Author : Binta Umar Abale Category : Romance
kallonsa sai ta sake rurucewa da kuka tana nuna masa Mommynta dake kwance, baki na rawa tace"Abbanmu mommy ta'ki tashi sai tashinta nake yi gashi babu kyau baccin yamma." Yace."Insha Allahu za tashi ki kwantar da hankali yanxu tashi kije ki sanja kaya kizo ki rakani na siyo mana abinda zamu ci." Jiki a sanyaye ta kalleshi kafin tace"Abbah mommy tayi girki gashi can ta jera kan tevur." murmushin takaici yayi yace."Babu komai a cikin kwanukan dake jere a tevur kawai tayi hakane dan ta 'bata min rai." shuru yarinyar tayi tana nazarin maganarsa, babu shakka akwai abinda ke faruwa wanda bata sani ba
Yace."Maza tashi ki sanjo kaya mu tafi kada magariba tayi." mi'kewa tayi ta dauki jakarta ta nufi dakinta, A nutse ya juya yana kallon Halisa dake sheme 'kasan kafet idanunta duk sun zurma ciki lokaci guda duk ta furgice ta rame, tausayi ta bashi kad'an! ya shiga girgiza kansa mamaki yake sosai Halisa ta kai matakin shekaru talatin da biyar a duniya amma har yanxu ba tayi hankali ba, wai wu'ka ta d'auko zata yi masa rauni kawai saboda zai raya sinnar ma'aiki, to meye a ciki kuma meye abun damuwa dan ya auri Naja'atu, sam bai aikata haram ba sai ma sinna daya 'karfafawa kansa dan ya auri Naja'atu tana da shekaru 16 a duniya a ganinsa ba aibu bane, tunda Annabi Muhammad (s.a.w) ya auri Nana Aysha tana da shekara tara, to kuwa idan hakane ai babu laifi gurin auransa da Naja'atu, wani sa'in mutane sunfi girmama al'ada akan addini shiyasa su suke ganin kamar ya aikata haramci! auransa da Naja'atu kuwa yana tunanin babu wani mahalukin da ya isa ya hana, idan ba'ayi ba to babu shakka Allah ne bai so ba
Mufida ta fito a kintse itama tasha hijab dinta har'kasa, haka yake sawa ana d'inka musu hijab manya manya, kasancewar sa mabiyin sinna kai idan kaga yanda yake mu'amula da mutane da yanda ya tsayar da (gemu) zaka fahimci cewar bai yarda da wata bidi'a ba, abokanshi wataran har tsokanarsa suke idan yana kawo musu 'kauli da ba'adi, koda yake irin wannan dama ya saba faruwa a tsakanin mutane kowa da d'ari'kar da tayi masa shi dai Abbah Abbas 'Dan izala ne sosai dan gabad'aya bai yarda da bidia ba shiyasa bai fiye sakin jikinsa da mutane ba.
Da kansa yake draving din yana tunanin rayuwa da abubuwan da suke faruwa dashi da 'yayansa, babu shakka mutuwar Halimatu babban gi'bi tayiwa rayuwarsa data 'ya'yansa da Halimatu na raye babu wanda zai samu dama a kansa, Kira ne ya shigo Wayarsa dake gefansa ya d'an kalli wayar sai yaga My dota na yawo kan screen din wayar......Dauke kansa yayi ya cigaba da draving d'insa, hakika abinda yarinyar nan keyi masa yana mugun 'bata masa rai!
Ita kuwa Naja'atu cigaba tayi da kiran wayar so take ya d'aga ta fad'a masa magana mai zafi dan yanzu suka gama waya da Salim ya sake tunzura mata zuciyarta, ya fad'a mata duk yanda sukayi da Abba Abbas din dazu da safe da zai kaisu kasuwa, shine ya kira wayarta ya fad'a mata komai ya ingizata kan tayi fito na fito dashi tunda shine ya zubda mutuncinsa, lokacin itama zuciyarta ta gama 'ke'kashewa tana ganin zata iya fito na fito dashi tinda hausawa na cewa idan babban ya zubar da girmansa to shi 'karami sai ya hau ya taka............Kiran wayar take yi jikinta sai kyarma yake tana had'a gumi, shi kuma yana kallon wayar nayi tana katsewa bai dauka ba kamar yasan abinda zai faru.
Mufida tace"Abba ana ta kiran wayarka fa." hankali yace."Mufida bana so ina draving ina amsa waya idan muka sauka zan kira ko waye." Shuru tayi na minti biyu kafin tace"Abbah dan Allah me ya had'aku da Mommyna ta d'auko wu'ka zata caka maka."
Yayi jim kafin yace."Mufida babu abinda ya had'a mu kawai tayi ra'ayin kasheni ne."! Yarinyar tayi shuru na minti biyu kafin tace"Abbah dan Allah kayi hakuri kaji ko." Murmurs yayi yana kallonta yace."Nayi hakuri saboda ke Mufida da mahaifiyar ki nada hankali irin naki da naji dadin zama da ita." Murmushi tayi tana rufe fuskarta tace"Abba nagode Yana farin ciki yace."Ubangiji Allah ya raya min ku tafarkin addini musulunci." Ta amsa da ameen Abbah............Naja'atu kuwa wani 'katon abu ne yazo ya tokare mata a ma'kogwaronta ta jefar da wayar kan katifa ta kwanta rigingine had'e da 'kurawa rufin dakin ido! Abba Abbas ya'ki daga wayarta saboda yasan bashi da gaskiya eh ai dama dole da ya'ki d'aga wayarta saboda ya kasance munafikin mutum kuma azzalimi! Hawaye suka kwaranyo daga idonta.
Muryar Mussadiq taji a kanta yana fad'in "Yaya Naja'atu ya jiki ki tashi kiyi sallah magariba tay.......A fusace! ta mike zaune tana nuna masa 'kofar futa da fad'in " Fita ka bani guri munafikin yaro babu dama na shigo daki na kwanta zai shigo ya dame ni."!
Yaron ya dinga kallonta a tsorace! dan tunda suke bata ta'ba yi masa tsawa irin ta yau ba.
Baba Talatu da Saddiqa sun jiyo abinda ke faruwa ransu ya 'baci sosai Saddiqa ta d'aga labulan d'akin tana kallon Mussadiq din cikin rawar murya tace"Kai Mussadiq fito ka bata guri."!
Cikin sanyi jikin ya juya da niyar fita daga d'akin, gabad'ayansu tabi su da wani irin kallo wanda na kasa tantance ko na meye......Baba Talatu ta kalleshi a nutse cikin tausasawa tace"Mussadiq kada ka 'kara zuwa kace tazo taci abinci ko tayi wani abu Yunwa dai ba 'kanwar uwarta bace da kanta zata nemi abinda za taci , kada ka kara zuwa inda take ballanta ta hantareka ko ta zageka duk abinda take ganin shine dai-dai da Rayuwarta sai taje tayi, tunda Ita ba tajin magana."
Mussadiq da Saddiqa suka zauna tsuru cikin sanyi jiki, sai da malam ya shigo sannan suka samu sakewa suka ci abinci tare dashi yana jansu da wasa da dariya.
Take away yayi musu na abinci mai rai da lafiya ya siya musu lemuka da yught masu sanyi da dad'i! Kowa da nasa ledar, Yana draving ya kalli Mufida yace."Kafin mu koma gida zamu je ki gaisa da 'yan uwanki sai na basu na yught d'in ko." Tace."Yawwa Abba dama nayi kewarsu da Yaya Naja'atu ma." Yace."Zan kai ki yanzu ku gaisa sai mu shiga gidan Alhaji ma ku gaisa dasu Hajiya ko." Tana ta murna tace"Abbah nagode sosai kuma naji dad'i." murmushi kawai yake yi a kaso d'ari na damuwar da yake ciki kaso hamsin ya zube sakamakon nutsuwa da nagartar 'yarsa Mufida, a duk sanda zai kalleta wani farin ciki ne yake lullu'beshi dama haka Ubangiji yake sai ya fitar da shiryayye daga jikin mara hankali, yanzu yanda Mufida take mu'amula waye zai ce Halisa ce ta haifeta, Yarinya 'karama tafi uwarta hankali.........Ana kiraye kirayen sallah magariba suka shiga unguwar 'kofar Na'isa, a bakin gidan Alhaji yayi parking din motarsa, ya umarci Mufida ta shiga gidan Alhajin shi zai shiga massalaci...........tare suka fito daga motar Mufida ta nufi gidan Alhajin shi kuma ya nufi masjid din dake jikin gidan...........Baba Malam ne da Mussadiq suka fito daga gida da niyyar shiga massalaci Mussadiq na ganin Abbansa na daura alwala yayi murmushi cikin farin ciki yace."Baba Malam ga Abbanmu can yazo." Baba malam na fara'a yace."Eh kwarai kuwa watakila zuwansa kenan."
Abba Abbas na ganin zuwansu gurin sai ya mi'ke cikin fara'a ya mi'kawa Baba Malam hannu suka gaisa cikin mutunci Mussadiq ya mika masa hannu yana dariya yace."Abba barka da zuwa."Ya amsa da barka dai Mussadiq." Alhaji Sama'ila ne ya fito daga cikin gida dai-dai lokacin da limami ke kokarin tayar da sallah dan haka gabad'ayan su sai suka shiga cikin massalacin domin gabatar da sallahr magariba.
Koda suka fito daga masjid din sai da suka sake gaisawa, Mussadiq ya ri'ke hannun mahaifinsa sai walwala yake, shi kuwa Baba malam sai tsokanarsa yake ganin ya manta dashi dan yaga babansa, Baba malam na kallo Mussadiq yabi bayan mahaifinsa zuwa cikin gidan Alhaji, sai kawai yayi murmushi ya juya domin shiga cikin gidansa, yana mamakin halin 'kuruciya.
A nutse suka gaisa da mahaifiyarsa tana tambayarsa Halisa yace."Tana nan lafiya kalau alhamdullhi." gurin yayi shuru na minti biyu kafin Alhaji Sama'ila dake zaune kan kujera yayi gyaran murya, a nutse yace."Naji dadin zuwan nan naka kwarai da gaske, domin ina so mu tattauna magana da kai mai muhimanci." Gyara zamansa yayi a nutse yace."To Alhaji inajin ka." Alhaji Sama'ila yace."Dazu Ramlatu tazo da wata magana wacce ni ban san da ita ba wai ashe Salim d'an wajenta ya d'ade yana son ya auri yarinyar nan Naja'atu wacce ake maganar aure a tsakaninku, tace tun tana yarinya yake sonta kuma kai kasan da maganar domin har al'kawari kayi masa kan cewar zaka shige masa gaba ya aureta ya akayi kuma kasan da wannan magana a tsakani ka bijiro da bukatarka." ? Abbah Abbas yayi shuru yana nazari maganar mahaifin nasa, a nutse yace."Eh kwarai kuwa Salim ya dad'e da fada min cewar yana son Naja'atu kuma ni da kaina nine nayi masa al'kawari kan zan bashi auranta, kuma ina nan zan shige masa gaba akan lamarin mutukar Allah ya kaddara yarinyar matarsa ce."
Alhaji Sama'ila yace."To alhmdullhi wannan magana da kayi tana nuna mana cewar ka janye kudirinka na auran yarinyar ma'ana ka barwa Salim din ya aureta."? Kai tsaye yace."Eh idan hakan shine alkairi a gare mu baki daya." Alhaji Sama'ila yace."Masha Allah to Allah ya tabbatar mana da alkairi yanzu idan mun fito daga sallahr isha'i zan shedawa malam din abinda ake ciki.
Yace."A'a Alhaji kada kayi masa magana ka kyaleni da kaine xan masa maganar yanda zai fahimta." Alhaji Sama'ila yace."To babu damuwa duk dai yanda ake ciki nasan zaiyi min bayani Allah ya tabbatar da alkairi."
Ya amsa yana kokarin danne damuwa dake taso masa.........Mi'kewa yayi yace."Bari na shiga gidan malam din mu gaisa zan d'an duba yara ina tunanin daga can zan mu wuce gida."
Ya kalli Mufida data kurawa tv ido yace."Mufida tashi mu tafi ko zaki zauna tare da hajiya ne." Mikewa tayi tana murmushi, Hajiya Talatu tace"Nima ban nema ba, kai da baka so 'ya'yanka na zuwa ko'ina yanzu ma ka fad'i hakane dan kaji dad'in bakin ka." Dariya yasa, ya rike hannun Mufida yana musu sallama.............Mussadiq na jikin motarsa a tsaye suka fito suka same shi, ya bude motar ya fito da tsarabar da yayi musu leda uku ya mika masa da fad'in "Ka dauki naka ka bawa Naja'atu da Saddiqa nasu." Ya kar'bi ledojin yana murna suka shiga gidan malam din shida Mufida.
Malam na zaune kan dadduma a kan dakalin gidansa yana kallon zuwansu, yayi murmushi yana kallon Mussadiq din cikin tsokana yace."Zo ka bani nawa." Mussadiq yasa dariya yana fad'in "Baba Malam ai kai baka shan za'ki baka shan Ice cream." Yace."In dai ka bani to zan sha yanzu." Mufida ta mi'ka masa ledar hannunta tace"Ni ga nawa na baka." Baba malam yayi murmushi yace."To godiya nake yi Mufida wasa nake ni ban iya shan kaye kayen za'ki ba wannan sai ku yara." Abbah Abbas ya karaso gurin yana murmushi yana jin dadin yanda mutumin ke wasa da dariya da 'yayansa shi duk mutumin da zai kula da d'ansa to yana da daraja da martaba a idonsa.
Mufida da Mussadiq suka shiga cikin gidan baba malam din, shi kuma ya nemi gefan daddumar malam din ya zauna a nutse ya sake bashi hannu sukayi musahaba kafin yace."Malam naji dadin samun ka kai kad'ai , dan saboda dama ina so muyi magana da kai mai muhimanci."
Baba malam ya gyara zamansa yana kallonsa a nutse yace."Ina sauraranka." Shuru yayi na minti biyu kafin yace."Magana ce kan Yarinyar nan Naja'atu kwana biyu da suka gabata nazo maka da bukatar son ka bani auranta saboda inaso ta zama *MADADIN* halimatu a gurina, to malam ka gafarce ni da maganar da zan fad'a maka a yanxu na janye maganata ta farko kan yarinyar nan, inaso a bata wanda take so ta aura kuma insha Allahu ina nan a matsayin uba a gareta zan dauki nauyin komai idan auranta ya tashi."
Malam Ya shiga girgiza kansa yana kallonsa yace."Abbas ni ba 'karamin mutum bane kuma ba'a magana biyu dani! kamar yanda ka bukaci na baka yarinyar nan ka aura na kuma ce na baka to na baka ita har abada idan nine na haifi Naja'atu to bata da miji sai kai dan haka ka daina kawo wata magana ta daban." Abbah Abbas ya bude baki zaiyi magana Alhaji Magaji ya iso gurin, hannu ya mika musu su gaisa ya samu guri ya zauna yana kallonsu ganin dukkaninsu fuskokinsu babu walwala yasa ya tambayi abinda ke faruwa.
Baba Malam ne ya sheda masa abinda ke da a kawai
Alhaji Magaji ya shiga kallon abokin nasa cikin takaici yace."Banyi tsammanin haka daga gurinka ba Alhaji Abbas! Ya zaka zo da magana mai muhimanci daga baya kuma ka dawo da wani zance da daban. Gaskiya bamu ji dadin wannan furucin naka ba, dukkaninmu munfi kaunar ka zama miji ga Naja'atu dan haka wannan maganar da kazo da ita ka ajiye ta kamar yanda malam ya fad'a maka cewar Ya baka yarinyar nan har abada to bata da miji sai kai."
Abbah Abbas yayi shuru yana jimanta al'amarin yaso ya daurewa zuciyarsa ya hakura da yarinyar duk domin samun daidaito da kwanciyar hankali ta kowane 'bangare to amma ya lura dasu malam ba zasu amince masa da bukatarsa ba......Yana kokarin yin magana, Mufida da Saddiqa da Mussadiq suka fito daga gidan malam d'in Mufida hawaye take sharewa Mussidiq na sharewa hawaye Saddiqa ce kawai mai dauriya a cikinsu.
Abbah Magaji ya kallesu da sauri yace."Kai kukan me kukeyi Saddiqa me ya faru."?
Shuru tayi ta kasa magana bakin ciki kamar ya fasa mata zuciya, wai yau an wayi gari Yaya Naja'atu itace ke zaginsu tana wasa musu yught a jiki.
Mussadiq na goge fuskarsa da jikinsa yace.''Yaya Naja'atu ce tayi mana tsawa! ta watsa mana Yught a jikinmu nida Mufida." Abba Abbas ya dinga bin jikin yaran nasa da kallo Eh tabbas gashi nan duk yught a jikin hijabin Mufida da 'kasan rigar Mussadiq."
Abbah Magaji yace."Me kukayi mata to." Mufida tace"Abbanmu ne ya siyo mana yught da snacks shine ya bamu kowa leda d'aya yace mu kai mata nata shine muna shiga dakin ta zage mu ta watso mana yught nida Mussadiq."
Gurin ne yayi shuru kowa na 'kokarin danne 'bacin ransa, mussaman shi Uban yaran da baya so ko 'kuda ya sauka a kansu, kokarin danne fusatarsa yake gudun kada ya aikata abun kunya yasa ya mike yana fad'in "Zamu tafi da yaran gabadaya dan monday zasu koma makaranta.
Jikin sanyi jiki Baba Malam yace." Alhaji Abbas ban tari hanzarin ka ba, ka koma ka zauna ai bamu gama magana ba."
Abbah Abbas ba yanda ya iya ya koma ya zauna yana ta ya'ki da zuciyarsa......Abbah Magaji kuwa mikewa yayi a fusace! ya shiga cikin gidan, Tana tsugune da buta a gabanta zata daura alwala ta kasa ta had'a tagumi sai tunani take yi, kawai taji saukar duka a jikinta.
Abbah magaji ne yake zabga mata igiyar shanyarsu dama yana shigowa gidan igiyar ya tsinke ya nad'e a hannunsa ya nufe ta da ita.
Ihunta ne ya fito da Baba Talatu daga daki hannunta rike da carbi da hijabi a jikinta, Baba Talatu kullum ta idar da sallahar magariba sai tayi zaman lazimi kafin a kira sallahr isha'i sai ta tashi ta gabatar da sallahar shiyasa bata san abinda ke faruwa ba tunda tana cikin daki su Mufidan suka shigo........Da gudu taje ta ru'kunkume Baba Talatun tana kuka da ro'konta kan ta hana Abba magajin dukanta, Baba Talatu ta dinga kare ta tana tambayarsa abinda tayi.
Igiyar ya jefar yana huci yace."Baba Talatu ashe yarinyar nan rashin mutuncinta har ya kai ta zagi Alhaji Abbas kan yayi mata abun alkairi ta zageshi gaban 'yayansa ta 'bata musu jiki da Yught saboda tana jin haushin Ubansu, hakika banta'ba ganin butulu mai manta alkairi ba kamar wannan yarinyar."
Baba Talatu ta koma ta zaune kan dadduma tace"Magaji yini guda yau a haka muka yini ni kaina zagina ne kawai yarinyar nan ba tayi ba hantara da kyara kuwa babu irin wacce ba tayi wa su Saddiqa wai jinin 'yar uwarta take wulakantawa." Baba Talatu ta'kare maganar cikin rawar murya.
Abbah Magaji ya kalleta tana tsaye jikin bango(garu) tana rawar jiki sai kuka take, da hannu ya nuna ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yaja tsaki ya fita a fusace!!
Cikin nutsuwa ya d'ago kansa bayan ya gama sauraran maganar da Baba Malam din keyi yana kokarin yin magana Baba Malam yace."Kada kace komai ko ka kawo min wata magana, na riga na gama yanke magana mutukar ni na haifi Naja'atu to na tsayar da ranar daurin auren ka da ita Gobe Juma'a Sadakinta kawai zaka bani, idan yaso idan ta tare a gidanka sai ta nuna maka 'karshen 'kiyayya."
Yace."Baba Malam anya ba'ayi gaggawa ba kuwa wannan al'amarin yana bukatar nutsuwa ni da kunbi ta maganar da nazo da ita da ina ganin sai amfi samun maslaha ga junanmu."
Abba Magaji yace."Magana fa ta kare abokina insha Allahu gobe bayan an idar da Sallahr juma'a za'a daura auran nan sai kowa ya huta itama kuma idan taga an daura auran duk wani iya shege da take zata daina shi kuma wannan yaro Salim sai muce Allah ya bashi wata macan wacce zata zame masa alkairi a rayuwarsa."
Abbah Abbas ya jima shuru yana tunanin yanda al'amarin ya kasance sam baiyi tsammanin zasu yanke irin wannan hukuncin ba, to alkairi kullum yake fatan Allah ya sada shi dashi idan hakan shine alkairi yana ro'kon Allah ya tabbatar masa dashi..
*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*
*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO