Madadi 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Abale Category :  Romance

Chapter   6 / 17

15K to 18K   out of 48.8K words

rufar wa Naja'atu da duka har sai da ta durkushe a gurin!! Ihu! takeyi tana kokarin kwatar kanta....
Halisa ta fito daga daki a guje! jama'ar dake waje suka shigo palon suna tambayar abinda ke faruwa.
Shamsiyya tana hura huci! ta shiga fada musu karya da gaskiya. Yaya Ramlatu tazo ta tsaya a kan Naja'atu tana zaginta ta uwa ta uba! Naja'atu kasa motsi tayi dan ta daku sosai! Halima ce tazo ta kama hannunta ta mikar da ita, tana kuka itama tana kuka su Saddiqa da Mussadiq na kuka! abin gwanin ban tausayi! Ita kuwa Yaya Ramlatu kamar kara zugata akeyi ta tara mutane sosai sai aibata Halima da Naja'atu take da iyayensu kowa na tofin ala tsine a kansu! Halisa ganin abin ya kwa'be! yasa tazo tana bawa Ramlatu hakuri saboda tasan idan maigidan ya samu labarin abinda ya faru to babu shakka al'amura zasu 'baci! dan rayukan kowa sai ya 'baci! da kyar ta rarrashin Yaya Ramlatu tayi shuru taja tawagarta suka fita harabar gidan domin cigaba da rabon abinci.........Halisa ta dinga yiwa su Shamsiya fada kan abinda suke kokarin janyo mata, dukan Naja'atu da sukayi yana nufin abubuwa da yawa a gareta hakan na iya barazana ga auranta, shiyasa bayan ta shiga dakin tasa Mussadiq ya kira mata Naja'atun! K'in zuwa tayi sai da Halima ta rarrasheta sannan ta shiga dakin.

Halisa ta kwantar da kanta tana fadin "Naja'atu kiyi hakuri kinji ko abinda su Shamsiyya sukayi miki kinga dai a gabanki na hukunta su kuma nayi musu fada dan Allah kada ki fadawa Abbanku." Zum'bura bakinta tayi tace"To me yasa baki rama mun dukan da sukayi min ba! Ni wallahi bazan yarda ba sai na fada masa sun zageshi sun zagi Baba malam sun dake ni kuma sun kushe hallitar Allah."
tana k'are maganar ta ta fita daga dakin, Halisa rakata tayi da kallo baki a sake.

Tana fita daga dakin ta dauki wayar Mamanta wani guri ta 'buya ta kira numbarsa, ganin numbar Halimatu yasa ya dauka da sauri yace"Ranki ya dade yaya ina fatan komai lafiya."? ai kawai sai yaji fashewar kukan Naja'atu a kunnansa! Ya mike tsaye da sauri! Yace''Naja'atu lafiya kike kuka yi shuru ki fada mun abinda akayi miki?" cikin sar'kewa tana jawo numfashi irin na sharri ta shiga wassafa masa abinda ke faruwa a gidan sunan." Ranshi idan yayi dubu ya 'baci! Yace."Daina kuka kinji ko? zan dauki mataki wato Halisa ta tara mutane ne dan ta tozarta ni! babu laifi ki bawa maman taki wayar zamuyi magana." Tana shashsheka da goge fuska tace"To." Zuwa tayi ta kaiwa Halima wayar da fadin "Gashi Abbanmu zaiyi magana dake." Halima ta fita daga cikin mutane ta samu guri tana amsa wayar, Jinsa a fusace! yasa ta sassauta mirya tana so ta fahimtar dashi yaki sauraranta yace."Zai turo Salim yanzu yazo ya daukesu ya mayar dasu gida ita kuma Halisa zata gamu dashi." Kafin ma tace wani abu ya kashe wayarsa.....Kasa'ke tayi da waya a hannunta tana mamakin wannan al'amari! gabadaya idan Naja'atu zata fada masa magana baya tsayawa yayi nazari zai hau kai ya zauna, tabbas ba sune suke da laifi kan faruwar hatsaniyar ba, to amma yana da kyau yabi komai a sannu tasan halinsa da mugun zafin zuciya zai iya aikata abinda ba shikkenan ba.

Aikuwa dai bayan watsewar taron suna da ya shigo gidan Halisa sai da ta fuskanci 'bacin rai sosai dan cewa yayi ta ajiye masa 'yarsa ta fice masa a gida tunda dama abinda ta shirya yi kenan shiyasa ta damu sai tayi taron suna dan haka ta ajiye masa 'yarsa ta bar masa gida, kuka wurjan-wurjan ta dinga yi tana bashi hakuri tana kuma gaya masa yanda al'amarin ya kasance cewar ita sanda abun ya faru ma tana daki bata da laifi.
Jin tana ambatar sunan Shamsiyya a maganar yasa ya 'kwala mata kira tana zaune a palo tayi tsuru tsoronta Allah tsoronta annabi kada yace ta bar masa gida, Da sauri ta shiga dakin, yace"Kece mai gwada yanda matata Halima take tafiya ko."? Girgiza kanta ta shiga yi tana rantse-rantse! Yace."Duk abinda kukayi wa Ubangiji ku dashi ne dan haka bana bukatar ganin ki a gida nan ki dauki kayanki ki tafi." ai ta haihu babu wani sauran aiki yanzu." Hannu ya zira cikin aljihu ya dauko dubu daya ya mika mata da fadin"Ki shiga mota." Kar'ba tayi jiki a sanyaye ta fita daga dakin, zuwa tayi ta shiga hada kayanta tana kukan takaici taso ta zauna a gidan har sai ranar da Antin nata tayi ar'bain sai ta tafi amma mutsiyaciyar Yarinyar nan Naja'atu tasa an koreta......Abba Abbas bai bar gidan ba sai da ya tabbatar da cewar Shamsiyya ta bar gidan sannan hankalinsa ya kwanta ko sallama baiyi da Halisan ba yayi tafiyarsa.
Gidan Yaya Ramlatu ya nufa koda taga yanayin da yazo mata dashi sai tasha jin jikinta, ta shiga yi masa rawar jiki, ya dinga kallonta takaici kamar ya kashe shi, Ramlatu ta girma amma bata san ta girma kullum abubuwa take irin na marasa tunani, ganin yanda take rawar jiki a kansa ne yasa ya sassaura zuciyarsa ya shiga nuna mata illahr abinda takeyi take kuma tara mutane na wulakanta masa matarsa hakuri ta bashi kamar gaske tace insha Allahu ta daina........Yaji dadi sosai hakan yasa ya zauna sukayi hira irin ta 'yan uwantaka.


Fushi sosai ya shiga yi da Halisa duk domin ya nuna mata kuskuranta a ganinsa idan da bata bada goyan baya ba to babu wanda ya isa yaci zarafin matarsa da iyayanta, Halima ba tayi musu laifin komai ba amma sun dauki karan tsana da tsangwama sun dora mata.


*BAYAN SHEKARU UKU*

Lokacin Naja'atu nada shekara goma sha shida a duniya komai nata ya fito a zahiri macace doguwa mai fadin 'kugu da cikar kirji bata da haske sosai amma ba za'a sata a layin bakake ba fatar ta mai kyau ce mai kuma wahalar samu, tana da kyau a fuska da jikinta wannan dalilin yasa bata fiye yin kwalliyar fuska ba, kuma bata sanya mayafi sosai tafi amfani fa hijabai saboda ta tsani kallon da maza ke mata a duk sanda zata fita babu hijab a jikinta takan fuskanci 'bacin rai sosai! maza sun dinga kallonta kenan har da masu tsayr da ita, shima Abban nasu ya fahimci yarinyar nada wani irin jiki mai daukar hankali duk wani lafiyayyan namiji, wannan dalilin yasa kullum idan yana gida zasuje wani gurin idonsa a kai! idan sun saka hijabin da be rufe musu jiki sosai ba sai yace suje su sanja wani, sosai yake kula dasu da takatsantsan a kansu. mussaman ita Naja'atun da ya lura tana kan lokacin balagar ta....to a dai dai lokacin ne kuma suka gama secondary ita da Ilham 'Yar gidan Baba Magaji ita kuma Saddiqa na aji ss1 aji hudu kenan....... Lokacin kuma Halimatu nada tsohon ciki haihuwa ko ya yau ko gobe........ a wannan lokacin ne kuma sha'kuwa gami da soyayya mai kar'fin gaske ta shiga tsakanin Salim da Naja'atu, hatta da manya sun san da maganar! mahaifiyar Salim wato Yaya Ramlatu kwata kwata bata kaunar al'amarin ta zuba musu ido ne kawai tana kallonsu! Ita kuwa Naja'atu soyayyar da takewa Salim din tasa ta manta wacece mahaifiyarsa tana gani ita in dai Salim din zai aureta babu ruwanta da masifar Mahafiyarsa, Abbah Abbas kuwa ganin yanda suke kaunar junansu sai al'amarin yayi masa dadi sosai yana fatan Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninsu, kenan shi ya kasance waliyyin mutum biyu Salim din da ita Naja'atun.

A dai-dai lokacin da suke kokarin tafiya babbar makaranta, Allah ya saukar da ikonsa kan Halimatu gurin haihuwar cikin dake jikinta Ubangiji ya dauki ranta! bata tare data haife abinda ke cikin nata ba, mutuwar data girgixa zukatan al'umma da dama! mussaman Yaya Ramlatu da Halisa kwana sukayi suna sambatu da zabure zabure! Halima ta mutu da kalmar shahada a bakinta kuma ta mutu sanadiyar haihuwa babu shakka abun alfaharin ko wane musulmi kenan, duk wani mai kaunar Halimatu zai taya ta farin cikin samun rahamar Allah da tayi dalili kenan da ya sanya mijinta da iyayenta ke jin sassauci a cikin zuciyoyinsu idan suka tuna da cewar fa Halima tuntuni ta manta da rayuwar duniya domin ta riga ta gama dacewa, duk wanda zai budi baki alharin ta zai fad'a! Tabbas Annabi yayi gaskiya da yake cewa mutuwar mumini itace ke sawa mutane su girgiza kuma duk wanda ya mutu jama'a na fadar alherinsa babu shakka Allah yaso shi da rahamarsa.
*Ubangiji Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ameen*

To Bayan kwana bakwai ne da rasuwar Halimatu al'amarin ya kasance.......
Inda su Baba Malam Alhaji Samaila Abba Magaji dashi kansa Uban gayyar suka zauna suka tattauna maganar yin *MADADI* da Naja'atu wato Naja'atu ta maye gurbin 'Yar uwarta Halimatu data dauka a matsayin mahaifiyarta.


*A Pege na gaba zamu dawo ainihin labarin da muka fara da farko*



*NAGODE 'KWARAI DA ADDUARKU A GARE NI NAGODE👏🏻*



*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262.....IDAN KIN SAN BA BIYAN KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*
*🗯️MADADI!!💍*
_(Ba Haram Bane!!)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~~~
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION📚🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
~~~~~~~~~



_*Na gaishe daku 'Yan 'Kungiyata ta Manazarta Writers Association, Hakika ina jin dad'i had'in kanku, kuma ina alfahari daku mutu'ka! gabad'ayan ku ina rokon Allah ya d'aukaka min ku d'aukaka mai amfani Ubangiji Allah ya baku ikon rubuta abinda al'umma zasu amfana dashi*_


*PEGEN YAU NAKI NE*

*UMMU HANIFA*
Marubuciyar littafin
*ANYA MUTUM CE?🤔*

Ina mutukar alfahari dake 'Yar d'akina Allah ya 'kara miki basira da haza'ka, ki cigaba da rubuta littafai masu dadi da ma'ana♥️



*7*
Kanta a tsakanin cinyoyinta ta d'ora duka hannuwanta saman kanta ta takure kanta guri guda sai kuka take tana girgiza kanta, Baba Talatu ta dafa bayanta a sanyaye tace"Naja'atu yanzu kinji komai daga bakin malam ko? Alhaji Abbas bashi ne ya haife ki ba kamar yanda kike tunani, A'a ba haka bane shi d'in ya kasance miji ga 'yar uwarki Halimatu Allah ya ji'kanta da rahama, wannan dalilin ne yasa su malam suka yanke wannan hukuncin a kanki babu laifi dan kin auri mijin 'yar uwarki kuma dukkanin mu bamu aikata haramci ba kamar yanda kike tunani da farko, idan kin auri Alhaji Abbas hankalin mu zai kwanta saboda mun san zai ri'ke mana ke da kyau da amana kuma su Saddiqa da d'an uwanta Mussadiq zasuji dad'in kasancewar ki a matsayin matar babansu zasu dinga kallonki tamkar mahaifiyar su." ............Fuskarta jage-jage da hawaye ta d'ago kanta tana kallon mahaifiyar tata, girgiza kanta ta shiga yi kana tace"Ni wallahi bazan iya zaman aure dashi ba, a Uba fa na daukeshi kuma ya za'ayi kuce zaku daura min aure dashi, bayan dukkanin ku kusan da maganar Salim wannan ai abun kunya ne a gurunsa ace ya aure ni bayan shine ya raine ni ya rike ni a matsayin 'yarsa, kawai kuma saboda mutuwa ta ratsa tsakaninsa da matarsa sai kuce zakuyi masa *MADADI* dani ni wallahi bana sonsa."
Ta'karashe maganar cikin gursheken kuka mai karfi.

Baba Malam yace."Ai dama ba cewa muka yi dole sai kin so shi ba, cancanta muka duba shiyasa muka yanke wannan hukuncin saboda haka ina so ki cire maganar ko wane namiji a cikin ranki domun kuwa mutukar ni ne na haifeki to baki da miji sama da Mijin 'yar uwarki wato Alhaji Abbas, zaki aure shi ko bakya sonsa nan gaba idan kinyi hankali zaki gane abinda muke nufi dayin hakan."

Da rarrafe ta isa inda yake ta ri'ke hannunsa jikinta sai kyarma yake tace"Wallahi Baba malam zaku jefa rayuwa ta cikin garari saboda na fada muku iya gaskiya shine ni ba zan iya zaman aure dashi ba, na farko yayi min tsufa kuma abun kunya ne ace ya aure ni alhalin Ni 'yarsa ce bayan haka kuma yasan shine waliyi na gurin daurin aurena da Sali.......Abba Magaji ya fusata! ya kai mata mari da bayan hannu! jikinsa na tsuma! yace."Dan ubanki har wata cancanta kike nema? dame kika fi Alhaji Abbas din ? da har kike kiransa tsoho! ana nuna miki abinda ya dace dake kina maganar abin kunya, kina nufin dukkaninmu bamu san abinda ya dace ba kenan? to wallahi tallahi na 'kara ji kin bud'e baki kinyi wata magana anan gurin sai na futar miki da jini shashashar banza da wofi."
Shuru tayi jikinta sai rawa yake hawaye kuwa kamar an bude famfo! sai famar girgiza kanta take tana toshe bakinta tamkar wata zautacciya.

Tausayi ta bawa Baba malam ya kalli Alhaji Magajin a nutse yace."Yarinyar nan taurin kaine da ita ina ganin zamu sake zama mu tattuna kan maganar, bana so ayi abu daga baya kuma azo ana dana sani.
Alhaji Magaji yace."Malam babu wani zama da za'a sakeyi idan wata magana ta fito daga 'bangaran mu ba zasuji dadi ba, tunda kaga sune suka zo mana da maganar yana da kyau mu basu goyon baya kan abinda suka zo mana dashi duk mutumin da ya nuna yana kaunar had'a zuria da kai to ka tabbata ba 'karamin so yake maka, hakika nasan abokina Abbas yaji dadin zama da Halimatu shiyasa ya bukaci a bashi Naja'atu ta zame masa *MADADIN TA* dan haka tunda mun riga mun gama magana babu dadi kuma aje ace musu wani abu daban."


Baba Malam yace."Yarinyar ce take bani tausayi bana son wannan kukan da take yi yana d'aga mun hankali amma tunda kace haka shikkenan Allah ya sanya alkairi cikin al'amarin ya kauda kowace irin fitina da zata biyo baya.

Baba Talatu dashi Magajin suka amsa da "ameen" Mikewa yayi yai musu sallama da niyar tafiya gida dan lokacin goma na dare ma ta wuce! Fatan sauka lafiya sukayi masa ya dauki hularsa da key dinsa ya fita daga gidan.

Cikin tausawa ya kalleta da fad'in"Ki tashi kije ki kwanta komai yayi tsanani maganinsa Allah kuma ina so ki zauna kiyi tunani kan wannan hukuncin da muka yanke a kanki, mune muka haife ki ba zamu cutar dake ba, da mutumin nan da ba nagartacce bane to da baza mu amince da bukatarsa ba to mun tabbatar da cewar idan muka dauke ki muka bashi muna da tabbacin zai kula dake kamar yanda ya kula dake a lokacin da baki san kanki ba."
Mikewa yayi ya shiga da'ki bayan ya gama maganarsa, Baba Talatu ta jima tana rarrashinta kafin ta mike itama tabi bayan Malam din suka barta ita kadai a tsakar gidan tana kukan zucci.

Mamaki take sosai! wai ashe dama Abban Abbas din ne ya bukaci auranta ita duk a tunaninta su Baba malam ne, girgiza kanta kurrum take tana mamakinsa, to ta aureshi tayi yaya dashi? ta yaya za ta iya rayuwar aure dashi? lallai ma! ita abun ma mamaki yake bata ko kunya bai ji ba yace zai aureta bayan yana amsa sunan Uba a gurinta, gashi kuma yasan da maganar Salim hummm! aikam ba zata yarda ba duk yanda za tayi sai ta rushe wannan auran, sam ba zata auri tsoho dan shekara hamsin ba haka kawai sun gina soyayyarsu da masoyinta yazo yayi musu kutse a rayuwarsu ko kunya baya ji zai zo da wannan maganar! 'Kwafa tayi ta mike ta shiga d'aki!

Tana shiga dakin taji shashshekar kukan Saddiqa suna kwance ita da Mussadiq a katifa ta rungume shi sai kuka take!

A gigice ta kunna haske wayarta, tana haske su! Saddiqa ta rufe idonta tana sake takure jikinta guri guda......"Ke Saddiqa menene? dama ba kiyi bacci ba."? Saddiqa ta mike zaune tana goge fuskarta, 'Karasawa tayi ta zauna gefan katifar tana kallonta, a sanyaye tace"Meye kika kuka? nafada miki ki dainawa Mamma kuka idan kina so ta dinga samun rahamar ubangiji."
Saddiqa ta goge fuskarta tana kallonta tace"Ni ba Mamma nakewa kuka ba, nasan abinda nake yi a halin yanzu Mamma babu abinda take da bukata a gurinmu sai addua ba kuka ba."

A d'an sanyaye tace"To me kikewa kuka."? Saddiqa ta kalleta wasu hawayen na sake zubo mata tace"Yaya Naja'atu me yasa kike nuna 'kiyayyar ki 'karara a kan Abbanmu."!? Gabanta ne ya fad'i! sai tasha kunu! tace"Wace irin magana ce wannan Saddiqa? kada kice min kema kina goyon bayan na aureshi."

Saddiqa taja majina tana goge hancinta tace"To menene aibu a ciki? dan kin auri Abbanmu ai ba wani abun bane kuma ba ke kad'ai ce kika ta'ba auran *MADADI* ba Yaya Naja'atu idan kika maye gurbin mahaifiyarmu zamu ji dad'i sosai dan Allah kiyi mana wannan alfarmar ki daina nuna 'kiyayyar ki a fili."

Shuru tayi tana nazarin maganar yarinyar! Wai shin da suke ta wannan maganar ta yaya zata fara ne? wane matsayi zata ajiye shi miji ko mahaifi? bafa zai yiwu ba.! Ta kalli Saddiqan data kura mata ido tana jiran amsarta tace"Saddiqa nayi wa Abbanku 'kan'kanta kuma shima yayi mun girma bayan nan kuma ni matsayin mahaifi yake a gurina bazan iya rayuwar aure dashi ba, kuma ki daina tunanin ina 'kinsa wallahi bana 'kinsa saboda Abba Abbas yayi min abinda ba zan ta'ba mancewa dashi ba, kawai dai bana tunanin zan iya rayuwar aure dashi."

Saddiqa tace"To idan baki aureshi ba kin san dole yayi aure kuma gabadayan mu bamu san matar da zai aura ba, kinga zamu shiga halin 'kaka na kayi tunda dai kin san ba 'kaunar mu Anti Halisa take ba, kinga rayuwarmu na cikin 'kalubale nida Mussadiq."

"Eh gaskiya ne duk maganar da kika fad'a to ai ba dole sai kun zauna tare da matansa ba, sai ku dawo gidan Alhaji da zama ko kuma ku dawo gidanan nan nasan Baba Talatu zata ri'ke ku to meye abun tashin hankali.

Saddiqa ta shiga girgiza kanta zuciyarta na wani irin d'aci! tace" Yaya Naja'atu kin manta maganar Abbanmu kenan kin san fa yasha fad'a cewar mutuwa ce kawai zata rabashi da 'yayansa

6 / 17