Author : Binta Umar Abale Category : Romance
masa abinda ke faruwa, da kyar tayi masa magana tana hawaye gwanin tausayi tace ita taga ji tunda bata haihuwa ya 'kara aure ko kuma ya saketa dan cin zarafin da Yayarsa take mata ya isheta.
Ransa idan yayi dubu ya 'baci! shin wai me yake damun Ramlatu ne? ina ruwanta da matarsa ina kuma ruwanta da rashin haihuwarsa, idan zai mutu bai haihu ba bai dameta ba shine yaga zai iya zama da matarsa a haka, shi kam ya rasa wace irin 'kiyayya Ramla keyi wa Halimatu, hakuri ya bata sosai yace zai same ta yaja mata kunne kan kada ta sake zuwar masa gida.
Jin abinda ya fad'a yasa hankalinta ya tashi sai ta dinga bashi hakuri tana nuna masa illar abinda zai aikata, mutukar ya tunkari Ramlatu da wannan maganar to babu shakka ya sake rura wutar gaba mai zafi a tsakaninsu, kuma ita ba zata so su samu matsala da 'yar uwarsa ba, Nuna mata yayi ya hakura ba zaije gidan Ramlatun ba........Washe garin ranar kafin ya tafi kasuwa sai da ya tsaya gidan Ramlatun sukayi ta babu kyau babu dad'i a tsakaninsu, dan ya nuna mata mahimanci da matsayin Halima a gurinsa kuma ya nuna mata cewar itama ta tsaya a matsayinta na 'yar uwarsa mutukar tasan wata fitina ce zata kaita gidansa to kada ta sake zuwar masa gida, dan tuntuni shi ya riga yasan Allah ne ke bada haihuwa ba wani mahaluki ba! Ramlatu kuka taci ta 'koshi 'dan uwanta da take alfahari dashi shine yazo ya ci kata mutumci a gaban kishiryata lallai babu shakka dole sai ta tashi tsaye kan Halima dan da alama Iyayenta suna tsaye a kanta gurin ganin ta mallake mata d'an uwa.
*Kaji rigima ta Ramlatu ke ba uwar Abbas ba komai ba amma kina kishi da matarsa, Uwar miji aka sani da kishi da matar d'anta Uwar mijin ma irin wacce bata san abinda take ba.*
Abbas zuciyarsa wasai yaje kasuwa yayi harkokinsa......koda suka tashi daga kasuwar kai tsaya 'Kofar Na'isa suka nufa dan ji yake idan bai fad'awa mahaifiyarsu abunda Ramla ke masa ba za'a iya samun matsala nan gana gwara ya fada mata ta kira ta ta ja mata kunne.
Hajiya Abu ranta ya 'baci sosai tace"Ni dik abinda ke faruwa a tsakaninsu ban sani ba wallahi amma Wannan yarinya anyi babbar kwabo wallahi dan taga matar taka mai saukin hali ce shiyasa take mata cin kashi a ko'ina amma kayi hakuri ka kuma bawa Halimatun hakuri insha Allah zan aika yara har gidanta su kira min ita zan mata tsakani da matarka duk sanda ta sake zuwa gidanka domin ta kuntatawa matarka to babu shakka na samu labari da Alhaji maihifinku zan had'ata....
To tun daga wannan rana Halimatu ta samu lafiya Ramlatu ta saurara mata da gorin haihuwa ammafa sa'i da lokaci suka had'u a wata sabgar sai ta yar mata da habaici al'amarin Ramlatu sai addua.
*****
Halisa ce ta shiga kara kaina a gidan, mussaman ranaku guda biyu Juma'a da Lahadi ranakun da ta tabbatar da cewar maigidan nan bai futa sai taci uwar kwalliya ta sanyo turare mai 'kamshi tazo ta yini a gidan! idan sun had'u dashi tana nuna masa kamar babu wani abu a ranta, ta hakura dashi kawai ta zuwa ziyara ne gurin 'kawarta! Sai dai ya girgixa kansa kawai ya shareta dan shi ba yaro bane ballanta ta raina masa hankali.........Ita kuwa Halima zuciyarta ce ta shiga sa'ka mata wani abu! tana ganin tunda dai har yanzu Halisan bata da tsayayye mai zai hana ya aureta ya had'asu tunda ta lura da Halinsa tayi hankali kuma duk wasu alamu da take nunawa a kan mijin nata ta gane sabida shi take zuwa gidan........Koda ta sameshi da maganar cewa yayi zaiyi shawara zai fada mata kome ya yanke!
Kwana biyu ta sake tuntu'barsa da maganar ya dinga kallonta yana mamakinta yace."Ke kina ganin idan na auri Halisa na had'aku babu matsala kuma zaki iya zama da ita."?
Cikin farin ciki tace"Zan zauna da ita tsakani da Allah nasan ko ta nufe ni da sharri zai koma kanta tunda ban cuce ta ba, sannan kuma ina so ka aureta kaga tanan za'a tabbatar da rashin haihuwar mu shin waye yake da matsala tsakanina da kai."! Wannan magana da tayi sai ta sake sa masa 'kwarin gwiwa shima yana so ya tantance waye mara lafiya a cikinsu, kai tsaye ya tunkari Halisa sa maganar, ranar kamar ta zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki! ta dinga murna da godewa Allah! Yace."Ina so ki zauna lafiya da Halimatu dan da yawun bakinta nazo nan neman auraki kada ki shiga gidana ki tayar mana da hankali mun gina rayuwarmu cikin mai kyau da inganci" Halisa taji wani irin d'aci a ma'kogwaronta! wato ma ba'a karan kansa yazo neman auranta ba sai da izinin matarsa! 'kwafa tayi a cikin ranta! a zahiri kuwa cewa tayi" Haba Alhajina kada ka damu zan zauna lafiya da ita ai ko lokacin baya ma kuruciya ce ta janyo nayi wannan furucin amma ka daina kokwanto da shakku a kaina."
Yaji farin ciki ya kamashi dama can yana son Halisa halinta ne baya si to tunda dai yanzu tayi hankali zai aureta su zauna tare cikin inuwa daya.
Ba'a wani ja dogon lokaci ba aka d'aura aure Halisa ta tare a dakinta, da yake gidane mai dauke da bangare uku sai kowa ya dauki d'aya, kasancewar babu yara a gidan yasa maigidan ke bin 'Dakunan matayen nasa bai tare a nasa part ba din sai ranar da ya tara iyali tukkuna.
*Rubuta 'karya sakaka! babu tushe ballanta makama ba za tayi armashi ba! My Fans ku cigaba da karanta tushen labari domin shine makamar zance Labari na gaba.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Allah Sarki My real Fans♥️ kuyi hakuri ban san maganar da nayi zata 'bata muku rai ba, nagode kwarai da kulawa, kamar yanda bakwa so mutumcina ya zube nima bana so naku ya zube, ammafa kusa ni sun d'auke ni sun sani a gruop dinsu dan su samu damar cin mutumcina, To ina ro'kon Allah ya mutuntani wanda yake da tunanin tozarta ni ko yaci mutuncina Allah gaka nan gashi nan........Ke kuma my Aminiya kiyi hakuri kinfi kowa sanin halina yanzu ma raina ne ya 'baci! to amma insha Allah kome zai biyo baya na sharri zan had'a mutum da Ubangijin da ya hallice shi.🤗*_
*Wallahu galibun Ala amrihi👏🏻*
*4*
Sati biyu da shigowar Halisa gidan al'amura suka sauya, Halimatu ta kasa gane kan mijin nata gabad'aya Halisa ta ri'ke masa wuya ko yana kasuwa bashi da nutsuwar kirki mutukar bai dawo gida yayi tozali da ita ba, ranar girkin Halimatu sam bai da wani kuzari da walwala yakan dad'e ma a waje bai shigo ba, idan ma ya shigo d'in babu wani abun arziki da yake tsinana mata ba kwanciyarsa yake yi yai bacci! Halima ta shiga damuwa matsananciya ta rasa wanda zata samu ta fad'awa damuwarta gabakidaya Abbas ya sanja mata baya kula da ita sannan ba ya zama yaci abincinta kamar da idan tayi masa magana sai yace."A koshe yake shine dalili, Ita kuwa Halisa data fahimci rashin jituwa a tsakaninsu sai ta sake zage damtse gurin ganin ta sake mallakarsa, kissar yau daban ta gobe daban, duk abincin da zata bashi sai ta bad'e shi da magani abun mamaki kuma Yayarsa Ramlatu itace ke kawo mata maganin mata dana mallakar zuciyarsa, ita dai burinta Halimatu ta wulakanta a gidan.
Ranar Asabar har ya futa kasuwa da jaraba ta ciwo shi ya dawo gida, a maimakon ya nufi 'bangaran Halimatu tunda Girkinta ne sai kawai ya nufi bangaran Halisa, domin a yanda yake jin kansa yana ganin kamar Halimatu ba zata iya dashi ba, sai yanzu ya gane cewar Halisa ce dai-dai dashi dan tana iyawa da fitinarsa ita kuwa Halimatu rashin kuzarinta a ko'ina ma gwadawa take, ada hakan bai dame shi ba sai da ya auri Halisa ya gane cewar itace zata iya dashi, dan jaraba irin tashi baya tsayawa kan hallitar da Allah yayi masa duk karfi da kuzarinsa sai ya had'a da maganin 'karfin maza, kullum akwai wanda yake kawo musu magani kasuwa suyi ta siya suzo suna gallabar matansu da daddare.
Halisa duk da tasan ba girkinta bane bai hanata nuna masa kulawa ba kar'barsa tayi hannu biyu suka shiga d'aki suka shafe awa kusan hud'u suna abu daya............Halimatu ce ta shiga sashin tana sallama a palon taji shuru idanunta ne ya sauka kan hular maigidan da key dinsa na mota da kuma rigarsa kan kujera.
Tabbas kayan daya sa ya futa dashi ne a dakinta ya shirya kuma asali ma itace ta dauko masa kayan dole kuma tayi mamaki! kafin ta dawo daga tunaninta suka fito daga dakin a tare dashi da halisan daga shi sai gajeran wando, ji tayi yana fad'in "Zo ki bani abinci naci a gurguje na koma kasuwa na bar mutane na jirana." Had'a ido sukayi ita dashi! sai ya wani dake! kamar ba mara gaskiya ba, ya bude baki zaiyi magana kawai sai ta juya ta fita daga palon.
Jikinsa ne yayi sanyi ya zauna kan kujera yana kokarin mayar da kayansa, tabbas yasan wani abun da yake a gidan baya kyautawa sam be san meya sa ba yanzu kwata kwata baya damun cikakken satisfaction da Halimatu! bata da ni'ima kuma bata gamsar dashi kamar yanda Halisa ke gamsar dashi, gashi Halisa ta iya salo-salo shi kuma haki'kanin gaskiya yana so a dinga kula dashi kan shimfida.
Halisa ta fito daga kicin da abinci a hannunta, mikewa yayi da fad'in" Bana jin zan tsaya cin abincin nan zan koma kasuwa yanzu.''
"Haba dai don Allah ka zauna kaci gashi da zafinsa dama ban jima da gamawa ba." Girgiza kansa yayi ya nufi hanyar fita yana kallon agogon hannunsa da fad'in "Biyu da rabi yanzu na fada miki akwai mutanan dake jirana."
Sakin bakinta tayi ta bishi da kallo tana girgiza kai, da sauri kuma ta ajiye plate din abincin taje bakin window ta d'aga labule tana le'kensa, gani tayi ya nufi gurin Halimatu, shi da yace sauri yake yi to mai kuma ya kai shi gurin ta........Takaici kamar ya kasheta ta zauna kan kujera tana cizar yatsa.
Koda ya shiga palon samunta yayi zaune a kan kujera ta tsirawa guri guda ido tana kuka! yaji wani irin tausayinta ya kama shi, yana sonta baya son ganinta cikin damuwa shiyasa yaji wani irin rashin kuzari a jikinsa.
Kafin ya karasa inda take sai da ya tanadi kalaman da zai wanke kansa a gurinta.
Cikin wata mayaudariyar murya ya kira sunanta had'e da kamo hannunta, shuru tayi bata amsa ba, yace."Ki gafarce ni hakika nasan ni mai laifi ne a gurinki, kin san dan adam ajizi ne, ina tausaya miki ne shiyasa bana so na dinga d'ora miki lalurata."
Hannunta ta cire a cikin nasa tace"Wallahi ban ta'ba tsammanin haka daga gurinka ba, ashe dama duk wani abu da kake fad'a a baki ne? Halisa ko wata uku cikakku ba tayi ba ka sauya gabadaya ka daina kula dani baka sauke hakkina dake kanka, yausha rabon daka hada shimfida dani? ina tunanin tunda Halisa ta shigo gidan nan tsayin wata uku sai biyu ka kwanta dani shima sai dana nema sannan kuma abun har ya kai ka dinga satar kwanana kana kai mata, ina hankali da tunaninka suka tafi? idan ni bana ganinku ai Allah yana kallonku kuma kasan sai ya saka mun." Jiki na kyarma yace"Na sani wallahi kiyi hakuri ki dauki hakan a matsayin tsautsayi! na fada miki ajizanci ne irin na d'an adam amma ba zan sake ba kuma inaso kice kin yafe mun."
Tace" Sai ka fad'a mun sau nawa kana satar kwanana kana kai mata." Da sauri yace."Yau ne kawai shima kuma akashi aka samu." Ta goge hawayenta a hankali tace"Na yafe maka amma dan Allah ka dinga kiyayewa kana kokarin sauke hakkina dake kanka.
Yace."Insha Allah ki tayani addua nima cikin 'yan kwanakin nan wani iri nake jina." Tace."Insha Allah zan cigaba dayi maka addua harkarshen numfashina." Mikewa yayi yana fadin." Muje ki rakani ko." Ta mike tana mirmushi tamkar baiyi mata laifi ba suka jera tare suka futa har inda motarsa take.
Halisa har yanzu na tsaye bakin window tana kallonsu suka futo suka tsaya a bakin mota suna magana! gani tayi Halimatun na dariya tana kallonsa shi kuma ya kamo fuskarta ya sumbuta, ya shiga mota hade da daga mata hannu.......Zaman da'baro tayi kan kujera tana hargitsa gashin kanta, kai jama'a!! wai shin Halimatu wace irin macace ne? wacce bata da zuciya bata kishin kanta! ai idan itace mijinta ya saci kwananta ya kaiwa kishiyarta ranar sai ta kusa kashe shi da tashin hankali, amma ita duba dariya ma take harda rakoshi bakin mota.
Wayarta ta dauka ta kira Yaya Ramlatu! ta daga wayar suka gaisa, Murya na rawa tace"Yaya al'amura fa sun dagule wallahi! ban san wane irin so Abbas kewa Halimatu ba! daga aiki ya fara sai kuma ya karye! gashi itama kamar mayya duk abinda za'ayi mata bata fushi, 'karewa ma kwananta ya kawo min a maimakon taji haushi sai ma take dariya harda rakoshi bakin mota." Yaya Ramlatu ta shiga girgiza kanta tace" Nasha fad'a miki Uwarta da Ubanta ba'a zaune suke ba dan ita bata da kuzari da 'kafar yawon gidajen malamai Ubanta 'kasurgumin dan tsubbu ne duk wasu asararai yana dasu, ina kyautata zaton yayi aiki mai zafi akan Abbas din, amma duk yanda zanyi sai nayi na wargatsa shirinsu." Halisa tace"Ni wallahi yanzu babban burina ta fita ta bar min gidana sannan naga na samu ciki na haihu." Ramlatu tace'' Kada ki damu zaki haihu ita kuma zata fita ta bar miki gidanki zaki zauna tare da 'yayanki insha Allah zanyi miki kokari akan wannan lamarin." Tace"Nagode Yaya Ramlatu! Sallama sukayi Ramlatu tace"Yauwa dama inaso kiyi dubara a gurin mijin naki ki samu 'yan kudi masu kauri sai ki kawo min dasu nake so naje a taimaka miki." Tace"Insha Allah zanyi kokari kamar nawa ." Tace"Dubu hamsin ma ta isa."
Ajiyar zuciya ta sauke tace" Zan duba inda yake ajiyar kudinsa idan ya bar key din a jiki zan dauko zan kawo miki anjima dan nafi so ayi komai da zafi-zafi."
Ramlatu tace"A'a kada ki daukar masa kudi ya gane fa." Tace"Ai suna da yawa ba zai gane ba tunda kusan kullum sai ya shigo dasu kafin ya kai banki." Tace"To shikkenan ina sauraranki idan kin kawo min ni kuma nayi miki al'kawari komai yamma zan tafi gidan *Yar Sa'adu."*
Halimatu kuwa zuciyarta fes ta futo daga bangaranta ta nufi na Halisa domin yi mata sallama tana so taje su gaisa da iyayenta sannan kuma ta shiga gidan Dan uwanta su gaisa da matarsa Maryam, abinda yasa Maryam ta rage shigowa gidan saboda zuwan Halisa dan bata so wata hatsaniya ta tashi a tsakaninsu sunanta ya fito, dama kuma ta lura da irin wulakantaccen kallon da Halisa ke mata, shiyasa gabadaya ta dauke kafarta daga gidan, sai dai sa'i da lokaci ita Halimatun ta shiga su gaisa.
Halisa na kokarin zaro kudi cikin drowar taji sallamar Halimatu a palonta, da sauri ta zabura ta futo palon tana kallonta, Halimatu ta fahimci rashin gaskiya a tare da ita, girgiza kanta tayi tace"Halisa zan je gida mu gaisa dasu Baba Malam sai nadawo." Cikin ya'ke tace"To sai kin dawo dan Allah ki mi'ka min gaisuwata gurinsu."
Tace"Zasuji insha Allah." Juyawa tayi ta fita, Halisan ta rakata da wulakantaccan kallo tana cin laya a kanta.....Tsaki taja ta koma dakin ta cigaba da ciku-cikun dauko kudin daga drowar da take a kulle dan ba taga key din ba amma dan jaraba sai da tasan yanda tayi ta zura hannunta ta zaro kudin duk sun ya mutse, da kyar ta samu ta ciro dubu talatin da biyar ta hakura haka, kaya ta sanja ta zuba kudin a jaka tasa kai ta fita daga gidan ba tare da maigidan ya sani ba.
Baba Malam da Baba Talatu sunji dadin zuwan 'yar tasu duk sanda ta kai musu ziyara sukan yi murna da farin ciki ganinta cikin nutsuwa da wadata!
Bayan taci abinci sai suka shiga hira da mahaifiyarta Na'ajatu ce ta shigo gidan hannunta rike da buhun kayan wasanta duk tayi bud'u-bud'u da jikinta, Baba Talatu ta harareta da fadin" Kin gama yawon wasan naki yunwar cikin ki ta koro ki ko."'? Zum'bura bakinta tayi tana kokarin yin kuka. Baba Talatu tace"Ai sai ki nemi me baki abinci dan banyi dake ba dama na fada miki tunda baki zuwa makaranta to zakiyi ta zama da yunwa." Kuka ta fashe dashi ta jefar fa buhun kayan wasan nata tana kallon Yayar tata. Halima ta riko hannunta tana rarrashinta, kwanciya tayi a jikinta tana kuka cikin rashin iya magana sosai tace"Ni ba zani makaranta malam ya dakeni ba kuma sai an bani abincina." Halimatu ta dinga dariya tana kallonsu suna drama Baba Talatu tace"To sai naga wanda zai baki abinci a gidan nan." Kuka take sosai tana fad'in "Ni sai an bani abinci yunwa nake ji."
Halimatu tace"Yi shuru autar Baba Ni da kaina zan baki abinci ki fad'a min ma me kike so na siya miki kici ki kyalewa Baba abincinta."
Hawaye tagoge tana kallonta tace"Zan biki gidanki ki dinga bani shayi da bredi ita Baba Talatu kullum koko da kosai take bani, sannan bata bani na siyo alawa da biscuit. " Baba Talatu ta ri'ke ha'ba! tana fad'in "Ikon Allah! Wato Naja'atu abinda zakiyi mana kenan! kullum fa sai na dafa miki shayi malam ya siyi miki bredi da madara ga kwai amma kice koko da kosai nake baki." ? Halimatu tace"Gaskiya Baba bakya ji da wannan autar taki! dubeta dan Allah yanda kika barta tayi daud'a dubi kitson kanta duk ya tsufa, gashi bakya bata ta siyi sweet da biscuit saboda haka ni zan tafi da ita gidana, zaki bini ko Auta."!? tafada tana kallonta, Da sauri ta daga kanta tana dariya.....Baba Talatu ta gyara zamanta tana ta'be baki tace"Ai sai kuje dama nima na gaji da bari bari yarinya kullum nakan layi tana yawo