Author : Binta Umar Abale Category : Romance
ta'ki zama a makaranta malam na kaita kafin ya dawo gida ta rigashi, ki tafi da ita ku sata a makaranta tayi karatu watakila idan taga babu idanmu zata zauna a makarantar.
Halima tace"Aikuwa dai bari Baba Malam ya shigo na fada masa.......To koda Baba malam yaji kudirin Halima na tafiya da Naja'atu gidanta, be'ki ba yace dai idan taga da akwai matsala to ta dawo da ita." Baba Talatu ta hada mata kayanta tsaf suka tafi.
*Wannan shine mafarin dawowar Naja'atu hannun 'Yar uwarta, a lokacin tana da shekaru hud'u a duniya dalili kenan da yasa ta girma da tunanin cewar Abba Abbas da Halimatu sune suka haifeta.*
Ita kuwa Halisa koda ta fita kai tsaye tudun wuzurci ta nufa gidan Yaya Ramlatu! basu ja dogon lokaci ba suka dauki hanyar gidan *'Yar Sa'adu* abin mamaki mata ne dan'kam! a gidan! d'aki guda idan waccan ta shiga ta fito sai waccan ma ta shiga ta fito har akazo kansu! koda suka shiga dakin *'Yar Sa'adu* na zaune kan wata kujera katuwar macace mai ki'ba taci uwar kwalliya ga hancinta da wani abu mai kyalli a jiki, hannu da wuyanta duk gold ne! taci ubab bleecig kana ganinta kaga 'yar duniya, suka gaisa da juna, Halisa sai kallon dakin takeyi ganin ko ina manne da hotonan mace da namiji tsirara! sannan ga wasu manya manyan drowars ko wanne kayan mata ne a cike a gurin kala-kala! Yaya Ramlatu ta ciro kudin jakarta dubu talatin da biyar ta zube gaban *'Yar sa'adu* tace" Uwar dakina wannan itace matar 'kanina da nake baki labari gata nan na kawo miki ita don Allah ki san maganin da zaki bata wanda zai sanya ta mallaki mijinta ita kad'ai."
*'Yar Sa'adu* tasa dariya ta bata hannu suka tafa tace"Lallai 'kawata kina ji da matar 'kanin nan naki! Allah yasa idan ta samu duniya ta tuna dake, akwai wata mallaka da zan bata! Amma gaskiya tana da tsada kuma naga kudin da kuka ajiye bashi da yawa! Wannan mallakar tana da sirri dan da yawa mutane sunyi amfani da ita sun tabbatar da gaskiyar maganata, ina zaune ake zuwa anayi min tukwuci da kujerar makka had'e da gida da filaye, dan haka idan kuna da bukatar na baku ita to gaskiya zaku ajiye min dubu dari biyu."
Halisa tayi saurin kallonta tana marairaice fuska tace"Dan Allah ki bani wallahi nayi miki al'kawarin idan bukata tabiya zanzo na kawo miki kudinki har inda kike." Ramlatu tace"Eh kwarai kuwa ni zan zama sheda a tsakaninku tunda dai kin tabbatar da ingantuwar maganinki to ki amince ki bamu insha Allah cikin sati guda za'a kawo miki sauran kudinki."
*'Yar Sa'adu* tayi shuru tana tunani! Wani littafi ta dauko ta mikawa Halisa da biro tace"To na amince zan baki amma kisa hannu! sannan ki rubuta abinda kika bani da farko."
Halisa ta kar'ba da sauri tasa hannu! sannan ta rubuta kudin data bayar dubu talatin da biyar! *'Yar Sa'adu* ta kar'ba ta ajiye, sannan ta mike taje ta dauko mata wata 'yar mitsitsiyar kwalbar fiya-fiya! wani abu mai mai'ko da yau'ki! ne a ciki tace"Gashinan duk sanda zakuyi auratayya da mijinki to sai ki lakata kad'an a d'an yatsan ki! sai ki tofa maliki yaumin dini 'kafa takwas a jiki sai ki lakata maganin a gabanki, kafin kwana biyu zaki bani labari." Halisa ta dinga washe bakinta tana godiya, *'Yar Sa'adu* tace''Mijin ki zai zame miki kaska sannan ba'kin ciki zai kashe kishiyarki wannan shine la'kanin maganin." Wani sanyi ya sauka a zuciyoyinsu jin abinda 'Yar Sa'adu ta fada, godiya sukayi mata sosai tare da al'kawarin insha Allahu cikin satin nan zasu kawo mata kud'inta........
*Ayar Allah da ita ake wasa, wai kuma mutum yace yana so yaga dai-dai a rayuwarsa, Ubangiji Allah ka karemu daga fad'awa halaka*
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #400 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
*5*
Kamar dai yanda 'Yar Sa'adu tafad'a musu hakane ya kasance, kwana biyu zamantakewar gidan ta samu tangard'a! Abbas hankalinsa ya dauke gabad'aya baya ganin kowa a gabansa sai Halisa! Komai ta tambayeshi baya yi mata musu da gardama, kuma koda ya duba gurin da yake ajiyar kudinsa yaga ba yanda yake ba, da yayi mata magana kai tsaye tace"Ita ta dauka tayi ba'ki ta sallamesu! shuru yayi mata baice komai ba, tana ganin ya shiga toilet ta bude drowr ta dauki dauri d'aya ta mayar ta rufe! Sai da ya fita sannan ta lissafa kudin dubu dari ne, kai tsaye ta yafa mayafinta ta nufi gidan Yaya Ramlatu da kudin, Gidan 'Yar Sa'adu suka nufa, nan Halisa ta zauna tayi ta basu labarin yanda al'amura suka kasance ta dinga basu labarin irin abun da Abbas din yake mata idan suna kwance da daddare! 'Yar Sa'adu da Ramlatu suka dinga dariya suna tafawa! ita kuwa Halisa tace"Ai gaskiya maganin nan karshene kuma yaci kudinsa, dan a tsakanin kwanaki bakwai d'in nan sai da na samu kudi a gurin sa sama da dubu dari! kullum in zai futa sai na tambayeshi kudi kuma sai ya bani! baya tambaya me zanyi na lura yana tsoron kada dare yayi yazo da wata magana nace masa wani abu daban." 'Yar Sa'adu ta gyara zamanta kan kujera tana dariya had'e da 'kas-'kas! da cingum din bakinta, tace"Ke waye ya fad'a miki dama mata na zama yanzu! ai yanzu dama na hannuki kiyi kiyi ki samu abunda kika samu kuma ba zama zakiyi ba idan maganin ya kare ki sake zuwa ki siyi wani."
Halisa tace"Insha Allahu ai na gane hanya kuma." Cike da farin ciki sukayi sallama da 'yar Sa'adu suka nufo gida.
****
Bayan wata uku kullum jiya iya yau a gidan, Halisa ta k'wace miji gabadaya Halimatu ita dashi sai ido da gaisuwa, Kullum kafin ya futa zai shigo su gaisawa ya zauna suyi ta wasa da Naja'atu! yana kaunar yarinyar sosai kasancewar sa mutum mai son 'yaya gashi har yanzu Allah bai bashi ba! Itama Naja'atu d'an zamanta a gidan ta saba dashi sosai idan ya shigo zuwa take ta zauna a cinyarsa tayi tai masa labarin makaranta da kawayenta shi kuma ya dinga biye mata, dan wataran gurin tsayawa sauraran shirmenta har makara yake a kasuwa, Idan kuwa zai futa sai ya tambaye ta me take so ya siyo mata, sautu iri-iri take masa na kayan wasa dasu biscuit da chocolate, aikuwa duk abinda tace ya siyo mata baya mancewa sai ya tsaya a danja ya siya mata ya shiga ya kai mata, wannan abinda yake yana masifar 'batawa Halisa rai! ta tsani taga yana nuna kulawarsa kan yarinyar ko kadan tana so kamar yanda ya banzatar da Halimatun to ya kasance itama yarinyar itama ya daina kulawa da ita, Idan tana fushi kan abinda yake wa Naja'atun har mamaki take bashi, rabuwa yake da ita idan tayi ta gaji sai ta hakura.
Ita kuwa Halimatu ganin yanda yake kula da kanwarta yasa ta rage jin zafinsa a zuciyarta, addua takeyi kullum Allah ya karkato da hankalinsa kanta tabbas tasan abinda yake yi ba a hayyacinsa yake ba, tunda tasan irin kauna da son da yake mata, babu shakka Halisa ba'a haka ta barshi ba.
To Haka dai Halimatu ta cigaba da zaman hakuri a gidan, tana ji tana gani mijinta yafi karfinta dan sai yayi wata biyu uku bai kwanta da ita gabadaya an cire masa sha'awarta a cikin zuciyarsa.
*IDAN RABO YA RANTSE*
Ranar Juma'a bayan an sauko daga massalaci ya dawo gida a gajiya ga kuma sha'awar dake damunsa tun daran jiya dan kwana sukayi rigima da Halisa ta yanko masa uban kudi wai sai ya bata sannan zata amince ya biya bukatarsa, shi kuma yace ba zai bayar ba sai ta fada masa abinda za tayi dasu, nan ta shiga inda-inda! ya fahimci bata da hujja sai yace ba zai bayar ba, shine tayi fushi tace itama ba zata bashi kanta ba, da yake mutum ne mai zuciya kawai sai ya kyaleta ammafa daurewa kawai yake dan baida hakuri ta wannan 'bangaran......Washe garin ranar Halisa naganin ya futa itama ta shirya ta futa itama ta nufi gidan Yaya Ramla domin tafada mata abinda yake faruwa.......koda ya shigo gidan kai tsaye gurin Halisa ya nufa gabadaya idonsa a rufe yake bukatarsa kawai yake so ta biya yanzu ya amince zai bata kudin mutukar dai zata biya masa bukata.
Ya dubata ciki da waje bata gurin, rai a 'bace ya nufi gurin Halimatu, suna Tare! Da Naja'atu a palo tana koya mata karatu ya shigo bakinsa dauke da sallama!
Naja'atu ta mike a guje taje ta d'ane jikinsa tana fad'in "Oyoyo Abbana."! Dariya yasa ya mi'ka mata kumatunsa kamar yanda suka saba! aikuwa ta manna masa kiss a gurin! shima yayi mata sannan ya sauketa kasa, yana d'an ya mutsa fuska ya kalli Halimatu dake ta faman yi musu dariya! hannunsa ya mi'ka mata da fad'in " Ranki ya dad'e zo muje daki ina da magana." Halimatu ta tsira masa ido tana kallonsa da mamaki a tare da ita!
Gira ya daga mata yana yi mata wani irin kallo. Girgiza kanta tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa, lallai wato sai yau take da amfani a gurinsa kenan! duk sanda yake cikin halin sha'awa tana ganewa.
Ji tayi ya kamo hannunta ya mikar da ita tsaye, gudun kada yayi abun kunya a gaban Yarinya yasa tayi saurin cire hannunta tace"Kaje ganin nan zan shigo." Babu kunya ya nufi bedroom dinta yana wata irin tafiya.
Zama tayi kan kujera tana kallon Naja'atu na rubutunta sai da ta tabbatar abinda take ya dauke mata hankali sannan ta mike a nutse ta bishi dakin.
Wannan had'uwar tasu ta firgita Halimatu gabad'aya mijin nata ya sanja mata hallitarsa ma kamar ta sauya, ya zage karfi a kanta yana bugunta babu tausayi da jin 'kai irin wanda yake mata, sosai yake sarrafata salo-salo duk ya fice daga hayyacinsa itama sai wuya yake bata, kukan wahala take masa tana bashi hakuri ya saurara mata haka, sam ba haka ya saba yin mu'amula da ita ba, da kyar ya saurara mata ya kwanta gefanta yana maida numfashi........To tun daga wannan had'uwar Ubangiji ya zartar da ikonsa ciki ya shiga ya zauna daram a mahaifar Halimatu, cikin kuma da bai bayyana kansa ba sai da yayi wata hudu tukkuna sannan Allah ya bayyana shi, saboda ita kanta Halimatu bata san da ciki a jikinta ba kasancewar ba ko wane wata take al'ada ba shiyasa duk ta rikirkice, ta dinga kokwanto a kan ciki.......Kai tsaye asibiti ya dauketa sukaje, likita ta dubata sosai dan har scanning akayi mata ciki wata hudu kuma yana cikin koshin lafiya. Abbas ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki, tun a mota ya kira wayar mahaifiyarsa ya sheda mata abinda ke faruwa, Hajiya Abu tayi murna da farin ciki sosai ta kuma yi addua kan Allah ya sauke ta lafiya........Halisa kwanan kuka tayi da taji labari wai Halimatu nada ciki, ya akayi haka ta faru? wai dama mijin nata ashe yana lallabawa gurin Haliman yana biya bukatarsa bata sani ba, lallai zai shigo ya sameta.......Shi kuwa da farin ciki a tare dashi yake sake jaddada mata k'aruwar da ya samu! ta hasala! sosai ta dinga zazzaga masa rashin kunya kamar zata zage shi! aikuwa ta fuskanci 'bacin rai! dan lafiyayyun marika tasha wanda hakan bai ta'ba faruwa ba tsayin shekarun auransu, Yayi mata gargadi sosai kan tsaurin idon da take masa kana kuma ya dauke mata wuta gabadaya ya daina kulata, ya tare sashen Halimatu!!
Halisa ta zama tamkar mahaukaciya gashi *'Yar Sa'adu* bata gari ta tafi Nijar dama 'Yar can ce kullum ita kenan a tafe gurin zuwa gidan Yaya Ramlatu, suna tattauna yanda zasu 'bulluwa al'amarin, Ramlatu tsoron zuwa gidan takeyi saboda tasan halin 'Kanin nata zai iya kunyatata shiyasa ta zauna a gida, Halisan na zuwa inda take................Sau uku yana dawowa gida ya tarar bata nan a'lamarin da ya fusata shi sosai, ya tsaya harabar gidan nashi yana kai kawo kana ganinsa kasan ransa a 'bace yake, Tana shigowa ya buga mata tsawa da fad'in "Ta koma inda ta fito! gabanta ne ya fad'i baki na rawa tace''Wallahi naj.......Hannu ya daga mata yace." Bana bukatar naji komai daga bakinki sau uku ina dawowa gida bakya nan ina kike zuwa ba tare da na sani ba? saboda haka ki fuce min daga gida sai nazo gidanku inaso kafin nazo ki fada musu inda kike zuwa."
Halisa ganin yayi fushin mai tsanani yasa ta juya jiki a sanyaye ta futa daga gidan, kai tsaye gidansu ta nufa tana kuka.
A takaice dai sai da Halisa tayi sati biyu a gidansu sannan Yaje yayi bikon ta iyayenta ran su ya 'baci sosai jin irin abinda take aikatawa na fita yawo ba tare da izinin mijinta ba mahaifinta yace da Abbas duk sanda ta sake futa bata fada masa ba to ya sanar masa sai ranta ya 'baci sosai! Halisa ta tsorata sosai d'a zaman da tayi a gidansu har jikinta ya soma sanyi tsayin sati biyu da tayi a gidan nasu ji take tamkar shekara biyu tayi, ganin ya shere ta da ita al'amarinta yasa jikinta yayi sanyi tana addua kada Allah yasa yace zai saketa.....To tunda ta samu yanzu ya mayar da ita sai ta dauki aniyar gyara kuskuranta a gurinsa amma dai duk da haka ba zata fasa yiwa Halima zagon 'kasa ba.
Koda ta dawo gidan d kafin ya sakar mata fuska sai da ta dade tukkuna sannan ya warware gabadaya, tun daga sannan ta kiyaye abinda zai dugunzuma masa zuciya wanda zai haifar da sa'bani tsakaninsu har ta kaishi ga korata gidansu.
***
Cikin Halimatu nada wata bakwai Allah ya bawa Halisa nata, Halisa aka dinga murna da zumudi ana iyayi! shi kuwa maigidan ya dinga biye mata da duk abinda take so burinsa kawai yaga matayen nasa sun haihu lafiya shima ya shiga sahun mutanan da ake kira da Abbah, duk da sunan da Naja'atu ke kiransa dashi kenan Abbana, ko Abban Naja, a duk lokacin da zata kirashi da sunan yakan ji wani iri dan saboda yasan ba shine ya haifeta shi dai yafi bukatar 'yayansa na cikinsa su kirashi da wannan suna.
*****
Lafiya lau Halimatu ta haihu inda ta haifi 'yar ta mace ta d'an d'ebo kammanin mahaifinta gurin hasken fata gami da siririn hanci, Abbas mai kyau ne sosai irin namijin da mata keso yana da haske da cikin zati dogo ne amma ba sosai ba, yana da manya ido da dogon hanci wanda ya kyata masa fuskarsa, amma kuma bashi da fara'a da saurin sabo! Mutum daya ya amince dashi cikin abokansa shine Magaji Yayan matarsa kenan Abba magaji yasan sirrinsa kamar yanda shima yasan nasa...........Halisa ganin Halima ta haifi mace sai ta dinga addua Allah yasa ita ta haifi namiji dan tasan farin cikin da mijin nasu zaiyi sai yafi wanda yake yi a yanzu, hankalinta na masifar tashi a dik sanda taga ya shiga gurin Haliman ya jima bai fito takan shiga tashin hankali da damuwa saboda tasan yana can yana shiriritar da ya saba da shegiyar yarinyar nan Naja'atu da Babynsa wacce ya sanyawa suna Fatima amma sai suke kiranta da *Saddiqa* dalili kenan da ya sanya take Allah Allah itama ta haihu itama taga yana nuna kulawarsa a kan d'anta.
Haihuwar *Saddiqa* ta janyo masa bud'i da alkairai da yawa, harkokin kasuwancinsa suka bude sosai yake harkar gwangila na gina gidaje da ma'aikatu da sauransu........Wani 'katon gida yake ginawa a cikin unguwar *Danbare* sabuwar unguwa ce da masu kudi suka siyeta suke ta gasar gidana gida a gurin, gaskiya gidan da yake idan aka gama aikinsa babu shakka zai zama abun kallo a gurin jama'a.
Halisa ta haihu lafiya lau ta haifi namiji kamar yanda Scanning ya nuna mata, sai dai kuma cikin ikon Allah kwanan yaron d'aya a duniya ya koma.....Ihu! ta dinga zabgawa tana kuka dan rashin tawakkali cewa take wallahi Halima ce tayi mata asiri d'anta ya mutu saboda tana bakin cikin ita bata haifi d'a namiji ba.
Abba Abbas tun yana rarrashinta har ta si'ke shi haushinta ya rufeshi, ya shiga nuna mata illar abinda takeyi, Allah ne ya bata kuma ya kar'bi abinsa dan me zata d'orawa wani! sai da yayi mata kaca-kaca! sannan ta daina ikirarin cewar Halima ce tayi mata asiri.
***
Bayan shekaru uku Halimatu ta sake haihuwa inda ta haifi 'Da namiji! Wanda wannan haihuwar ta janyo tashin hankali sosai a gidan dan iskokai Halisa ta dinga tayarwa na 'karya dana gaskiya tana yun'kurin kashe maijego da jaririnta......Babu arziki ya tarkata ta ya kaita gidansu dan al'amarin yafi karfinsa haka kawai yana ji yana gani ta illata masa d'ansa.
Ashe iskanci ne Halisa na ganinta a gidansu, sai ta dawo hayyacinta mussaman da mahaifinta ya samo malamai, masu ru'kiya suka dinga jibgarta, babu arziki ta dai-dai ta nutsuwarta ta dinga kiransa a waya yazo ya dauketa taji sauki!
Shi kuwa dama tuntuni ya yanke shawara kan cewar zai raba musu gurin zama, dan gudun aikata mummanan aiki idan baya nan shima ya fahimci duk wani abu da Halinsan keyi sharri ne da ba'kin kishi da ganin kyashi!
Gidansa dake *'Dan bare* suka tare shida Halimatu da 'yayansa kana yasa aka gyarawa Halisan wanda suka bari ta zauna a ciki yana ganin hakan shine yafi alkairi a tare dasu baki daya...
Wannan al'amari ya sanya zuciyar Halisa kusan bugawa, gidan da take kulafucin zama a cikinsa shine zai ce ba zai je da itaba, kuka taci ta koshi tana tunanin mafita babu shakka ta ko'ina Halima tayi mata zarra! ta haihu har sau biyu kuma ta tare a