Author : Binta Umar Abale Category : Romance
magana mai muhimanci insha Allah anjima zakuje tare dake da ita ki za'bi irin kayan da kike so domin ita na wakilta ta had'a miki lefe." Tsakaninsa da Allah ya fad'i maganar dan shi yana ganin meye a ciki dan Halisa ta had'a mata lefe ai duk a zaman d'aya!
Ita kuwa Naja'atu maganar ce ta girmi tunanin ta wannan ma ai rainin hankali ne da zaice Halisa ta had'a mata lefe kuma har ya iya fad'a mata da bakinsa, zuciyarta tace mata "To ke meye abin damuwa ai ba sonsa kike ballanta na dan yace Halisa ta had'a miki lefe kiji haushi!!! " Eh duk da ba sonsa nake ba amma ai hakan bai dace ba abin kamar yazo da cin fuska a ciki, to idan ya kasance tana sonsa kuma haka zai dinga d'ora kishiyarta kan al'amuranta abinda ba zata iya jurewa ba kenan don ita ba Yaya Halimatu bace...........Dauk'e kanta tayi ba tare da tace masa komai ba, shi kuma yanayin yanda yaga ta nuna sai yaji wani farin ciki ya lullu'beshi yana addua Allah yasa yarinyar ta soma sonsa......Yana shiga daki, Ita kuma ta shiga fad'a da zuciyarta ganin kamar tana so ta takura mata gurin ganin kamar anyi mata rashin adalci a gidan zuciyarta sai ingizata take akan ta dauki mataki ta bishi daki ta tambaye shi me tsaya yayi a dakin Halisa har tsayin awa uku alhalin yasan a cikin kwanakin auranta yake, sannan kuma tace ita bata yarda Halisa ta had'a mata lefe ba!.....Allah mai iko! abinda zuciyarta keta sa'ka mata kenan duk ta kasa samun nutsuwa a gurin sai kallon kofar dakin nasa take tana tununin taje ko kada taje? Mikewa tayi ba tare da dogon nazari ba ta nufi dakin nasa har tasa hannu zata bude kofar sai kuma ta fasa, ta juya cikin sanyi jiki ta nufi dakinsu Saddiqa kwanciya tayi ruf da ciki kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka.
*Tofah!🤔 Ko kukan me Naja'atu take? Ita da take ikirarin bata kaunar Abbah Abbas din to meye najin haushi dan ta ga ya dad'e a dakin matarsa? Lallai akwai alamun tambaya dangane da Al'amarin.................Akwai-Akwai_Akwai!! Rikita_Rikita anan agaba! Wai shin ya zata kaya ne a tsakanin Abbah Abbas da Amaryarsa? Shin zai samu nasarar kar'bar budurcinta ko kuwa? Salim zai kyale Naja'atu tayi rayuwar aure da Mijinta Kuwa? Wane Babban kuskure Naja'atu zata tafka anan gaba? Meye makomar Yaya Ramlatu da Halisa? akwai sauran labari anan gaba!!!! Ga duk wanda yake da ikon biyan kudin littafin nan ya biya ya karanta #300 ko #600 basu isa su biya kudin littafin nan ba😅 Koda yake ai 'KARYA ce amma dai ni nasan 'karyar tawa tana Tasiri a wani gurin dan haka da kai da ke ina so duk ku biyo ni domin a cigaba da tafiyar daku Single #300 Vip #600 Babu tsada🤗 Kada ki nuna ganin 'kyashin biyan kudi ki karanta kice bari ki bari idan an sato ki kiranta Allah ya isa! Idan anyi magana kice kema gani kikayi an turo shiyasa kika karanta, to duk wanda ya'ki sharar massalaci zaiyi ta kasuwa!🤗*
*Masu had'a min decoment na books daga zarar na gama bazan ce komai ba sai dai na ro'ki Allah ya tattara muku zunuban da na d'auka gurin rubuta littafin ya d'ora muku a kanku😅Shikkenan sai a raba mana zunubin tare daku kun rage min nauyi.*
*Masu tambayar wai ni bana littafin free ne sai na kudi: Amsa To farkon littafina Nana Khadija Free ne zagi da 'korafi gami da rashin hakuri irin na redars yasa na mayar dashi na kudi, tun daga haka shikkenan na daina littafin kyauta amma akwai book dina RUWAN DARE free ne book1 yana nan yana yawo a groups ga duk mai bukatar karantawa sai ya tambaya a groups insha Allah idan na gama rubuta littafin MADADI zab cigaba da typing d'insa RUWAN DARE free ne bana kudi bane! idan na gama Madadi zan cigaba da rubuta muku shi🤗*
*Masoya masu sahihiyar kauna Ina alfahari daku♥️*
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*