Author : Binta Umar Abale Category : Romance
dawo nan kenan na dauki akwatin kayan ki na kai miki dakinmu."? Kanta ta d'aga masa idanunta na kawo ruwa, da sauri yaron yaje ya shiga jan jakar kayan Saddiqa ta mike taje tana taimaka masa, Naja'atu binsu tayi da kallo hawaye ya zubo mata tausayi yaran suka bata, tana ganin ko dan saboda su zata dinga adduar Allah ya sanya mata dangana domin ta zauna tare da dasu.......Halisa ce ta fito daga kicin hannunta ri'ke da tire jere da kayan tea ko kallon inda Naja'atun take ba tayi ba tayi ba ta nufi dakin maigidan, Naja'atu ita dai binta da kallo kawai take..........
Yana zaune 'kasan kafet ta shiga dakin, ajiye tiren tayi ta zauna tana kokarin had'a masa tea din yace."Ki bawa Naja'atu abinci dan bana tsammanin taci wani abu tun jiya." Kallonsa tayi kamar za tayi magana kuma sai ta fasa, ta hada masa tea kana ta zuba masa farfesun kayan cikin rago wanda yaji magani! ta mike ta fita daga dakin...........Saddiqa ta kalla tace"Ke Saddiqa ki shiga kicin ki girka muku abinda zaku ci dan ni ba baiwar kowa bace."! tana gama maganarta ta shiga dakinta......
Saddiqa ta mike da sauri tana kallon Naja'atun tace."Don Allah Yaya Naja'atu kada ki kulata." Murmushin takaici tayi tace."Jeki yi aikin ni ba'a gabana take ba ballanta na tanka mata." Saddiqa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce kicin din, mikewa tayi ta nufi dakin su Saddiqar nan ta tarar da Mussadiq yana ta jera mata kayanta a cikin wardorbe dinsu, Tace"Mussadiq daka bar kayan ma a jakar da yafi." Yace."Ai akwai guri a wardrobe din shiyasa nake shirya miki kayanki a ciki." Zama tayi tana bin dakin da kallo, gado uku ne kananu irin na 'yan boarding....Mussadiq yace."Yaya Naja'atu zan baki gado na ki kwanta kafin Abbanmu ya kawo miki naki." Tace"To nagode Mussadiq." ya mike da sauri yana fad'in "Bari ma naje na fada masa." Kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin....Dakin Abban nasu yake kokarin shiga Halisa ta hangoshi tsawa ta buga masa da fad'in "Me zaka shiga kayi."? Yace."Zan fad'awa Abbanmu ne cewar Yaya Naja'atu bata da gado." Cikin tsawa! tace"To sarkin iyayi da rawar kai ai ya fika sani." Abbah Abbas din ne ya fito daga dakin nan Halisa ta gyara yanayin fuskarta Tace."Gashinan wai yana so ya shiga yayi magana da kai shine nace masa kana cin abinci sai ka fito tukkuna." Ya kalli Mussadiq din a nutse yace."Menene."? Mussadiq yace."Abbah Yaya Naja'atu bata da gadon kwanciya amma kayanta sun samu guri a wardrobe d'in mu." Murmushi yayi yace."Gaskiya Magaji kana son Yaya Naja'atu sosai kada ka damu zansa a kawo mata gadonta itama." Murmushi yaron yayi yace."Nagode Abbah." Cike da farin ciki ya nufi dakin nasu yana so yaje ya fad'a mata abinda Abban nasu yace..........Abbah Abbas fita yayi daga gidan ya tafi sabgoginsa sai yamma likis ya shigo unguwar kuma bai shiga gidan ba sai bayan sallahar isha'i, Halisa yau ma ta cancad'a kwalliya kamar itace amaryar tana zaune a palo ita da yaran suna kallo kamar jiya, ita kuwa Naja'atu ta kasa zama a palon tana d'aki ta takure kanta sai neman Salim take a waya bata shiga.....Hannu bibbiyu Halisa ta kar'be shi, ta bashi abinci yaci kamar koda yaushe ya dawo palon ya zauna nan yaga babu Naja'atu a gurin, Ya kalli Mussadiq da fadin "Ina Yaya Naja'atu." Mussadiq yace."Tana dakinmu nace ta fito muyi kallo ta'ki." Kai tsaye yace."Je ka kirata." Yaron ya tashi da sauri! ita kuwa Halisa shan kunnu tayi ta wani tamke fuskarta....Da hijab a jikinta suka fito ta zauna kan kujera kanta a kasa tace"Abbah Sannu da zuwa." Ya amsa yana nazarinta yace."Me kike a daki ke kad'ai bayan kowa na palo." Shuru tayi, Ta kalli Halisa a nutse yace."Inaso nayi magana daku a dakina." Mikewa yayi ya nufi dakinsa." Halisa ta mike tabi bayansa, ita kuwa Naja'atu gyara zama tayi dan bata fahimci maganarsa ba, Minti biyar da shigar Halisa dakin nasa Kira ya shigo Wayarta koda taga numbarsa sai gabanta ya yanke ya fad'i! ta dauki wayar Yace."Ki shigo dakina zanyi magana daku." a raunane tace"To." Kashe wayarsa yayi, Halisa kam sai jijjiga kafa take ta cika ta batse sai wani 'kas-'kas take da cingum din bakinta, Ya kalleta cikin 'bacin rai yace."Malama ki cire wannan cingum din na bakin ki." Ta daina 'kas-'kas din tayi ta dauke kanta......Da 'kyar ta iya mi'kewa ta nufi d'akin nasa yayin da yaran suka bita da kallo, Saddiqa dai duk tafi su hankali ta gane Yanzu Yaya Naja'atu dai-dai take da Anti Halisa a gidan to dan ta shiga dakin Abban nasu ba abun mamaki bane.......
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~
_*Aunty Binta wai dan Allah me yasa duk littafin ki kike bawa maza Power akan mata ni dai duk na karanta novls din 'ki ban ta'ba ganin wanda kika bawa mace power ba*😅_
_*MAFI A KASARIN TAMBAYAR DA MUTANE KEYI MIN KENAN WAI ME YASA NAKE BAWA MAZA POWER! A LITTAFIN NA, TO GA AMSA, BANI NA BAWA MAZA POWER (IKO) BA ALLAH NE YA BASU, NAMIJI IN DAI SUNANSA NAMIJI TO KOMAI 'KAN'KANTARSA SAI YA JAGORANCE KI KODA KUWA KE KIKA HAIFE SHI, TO BALLANTA NAMIJI A CIKIN GIDANSA😅 TO AI NI KO LOKACIN DA NAKE KARATUN LITTAFIN HAUSA DAGA NA FARA KARANTA LITTAFI NAGA AN BAWA MACE POWER A KAN MIJINTA NAKE DAINA KARANTAWA DAN NA TSANI LUSARIN NAMIJI WANDA BAYA IYA JAGORANTAR GIDANSA, MEYE AMFANIN POWER MACE A GIDANTA🤔 IDAN YA KASANCE KINA JUYA MIJIN KI TO ME KENAN AKAYI? AI DUK GIDAN DA KUKA GA MACE NA MULKI A CIKINSA TO TA KAUCE HANYA NE, NI DUK MACEN DAKE MULKI A GIDAN AURANTA TANA JUYA MIJINTA YANDA RANTA YAKE SO WALLAHI BATA BURGENI SABODA NASAN 'KARSHEN TA NADAMA! MATA SU ZAUNA A 'KARKASHIN MAZAJEN SU KAMAR YANDA ALLAH YACE, SU KUMA MAZAN SU KULA DA DUK WASU HAKKO'KIN MATAYEN SU, AMMA BA WAI INA FIFITA NAMIJIN NOVEL AKAN MACEN NOVEL BA INA SO INA NUNA MUKA ABINDA YAKE FARUWA A ZAHIRI SHINE NAMIJI KO MAI 'KAN'KANTARSA JAGORA NE😁*_
*17_18*
Kanta a 'kasa ta shiga dakin da sallama a bakinta, Shi kadai taji ya amsa sallamar dan ko Halisa ta amsa ita dai ba taji ba.
Kusa da Halisan ta zauna tare da sunkuyar da kanta 'kasa, dakin ne yayi shiru na tsayin minti uku kafin yayi gyaran murya kamar yanda ya saba idan zaiyi magana yace." Gabad'ayan ku nasan kunsan abinda yasa na tara ku anan ko."? shuru sukayi babu wacce tayi magana.
Ya kalli Halisa a nutse yace."Tun kafin na kawo miki Naja'atu gidan nan mun gama magana dake ina fatan zaki kar'bi yarinyar nan hannu biyu ki dauke ta a matsayin *'ya* ba kishiya ba, wannan kad'ai za kiyi min ki nuna min ke mai kaunata ce." Halisa ta d'ago kanta da sauri ta kalleshi, lallai sai ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ba kishiya ba sannan zai gane ita mai kaunarsa ce maganar ma mamaki ta bata sosai kuma ta 'kara tabbatar da cewar namiji bashi da kunya, komai 'kan'kantar kishiyarta yaushe zata dauke ta a matsayin *'Ya* wannan magana ma bai mai yiwu bace. To shima dai da ya fad'i maganar yasan abune da ba zai ta'ba yiwu ba dan ya riga yasan yanda Halisa take da masifar kishi ai da wuya ta ri'ke yarinyar a matsayin *'Ya* ko *'Yar uwa*......Hankalinsa ya mayar kan Naja'atu ya dan tsira mata ido na minti biyu kafin ya kira sunanta.
Da sauri ta d'aga kanta tana kallonsa da idanunta da suka soma kawo ruwa.
Ganin ita yake kallo yasa tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa!
Yace."Ke ma d'azu kafin na kawo ki cikin gidan nan mun gama magana dake kuma ina fatan dukkanin abinda na fad'a miki sun shiga kunnan ki kiji ki kuma shiga hankalin ki, zaman aure kika shigo kiyi a gidana ba shirme da shashanci ba, wannan da take zaune tafi kar'fin raini a gurinki." Yafada yana nuna mata Halisa, bata kalleta ba sai sake sunkuyar da kanta 'kasa da tayi
Ya cigaba da cewa"Duk ina sane da rashin kunyar da kike mata a lokotan baya! bakya ganin girmanta duk irin maganar da tazo bakin ki fad'a mata kike bakya gaisheta a duk inda zaku had'u! tsaki! harara duk babu wanda bakyayi mata, to duk nasan da hakan nake kyale'ki koda ita Halisan zata kawo 'karar ki ina bata hakuri saboda a samu zaman lafiya ina kuma nuna mata ke yarinya ce idan kika kara hankali zaki daina.......Halisa tayi hakuri da halayen ki a baya, dan haka a yanzu kada naji kada na gani kin zageta ko kin fad'a mata bakar magana ko kuma kinyi mata tsaki! tsakaninku mutunci da mutunta juna inaso ki dauki Halisa a matsayin Uwa abokiyar shawararki wannan kad'ai zakiyi min nasan cewar ke d'in tarbiyar Halimatu ce."...............Tsit dakin yayi bayan gama maganarsa Halisa tamkar ta zuba ruwa a 'kasa tasha dan farin ciki taji dadi sosai yau da ya nunawa yarinyar matsayinta a gurinsa, ashe duk yana sane da iskancin da yarinyar ke mata a baya amma bai ta'ba magana ba, ji tayi duk wani haushinsa da take ji ta daina, sai wani murmushi take tana jijjiga 'kafa.......Ita kuwa Naja'atu kanta a kasa ta kasa dagowa dan tasan idan ta dago 'kwallar dake kokarin zubowa daga idananunta zata tona asirin zuciyarta...........'Dan kashingid'a yayi kan bed din yana kallon Halisa babu alamun wasa a fuskarsa yace."Yarinyar nan zata cigaba da zama anan dakin! tunda ya kasance d'akuna uku ne to bai kamata ta kwana cikin yara ba idan yaso ni nabi da'ki-d'aki! kafin komai ya daidaita." Halisa ba haka taso ba amma sai tayi kokarin danne kishinta tace"To shikkenan hakan ma yayi dai-dai ai." Yace."To tunda kece uwargida sai ki shirya yanda al'amarin zai kasance."
Cikin ya'ke! da danne wani mugun kishi tace"Kwana biyu zaka dinga yi kamar dai yanda kake yi lokacin Halimatu." Gemunsa ya shafa yana d'an murmushi yace."Ai na dauka ko zaki sanja tsari ne shiyasa na tambaye ki."? 'Yar dariya tayi tana ta'be baki tace"Kwana bibbiyu shine tsari mai ma'ana idan kuma kafi son kwana d'ai-d'ai to." Ya kalli Naja'atu had'e da kiran Sunanta! A firgice! ta kalleshi dan ita bata san wainar da suke toya ba tana can tunanin ya za'ayi ta fece daga gidan.
Yace."Ke a ganinki kwana nawa-nawa zan dinga yi a tsakaninku."? Murya na rawa tace"Ban gane maganar ba." Mikewa zaune yayi yana kallonta yace."Muna maganar raba kwanan girki ne a tsakaninku shine nake tambayar ra'ayin ki." Shuru tayi wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska wai yau itace Abbah Abbas ke tambayarta maganar kwanan girki.
Ganin tayi shuru yasa ya kalli Halisa yace."Kwana bibbiyu din shi zamu dauka kamar yanda kika ce."Mikewa tayi tana fad'in "Hakan yayi! to ni dai sai dai nace Allah ya bamu alkairi." Hanyar fita ta nufa zuciyarta kamar ta babbake! Kallo ya bita dashi kafin yace."To Allah ya tashe mu lafiya idan kin fita kisa yara su tashi daga kallon da suke suje su kwanta haka." Ai fad'ar wannan magana da yayi sai ya 'kara tunzura ta a fusace! ta bud'e kofar dakin ta fita tare da doko kofar da karfin gaske........Tana fita palon ta raraka yaran d'akinsu sai masifa take tana zaginsu kamar sune sukayi mata laifi......Mussadiq da Saddiqa a tsorace suka bar gurin.
Innalilihi wa'ina ilaiji raji'un! kawai take ta ambata bayan fitar Halisa daga dakin gabadaya Jinin jikinta ya daskare hatta da kafafunta jinsu take sunyi mata nauyi da sanyi tana ji kamar ba a jikinta suke ba.........Gyaran muryarsa taji kafin taji ya kira sunanta, amsawa tayi tana kallonsa ya iya kiran sunanta tamkar a bakinsa a ka rad'ashi.
''Kinci abinci ko."? Yafada yana mata wani kallo na 'kasan ido! 'Daga kanta tayi tana mai dauke idonta daga kansa, Yace." To shiga toilet ki dauro alwala kizo muyi nafila ta godiya ga Allah." Mi'kewa tayi salo-salo ta nufi toilet d'in.........Minti biyar ta fito daure da alwala ya mike ya shiga toilet din shima ya dauro alwala ya fito.
Nafila sukayi raka'a biyu kamar yanda Annabi ya koyar da sababbin ma'aurata! Abba Abbas ya jima hannunsa a saman kanta yana addua kafin ya cire ya d'aga hannunsa sama nan ya jima yanayi wa Allah kirari, daga bisani ya rufe adduarsa da fatihatulkitabi suka shafa ita dashi, mikewa yayi daga kan abun sallahr ya dauki key motarsa dake kan drowar taga ya bude dakin ya fita.
Zukud'un!! tayi bayan fitarsa daga d'akin, ita yanzu abun ma mamaki yake bata gami da tsoro! da gaske dai sai tayi zaman aure dashi, tunda gashin nan har ya zaunar dasu tare da matarsa yana kawo mata tsare-tsarensa harda kashedi da gargadi kada ta zagi matarsa, lallai Abbah Abbas yayi masifar bata mamaki! to ita yanzu ba wannan ne ma yake sake furgitata ba sai kawo ta dakinsa da yayi, to me zaiyi mata? bata da mai bata amsa! mikewa tayi da saurin gaske ta nufi kofar fita, cikin ikon Allah kuwa tana jan kofar ta bude! palon ta fita tana zazzare ido! tv a kashe yaran duk sunje sun kwanta.
Kujerar data zauna a dazu nan ta nufa ta duba wayarta zama tayi kan kujerar ta shiga lalubar numbar Salim.......Lokacin shi yana ma can gidan kallo hayaniya ta hanashi ya daga wayar sai ihu suke shida abokansa sunci 'kwallo.
Text ta tura masa tana hawaye tace.
_Salim anya kuwa kana sona kuwa? tun jiya nake kiran wayarka baka dauka ba ashe dama duk soyayyar da kake min karya kake......Kada fa ka manta kai kad'ai nayi wa alkwarin mallakawa kaina da komai nawa dan Allah kada ka bari Abba Abbas ya samu nasara a kanmu dan gani nan a gidansa a cikin dakinsa ya kulleni kasan hakan da yayi yana nufin abubuwa da yawa, dan haka dan Allah ka daure kayi wani abu akan wannan al'amarin."_
Tura masa tayi tana adduar Allah yasa ya duba ya bata amsa.......Salim shida abokinsa suna cikin mota bayan fitowarsu daga gidan kallo ya dauko wayarsa yana dubawa, ganin Kira da text din Naja'atu yasa yaja tsaki! text din ya shiga dubawa! bayan ya gama karantawa ya nunawa abokinsa, shima ya karanta, dariya yasa ya bashi hannu suka tafa yace."Amma gaskiya yarinyar nan na sonka da yawa, yana da kyau ka fara gudanar da aikinka dan na lura dattijon nan zulamamme ne! ya samu 'karamar yarinya sai 'barin jiki yake kada ka barshi ya lashi zumar nan ta dad'in rai."
Salim yayi wani murmushi yana shafa siririn sajensa yace."Ai wallahi sai na d'and'ana masa d'aci! da bakin cikin daya jefa ni a ciki dan haka bari kaga ni." Sai kawai ya shiga kiran wayar Naja'atun, da sauri ta dauki wayar ta kara a kunnanta.
Salim ya wani narkar da murya cikin sigar yaudara da janye hankali a kasalance yace."My Princess bani da lafiya zuciyata ta kusa ta daina aiki yini nayi ina aman jini! soyayyarki ina tsammanin itace ajalina! na kasa daga wayarki ne saboda ni kadai nasan irin masifar da zan shiga idan naji sautin muryarki, to amma ganin wannan text din naki na yanzu ya firgitani sosai har naji sha'awar na kira ki a waya na gargade ki kan cewar komai rintsi kada ki kuskura ki mallakawa wannan tsohon jikinki kada ki bari ya kusanci inda kike my princess ni kad'ai nasan irin yanda nake jin fleengs a duk sanda na tuno zubin hallitarki hakika na jima ina kwadayin na ganni ina tsotsar bakin ki! sannan babu babban abinda yake d'aga mun hankali kamar breast dinki na jima ina mafarki gasu a hannuna ina wasa dasu ina tsotsa ina lailayasu a hannuna! dan Allah my princess kada ki bari wani yayi amfani da damata duk rintsi duk wuya kiyi min wannan alfarmar."
Tunda yake maganar take 'kan'kame wayar a kunnanta tana sauke ajiyar zuciya tsigar jikinta na tashi, ji tayi gabadaya jikinta ya rikice ta dinga jin sha'awar Salim din na taso mata...........Murya a dushashe tace"My prince kada ka damu zan kula maka da kaina da jikina nayi maka alkawarin babu mai mallakata sai kai kuma insha Allahu zan fito daga gidan Abba Abbas da budurcina muyi auranmu tinda shari'a bata rahamta mana ba."
Salim ya sakeyin 'kasa da murya yace."Yawwa my princess nagode kwarai da soyayyarki gareni nima insha Allahu zan cigaba da yi mana kokarin dan ganin bukatarmu ta biya." Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin magana, taji alamun bude kofar palon..........Da sauri ta mike ta nufi dakinsu Saddiqa da wayar a kunnanta tana magana 'kasa-'kasa tace"Salim gashinan ya dawo zan kashe wayar yanzu." Yace."To shikkenan my Prince. " Kashe wayar yayi ya kalli abokinsa dake draving sai kawai suka kwashe da dariya kamar wasu shashashai! Kamalu yace."Gaskiya Salim ka iya tuggu! yarinyar nan fa gabadaya ta mato a kanka duk maganar daka fada mata da sauri take amsawa kamar wani ubanta." Salim ya shafa sajensa yana dariyar mugunta yace."Ai na fada maka dama gangar jikinta kawai ya aura, amma zuciyarta na tafin hannuna." Yafadi maganar yana nuna hannunsa.
Abbah Abbas ya shigo hannunsa ri'ke da ledoji guda uku, kulle kofar palon yayi kai tsaye ya nufi dakinsa a hannunsa rike da ledojin dake hannunsa................Jim yayi yana bin dakin da kallo sai kuma ya ajiye ledojin hannunsa kasan kafet ya nufi toilet, dan kwankwasa kofar yayi yana kiran sunanta, shurun da yaji ne yasa ya dan tura kofar toilet din yana dubawa, ganin bata ciki yasa yayi saurin fita daga dakin, kai tsaye dakinsu Saddiqa ya nufa domin yasan tana can dan babu wata hanya da zata