Author : Binta Umar Abale Category : Romance
zan amince da kai ba wallahi sai yarinyar nan ta shigo gidanka naga irin zaman da zakayi da ita."
Murmushi takaici yayi cikin sigar 'kuntatawa yace."Zanyi zama da ita irin na ma'aurata kuma ba zaki hana ni na ji dad'ina da ita ba." A fusace! taja tsaki! da fad'in "Kana tare da kunya kuwa duk ranar da 'yayanka su kaga ka kwana a d'akin wacce suka d'auka a matsayin yaya a gurinsu, sai ka tanadi abinda zaka fada musu."
Girgiza kansa kawai yayi ya dauki rigarsa yasa a jikinsa ya sauka daga bed din hanyar fita ya nufa jiri naso ya kayar dashi, gabad'aya ji yayi duniyar tayi masa zafi ko ina babu sassauci tabbas sai yanzu ne zai fara kukan rashin matarsa da yayi, a da baiyi kukan rashin Halimatu ba sai yanzu da Halisa da Naja'atu suke gwara kansa a bango....
'Bangaran Naja'atu kuwa yanda taga rana haka taga dare daga zarar ta tuna da cewar gobe za'a daura mata aure da Abba Abbas din sai gabanta ya fad'i ta hau takure jikinta, ta jima tana sa'kawa da kwancewa da tunanin mafita a gareta, tana so gari ya waye ta kira Salim a waya ta sheda masa hukuncin data yanke.......Aikuwa tana idar da Sallahr asubahi ta shiga kiran wayar Salim din inda akaci sa'a yau ya tashi da wuri, ya dauki wayar cikin mayaudariyar miryarsa yace.."My Princess kin tashi lafiya."? Murya a 'kasa tace"Lafiya kalau my prince." Ya wani narke murya irin yanda yake mata yana kashe mata jiki yace."My Prince jiya kwana nayi da tunanin ki da begen ki har mafarki nayi dake muna kwance a gado d'aya kina bani kulawa."
Ta rintse idonta hawaye na zuba tace."My Prince Abba Abbas naso ya yanke mana jin dad'inmu bana tunanin zan iya mallakawa wani da namiji kaina sai kai! bana sha'awar kowa sai kai soyayyar ka kawai nake muradi! amma ina tunanin mafarkina dakai ba zai tabbata dan ganin yanda magauta suke 'kokarin kassara mana rayuwarmu." Mikewa zaune yayi yace."My princess ki fad'a mun yanzu a wace matsaya aka tsaya dangane da maganar auranki da Abbah Abbas din.
Tace."Komai yazo karshe My Prince jiya da daddare Baba Malam naji yana fad'awa Baba Talatu cewa gobe bayan sallahr juma'a za'a daura aurena dashi, wannan dalilin yasa na yanke hukuncin guduwa daga garin gabadaya su neme ni su rasa."
Salim ya shiga goge gumi ma'kogwaronsa ya bushe sosai, yace."Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! abinda ya iya fad'a kenan, murya na rawa yace."My bani da kuzarin yin magana yanzu saboda na shiga rud'u da tashin hankali jin wannan maganar taki, zan kira ki anjima kafin nan nayi nazari kan hukuncin da kika yanke."
Kashe wayar yayi ya zauna yana tunani.......Ashe dai dattijon nan da gaske yake sai ya dasa masa 'kunci da ba'kin ciki! to kuwa in dai ya kasance cewar ya samu nasara a kansa gurin auran Naja'atu to shi kuma zaiyi amfani da damar sa, a gurin ita Naja'atu duk wani abunda yake bukata a gurin yarinyar ba zai same shi ba sai ta zame masa mafisa wanda da kansa zai gaji ya saketa, koda ya saketa shi ba auranta zaiyi ba yana so ya kawai ya dasa masa 'kunci da 'bacin rai kamar yanda ya dasa masa a zuciyarsa.
Mikewa yayi ya shiga cikin gidan...Yaya Ramlatu na kicin tana kokarin kunna wuta, taga shigewar d'an nata, sai da ta kunna wutar ta d'ora ruwan kunu kan murhun, sannan ta bi bayansa, koda ta shiga dakin gani tayi ya takure kansa hade da dafe kansa, Kafin ma tayi magana taga yana hawaye.
Tace."Salim lafiya me yake faruwa."? Cikin tsabar bakin ciki yace."Yaya 'Dan uwanki bashi da kirki ya kasance mutum mai son kansa, ya cuce ni ya cutar da rayuwata kuma ya yaudare ni da yasa na amince masa na daukeshi a matsayin uba ya ha'ince ni, yarinyar dana 'kwallafa raina a kanta yau xa'a daura masa aure da ita, ba zan ta'ba mantawa da wannan mutumin ba."
Yaya Ramlatu ta dinga mamakin maganar tace."Kai waye ya fad'a maka yau za'a daura auransa da Naja'atu da har kake wannan maganar......A fusace! yace."Ita yarinyar ce ta fad'a min yanzu ta kirani a waya tana kuka tare da sheda min hukuncin data yanke kancewar zata gudu daga garin gabadaya."
Shuru Yaya Ramlatu tayi takaici da bakin ciki kamar ya kasheta, lallai Abbas bai da alkawari kamar dai yanda Salim din ya fada hakane Abbas yafi son kansa akan kowa bai duba soyayyar dake tsakanin Salim d'in da Naja'atun ba sai da ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu......Tace."To shikkenan sai ka hakura ka fawwala wa Allah tunda Allah yasa ya samu nasara a kanka, maganar Naja'atu zata gudu ta bar gari bata taso ba dan idan hakan ya kasance to kowa zai d'ora zarginsa a kanka, dan haka kace mata baka amince ba, dan bana son abinda zai janyo min 'bacin ran iyayena."
Yace."Idan ya kasance Naja'atu ta tare gidan Kawu Abbas wallahi tallahi nayi al'kawari sai na 'kunsa masa ba'kin ciki da takaici kamar yanda ya 'kunsa min, tunda dai Naja'atu ni take so ai magana ta 'kare zuciyarta tana hannuna shi kuma yana tare da gangar jikinta."
Yaya Ramlatu tace"Duk wani iya shege da rashin arziki da zaka yi masa ban hanaka ba, kaje kayi domin shima yaji idan da dad'i abinda yayi maka d'aurin aure suje suyi babu inda zanje." Yace."To dama me zaki je kiyi a gidan gabad'aya ma da Alhajin da ita Hajiyan basa kaunarki da suna kaunar ki ba zasu bari haka ya faru ba, sunfi kaunar Kawu Abbas d'in saboda yana da kud'i." Yaya Ramlatu ta dinga girgiza kanta takaicin da ba'kin ciki dik ya cika mata zuciya.
Da asubah da kafin ya tafi massalaci sai da ya shiga ya tashi yaransa domin suyi sallah, koda ya fito daga dakin nasu bai ko kalli dakin Halisa ba dan har yanzu haushinta yake ji yana ganin duk wani kokari da ya kamata yayi a kanta yayi zai dauke mata wuta gabad'aya dan ba zai cigaba da rarrashinta taba tana masa iskancin da taga dama.
Bayan ya dawo daga massalaci ya koma dakin nasu nan ya tarar dasu sunyi sallah suna zaune Saddiqa da Mufida suna magana, dukkaninsu suka shiga gaishe shi ya dinga amsawa cikin nutsuwa da kulawa, ya kalli Saddiqa a nutse yace." Saddiqa ki shiga kicin ki dafa muku tea da abinda kike ganin zaki iya." Tace."To Abbah." Mikewa tayi tana kokarin cire hijab d'inta shi kuma ya fita daga d'akin, Kai tsaye d'akin Halisa ya nufa domin ya dauki loptop dinsa.
Tana kwance kan bed din ta tsirawa rufin dakin ido, da alama ma ba tayi sallah ba, Ko kallon inda take baiyi ba ya dauki loptop dinshi ya kama hanya ya fita daga dakin, Halisa tabi bayansa da kallon ba'kin ciki tamkar ya tarwatsa mata zuciyarta..............Saddiqa na tsaka da aiki a kicin taji an buga mata uwar tsawa! "Ke dan Ubanki waye ya baki dama ki shigo min kicin."!? Jiki na rawa tace." Abbah ne yace na dafa mana tea da indomee." Da hannu ta nuna mata 'kofar fita da fad'in "Fice ki bar min kicin 'yar iska munafuka masu gadon mugun abu." Saddiqa hawaye ne suka tawo mata, tayi saurin mayar dasu tana kokarin fita daga kicin din Halisa ta kai mata ran'kwashi a kanta tana zaginta. Da sauri ta 'karasa ficewa daga kicin din hawayen da take ta kokarin mayarwa suka zubo.......Ganin yarinyar ta fito a firgice yasa ya kalleta yana tambayar ta menene."? Tana share hawaye tace"Babu komai." Tsawa yayi mata da fad'in "Ba zaki fad'a min menene ba."? Tace." Anti ce tace na fice mata daga kicin." Yace."Zoki zauna anan." Kusa dashi ya nuna mata, taje ta zauna tana goge fuska, cikin tausasawa yace."Kiyi hakuri ki daina kuka kinji ko." 'Daga kanta tayi tana goge hawaye, laptop din dake cinyarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya nufi kicin din, Halisa na tsaye tana feraye doya ya shiga ya sameta......Babu walwala a tare dashi yace."Me yasa kika hana Saddiqa ta had'a musu abun kari."?
Juyowa tayi dan ba tasan ya shigo kicin din ba, ganin fuskarsa a murtuke yasa itama ta murtuke tata fuskar tace"Ai sai ka tsaya ka gani idan nayi ban basu ba sai ka bata umarnin tayi musu meye wani zaka ce ta shigo min kicin."!! Girgiza kansa yayi bai ce mata komai ba ya juya ya fita daga kicin d'in, sam bai dauka Halisa za tayi abinci ta bawa yaran ba dan ganin irin rigamar da sukayi ita dashi jiya shiyasa ya umarci Saddiqan ta shiga kicin domin ta samar musu da abinda zasu ci........Suna zaune shida yaran Yaya Ramlatu tayi sallama ta shigo, turus tayi ganinsa zaune a palon, shima cike da mamaki yake binta da kallo, har ta'karaso ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa, Yaran ne suka shiga gaisheta ta dinga amsawa tana washe bakinta.
Cikin nutsuwa ya gaisheta ta amsa tana ta dariya kamar wacce ta shigo gidan da abin arziki, Tace."'Dazu Salim yake sheda min cewar anjima wai za'a daura auranka da Naja'atu hakane ko." ? Yace."Eh insha Allah bayan an sakko daga sallahr za'a daura anan massalacin jikin gidan Alhaji."
Tace."Allah ya sanya alkairi yasa haka shi yafi alkairi, amma banji dadi ba da baka fad'a min ko a waya ba sannan daga can gidan Alhajin ma babu wanda aka turo domin ya fad'a mun sam ba'a daukeni a bakin komai ba, ace maganar daurin auren ma sai a bakin Yarinyar mukaji dan da asussuba ta kira Salim tana kuka tana fad'a masa cewar za'a daura auran kuma idan an d'aura to zata gudu ta bar gari a neme ta a rasa, wannan maganar ta tayar min da hankali sosai saboda nasan yarinyar nan ta gudu to da kai da Salim zaku shiga cikin masifa, dalilin da yasa na umarci Salim din maza ya kira ta a waya sheda mata cewar bai amince da 'kudirin data dauka ba, Kuma nace ya fad'a mata cewar shi tuni ya cire ta a zuciyarsa, dan haka ta daina tunanin guduwa a kansa ta zauna a gidan mijinta tayi zaman aure mai tsafta."
Abbah Abbas ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Yaya Ramlatun yace."Dukkanin abinda ki kaga yana faruwa to dama can haka Allah ya 'kaddara zai faru, ko a mafarki ban ta'ba tsammanin wai zan auri yarinyar nan ba, sai dai kuma babu yanda Allah baya tsara al'amarinsa, mutuwar Halimatu ta janyo min sha'awar auran yarinyar domin ina ganin yarinyar tarbiyar tace kuma zata zame min *MADADIN TA* ta gurin kyawawan halaye da sauransu, sai dai kuma ashe ba haka al'amarin yake ba , Allah shine ya hallici Halimatu ya kuma Hallice Naja'atu a bigire d'aya, sai kuma ya bambamta musu halaye, Halin Halimatu daban Halin Naja'at daban, A jiya mun zauna da Alhaji mun tattauna magana kan cewa na janye bukatata tasan auran yarinyar, zan kuma shige gaba gurin ganin Salim ya mallaketa, a lokacin da naje wa da Baba Malam da maganar shi kuma ya nuna bai amince ba, yace yarinyarsa bata da miji sai ni saboda ni yayi ra'ayin bawa auran 'yarsa, dik yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta, haka nayi musu sallama na dawo gida ina fatan Allah yasa hakan shine alkairi a gare mu baki d'aya."
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*14*
Yaya Ramlatu zagin Baba malam kawai take a cikin zuciyarta amma a Zahiri dariyar ya'ke tayi tace"To ai shikkenan ni a gurina da kai da Salim din duk d'aya ne, kuma na zaunar dashi nace masa ya cire yarinyar daga cikin ransa gabadaya domin kai ba tsaransa bane ballanta ya had'a neman aure da kai."" Abba Abbas yayi murmushi yace."Kwana biyu ma bana ganinshi a kasuwa ko kiransa nayi a waya baya d'auka nasan duk akan hakane." Tace."Ai yanzu komai ya wuce na nuna masa dama can kai kafi cancanta daka auri yarinyar." Murmushi yayi yana girgiza kansa, gaskiya bai tsammaci zai zauna da Yaya Ramlatu haka suyi magana ta fahimta ba yaji dadi sosai da sosai data fahimce shi.
Yaya Ramlatu a gidan ta karya kummalo suka shiga daki ita da Halisa, suna 'kulle-'kullensu, Halisa ta fad'a mata duk yanda sukayi da mijin nata da maganar zai bata kudi ta had'o lefe kuma zai sanja mata mota bayan haka kuma yace ta fadi duk abinda take so zai bata kudi ta siya.....Jin haka yasa Yaya Ramlatu tace"Kinga aikin malam ya fara yi ko ai dama na fad'a miki sai Abbas ya dawo tafin hannunki sai yazo yana miki rawar jiki, dan haka ki daina d'aga hankalin ki kan auransa da yarinyar nan nasan idan muka ri'ke Malam mai al'mutsutsai! a hannunmu to bukatar mu zata biya dama kuma babban burin ki shine ki mallaki Abbas a hannu ina ganin nan da 'kan'kanin lokaci zaki mallake shi da duk wani abu nashi tunda har ya bud'e bakinsa yace miki dashi da duk wani wanda yake 'kar'karshinsa a 'kasan ki suke to kinga kuwa ai sai ki godewa Allah ki sake tanadar kudi masu kauri domin tukwici ga malam bisa ga aikin alherin da yayi miki." Halisa tace."Nifa Yaya Ramlatu sai nake gani kamar dan zai yi aura ne yasa yake kwantar da kansa ba wai asiri ne yayi tasiri a kansa ba, ki duba fa ki gani tsayin shekaru nawa muka dauka muna yawan bin malam tun Halimatu na raye asiri baya tasiri a jikinsa, sai yanzu."
Yaya Ramlatu ta 'bara rai tace"Kada ki sake wannan maganar, wato duk kokarin da nake miki bakya gani sai kin 'karya ta ni! kin 'karya ta aikin malam to babu ruwana wallahi idan kika lalata a aikinki, kada ki sake cewa na taimaka miki, inaso ki sani ko wane malami da irin kalar aikinsa, wani da ruhainai yake aiki wani kuwa da turawan aljanu yake aiki wani kuwa da ba'ka'ken aljanu yake aikinsa, to shi mai al'mutsutsai da ba'kaken aljanu yake aikinsa, idan kin san ba'kar wuyar da muka sha nida 'Yar shagamu kafin mu je zauren malam d'in sai kin tausaya mana, amma kin samu aiki yayi shine kike 'karyata wa to wallahi babu ruwana."
Halisa ganin ran Yaya Ramlatu ya 'baci sai ta shiga bata hakuri tace"Ba wai ina karyatawa bane nasan kina kokarina akaina kiyi hakuri dan Allah." Yaya Ramlatu tace"Koda can ma ba wai asirin ne baya tasiri a jikinsa ba yana tasiri sai dai yana saurin karyewa ne saboda yawan addua da zama da alwala dashi mijin naki yake, amma nasan wannan aikin da akayi masa zai dade kafin ya bar jikinsa."
Halisa ta sauke ajiyar zuciya da fad'in "To shikkenan insha Allahu zanyi kokarin ganin na kauda duk wani abu dake raina dangane da auran, ammafa nace ban yarda ya raba mana gida ba dan ina ganin kamar za'a cutar dani, sannan kuma wa 'yan nan 'ya'yan nasa daya kawo min sam bana son ganinsu wallahi."
Yaya Ramlatu tace"Eh kina da gaskiya gwara ya had'aku a gida d'aya duk da nasan ba wani d'okin auran yarinyar yake ba amma hausawa nace wa amarya ko mahaukaciya ce dole ayi d'okinta, dan haka tana tarewa ya kwashe yara ya kai mata dama ai saboda ta zama *Madadin* Uwarsu ya aureta."
Halisa tace"Yace idan an d'aura auran sai bayan sati biyu zata tare." Yaya Ramlatu tayi shuru tana nazarin maganar tace"To shikkenan sai ki hakura ki ri'kesu kafin lokacin amma ban amince ki zalince su ba tunda basu ne sukayi miki laifi ba." Cike da mamaki Halisa ke kallon Yaya Ramlatun wato idan ta fahimta tana so ta nuna mata cewar ita tana 'kaunar 'ya'yan d'an uwanta, Halimatu da Naja'atu ne bata kauna! To idan hakane kuwa 'kiyayyar da take musu ba takai har zuciyarta ba tunda ba zata bari a zalinci jininsu ba.
To Duk abinda Allah ya tsara ya hukunta sai ya kasance dama haka al'amarin yake mutum baya ta'ba tsarawa kansa rayuwa sai irin wacce Allah ya tsara masa, Abba Abbas da Naja'atu ko a mafarki basu ta'ba tsammanin zasu zauna a inuwar ma'aurata ba, sai gashi Ubangiji ya zartar da ikonsa a kansu, Sai gashi a yau jama'a masu yawa suka sheda daurin auransu, kowa sai fatan alkairi yake gami da fatan zaman lafiya, Alhaji Sama'ila da Baba Malam da Abba Magaji bakin su ya'ki rufuwa sai gaisawa suke da jama'a Abba Magaji na raba goro da alawa fuskarsa tamkar gonar audiga........Shi kuwa ango fuskarsa kadaran kadahan yana ta mi'kawa abokanshi hannu suna gaisawa suna taya shi murna da fatan alkairi yana amsawa fuska d'auke da murmushi.
Cikin gida kuwa, Naja'atu kasa gane kanta akayi ta rufe d'aki! da sakata, sai kuka take tana kiran mutuwa tazo ta dauketa, Baba Talatu da 'yan uwanta da suka cika gidan hankalinsu ya tashi suka dinga buga 'kofa suna kiran sunanta, tana jinsu tayi shuru sai ihu! take tana birgima 'kasan d'akin.
Baba Talatu ta fashe da kuka tana fad'in "Wannan yarinya tana so ta jawo min abin kunya a idon jama'a innalilihi wa'ina ilahi raji'un! Daki ta shiga ta zauna gefan gado tana share hawaye babu shakka Naja'atu ta fita zakka a cikin 'yayanta.......Abba Magaji ne ya shigo gidan ya gansu tsaye a kofar d'akin! Gashi sai gunjin kukan Naja'atun yake ji daga cikin d'akin, Ya karasa gurin da sauri yana tambayar ba'asi.........Baba Larai wacce ta kasance Yaya ga Baba Talatu itace tayi masa bayani duk abinda ke faruwa, Ya shiga bubbuga kofar yana kiran sunanta, tana jinsa taki kulashi.
Cikin rarrashi yace." Naja'atu bude kofa kinji ko duk kinsa hankalinmu ya tashi yi hakuri