Author : Binta Umar Abale Category : Romance
bana tunanin zai amince ya kawo mu nan mu zauna ke ko gidan Alhajin da kike magana ba zai barmu muje ba duk da cewa gidansu ne."
Naja'atu shuru tayi tana tunanin al'amarin Babu shakka zaman Saddiqa da Mussadiq hannun Halisa gagarimun had'ari ne zata iya cutar dasu ta ko wace siga! Itace zata rike su tamkar uwarsu, to ita kuwa ko a mafarki bata tunanin zata koma gidansu a matsayin matar mahaifinsu, insha Allahu ta bar gidan har abada.
Ganin Saddiqan ta tsura mata ido yasa tace"To ki kwanta kiyi bacci zanyi tunani kan maganar ki." Saddiqa taji farin ciki ya rufe ta tace"To shikkenan Yaya Naja'atu nagode Yaushe zaki gama tunanin."? Kallonta tayi na minti biyu tace"Ke dai tunda nace zanyi to zanyi duk hukuncin dana yanke zan fada miki."
Saddiqa tace"To Ubangiji Allah yasa naji alkairi." Amin tace a takaice, Saddiqa ta juya ta kwanta tana adduar Allah yasa ta amince da maganar ta.........
Tsuru tayi ta tsirawa guri guda ido tana tunanin yanda za tayi ta rusa wannan gagarimin al'amarin daya tunkaro ta, kira ne ya shigo Wayarta dake gefanta, ta dauka hannu na rawa, a kunne tasa wayar, ta fashe da kuka 'kasa-'kasa tace"My prince kaji abunda Abbah Abbas ya 'bullo dashi ko.''
Salim dake kwance kan katifar sa yace." Menene ya faru ni banji komai ba." Juyawa tayi tana kallon bayanta, dan bata so tayi wata magana ya kasance Saddiqa taji, sai da ta tabbatar da bacci takeyi sannan ta sake sassauta murya ta shiga fada masa abinda ke faruwa.......Mi'kewa zaune yayi da sauri! lokaci guda gumi ya tsatstsafo masa, yace."Da gaske kike wannan maganar ko kuma dai tsokanata kikeyi."?
"Humm! wane irin tsokana wallahi tallahi da gaske nake wai Abba Abbas shine ya bude bakinsa yake fadawa su Baba malam yana so ayi masa *MADADI* dani!!!
Katifar da yake kai ya doka! da hannunsa da 'karfi! Yace." Kai kaji wata tatsuniya! shi yanzu dan girman Allah baiji kunyar fad'ar wannan maganar ba!!? To shin wai ko ya manta abinda yake tsakanina dake ne da har zai bijiro da wannan tatsuniyar."
Tace"Oho! ni gani nake kawai san zuciya ne yama za'ayi yace haka bayan shi da bakinsa ne yace."Mu daidaita kanmu zai daura mana aure kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da matarsa sai yace a mayar masa dani a *MADADINTA."*
Salim yayi wani murmushi na takaici yace."Ke nifa na daina mamaki! wallahi zai aikata dama yanda yake wani kula dake da wani takatsantsan a kanki akwai alamun tambaya dama so yake matarsa ta mutu ya aure ki! saboda haka ni kuma wallahi bazan bar masa ba, to in banda ma rigima ina ke ina shi! shekara hamsin har yake tunanin auran yarinya 'yar 'karama kamar ki 16years fa to idan ya aure ki yayi yaya dake? mtwwss."!!
"Humm! ni wallahi Salim mamaki ma ya hana ni nace komai ba kaga yanda su Baba malam suke murna ba, wannan ai tauyewa mutum hakki ne. Ni duk na rasa ma yanda zanyi."
Yace."Kece kuwa kike da yanda za kayi, tun kafin yafiya tayi nisa ki kokarin ganin kin rusa maganar ni kuma gobe idan Allah ya kaimu idan naje daukarshi domin zuwa kasuwa zanyi masa magana akan inaso yazo gurin Baba malam kan maganar auramu sai naji me zaice."
Tace"To yauwa kayi masa hakan nasan dole kunya tasa ya kasa magana ni wallahi duk mutuncin sa ma ya zube a idona mtssssw!!! Takarashe maganar tana jan tsaki!
Yace."Baby ki daina wani damuwa ki kwanta kiyi bacci bazan bari wannan al'amari ya tabbata ba, duk yanda zanyi to zanyi na rusa al'amarin.
A sanyaye tace"Tom shikkenan my Prince kayi bacci mai dad'i kaji ko." Yace."Ke ina wani maganar bacci mai dadi a gurina Wannan dattijon na nema yasa zuciyata ta buga."!!
"Hummm! kawai tace dan ta rasa ma abin cewa, kashe wayar tayi ta zurfafa cikin tunani da nazari! gabad'aya bata so tayi masa rashin kunya saboda shi mutum ne mai muhimanci a gurinta to amma tunda ya 'bullo da wannan maganar kashi hamsin na 'kima da mutuncinsa suka zube a gurinta.
Numbarsa ta laluba ta dinga kallon numbar kamar shi take kallo, shawara take da zuciyarta shin ta tura masa text ko kuwa, wata zuciyar tace" Idan kika tsaya lako-lako kan wannan al'amarin to za kiyi kuka da idonki.......Da sauri ta shiga rubuta masa text kamar haka.
_Assalamu alaikum Abba nmu barka da dare ina tafan kana nan lafiya? Abbah wata magana naji daga bakinsu Baba malam kuma sun ce kaine kazo musu da maganar shine nake so naji daga bakin ka._
Tana tura masa text din ta kashe wayar! kwanciya tayi tana takure jikinta hawaye ne ke kokarin 'kwace mata tana kokarin hana shi fita.
Sai bayan da ya dawo daga sallahr asubahi ne ya kunna wayar tasa, aikuwa text din ne ya shigo yayi saurin bud'ewa yana dubawa............Ya karanta ya kai sau biyar ya girgiza kanshi! lallai To bata yarda ba kenan tana so taji daga bakinsa, shi kam bai san abinda zaice mata ba, kawai sai ya share bai mayar mata da amsa ba, ya cire jallabiyar jikinsa, ya kwanta rigingine kan bed din yana tunanin rayuwa, Halisa ce ta shigo dakin jikinta sanye da hijab kamar wata mutuniyar arziki, tun bayan mutuwar Halimatu wata shiriya tazo mata takeyi komai cikin rashin kuzari.
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*8*
Tana tashi da asubah ko sallah ba tayi ba ta dauki wayarta ta kunna ta shiga dubawa wai ko ya turo mata da amsa, wayar ta kai minti goma a hannunta tana jiran shigowar replay dinshi bai shigo ba, a sanyaye ta mike ta fita domun daura alwala, tana shigowa dakin ta sake daukar wayar tana dubawa, ganin alamun shigowar sa'ko yasa hannu na rawa ta bud'e! tsaki! mai 'karfi taja ganin messege din daga *Mtn* ne, jefar da wayar tayi kan katifa, idanunta na kokarin kawo ruwa ta shiga tayar dasu Saddiqa daga baccin da suke.........Suna bude ido tace"Ku tashi kuyi alwala kuyi sallah." Saddiqa ta sauko da sauri ta bude akwatin kayansu makilin da brush ta dauka ta fita domin daura alwala.....Cikin tsawa ta kalli Mussadiq kamar shi yayi mata laifin tace"Kai ba zaka tashi ba sai na gaggaura maka mari ko."! Yaron ya tashi a furgice yana kallonta! da hannu ta nuna masa 'kofar fita tace"Kaje kayi alwala gari ya waye." sakkowa yayi daga katifar shima ya dauki abun wanke baki ya fita.
Hijab ta zura ta gyara dadduma ta tayar da sallah, Tana idarwa ba tayi wata adduar kirki ba ta sake daukar wayar tana dubawa, har yanzu dai babu amsa! Tsaki ta dinga ja zuciyarta na wani irin tafarfasa! babu shakka Abbah Abbas da gaske yake! tasan yaga text d'inta kunya ta hana shi bata amsa shiyasa ya shareta.
Numbar Salim ta laluba ta shiga kira. sai dai wayar a kashe take dan bai tashi ba ballanta ya kunna wayar......Mi'kewa tayi ta koma bakin katifar ta zauna had'e da cire hijab din jikinta, Numbar Abbah Abbas din ta sake nema ta 'kara tura masa wani text in kamar haka.
_Abba ina jiran amsa nasan dai kaga text d'ina dan Allah ka bani amsa shin kaine ka nemi aure na? ko kuma su Baba malam ne suka baka ni."?_
Tura masa tayi ta tsirawa wayar ido tana adduar Allah yasa yayi mata magana.............Shi kuwa Abbah Abbas yana kwance Halisa na matsa masa a jikinsa yana lumshe ido baccin da ya tara kwana da kwanaki ne yake damunsa, tinda Halimatu ta rasu bacci da nutsuwa suka 'kaurace masa, mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa rayuwarsa, gani yake ma ba zai ta'ba samun mace tagari kamar ta ba, Yayi yun'kurin auran Naja'atu ne ba dan komai ba sai dan yasan ita d'in tarbiyyar Halimatu ce yana kwadayin ta zama matarsa domin hausawa suna cewa gida bai 'koshi ba to ba za'a bawa dawa ba, bayan haka kuma yana tausayawa 'yan 'ya'yansa sosai saboda yanxu suna bukatar mai kula dasu sun saba da mamansu sosai dole idan suka dawo gidan suka ga babu ita su shiga damuwa, amma duk rintsi idan suna kallon Naja'atu a gidan kuma a matsayin matarsa to zasu samu sassauci a tare dasu.
Babban abinda yake d'aga masa hankali acikin al'amarin shine! yanda zai tunkare su da maganar! Salim da Naja'atu gabadayan su bai san abinda zai ce musu ba, Salim bashi da Uban da yafi shi, hakan nan itama Naja'atu bata da uban da yafi shi, tabbas da zai iya hakura da ya hakura ya kyalesu sunyi auransu, amma ba yajin zai iya janye kudirinsa ba dan komai ba sai dan samun walwala da farin cikin 'yayansa guda biyu, saboda ya riga ya sani cewar babu wata mace da zai aura ta ri'ke masa su tsakani da Allah! shiyasa yake ganin auran Naja'atun shine yafi alkairi a garesu baki daya.
'Dan juyawa yayi ya d'auki wayarsa ya bud'e text din ya sake bud'awa domin ya sake karanta sai yaga wani ya sake shigowa, Ya bude idonsa sosai yana karantawa! Murmushi yayi wanda yasa Halisa kallonsa da sauri tace"Allah yasa alkairi ne naga kana murmushi." Kallonta yayi yana kokarin rufe wayar dan ganin tana le'ko da kanta tana so ta ga abinda yakewa murmushin, a hankali yace."Alkairi ne insha Allahu." Tace"To Allah ya tabbatar mana dashi, mikewa tayi ta fita daga dakin tana fad'in "Bari na shiga kicin na shirya abin karin kummalo." Ya bita da kallo Ba tare da yace mata komai ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta daga d'akin, tabbas idan Halisa taji wannan babban al'amarin akwai tashin hankali! ya riga yasan halinta da mugun kishin tsiya! uwa uba kuma tsakaninta da Yarinyar basa jituwa ko kadan yanzu yanda zai tunkareta da maganar yake tunani.......Kira ya shigo wayar dake hannunsa, koda ya duba numbar Naja'atun ce yayi serving da My doghtar! kamar kada ya daga sai kawai yayi 'kundumbala ya d'aga wayar yana d'an gyaran murya, kafin ma yace wani abu yaji shashshekar kunanta a kunnasa.
Jikinsa ne yayi sanyi ya sassauta murya irin yanda yake mata idan tana irin wannan kukan yace."Dota ya akayi kuka da sassafe kiyi shuru muyi magana ko."!! hanci ta sha'ka! zuciyarta sai tafarfasa take tace"Abba tun jiya na turo maka da text baka bani amsa ba kuma nasan ka gani dan girman Allah ka bani amsar abinda na tambayeka ko na samu zuciyata tayi sanyi."""" Jim yayi kafin yace."Kinga ni ban ga text d'inki ba ballanta na baki amsa amma kome kika rubuta min a text din ina sauraranki yanzu ki fad'a min."
Cikin rawar baki tace"Jiya bayan kasa Salim ya kawo mu gidan Baba Malam shine naji suna wata magana wacce tasa raina ya kusa futa daga jikina, ashe wai kai ba kaine ka haifeni ba , sannan babban abinda ya furgita ni yasa na shiga cikin halin damuwa da tashin hankali wai kaine da bakin ka kace musu su baka ni na zama *MADADIN* matarka da ta rasu, shine nake ganin kamar sune suke so suyi wannan had'in da bai dace ba! ai abun kunya ne ace wanda nake amfani da sunansa ako ina a matsayin mahaifina aji shine kuma zai aureni ina zan saka raina idan hakan ya tabbata."!! Cikin sar'kewar murya ta 'karasa maganar........Shuru yayi kawai yana jin saukar numfashinta a kunnansa bakinsa yayi masa nauyi gabad'aya ma ya rasa me zai ce mata.
Murya na rawa tace"Abbah wannan shurun da kayi yana nuna min cewar da gaske ne maganar daga bakin ka ta fito!!! Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! kaico da wannan furucin naka! Abbah! dan girman Allah ka janye wannan maganar da kayi, na rantse da Allah ba zan iya zaman aure da kai ba ni a matsayin Uba na dauke ka."
Tana wani irin kuka take masa maganar, Yaji jikinsa duk ya mutu! Gumi ne ma yake tsatstsafo masa kamar ba safiya ba, da kyar ya iya cewa" To naji maganar ki zanyi shawara a kai idan da akwai yuwuwar na hakura dake zan samu su malam d'in na fad'a musu duk shawarar dana yake, ki daina kuka haka kada ki janyowa kanki wani ciwon na daban." Tace"To Abbah ni da daina kuka ai sai naji maganar wannan auran ta rushe sannan zan daina kuka."!! Mamaki ya kama shi, da jin maganarta sai ma ta bashi dariya yayi kad'an kafin yace."Naja'atu me yasa bakya son na zama abokin rayuwarki."? Taji wani irin fad'uwar gaba jin abinda yace. Tace."Abbah Please ba girman ka bane dan Allah kada ka 'kara yi min wannan maganar kai ubana ne *Salim* kuma shine abokin rayuwata." Kishi ne ya kama shi jin abinda tace kawai sai ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan kashe wayar tasa, ta juya tana kallon Bayanta, Saddiqa da Mussadiq sun futa daga dakin tun d'azu! taji dad'in hakan, sai ta mike itama tabi bayansu dakin Baba Talatu.
Suna zaune a kusa da Baba Malam suna karyawa da kunu da kosai ta shiga da sallama a bakinta, a hankali ta tsuguna kusa da Baba Malam tana gaishe shi ya amsa cike da kulawa yana d'an nazarinta ganin idanunta sunyi jawur! yasa yace."Ya kwanan kuka."?
'Kasa tayi da kanta! Baba Talatu tace"Kina so ki janyowa kanki damuwa da ciwo da kinyi halin Halimatu da ba kiyi mana gardama ba, Halimatu komai muka umarceta dashi tana mana biyayya dai-dai gwargwado amma ke tun jiya ake magana daya dake, idan kika bujirewa umarninmu baki kyauta mana ba kuma baki kyautawa 'Yar uwarki ba, a yanzu babu abinda za kayi kisa ta farin ciki illah ki zama *MADADIN TA* Ki tallafi abinda ta bari gasu nan suna kallonki." Ta nuna su Saddiqa dake zaune.
Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abin cewa ba kawai dai bata son suyi ta sa'insa da iyayenta.....Baba Malam dai shuru yayi ya dauki kofin kununsa yana sha yana had'awa da kosan sa dake cikin wata silba dake gabansa.
Saddiqa ce ta zuba mata kunun ta ajiye mata a gabanta sannan ta mi'ka mata abun da 'kosan ke ciki tace"Yaya Naja'atu gashi nan ki karya kema." Kallonta tayi sai taji zuciyarta ta tsinke! sosai yaran suke bata tausayi Saddiqa ta damu da ita sosai koda can bata son taga 'bacin ranta, tabbas a wannan lokacin ne ya kamata tayi mata sakayyar abun alherin data dad'e ta nayi mata.
Domin Saddiqar taji dadi yasa ta dauki kofin kunun tana kur'ba a hankali tana had'awa da kosan dake gabanta, Baba malam na gama karyawa sai ya dauki redion sa ya mike yana kallonta yace."Idan kun gama kun kintsa ku shiga gidan Alhaji dake dasu Saddiqa ku gaishe dasu." A sanyaye tace"Inasha Allah." takalmansa dake bakin kofa yasa ya fita daga gidan hannunsa ri'ke da redionsa.
Suna gama karyawa sai sukayi wanka suka shirya tsaf! Naja'atu da Saddiqa suka shirya cikin kaya iri daya hatta da d'inkin jikin atamfar iri daya ne komai iri daya Abbah Abbas ke musu baya bambamta su sai da gurin d'inki na Naja'atu yana d'ara na Saddiqa da wani abun, milk din hijabi toyobo ne a jikinsu ya sauka har 'kasa! Suna kokarin fita daga gidan da nufin shiga gidan Alhaji Sama'ila, Shi da Salim suna kokarin shigowa cikin gidan.
'Kamshin turaransa ne ya tabbatar mata da cewar shine Kafin ma tayi wani yunkuri sun shigo Shine a gaba Salim na take masa baya, Yana sanye da farar shadda kar 'Dinkin tazarce har kasa, da adon surfani a wuyan rigar da hannunta kansa sanye da farar hula mai ratsin 'baki! a zahiri idan ka kalleshi ba zaka ce ya kai shekarun da yake dasu ba, za'afi tunanin shekarunsa ba sufi 43 zuwa 45 ba, Abbah Abbas mutum ne dan gayu mai yawan ado da kwalliya, kuma ma'abocin kamshi shiyasa kullum baka ganin tsufasa, dan idan yace ya kai matakin shekara 50 a duniya da yawa wasu ba zasu yarda ba, sai dai kuma masu nazari da tunani idan sukayi masa kallon tsanaki a zasu fahimci cewar ya kai shekarun da ya fad'a d'in.........Da gudu Mussadiq yaje ya rungumeshi yana fad'in ''Oyoyo Abba." Yana d'an murmushi ya bashi hannunsa tare da fadin"Barka da Asuba magajin Abbah." Mussadiq na dariya ya rike hannun mahaifin nasa suka gaisa sosai........Saddiqa na murmushi tace"Abba ina kwana ka tashi lafiya."? A nutse ya d'aga kansa yana kallonsu ita da Naja'atun Yace."Lafiya lau na tashi Ina zakuje da sassafe haka."? Yana kallon Naja'atu yayi maganar."!
A kanta a kasa ta gaishe kafin tace"Zamu shiga gidan Alhaji ne mu gaisa." Yace."To babu damuwa nima yanzu zan shigo gidan.'' Kokarin ratse ta yake ya shiga cikin gidan, tayi saurin bashi hanya, tana sunkuyar da kanta, gani tayi yau fuskar sa babu walwalar da ya saba yi mata koda yake ai dole dama ya kasa sakin jiki da ita saboda yasan abinda yayi.
Ta kalli Saddiqa tace"Kuje gani nan zan biyo bayanku." Saddiqa ta kalleta tana kallon Salim da yayi wani kici-kici da fuska yana kallonta ya wani zuba hannuwansa a cikin aljihun jins din dake jikinsa.....Saddiqa jikinta sanyi yayi ganin yanda Naja'atun ta wani d'aure mata fuska! sai taja hannun Mussadiq suka fita daga gidan
Salim ya tsira mata ido bayan fitar su Saddiqa yace."Me kike fahimta ne daga gurin wannan Dattijon."? Cikin sanyin jiki da sarewa da al'amarin tace"Ni wallahi har yanxu na kasa gane inda ya dosa, dazu dai munyi waya dashi na ro'ke shi akan ya janye kudirinsa yace."zai yi shawara idan ya yanke magana zai fad'awa Baba malam abinda ake ciki."
Cikin