Madadi 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Abale Category :  Romance

Chapter   14 / 17

39K to 42K   out of 48.8K words

ta saba ri'ke shi ko ta rungumeshi ba, a duk sanda xata r'ike shi ko ta rungume shi a lokotan baya baya jin komai a cikin zuciyarsa da jikinsa, amma yau ji yayi jikinsa na wani irin rawa mussaman da yaji tudun breast d'inta a cikin kirjinsa ajiyar zuciya ya sauke mai zafi! ya d'an cire ta daga jikinsa, yana kallon fuskarta yaga duk tayi wujiga-wujiga ga alamun furgici nan a tare da ita! gyaran murya yayi kafin yayi magana, Yace."Dota wato har yanzu baki daina kuka ba ko ki fad'a min abinda ke damun rayuwarki."! Hanci ta sha'ka tana sake shigewa jikinsa da rarraba ido a palon murya a dashe tace."Abbah Yaya Halimatu ce tazo tana yi min magana dan Allah ka taimaka min ka rabani da wannan rayuwar da nake cikinta ka mayar dani gida gaban iyayena wallahi ba zan iya zama a gidan nan ba ka taimaka min Abbah rayuwata na cikin garari da tashin hankali."! Tana rirrikeshi take wannan maganganun
Hannunta ya ri'ke ya dan sassauta muryarsa sannan yace."Ki kwantar da hankalin ki Dota wanda ya mutu baya dawowa kawai kinsa tsoro acikin zuciyarki shiyasa kika kasa samun nutsuwa a gidan.....Shuru tayi tana goge fuskarta, yaja ta suka nufi bedroom dinshi, koda suka shiga dakin sai yaga shimfidar gadonsa a hargitse ga bargonshi a 'kasa, ya kalleta cikin nazari yace."A dakin nan kika kwana ne."? Hawaye suka wanke mata fuska tace."Eh ko ina tsoro ake bani shine na shigo nan na kwanta to anan din ma ban daina firgita ba." shuru yayi yana bin dakin da kallo, kafin yace."Babu wani abin tsoro a cikin gidan nan ke kanki kin sani lafiya lau mukayi rayuwa a ciki ina ganin kamar kin sanya tunanin Halimatu a cikin ranki shiyasa kike furgita ina so ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki san da cewar wanda ya mutu baya dawowa, fargaba da damuwar da kika sanya a ranki duk itace ta janyo miki firgita."
Girgiza kanta tayi tana ri'ke hannunsa tace"Abbah ba zan iya zama ba dan Allah ka mayar dani gidanmu ka dubi halin da nake ciki ka tausayawa rayuwata." Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta ya tausayawa rayuwarta to wane irin tausaya mata zaiyi bayan wanda yake mata, Yace."Yanzu dai je kiyi wanka tukkuna naga alama ma kamar baki karya ba ko."? Daga kanta tayi tace"Ba zan iya shiga dakin ba tsoro nake ji." Kai tsaye yace."To sai kiyi a toilet dina." Tace"To kayana na dakin ai." Yace."Bari na dauko miki." Fita yayi daga dakin, ta dinga zazzare idonta tana bin dakin da kallo, shi kansa dakin nasa tsoransa take ji, tana tsaye ya shigo hannunsa rike da riga da zani na atamfa super ire-iren kayan da yake d'inka musu, ya ajiye kan bed yace."Baki shiga wankan ba." Hanyar toilet din ta nufa salo-salo! ya bita da kallo mai tarin ma'anoni! bayan shigarta toilet din ya dauki bargon dake kasa ya mai dashi kan bed din ya xauna gefen bed din hade da kunna wayarsa yana dubawa, kawai yaji ihun ta daga cikin toilet din kafin ma yayi wani yun'kuri ta fito a guje jikinta duk kumfar sabula ta dauro towel dinsa yana kokarin fad'uwa daga jikinta, ya mike a gigice yana tambayarta ihu! take tana nuna masa toilet din, Ya rike hannunta yana tofa mata addua tangadi ta shiga yi tamkar 'yar maye ta tafi luuuu! zata fad'i! ba tare da 'bata lokaci ba ya ri'ke ta sosai a jikinsa, cikin tashin hankali da damuwa ya nemi gefen bed ya zauna da ita rungume a jikinsa, ji yayi jikinta na wani irin kyarma! yana rawa kamar wacce take cikin zazzabi mai zafi! babu shakka a firgice take, adduoi ya shiga tofa mata a jikinta yana me tsirawa fuskarta ido, a fizge suna dan kama da Halimatu kad'an, nan ya shagala da kallonta dan gani yayi tana nema ta rikid'e ta koma masa Halimatu.......Lokacin ne kuma ta dan samu nutsuwa ta bude idonta tana ambatar kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Ta mike da sauri ganinta kwance lakadan a jikinsa ga towel din jikin ya sa'bule! brest dinta duk a waje! Da sauri shima ya gyara yanayin sa amma dai duk da haka kana kallonshi sai gane ya hau network, Yayi dan gyaran murya as'usul Yace."Sannu ki dinga yawaita addua ina ganin tunda kin firgita da zaman side din nan zan sa a gyara miki Side din da ya kasance nawa sai ki koma can." Gyara towel din jikinta tayi ta mike daga jikinsa, kayan ta dake kusa dashi ta dauka tana so tasa tana jin kunyarsa, Yace."Ya zaki sa kayan bayan duk ga sabulu nan a jikinki." Cikin rawar Murya tace"Ba zan iya komawa toilet din ba, dan ina wanka naji kamar ana kiran sunana." Ya dinga kallonta abin na bashi mamaki! Mikewa yayi ya rike hannunta yace."Muje na raka ki kiyi wankan." Ma'kale kafad'a tayi tana komawa baya! Yace."Zan tsaya har ki gama fa kuma bazan kalleki ba." Hawaye ta share tace''Na hakura da wankan."Ya girgiza kansa da fad'in "A'a ai bai dace ba kina amarya ki zauna da datti ba zakiyi ba'ki fa." Kallonsa ta dinga yi tana mamakin maganarsa, Tace."Abbah ni d'in amaryar waye."? Ya nuna kansa da hannu da fad'in "Amaryata mana." Taji wani irin ciwo da takaici a cikin zuciyarta, hawaye suka kece mata tace."Kaico da wannan kalmar taka Abbah! Kaico da wannan maganar dake fitowa daga bakin ka, ni ba amaryarka bace 'Yar ka ce." Tana gama maganar ta ta cire hannunta daga cikin nasa ta fita daga dakin, gabadaya ma ji tayi ta daina jin tsoron akan ta zauna a dakinsa yana kiranta da amaryarsa gwara ta fito koma meye ya cutar da ita....
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~~~~~~~~ *16* Ya jima a dakin yana sa'kawa da kwancewa kafin ya fito palon, inda ya sameta a takure a kan kujera har yanzu bata daina zubar da hawaye......Saboda jin haushin maganar data fad'a masa yasa ya kama hanyar fita dan baya so ya zauna a gidan zuciyarsa ta tunzira shi a kanta, dan ya lura koda 'kuruciya a tare da ita to da akwai iskancin dan iskancin ma yafi yawa a tare da ita, gabad'aya ya lura ta raina shi kuma ta daina ganin girmansa, wannan d'abi'un da take masa na 'bata masa rai sosai da sosai! Yana dab da fita yaji ta ri'ke masa hannu, ya juyo fuskarsa babu walwala yana kallonta yace."Me zanyi miki kuma."? Cikin rawar murya tace"Dan Allah zan bika dik inda zakaje kada ka barni ni kad'ai wallahi ba zan iya zama ba." Shuru yayi yana kallonta na minti biyu kafin yace."Jeki dauko hijab din'ki." Da sauri ta saki hannunsa Hijab dinta dake kan kujera ta d'auka tasa ya nuna mata 'kofar fita da hannunsa, da sauri ta fice tana sauke ajiyar zuciya, kwana d'aya tayi a cikin gidan jin ta take tamkar a cikin 'kaya, kulle 'kofar palon yayi yazo shigeta ya nufi motarsa....Bin bayansa tayi da saurin gaske, ta ma rigashi bude motar ta shiga ta zauna tana zazzare ido, sai da ya gama magana da maigadinsa sannan ya shiga motar, yana zama tace."Jakar kayana na manta ban dauko ba kuma tana d'akin Yaya Halimatu.'' Ya kalleta cikin rashin walwala yace."To meye amfanin daukar jakar kaya ke a tunaninki ina zan kai ki."? Tace."Na dauka zaka mayar dani gidan Baba Malam." Girgiza kansa yayi yace."Ba can zan kaiki ba zan kai ki gidan Halisa ku zauna da yara zuwa dare sai mu dawo gidan tare." Fashewa tayi da kuka tace"Dan Allah ka daka mu dawo ni wallahi akan na zauna gidan nan gwara na zauna a gidan Anti Halisan yafi." Yace."Kina ganin zaki iya zama a gidan."? Da sauri tace"Eh zan iya." Ba tare da yace komai ba ya bud'e kofar motar ya fita, cikin gidan ya koma ya shiga, jakar kayanta dake dakin Halimatu ya dauko mata ya fito.Ganinsa dauke da jakar kayanta yasa ta sauke ajiyar zuciya,tana ganin gwara ta zauna a gidan Halisa akan ta zauna ita kadai a wannan uban gidan wanda ake bata tsoro, bayan mota yasa jakar, ya shiga ya zauna ya tada motar ya fita daga cikin gidan........Tana ganin sun hau kan titi ta sauke ajiyar zuciya wacce ta sanya shi dan kallonta da gefan ido, ya dauke idonsa tare da maida hankalinsa gurin draving din da yake.............Motar tayi tsit! na kusa minti goma kafin yayi gyaran murya a nutse ya ambaci sunanta! ta kalleshi tare da amsawa, Yace."Ina so inyi miki wata tambaya bana son ki munafurce ni ko kuma ki 'ki fad'a min gaskiya." Tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta, Yace."Me yasa bakya so kiyi rayuwar aure dani."? Kallonsa tayi ya gyada mata kansa a nutse yace."Amsa nake so ki bani bance kuma ki bani amsar da zata 'bata mun rai ba." Tace"Saboda na dauke ka a matsayin mahaifina shiyasa nake ganin kamar haramun ne nayi rayuwar aure da kai." Yace."Waye ya fad'a miki haka? shiru tayi Ya cigaba da cewa" Aure a tsakanina dake ba haramun bane Naja'atu, dan na ri'ke ki kin girman a hannuna hakan ba zai hanani na raya sinnar ma'aiki dake ba mutukar Allah ya kad'dara hakan a tsakanina dake, mutane nawa ne sukayi irin wannan auran na *MADADI* kuma auran yayi albarka, inaso ki sani da badan mutuwa ta raba tsakanina da Halimatu ba to da babu abinda zai sanya ni naji sha'awar auranki, na kwadaitu da auranki ne dan ina ganin kamar zaki maye min gurbin matata ta gurin kyawawan halaye gami da sadaukarwa, ashe ba haka abin yake ba, Allah yasa kun fito ke da Halimatu ta tsatso daya amma kuma halin kowa ya bambanta, shin meye aibuna da bakya so kiyi rayuwar aure dani? ko kina ganin ba zan iya dauke miki dukkanin bu'katunki ba ne? Shuru tayi kanta a kasa tana ta nazarin maganganunsa, Ya cigaba da cewa....."Nasan babu irin sa'ke-sa'ke da zuciyar ki ba tayi miki a kaina, kina ganin kamar nazo da son zuciya a cikin al'amarin a matsayina na babba ba yaro ba na aure ki, kina ganin tamkar na cutar da rayuwarki ne tunda na hanaki auran saurayi wanda ya dace da rayuwarki ko ba haka bane".? Kasa magana tayi, Ya cigaba da cewa" Nasan kin san da cewar Annabi Muhammad (slw) ya auri Nana Ayshatu tana 'yar shekara tara, yayin da shi kuma yake da shekara Hamsin, to kuwa idan hakane aurena dake babu haramci a ciki tunda wanda akayi duniya dominsa ma ya auri 'yar 'karamar yarinya wacce bata kai matsayin shekarun da kike ba a yanzu, ina ganin ni na aikata sinna mai kyau tunda nayi irin abinda Annabi ya aikata."......Naja'atu duk jikinta yayi sanyi da maganganunsa, Ya cigaba da cewa" Inaso ki san da cewar abinda kike tunanin wani saurayi mai tashen balaga zaiyi miki a zamantakewar aure to Matashin mutum kamata dan kimanin shekara hamsin zaiyi miki abinda yafi wanda kike tunanin shi saurayin zaiyi miki." ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa" Mafi akasari 'yan matan yanzu abinda ke damunsu kenan.... ((('kalubale gare ku 'yan mata masu tashe saboda ku na zauna nayi wannan littafin, dan akwai masu 'karamar 'kwa'kwalwar da za suce su baza su auri tsoho ba sai saurayi, toh wallahi bari na fad'a muku a wannan zamanin ba'a tsayawa za'ben miji, idan kikace xaki tsaya za'be-za'be to zaki tsufa baki yi aure ba, idan magidanci mai mata yazo auranki idan har anyi binkice mai kyau a kansa an gane cewar yana tsaye a kan gidansa da kula da iyalinsa to ki lalla'ba ki shiga daga cikin, idan kin tsaya kince ke sai saurayi to zaki iya auran saurayin kuma ki kasa samun biyan bukatarki, Samarin yanzu duk 'yan bana bakwai ne kuma mafi akasari auran sha'awa suke daga zarar bukatarsu ta biya shikkenan zaki fuskanci kalubale, bance duka aka taru aka zama daya ba amma dai abinda yake faruwa na fad'a, idan kuwa kika auri wanda ya dan kwana biyu to shi yasan menene aure saboda ya dade a cikin inuwarsa zai ri'ke ki da kyau kuma duk wata soyayya da kike tunanin saurayi zaiyi miki to sugar Dady d'in da kika raina zaiyi miki wacce tafi ta saurayin domin shi tsohon hannu ne a harkar😁)))) Abba Abbas ya cigaba da cewa" Abinda yake damun su kenan sai suce su baza su auri tsoho ba dan suna ganin kamar idan sun auri mai shekaru baza su more kuruciyarsu ba, wanda kwata-kwata ba haka bane sunyiwa abun mummunar fahimta ne, inaso ki zauna kiyi tunani mai kyau a kan wannan maganganun da mukayi dake, Na farko ni ban haife ki ba, ballanta ki dinga ganin kamar kin aikata haramci dan kinyi mu'amular aure dani! Na Na biyu kuma wad'annnan abubuwan da kike yi sun soma isata idan baki gyara ba to zan dauki mataki a kanki, ni ba yaro 'karami bane ballanta ki dinga yi min iskancin da duk kika ga dama, a yanzu ni ina a matsayin mijinki ne ba Ubaba kamar yanda kike dauka a da to yanzu ba haka bane! Wallahi! duk ranar da na sake jin kin fad'i wata mummunar magana a kaina da aurana sai na 'bata miki rai! na dauka kuruciya ce ke damunki sai kuma daga baya na gane rashin arziki ne, to ni ba lusarin namiji bane ke zaki fadawa kowa hakan tunda kin taso a gidana kinga yanda nake zamantakewar aure da mataye na, suna bani girma suna mutuntuni babu wacce take fad'a min bakar magana ko kuma taja min tsaki! dan haka nake gargadinki ki kiyaye aikata abinda zai janyo miki 'bacin raina."
Tun kafin ya gama maganarsa ta rufe fuskarta cikin hijabi tana kuka, shima tunda ya gama maganarsa bai sake cewa komai ba ya cigaba da draving dinsa, daf da zai shiga cikin unguwar ne kira ya shigo wayarsa, koda ya duba sai yaga numbar Halisa a nutse ya daga wayar, Tace"Abban Mufida ya kuma ka fita baka karya ba."? Kai tsaye yace."Naje duba Naja'atu ne yanzu ma dai ganin zuwa tare da ita ta kasa zaman gidan." Da sauri tace."Kamar yaya."? Yace."Idan nazo zanyi miki bayani." Kashe wayarsa yayi dan ganin kamar zata 'kara masa wani 'bacin ran! Yana ta jin shashshekar kunanta sai damunsa take kawai dai yayi mata shuru ne yasan dole idan ta gaji zata daina........Halisa kuwa kasa'ke tayi da waya a hannu shin me hakan yake nufi da zai dauko mata yarinya ya kawo mata gida! cika tayi ta batse ta hard'e a kan kujera tana jiran zuwansu.........
Saboda yasan zai samu matsala daga gurinta yasa ya shiga gidan fuskarsa a murtuke dan baya so tayi masa rashin arziki ya lura ba tayi maraba da zuwan Naja'atun ba......Mussadiq na ganin Naja'atu tare da Abbansu ya tashi a guje yaje ya rungumeta, Allah sarki yaro kenan har ya mance abinda tayi musu, tsugunawa tayi ta rungumeshi tana sumbatarsa a fuska, Abba Abbas kuwa bai tsaya ba kai tsaye dakinsa ya nufa, Halisa ta mike ta bishi tana huci!! Dama ya tsammaci shigowarta, ya tsira mata ido yana kallonta ganin yanda idonta yayi jajawur lokaci guda, Ri'ke 'kugu tayi tace"Nifa bangane ba meye amfanin kawo ita gidana naga harda jakar kayanta." Yace."Eh kamar yanda na fad'a miki a waya hakane tana jin tsoron zaman gidan ita kadai shine dalilin da yasa na daukota na kawo ta ta zauna nan kafin na yanke hukunci." Murya na rawa tace"To ba sai ka kai mata su Saddiqa su taya zama ba, meye sai ka kawo min ita gida." Yace."Ina tunanin ko ta ganta tare dasu Saddiqar ba zata samu nutsuwar da ake bukata ba." Tace"To naji a'ina kake shirin ajiyeta." Cikin jin haushin titsiyen da take masa yace."A duk inda nayi ra'ayi gidana ne ai." Ganin ya fusata! yasa ta dan sassauta tace"Sai dai a gyara mata d'aya sashen ta zauna dan ni bana jin zan iya zama tare da ita." Yace."Ai dama ba'ace dole ki zauna da ita ba tunda ita tafi so ta zauna anan ke yanzu zanyi duk yanda zanyi cikin satin nan a gyara miki inda zaki zauna a can gidan." Girgiza kanta tayi tana 'kas-'kas! da cingum! din bakinta tayi wani murmushi tace"Ba zai yiwu ba! ai na fad'a maka ba zan amince da wannan rabe raben gidan ba, nima ina nan babu inda zanje." Daga mata hannu yayi yace."To magana ta 'kare kada nan gaba kice min zaki koma can dan ba zaki koma wallahi." Tace."Ai duk inda kake ina nan idan ka tattara ka koma can nima zan tattaro nawa nawa na biyo bayanka." Shuru yayi mata ya zauna gefan gado, ta juya ta fita tana fadin "Bari na kawo maka kayan break din." Tana fita ta gansu zaune a kujera sun kewaye ta har da Mufida sai murna sukeyi tamkar sunga wata sabuwar hallita, ita kuma sai murmushi take musu.....Halisa taja tsaki cikin tsawa tace"Ke Mufida me kike anan zo nan ki taya ni 'aiki." Yarinyar ta mike da sauri! Halisa ta nuna mata hanyar kicin tana fad'in "Bana son shashanci ni kun wani zauna kuna dariyar banza." Naja'atu dasu Saddiqa suka bita da kallo tana kokarin shiga kicin tana surutai.........Bayan shigewar Halisan, ta kalli Su Saddiq tana nazarinsu, kwana biyu da bata gansu ba sai taga kamar sunyi rama ta rike hannun Mussadiq tare da fad'in "Kayi rashin lafiya ne."? Girgiza kansa yayi yace." Yaya Naja'atu kema kin

14 / 17