KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   41 / 42

120K to 123K   out of 124.3K words

yau baki zuwa aikine? Waye kika ajiye wanda zaiyi miki voicing din labaran rana?"""

"""Haba kawata dama fa ina nemanki yanzu nake shirin kiranki Yau bazan shigoba bana jin dadi"""

"""To wallahi ki zo dai ki karanta labaranki domin yau copers din da kika saba jibgawa aikinki suyi miki duk basu zo ba. Nikuma kinga ni nayi nasafe bazai yuyu asake jin muryata a na rana ba"

"MD zaiyi magana"""

"""Dan Allah kawata kiyi min wallahi ina cikin matsala ne bazan iya zuwaba dama kuma ina"

"nemanki fa. Ina son mu tattauna"""

"""Shikenan Allah yakara sauki, wasa nake yimiki zanyi miki news din, anjima idan natashi zan"

"shigo. """

"Sallama sukayi ta dan kishingida tana bare kwan da ta dafa guda uku, daga karshe wai ta dan kunna kallo ko zata debe kewa. K'arfe biyu saura khulsum ta karaso gidan lokacin bilkisu na"

"kwance kan kujera, zama khulsum tayi tana cemata,"

"""Bani abinci yunwa nakeji..."""

"""Ai kuwa sai dai kisha tea dan ban girka komai ba, bana jin sha'awar girki wallahi"""

"""To shikuma fa?"""

"""Shima tea din yasha kadai yafita"""

"Dariya khulsum tayi,"

"""Kina shagalinki kawata, wato girkima sai kin gadama zakiyi, koda yake bake kadai bace ai..."""

"""Nida waye da?"""

"""Au ina kanwar taki?"""

"Yamutsa fuska bilkisu tayi sannan tace,"

"""Bata nanfa kwana biyu, amma may be zata dawo... Ke ni ba wannan ba dan Allah shawara nake"

"so kibani """

"""Allah yasa zan iya labour... Meya faru?"""

"Dan shiru tayi na wasu sakanni sannan tace,"

"""Kinga wannan cikin da wata dabi'a yazo min wallahi.... Wai karfi da yaji kulawar fahad nake"

"nema"""

"""Banfa ganeba. Yimin gwari gwari"""

"Harararta tayi sannan tace,"

"""Ina nufin ina bukatar mijina, shikuma fushi yake tayi akan last time da yazo na hanashi kaina"

"saboda munafurtata yayi.... Dan Allah tawacce hanya zan janyo ra'ayinshi batare da yagane ba. """

"Khulsum najin haka me zatayi inba dariya ba, dariya tafara yi harda buga kafa akasa,cikin jin"

"haushi bilkisu tace,"

"""Ya ina yimiki serious magana amma kina nema ki mayar da ita abun dariya?, dagaske fa nake"

"yimiki..."""

"""Kin san me yabani dariya? Zamanku da fahad na burgeni, ke son girma shikuma Jan aji Labour"

"kenan wallahi Allah ne ya kamaki, kin tuna lokacin bikinku, cewa fa kikayi ni yaron nan da"

"yadage sai ya aurene me zai bani idan munyi auren?, wai ma tsaya idan aka ajiye masa ni ta ina zai fara?, yaron da ko gama balaga baiyi ba. """

"""Dan Allah ni ya isheni, yanzu dai zaki bani shawara ko dariyar zaki cigaba da yimin? Kin dai san"

"bani kadai bace cikina zai iya samun matsala idan har bai samu abinda yake bukata ba """

"Shiru khulsum tayi ta daina dariyar da takeyi,"

"""Kin san me labour? Ai ke yakamata kisan hanyar da zaki bi wurin janyo hankalinsa saboda kinga kowanne namiji akwai ta inda ake kamashi Wani ta girki, wani ta kwalliya, wani ta magana,"

wani ta kamshi ma kawai zai zo hannu. Yanda maza suke kala kala haka hanyoyin kamasu ma

"yake kala kala. amma ke me mijinki yafi so?"""

"""Shima yana son abinci kuma gaskiya yanada son kamshi """

"Tsaki khulsum tayi sannan tace,"

"""Ashe ke da kin san ma abubuwan da yafiso shine bakiyi ba? To yanzu tashi zakiyi ki shirya masa lafiyayyen abinci sannan ki turare gidanki da dakinki da ke kanki da kamshi kinga yana dawowa"

"sai kuyi evening show kawai """

"Dariya bilkisu tayi cikin murna tace,"

"""Yawwa mutuniyas kokefa.... Nagode bari natashi nabada himma. """

"""Yakamata kam, yau dai ga ranar yaro tazo """

"Daga haka ta sabi jakarta tafita tana dariya. Bilkisu zagewa tayi ta gyara gidan tsaf ta turareshi da turaren wuta da freshener mai sanyin kamshi, shi kansa bedroom din ma yadda ta gyarashi abin kallo ne tasaka wani bedsheet pink colour da zanen heart atsakiya abin gwanin burgewa sannan ta danyi kwalliya da net din dake makale jikin gadon ta tattare shi yabada design mai kyau sannan gefe daya ga turaren wuta na stick mai masifar kamshi yana ci sai hayaki mai kamshine yake tashi ahankali. Ita kanta yau kwalliya taci cikin materia red colour dinkin gown gefe daya ta shirya lafiyayyen girkinta soyayyiyar shinkafa da salad kawai fahad take jira. Tana kwance kan doguwar kujera tana kallon wani film atashar African magic mai suna things i hate about you fahad yashigo, fuskarshi babu yabo babu fallasa ya nemi wuri ya zauna yana kallonta, matar nan fa dagaske kiba"

"take hadawa bata wasaba,"

"""Sannu da zuwa. "" Tafada idonta nakan tv amma fuskarta asake take sosai wanda har hakan yaso"

"bashi mamaki, cikin basarwa yace,"

"""Yawwa ranki yadade """

"""Ga abinci can fa..."""

"""Ok sannu da kokari bari na dan watsa ruwa tukunna..."""

"Daga haka yamike yawuce ciki nan tabishi da kallon sha'awa tana jin kamar tabishi, tana nan zaune yafito sanye da kananan kaya dukansu bakake daga rigar har wandon hannunsa rikeda p cap, wani bala'in kyau taga yayi mata ba kadanba bata taba sanin cewa fahad kyakkyawa bane sai yau,kallonshi kawai ta zauna tana yi sai take ganin kamar ma da biyu yake yimata wannan yangar da jan class din domin sai wani yatsine yatsine yakeyi kamar mace, da yake yau acikin shaukinsa take shiyasa take ganin komai nasa yau kyau yake yimata yana burgeta. Tana zaune tanata aikin satar kallonshi yagama cin abincin yamike yana kallonta shi fa yau yakula da fara'a ta tashi amma"

"baisan dalili ba,"

"""Zan fita. """

"Taji yafada, ji tayi kamar ta dora hannu aka tafasa ihu dan tsabar haushi, batayi masa magana ba"

"yasa kai zai fice har yaje bakin kofa taji yajuyo yace,"

"""Amm namanta..., gaskiya yau dakinki yayi kyau.... Da ke dinma kanki, style din da aka yiwa"

"dakin is something amazing..... I like ur style hajjaju..."""

"Daga haka yafice daga cikin falon, tana jin alamun tafiyarshi tafara kwalla, cikeda damuwa da"

"bacin rai takira khulsum tana fada mata, dariya khulsum tayi sannan tace,"

"""Ohh my God.... What a funny Wato darling fahad yagano mu shine bazai bada kai bori yahau"

"da wuriba har sai yabamu wahala? To inyasan wata ai bai san wata ba. Bari inyi miki text, insha"

"Allah bazai tsallake wannan tarkon namu ba"""

"""Are you sure...?"" Inji bilkisu,"

"""Am 100% sure dear... Kijirani yanzu"""

"Daga haka takatse wayar tana jiran text din khulsum babu jimawa kuwa saiga text din yashigo,"

murmushi bilkisu tayi tana bawa kanta tabbacin zatayi fiyeda yadda khulsum ta shirya mata.

"Har karfe 9 fahad bai dawoba sai wurin 9:30 sannan taji shigowarshi, tana kwance cikin net a kunnenta yashiga wanka yafito sannan yafita falo daga shi sai short nicker wanda tabada tabbacin abinci yaje yaci, yana shigowa yaji kamar nishin bilkisu da sauri yanufi gadon, kwance yaganta shame shame tanata faman sakin wahalallen nishi cikin wata atamfarta dinkin riga da skirt gaba"

"daya kayan sun matseta sosai, dagota yayi yana tambayarta cikin rudewa,"

"""Bilkisu menene? Meke faruwa...?"""

"Kirjinta ta nuna masa da hannunta alamun ciwo yake yimata,"

"""Ciwon kirji kikeyi?"""

"Kai ta daga masa tana sake dago kirjinta tana sakin nishi, gaba dayanta ya dauketa ya saka"

"ajikinshi yana cewa,"

"""Ai dolema dama kiyi ciwon kirji... Kallifa yanda kayan nan suka matse ki , bari acire kawai"""

"Runtse idanuwanta tayi tana sake sakin wani nishin kamar gaske dan sai ka rantse da Allah ciwon takeyi irin sosai dinnan, baiyi wata wata ba yazuge zip din rigar yacire sannan yazuge na skirt din shima yacire shi kamar yadda yayi expecting daga ita sai pant yarasa meyasa bilkisu bata shiri da"

"bra kamar wacce take mintsininta, kasa kawar da kansa yayi yadai yi kasa da murya yana cewa,"

"""Zaki sha maganine infita insamo miki?"""

"Kai ta girgiza masa cikin dakiya da muryar wahalar ciwo tace,"

"""A'a.... Kayi massaging dina may be i will be ok. """

Babu bata lokaci yafara abinda tace amma kuma bai dade da farawar ba shi kansa yaji al'amarin

"yafi karfin daurewa irin tashi shiyasa kafin ya farga har yasoma shiga cikin wani yanayi, daga shi har ita yau kowa yabaje basirarsa wurin kulawa da dan uwansa da samar masa da nutsuwa, bilkisu"

"kam kasa kallonsa tayi daga karshe ma ta tsiri baccin karya tana jinsa yana yimata magana akan tatashi tayi wanka amma tayi shiru. Yau kam tayi baccinta cikin nutsuwa domin tasamu abinda take muradi dan ko juyi batayi ba saida asubah tayi sannan fahad yatasheta, wanka tayi tai salla shikuma fahad yafita masallaci, abin mamaki lokacin da yadawo kwance ya isketa kan rug din salla tana faman haki da nishi kamar wacce tayi race, yanzunma abinda yafaru daren jiya shine yasake faruwa, shar da ita ta shirya ta shiga cikin kitchen bayan takashe kan 80,tana tsaka da soya doya fahad yafito cikin shirinsa, manyan kaya yasaka shadda ash colour amma babu hula, a kofar"

"kitchen din yatsaya yana dan kasa da idanuwanshi, daga ita harshi kunyar juna sukeji ta lura,"

"""Good morning sweetheart """

"Taji yafada ahankali,"

"""Morning, how was your night """

"Jin abinda tace yasashi dan murmushi yana shafa keya,"

"""It was amazing. """

"Shiru tayi tana dan murmushi batareda ta kalleshi ba,"

"""Yanaga kafito bayan gashi ina preparing break fast?"""

"Dan satar kallonta yayi suka hada ido,"

"""Ni ai azumi nake. """

"Dariya abinda taji yafada tayi tajuya ta kalleshi,"

"""Dama ana daukar azumi bayan alfijir ya keto?, malam bakada azumi kawai katsaya kayi"

"breakfast"""

"Murmushi yayi ya karasa shiga cikin kitchen din yatsaya abayanta yana taimaka mata, tare suka zauna sukayi breakfast din sannan yafita, tun da tasamu wannan dabarar shikenan kullum da ita take aiki babu dare babu asubah sannan babu rana sai yanzu take gasgata maganar khulsum da take cemata itafa ta godewa Allah da tasamu yaro sharaf ta aura wallahi zataji dadi domin duk lokacin da take son kasancewa dashi zai saurareta kuma bazai kosaba amma manyan mutane sai ahankali ga shekaru ga basir duk yagama dasu, yanzu kam ta yarda 100% auren yaro akwai advantage aciki kamar yadda shima auren babban akwai nasa advantage din. Koda fahad yakoma makaranta ma baya sati daya baizo gidaba saboda Bilkisu domin baya son ta bukaci wani abu shikuma baya nan, kullum yana hanyar kano wani abun mamaki har lokacin shi bai san ciki gareta ba. Ranar da yayi wani zuwa da yamma yan uwan husna sukazo suka kwashe kayanta ita bilkisu ma lokacin bata nan tana wurin aiki saida tadawo ta iske falon yayi wani fadi duk sai taji babu"

"dadi, fahad ta kalla wanda ke aikin goge mata tiles din dake cikin falon saboda yau haka tafita bata"

"dauke ko tsinke acikin gidanba,"

"""Wai bazaka dawo da husna ba kenan? Haba kai kuwa anayin fa fiyeda hakama kuma adawo"

"ashirya.... Dan Allah kaje ka dawo da ita..."""

"""Bakiga laifin da tayi min bane?, to be honest with you, she highly disappointed me and ban jin"

"zan sake zama da ita gaskiya """

"""Duk da haka u have to be patient... U have to forgive her... Remember bature yace without sins"

"there is no forgiveness.... Dan Allah kayafe mata..."""

"Tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa can yanisa yace,"

"""Ai yanzu ba laifina bane, itace lokacin da taje gida ta hada karya da kareraye ta fadawa mahaifinta shikuma yayi fushi akan wai zaluntar yarsa nakeyi dan haka tagama zaman aure dani...."

Kin gani da ace time din ta fadi gaskiyar abinda yafaru may be idan aka bani hakuri bayan na huce zan iya dawo da ita amma sai taje ta harhada karya ta fada. Gashi dai tana sona tana son zama

"dani har gobe amma babu hali Aurena da husna kawai mubarshi a matsayin kaddara"""

"""Allah yasa hakane yafi zama alkhairi """

"Daga haka ta mike tashiga bedroom din tausayi taji yabata saboda ganin yanda ya gyara dakin ya kintsa komai harda su turaren wuta, gaskiya fahad abokin rayuwa ne yanada halin manya komai nagidan yayi mata harda su wanke wanke, washe garin ranar yaje yasiyo babbar katifa mai round kamar gado yasaka adakin husnah ai bilkisu nagani tafara daure dauren fuska wato raba daki zaiyi da ita da zai wani kama yasiyo katifa? Wallahi bazai yuyu ba ai kuwa bai yuyunba, kwanansa biyu yakoma Kaduna bai dawoba sai ranar da ake sunan matar ya Abba wato nusaiba wacce ta haifi yaronta namiji, kasancewar exam yakeyi saida ya dan samu interval sannan yadawo gida sai ranar yasan bilkisu nada ciki saboda cikin yafito sosai ita kuma tasake kiba tubarkalla gaba daya kayanta sunki shiga dan dakyar tasamu doguwar rigar da ta shigeta, bra kuwa duk sunyi mata"

"kadan sai wata kwaya daya itace take iya sawa itama tana dawowa zata figeta ta yar,"

"""Wannan rigar ai ta matseki..."""

"Cikin jin haushi ta kalleshi,"

"""To ya zanyi? Kana ganima ahakanma ita kadaice ta shiga jikina"""

"""Allah yabaki hakuri, fito mutafi"""

"""Amin"", tafada cikin fada, dogon hijabi tasaka tafita suka tafi yana rakata gidan sunan yawuce kasuwa kananan atamfofi yasiyo mata guda shida yawuce shago duk ya yankasu ya dinka mata doguwar riga samfarin maternity saboda duk na cikin lefenta masu tsadane bazai yuyu abata ba."

Tunda cikinta ya tsufa fahad ke cikin zulumi sai kace shine mai haihuwar kullum addu'arsa Allah

"yasa kafin yakoma makaranta ta haihu, cikin ikon Allah yana gida suna tsaka da bacci ta tashi da daddare saboda azabar ciwo, tashinsa tayi sai faman ciccije baki take yi tana cemasa bayanta da kwankwasonta ciwo, gaba dayama rasa abinda zaiyi yayi daga karshe yakira mamuh yafada mata lokacin karfe 2 nadare, kafin su mamuh suzo duk ta jigata sai faman rokarshi gafara takeyi wai ya yafe mata mutuwa zatayi duk ta rudashi hankalinsa yatashi,bai taba sanin haka mata ke wahala ba wurin haihuwa sai yau lallai duk dan da baibi mahaifiyarsa ba yayi asara domin wahalar haihuwa kadai abar dubawa ce. Su mamuh na zuwa suka wuce asibitin haihuwa mafi kusa amma na kudi, c s za ayi mata saboda bazata iya haihuwa da kanta ba, acikin daren aka yimata aka ciro santaleliyar jaririya mai kamada fahad sak, komai na yarinyar irin nashine ba tayiwa bilkisu karar ko farce ba, mamuh nata faman tsokanarshi amma yaki kulawa saboda shifa ta matarsa yakeyi, da yake anyi aikin cikin nasara lafiya lau bilkisu ta farfado washe gari duk yan uwa suka cika asibitin amma banda ammah ita kam har aka sallamesu ana igobe suna bata zo ba. Ranar da suka koma gida bayan angama yiwa jaririyar wanka tanata faman tsaga kuka mamuh tace Bilkisu ta dauketa tabata tasha, daya dakin tashiga wanda fahad ke ciki domin nata su maama ne cike harda khulsum da sauran yan uwan fahad, yana kwance yana dan baccin gajiya, jin kukan baby yasashi tashi yana tambayar bilkisu mai yasameta? Zama tayi gefen katifa tana kokarin shayar da babyn, ido ta runtse"

"tana cije lips saboda zafi tarasa wannan zafin ko na menene,"

"""Sannu baby... Tsaya in tayata"""

"Banza tayi dashi ashe shikuwa da gaske yake dan shima matsawa yayi ya dan janye kafafun babyn ya dora kansa bisa cinyar Bilkisu, tarasa sai yaushe fahad zai daina fitina, tashi tayi tafita ta mayarwa da mamuh yarinyar domin za agasa mata cibiya, yana kwance adaki yana jin mamuh na yimasa dan biki tana cewa ina sabon shiga masu 'ya wanda dan za ahuda mata kunne harda kwallarshi?. Washe gari aka radawa yarinya suna Bilkisu dan fahad yace tunda yaga wahalar da bilkisu tasha wurin haifar yarinyar nan dolene yasaka mata sunanta, su meenah ne suka zaba mata sunan da za arinka kiranta dashi wai Hanfa, washe garin ranar da akayi suna yakoma makaranta yabar bilkisu anata kwaskware kwaskware dan gyara jiki shikam yana cike da farin ciki yanzu baida aiki sai na dora hoton yarshi akomai nashi shiyasa bilkisu har tafara kishi, ada ita yake kira da baby amma yanzu tunda yasamu wannan jaririyar yamaida sunan kanta. Bayan sunyi arba'in harda wasu kwanaki yazo tunda yazo yakama yarinyar ya nanuke ajikinshi bilkisu duk haushi ya isheta daga karshe

41 / 42