KAMAR DA WASA BY UMMI A’ISHA

Author :  Ummu Hairan Category :  Love

Chapter   30 / 42

87K to 90K   out of 124.3K words

domin yanzu tagane yagama rainata tsaf sam baya ganin

"girmanta gashi duk maganar da tazo bakinshi sai yafada mata sai kace wata mate dinshi,"

"""Ni Bilkisu naga takaina.... Wannan wacce irin rayuwa ce..."""

"Haka taketa fada cikin kuka har tsawon wani lokaci, saida tagama kukanta ta share sannan tashiga wanka tafito duk sai faman kumbure kumbure takeyi ita kadai ahaka su ammah suka dawo suka sameta duk bata da cikakkiyar walwala sai cika take tana batsewa ita dai ammah idone nata batace"

uffan ba.

"Washe gari awurin aiki khulsum tabi ta dameta akan takira fahad ta tambayeshi idan yabarta sai su wuce duba Christy basai sun koma gidaba saboda idan suka bari aka sallameta har tadawo aiki ba karamar kunya zasu jiba, agaba khulsum tasata da naci dole ta tashi tafita waje itafa bama ta da no"

"dinshi dan rainin hankali, maama takira tana dagawa tace,"

"""Maama kinada number din wannan dan rainin wayon ko?"""

"Dariya maama tayi tana cewa,"

"""Adda labour amarya. """

"""Maama ban son rashin kunya ina tambayarki kina yimin wasa..."""

"""Wai number waye kike tambaya?"""

"""Ban saniba ai kin san wanda nake nufi munafuka, kituro min yanzu"""

"Daga haka ta katse wayar takoma wurin khulsum, babu jimawa taji text yashigo sake tashi tayi"

"tafita har khulsum na tsokanarta tana cewa,"

"""Ohh su labour yau lobayya ce ta motsa koda yake ai amarya kike..."""

"Bata kulaba tafice takira number fahad tanata ringing amma ba adaga ba harta katse, sake Kira"

"tayi anan kuma sai aka daga amma ga mamakinta sai taji anyi shiru, ahankali kamar bata so tayi magana,"

"""Hello... Idan natashi daga aiki zanje dubiya """

"Kafin takarasa taji wata zazzakar murya tayi magana,"

"""Sorry mai wayar baya nan idan yadawo zan sanar dashi "" Batare da jiran amsar da zata bayarba"

"kawai taji ankashe wayar, wani kululun bakin cikine ya tokare mata kirjinta kawai sai taji tana dana sanin kiran da tayi masa, shine dan walakanci zai barwa mace wayarsa? To ko wannan din itace wannan yarinyar da suke yin waya da ita? Kai ba ita bace, ita can ai tasan muryarta, ita dai"

tasan mutane da yawa suna yaba baiwar muryar da Allah yayi mata but gaskiya ta wannan har tafi

"tata zaki da taushi da kuma sanyi domin kana jin muryarta kasan irin matan nanne da suka yi nutso cikin kogin daula jin dadi da hutu ya ratsa ko ina ajikinsu su akewa kirari da hurul aini na duniya,"

"Tsaki taketa ja tana kwafa tarasa ina zata saka ranta taji dadi amma fa abisa dukkan alamu ita wannan dinma babbace domin kamar zata girmeta, shiru tayi tana tunani, itafa takanas mutane suke wanko kafa suzo gidan radio ganinta saboda kawai dadin muryarta da sukeji to amma muryar"

"wannan ko ita mace saida tajita har cikin kwakwalwarta, to wacece ita? Meye hadinta da fahad?"

"Kafin tasake yiwa kanta wata tambayar da batada amsarta khulsum tafito rikeda hand bag dinta,"

"""Labour yadai?"""

"""Nothing, na kirashi ne ban sameshi ba shine nake jira ko zai kira..."""

"""Ok to kafin kugama bari naje nayi voicing din report din can... Ke kinyi nakine?"""

"Girgiza kai tayi cikin sanyin murya da na jiki gaba daya tace,"

"""A'a ni koma fassarar banyiba tukunna... Jeki kiyi nakin kawai """

Daga haka takoma cikin office ta zauna tasoma juyawa kan kujerar da take kai.

FAHAD

"Sosai Bilkisu taso rikita masa lissafi yau saboda kusancin da sukayi har yayi yawa jinta ajikinshi tana half naked yasaukar masa da wata irin kasala da sha'awarta mai karfin gaske amma koda yatuna ta auri wani kafin shi ahalin yanzu sai duk yaji bacin rai da bakin ciki sun rufeshi wadanda sune sukayi sanadiyyar gushe sha'awar data taso masa shiyasa ma yabar wurinta babu shiri yanufi gida, dakyar da sauraron karatun kur'ani yasamu yaji daidai. Washe gari dayaje asibiti sunada tarin ayyuka masu wahalar gaske wadanda zasuyi shiyasa dole sai mutum ya nutsu sannan yayi taka tsan tsan wurin fitar da result din, office din Dr murja yashiga yakai wayarshi da laptop domin suna yin good time da ita tana mutukar ji dashi duk cikin daliban da aka turo babu kamarshi awurinta shiyasa sauran students din ke zargin wai sonshi takeyi gashi ahaife ma zata girmi Bilkisu matarshi, system dinshi yasaka a charge ita kuma wayar yabata ajiya yafita shiyasa lokacin da bilkisu takira bata sameshi ba Dr murja ta daga, bai samu kanshi ba sai around 3 duk agajiye yake yashiga office din Dr murja yakarbi wayarshi da laptop domin tafiya gida, har zai tafi"

"yaji tace,"

"""Soul mate takiraka..."""

"""Ok tom zan kirata"""

"""Wacece ita?"" Tafada bayan tazuba masa gaba daya idanuwanta wadanda take juyasu cikin salo na"

"daukar hankali shi wallahi kunya ma yakeji idan tana yimasa wannan farin,"

"""Anty wife dinace fa..."""

"Yafada yana shafar kai, juya idanuwa tayi ta shagwabe fuska,"

"""Ashe kanada aure shine ban taba saniba?"""

"""Wallahi inada aure """

"""To amma tana kula dakai? Zo kafada min mana handsome..."""

"Dariya yayi cikeda kunya yafice daga cikin office din, tun yana cikin asibitin yake faman kiran wayar Bilkisu amma bata dauka ba kuma tana zaune tana fassara labarai amma taki dauka tana kallon wayar har tayi tagama bata daga ba ita tarasa dalilinta na jin mugun haushinsa yau fiyeda kullum. Wannan dubiyar dai bataje ba sai khulsum ce tatafi ita kuma tawuce gida tana zuwa gida taci abinci tayi sallar la'asar takira Abba ta gaidashi sannan tawuce toilet, wanka tayi tafito tashirya cikin kayan shan iska riga armless zuwa gwiwa da wandonta duk light purple, ta dauko system dinta ta fita zuwa dakin ammah da wayarta ahannu tana zama wayar tasoma ruri sam batayi niyyar dagawa ba saboda tasan ko waye amma sanin ammah na iya yin magana yasata"

"dauka,"

"""Ke wato shine zanyita kiranki amma dan rainin wayo ki k'i dagawa ko?"""

"Jin abinda yace yasata tashi sim sim tafita daga dakin amma zuwa nata,"

"""Ba dake nake magana ba...?"" Yafada cikin tsawa,"

"""Kaga malam ya isheka ni kar kayi min ihu aka, borin kunya kakeyi ba komai ba kuma wallahi sai kafadi wacece matar da ta daga wayarka lokacin da nakira idan bahakaba har kunnensu abba"

"maganar nan dan bazan iya zama da mai kula mata awajeba. """

"""An kula matan kiyi duk abinda zakiyi Meye naki aciki dan nakula mata? Kabarinmu dayane"

"dake? Ban son shisshigi """

"""Wallahi duk wadannan maganganun akunnen abba, mayaudari kawai """

"Daga haka takashe wayar gaba daya komawar da batayi dakin amma ba kenan, tun daga ranar rigima takice taki cinyewa har tsawon makonni biyu suka dauka suna wannan fadan ta waya domin bai samu zuwa gidan ba ita ta damu akan lallai sai yafada mata alakarsu da matar da ta daga wayarta lokacin data kirashi acewarta tana gudun sake facing irin abinda hamood yayi mata yadauko karuwa ya ajiye mata azuwan matarshi ce ita tunaninta kenan amma sam bata taba zargin"

"kanta da yin kishinsa ba, shikuma hakan da take ta fada ne yake bata masa rai shiyasa yau"

yashirya zuwa gidan domin ayita takare.

"Sai bayan da yayi sallar magrib sannan yaje gidan, kamar koda yaushe iya amma yasamu falonta tana kallo kasancewar mai aikinta tatafi, tashi yayi yafita cikeda kunya zuwa dakin Bilkisu wacce"

"ke zaune kan abin salla, yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da tasbihinta,"

Agefen gadonta ya zauna harda kwanciya tana ganinsa bata tanka masa ba text yake turawa shiyasa shima baiyi magana ba bayan mintuna biyu da tafiyar text din saiga kiran husnah dama ita

"yaturawa yana yimata barka da shan ruwa kasancewar yau alhamis,"

"""Husnah ta....kinsha ruwa lafiya..."""

"Kamar acikin mafarki Bilkisu taji tace,"

"""Ya fahad bayan azumin karyewa yayi bayan sallar la'asar saida nagama shan wahalat """

"Bai karasa jiba yaji bilkisu taja tsaki da karfi tamike tana nannade prayer rug dinta,"

"""Malam idan kagama karufe min kofar bayan kafita"", ganin dagaske fitar zatayi tabar masa dakin"

"yasashi ajiye wayar yamike dasauri yasha gabanta,"

"""Wai me kike nufine? Karfi da yaji nema kikeyi ki goga min kashin kaji ko bakin fenti """

"""Allah ko?"""

"Matsarta yayi yana kallonta fuskarta gaba daya babu annuri,"

"""Wai ke mai kike nufi? Dan kawai kinji mace ta dauki wayata? Waima ina ruwanki ne, budurwata ce wadda zan aura sunanta Dr murja medical Dr ce a asibitinmu she's 35 years old, ita kuma wannan husnah ce itama budurwata ce nurse ce yanzu haka tana yin bsc nursing dinta a BUK she's"

"22 years old nanda yan watanni zan aureta,sai me kuma kike son ji ?"""

"Ita kanta a lokacin nan tasan bata cikin nutsuwarta bata san dalili ba, cikin fushi da bacin rai tace,"

"""To kasan kana da duk wadannan meye naka na damuwa da lallai saika aureni? Ai da sai kaje"

"kazauna dasu..."""

"Murmushin rainin hankali yayi mata yana jan dan gemunshi na rashin kunya,"

"""Waye yadamu saiya aureki? Ni? Lallai """

"Afirgice ta kalleshi cikeda mamaki, idanuwansu ne suka sarke da juna cikin fada tace,"

"""To ai ba adole. Kana iya sawwake min kowa sai yahuta tunda bakaine ka damu da aurenba"""

"""Hmmm Bilkisu kenan. !"""

"Haushine da mamaki suka sake kamata har ta daga kai ta kalleshi akaro na biyu, har lokacin yana"

"wasa da gemunsa,"

"""Da kike cewa in sawwake miki da nine na aureki? Ai bani na aureki ba ina zaman zamana aka ce an aura min ke, tunda bakida ra'ayi kamar yadda nima banida interest akai kina iya zuwa kisamu"

"wadanda suka daura kisasu su warwareshi "" Yakarasa maganar yana daga kafada,"

"""Ni kake fadawa haka?"""

"""Yes ai gaskiya nafada miki ni ban nemi aurenki ba sadaka aka aura min saboda ance wannan"

"tsohon dan duniyar yaudararki yayi daga karshe ya sakeki..."""

"Kwallace taciko mata ido takai hannu zata dakeshi yarike yana yimata murmushi mai kona zuciya,"

"""Fahad sakeni... Ka sakeni ko ana aure dole ne?"""

"""Oho ni nasani ne? Nima ai dolen aka yimin tunda inada wadanda nakeso aka tashi aka bani matar"

"sadaka"""

"Wannan Kalmar ba karamin kona mata rai tayiba dan har saida tanemi sliver abakinta tarasa saboda dimuwa wai ita yakirada matar sadaka, shikuwa gegewa yayi ta gefenta yadauki wayarshi yafice nan ta durkushe tasoma kuka, tunda tazo duniya bata taba jin bacin rai irin nayau ba, tamkar zata mutu haka takeji, kwana tayi tana kuka wannan dalilinne yasa dasafe ta tashi da matsanancin zazzabi da ciwon kai sai kakkarwar sanyi take yi ga wani irin lafiyayyen ciwon kai asibiti ammah tasata agaba suka tafi suna zuwa akace jininta ne yayi kasa bama hawaba kasa yayi nan aka bata"

gado sai rawar jiki takeyi idabuwanta faful da hawaye duk sun kumbura.....

*_Ummi Shatu_*

*me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*

"45***Taimakon gaggawa aka fara neman bata domin inbanda kadawa babu abinda jikinta keyi kamar wacce ke tsakiyar kankara, bayan kamar wasu mintuna wadanda bazasu gaza 30 ba nurses din suka zo wurin ammah suna yimata bayanin yakamata fa suje su samo jini saboda su basuda shi anan, duk da ammah bataso ta sanarwa su Hindu to amma babu yadda za a yi dole sai sun sani, wannan gayawa wannan da haka duk zancen ya yadu a junansu babu bata lokaci duk suka yiwa"

"asibitin tsinke,text maama ta turawa fahad amma kasancewar yana cikin lab yana aiki bai ganiba."

"Tun abinda yafaru jiya tsakaninsa da Bilkisu da zarar yatuna sai yayi murmushi ita daukar kanta takeyi watta babba bayan shikuma awurinshi mararbarta da jaririya kadanne gaba daya yagama rainata sanine bata gama yiba, dayake yau juma'a manyan kaya yasaka saboda ta can zai wuce masallaci, duk da cewar karshen makone hakan bai hanasu samun ayyuka da yawa ba shiyasa bashi yasamu kansa ba saida lokacin sallar juma'a yayi. Har saida yafito daga salla sannan yaga text din maama tana sanar dashi Bilkisu babu lafiya sannan ana bukatar jini, harda kwatanccen asibitin da take kwance, batare da yakoma asibiti ba yawuce inda maama tafada masa an kwantar da Bilkisu, wani dan karamin asibitin kudine dake nan unguwar tasu sai dai da dan tazara tsakaninsu da gidansu, a reception yaga meenah wacce taje kiran wata nurse wadda zata auna jinin"

"mijinta aga ko zaiyi daidai da na Bilkisu,"

"""Ya fahad sannu da zuwa..."""

"""Yawwa meenah, ya mai jikin?"""

"""Dasauki tana ciki muje"""

"Tare suka karasa wurinsu ammah wadanda ke tsaye akofar dakin da Bilkisu take harda mijin meenah ganin fahad yasa amma gyara lullubinta suna gaisawa kuma tawuce tabar wurin, shi dinma hakan yafi sakewa shiyasa yasamu damar cemusu abar jinin mijin meenah shi sai adebi nasa dan baya ko tantama nashi zaiyi mata saboda shi jininsa irin wanda zai iya bawa kowa ne, tare suka tafi lab da nurse akayi komai da yakamata aka debi jininsa leda daya da rabi bai samu tashi ba awannan lokacin ya dan kwanta sai bayan kamar mintuna ishirin sannan yatashi yana dai dan jin jikinsa babu karfi but babu wani jiri ko hajijiya, wurinsu Hindu yakoma dama sunata zuwa suna lekashi suna komawa, suna zaune su uku daga Hindu sai maama sai meenah ammah tatafi gida da yan jikokinta haka shima mijin meenah yatafi, sannu suke tayi masa yana amsawa shi"

"idanma banda yar yunwar da yakeji ai da zai dan jima a asibitin,"

"""Tafarka ne?"" Ya tambaya yana kallon kofar dakin da Bilkisu ke ciki,"

"""Ehh amma yanzun dai gaskiya bacci takeyi...amma ai zaka iya shiga"""

"Juyawa yayi yashiga, tana kwance tayi fayau da ita ana kara mata jinin wanda har guda dayan yakusa karewa, jingina yayi ajikin bango ya harde hannuwanshi akirjinshi yana kallonta, hijabi ne ajikinta saboda sanyi sai doguwar riga ta atamfa, fuskarta ya kalla yaga ta wani bata fuska kamar"

"irin idonta biyun nan ba bacci takeyiba, murmushi yasaki mai kayatarwa sannan ahankali yafurta,"

"""Hajjaju ana fada da jinina kenan. """

Ahankali yakarasa gaban gadon duk fuskarta akode amma idanuwanta luhu luhu akumbure ga

"bakinta ya bushe sosai irin yadda yake yi dinnan idan mutum yana cikin halin jinya,"

"""Am very sorry soul mate... Nasaki kuka ko? Am sorry kiyafe min. """

"Kamar tana jinsa yaga tasake bata rai harda dan turo baki,"

"""Are we fighting?"" Yafada yana murmushi, bakin da ta dan turo yakai nashi kai ya tsotsa sannan"

"yadago yana murmushi,"

"""Ai nace miki am sorry.... Stop fighting with my blood Mana baby I said am very sorry about"

"what i did... Pls forgive me kinji.... Ki yafewa dan kaninki !"""

"Goshinta yayiwa light kiss sannan yasake yiwa lips dinta wadanda ada suke abushe amma tun lokacin da ya tsotsesu suka dawo kamar anshafa musu lipstick, sakin hannunta yayi wanda da"

"yakama yana murzawa cikin nashi saboda tsabar taushinsa,"

"""Tunda kin ki hakura am going, anjima zan dawo kinji """

"A kumatu yasake bata wani kiss din sannan yatashi yana kallonta murmushi yasake yi saboda yadda taketa hade rai tana motsa baki kamar mai yin fada alhali kuma bacci ma takeyi yasan abinda ke zuciyarta ne taketa amayoshi lokacin baccinta. Da baya da baya yake tafiya yana murmushi har lokacin idanuwanshi na kan fuskarta, saida yazo daf da bakin kofa sannan yayiwa tafin hannunshi kiss ya hura mata, ganin yana kokarin juyowa yasa su maama dake leke ta glass din kofa saurin guduwa kowaccensu kunshe da bakinta dan kar yaji, bude kofar yayi yafita yana"

"kallon su maama wadanda ke tsaye cirko cirko kamar marassa gaskiya,"

"""Maman hudah lafiya dai ko?"""

"""Lafiya lau ya fahad, mun dan fita ne dawowarmu kenan..."""

"Dan bata fuska yayi sannan yace,"

"""Ku da kuke da patient ina kuma zakuje dan Allah?"""

"""Ahhh ya fahad bafa nisa mukayi ba..."" Inji Hindu,"

"""Nidai dan Allah ga amanata nan zanje gida idan huta anjima zan dawo, pls and pls ku kular

30 / 42