke kallonta domin har cikinta ya dan fara turowa duk da dai tanada girman ciki amma kowa yaganta yaga mai juna biyu, saida suka sha hira afalon ammah ganin lokacin salla yayi yasa bilkisu tafiya dakinta tayi wanka tazura doguwar riga tayi salla tana idarwa maama tashigo tana rikeda hannun hudah, kwantar da ita tayi kan gadon bilkisu sannan ta yunkura zata tashi nan bilkisu tayi hanzarin"

"dakatar da ita,"

"""Yawwa maama wai dan Allah waye yakaini asibiti ne? Sannan hamood kuwa yayi sakin?"""

"Komawa maama tayi ta zauna tana kallon bilkisu,"

"""Adda labour wallahi ranar hudah muka kai asibiti nida abbanta, gaba daya sai najini ba anutse ba sannan hankalina duk yatafi gareki shine fa nace masa mubiya inganki dakyar ma yayarda wai yana gudun makara a office, ina shiga na iskeki cikin wannan halin hamood yanata kwallo dake...."

"Abban hudah ne ya daukeki yakai cikin mota bayan nakiraki shine muka wuce dake asibiti, sai"

"bayan da akayi admitting dinki sannan nakira su ammah """

"Jijjiga kai bilkisu tayi cikin damuwa sannan ahankali tace,"

"""To ya maganar sakin? Ya sakeni?"""

"Kai maama ta daga mata cikeda damuwa,"

"""Ya sakeki bayan sun debota da Abba domin Abba waya yayiwa uncle dinsa yasanar dashi komai nan uncle din nasa ke cewa shi dama bashida wani hadi dashi inbanda almajiranta da yazo yi har Allah yahadasu yake wanke wanke agidansa dahaka yazama tamkar dan gida. Ke intakaice miki"

zance ma shi kansa hamood din saida Abba yasa aka nemoshi sukayi babu dadi dan cewa yayi shi

"bazai sakeki ba har sai anbiyashi komai nasa tun daga kayan lefe har sadaki... Sai da Abba yabiyashi sannan ya sakeki saki biyu. """

"Tagumi bilkisu ta rafka tana jin kirjinta nayi mata suya,"

"""Lallai hamood yacika marar mutunci Nimafa akwai kudina a hannunshi wanda Abba yabani"

"yace wai in ranta masa wani mutum yasiyarwa da mota to kuma yanzu yadawo masa da ita shine zai cika yabashi kudinsa saboda already kudin hannunshi ya tura za a kawo musu sabbin cars. """

"""Babu komai adda maigado kawai kiyi addu'a insha Allah bazaki tagayyara ba kuma sai Allah yasaka miki... Ni wallahi idanma son samune tsohon mijinki yadawo kusake dinkewa. Allah"

"sarki ya fahad bawan Allah komai nasa na mutunci """

Shiru bilkisu tayi tana saurarenta har saida taji tayi shiru sannan tasauke nannauyar ajiyar zuciya

"tana kallonta,"

"""Maama kenan. """

"""Wallahi dagaske adda labour fahad shine yafi dacewa dake saboda yanada yakana da alkunya..."""

Rasa abin cewa tayi daga karshe taja bakinta tayi shiru tana jin maama sai faman kwarzanta fahad

take tayi.

"Sam abinda maama ta fada baiyi tasiri acikin zuciyarta ba sai dai yatsaya mata arai fiyeda tunanin mai tunani domin daren ranar kawai tunanin rayuwar da tayi agidansa tayita yi tana tuna dabi'unsa da kuma halayensa wadanda ko makiyinsa bazai kushe ba, tarasa a wanne aji yadace tasaka wannan al'amari, shin yanzu idan fahad yadawo zata iya aminta dashi? Wannan shine tambayar da"

"tayiwa zuciyarta amma sai ta girgiza kanta,"

"""Dan mutunci kam

25 / 42