JIDDA Kallo Daya, Zuciya Daya By Maman Maama

Author :  Maman Maama Category :  Romance

Chapter   89 / 106

264K to 267K   out of 316K words

mota suka fita, anyi ta kiran sa kuma yaki daga wa suma kuma su Maman duk basa daukan waya. Ga baban ku dama babu lafiya shine duk ya tada hankalin sa nace bara in kirawo ki inji ko ya kawo ta nan".

Na sake share hawayen da suka ki tsayawa nace "Aunty ga Yasmin nan tana tare da ni. Ki gaya wa Baba tana guri na"

Naji ta sauke ajjiyar zuciya tare da hamdala. "Alhamdulillah. Ya kawo ta kenan. Amma bai kyauta wa Asad ba gashi nan sai kuka yake yana neman ta"

Na lumshe idona na bude, a lokacin da Yasmin ta sake zabura tare da kwalla min kira "mommy!" Na kara rungume ta a jikina "shshshsh, is Okay, mommy is here, you are safe" naji Aunty tace "lafiya dai ko?" Nace "Aunty Yasmin tana tare da ni yanzu, amma ba Umar ne ya kawo ta ba, police ne suka kira ni suka ce inzo asibiti gata  nan sun tsince ta"

Aunty ta rafka salati "sun tsince ta? Yasmin din? Asibiti kuma? Me ya same ta?" Sai na kasa amsa mata dukkan tambayoyin ta kawai na saka kuka na ajiye wayar a gefe na, cikin kukan nake karanto adduoi ina tofa wa Yasmin dan ta samu saukin halin tsoratar da take ciki.

Ina cikin kukan ne naji motsin Umar, na juya side din da yake sai naga ya tashi zaune yana dafe da kansa da hannu daya sai kuma lokaci daya naga ya rikito daga gadon gabakidaya ya fado kasa hannayensa dafe da kirjinsa idanunsa a kan mu

"Yasmin!"

Ya fada cikin tsananin halin tashin hankali, sai a lokacin na tuna cewa shi bai san gaskiyar abinda ya faru ba ya dauka da gaske anyi din, a take kuma na yanke shawarar cewa ba zan gaya masa gaskiya ba, zan barshi ya cigaba da believing hakan maybe wannan ya zama silar dawowar sa cikin hayyacin sa.

"My baby!"

Ya fada hawaye suna gudu akan kuncinsa irin wadanda ban taba ganin ya zubar da irin su ba. Sai kuma ya fara tahowa akan guiwowin sa zuwa inda muke, na daga masa hannu da yanayin dakatarwa nima cikin hawaye nace" dakata Umar! Kar ka karaso inda muke, You have already done enough harm to us bama bukatar kari kayi wa girman Allah kar ka kuma shafa mana kashin kaji, ka riga ka dorawa yarinyar nan kwandon tsaba gashi nan ka jawo tsuntsaye sun fara binta, Allah ne kuma kadai ya san yaushe zasu daina bibiyar ta tunda ubanta ya riga ya siya mata da kuɗin sa"

Ya tsaya a inda yake, yana kukan da ya saka jikin sa gabakidaya yake karkarwa, yace "wallahi, Jidda, ban taba ko da gwada raping kowa ba, nasan na aikata munanan aiyuka da yawa amma duk yarinyar da na taba da amincewarta na taba ta, ni ban taba kula yarinyar da take underage ba ma, ni ban taba kula yarinyar ma da take secondary school ba, duk wadda na nema da amincewarta, da yawan su ma su suke kawo kansu gare ni ba tare da na basu ko kwandala ba, ba ina justifying actions dina bane ba amma ina nuna bambancin abinda nayi da wanda aka yiwa yata....."

Na daga masa hannu "babu banbanci Umar, zina dai zina ce, ko a yaya aka yi ta kuma ko da wa aka yi ta duk sunanta zina kuma duk laifinta daya ne a gurin ubangiji, banbancin kai da kayi da babbar mace bisa amincewarta da kuma wanda yayi da karamar yarinya bisa tursasawa shine shi bayan laifin zina kuma yana da laifin zalunci, wanda tsakanin sa ne kuma da wadda ya zalunta din, amma laifin da yake tsakanin sa da ubangiji dai dai yake da naka kai da kake ganin ka yi da babba a bisa amincewarta.

"ka sani Umar, kuma nasha tunatar da kai akan illar abinda kake aikatawa, na sha gaya maka cewa bashin zina dolen dole duk wanda ya dauka sai ya biya, masifar kuma shine ba'a kanka zaka biya ba akan makusantan ka ne, har na taba tambayar ka cewa ya zaka ji a ranka idan aka yi wa Yasmin, ko akayi wa Mufida? Ka tambayi zuciyarka kaji me take ji? To haka iyayen wadancan suka ji suma. Kuma fadar annabi yace wannan shine somin tabin hukuncin mazinaci, wannan wasa farin girki ne, masifu suna nan tahowa gare ka in dai baka tuba ba masifun da sai sun raba ka da komai a duniya kuma sun tabbatar da kayi karshe marar kyau sannan kuma ka tarar da na kabari ka kuma hadu da ubangiji ranar hisabi. Amma in ka tuba ka bi Allah ka gyara rayuwar ka shi Allah Algafur ne kuma Alrahim. Zai iya ya yafe maka komai yawan zunuban ka indai har ba shirka bace ba, kuma in dai har ranka bai kai gargara ba. Wannan tsakanin ka da Shi ne. Tsakani na da kai ni dai I want you as far away from me and my kids as possible, duk abinda ka jawo bana son in kasance tare da kai sanda zai iso gare ka"

Ya dago kai yana kallona hannunsa dafe da kirjinsa yace "naji, duk abubuwan da kika fada dazu da wadanda kika fada yanzu duk gaskiya ne, kuma da ace kinsan irin balain da ya saukar min bayan na bar gurin ki dazu, da kuma ace zaki iya shiga zuciyata kiji abinda yake cikinta, watakila da kin fahimci cewa ba kya bukatar maimaita min maganganun can, ba kya bukatar gaya min inyi nisa da ku"

"Allah ya san abinda yake zuciyata, kuma kamar yadda kika fada tsakani na da Allah ne, amma duk da haka kema na san na bata miki, dole kema zan nemi gafarar ki, zabin kine ki yafe min ko akasin haka, sai dai kuma ban san da wanne bakin zan nemi gafarar Yasmin ba, tabbas ba ta yi dacen uba ba, tabbas basuyi dacen uba ba. Kuma zama dani shima zabin ki ne, ba zan matsa miki ba kuma zan karbi dukkan hukuncin da zaki yanke a kaina"

Shigowar Abba ya dakatar da shi daga maganar da yake yi. Sai ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa daga kai ya kalli Abba, daga dukkan alama yau ne haduwar su ta farko tunda Abba ya san halin Umar.

Nayi kokarin tashi tsaye ina yiwa Abba sannu da zuwa, ya amsa yana kallon Yasmin da take kokarin rike hannu na a cikin baccin ta. Ya dafa kanta yana karanta mata addu'a yana tofa mata sannan ya juya ya kalli Umar yace "ka tashi ka fita ka bani guri zanyi magana da ƴata"

Umar bai ce komai ba ya dafa floor ya mike, ina kallon yadda yake layi kamar zai fadi har ya fita waje, sai bayan ya fita sannan Abba ya juyo kaina yace "me ya same ta?" Na cigaba da kuka na sannan na bashi labari kamar yadda naji daga bakin Aunty da kuma bakin police, ya jinjina kai cikin jimanta maganar sannan yace

"ina so ki bani labarin dukkan abubuwan da suka faru a gidan auren ki".

Na yi shiru ina tsara maganganun a zuciyata sannan na fara bashi labari tun daga yadda mukayi da yaya Jamila kafin bikina da kuma abubuwan da suka yi ta faruwa bayan bikin. Nayi amfani da kalmomi masu dan sauki gurin yi masa bayani yadda zai fahimta kuma ba zan ji girman maganar a bakina ba, na bashi labarin case din Mammy ban boye masa komai ba har abinda Mammy ta fada min na maganar asiri da kuma abinda na tone da hannu na da kuma shi abinda Faruq ya gaya min na cewa bai san duk abinda ya faru a tsakanin su ba. Na kara da cewa

"Wannan shine daya daga cikin dalilin da yasa na cigaba da zama da Umar bayan abinda ya faru, na farko saboda na tabbatar asiri Hajiya tayi masa dan ta raba ni da shi ta saka jikarta dan tana ganin kamar cikin jin dadi nake, na biyu kuma saboda bana son maganar ta fita, dan in maganar nan ta fita to zata ruguza dan kwanciyar hankalin da yake tsakanin mu da yanuwanmu, kuma bani da shaidar da zan nuna cewa asiri aka yi masa dan haka na tabbatar Hajiya zata tabbatar tayi amfani da maganar wajan bata sunana da sunan yayana har zuwa girman su. Sannan kuma bayan faruwar hakan Umar ya shiga tashin hankali da kuma nuna min kamar yayi nadamar gaskiya, sai na dauka rabon shiriyar sane ya saka abin ya faru, sai na kuma bashi dama tare da fatan cewa zai zama na karshe duk kuwa da cewa zama da shi bayan sanin abinda ya shiga tsakaninsu da Mammy ba karamin tashin hankali bane ba a gare ni. But I did it"

Sai kuma na bashi labarin Asabe, tun zuwanta gidan mu da kuma abinda naji daga bakinta da kuma abinda naji daga bakin shi Umar din.

Yayi shiru idonsa a kasa yana kallon kafafuwan sa, sai kuma yace "na jima ina tunanin cewa mata karamar kwakwalwa ce dasu basu da zurfin tunani, na jima ina ganin mata a matsayin masu raguwar zuciya, saurin gazawa da kuma korafi, wannan shine ya sa ka nake kin saurarar yayana mata akan duk wani korafi da zasu zo min dashi daga gidajen mazajen su, gani nake in na biye musu ba zasu yi zaman aure ba, zasuyi ta kashe auren su ne akan abubuwa marasa ma'ana ballantana tushe, na dauka hakan da nake yi ina basu kariya ne daga rudin zamani, a yau a fahimci cewa abinda na ke tunani ba haka bane ba, a yau na tabbatar mata ba kananan kwakwalwa ne dasu ba dan Jidda zurfin tunanin da kika yi ba kowanne namiji ne ma zaiyi irinsa ba, hakurin da kika yi da kawar da kai ba kowa ne zai iya irinsa ba. Allah yayi miki albarka. Allah ya shiga lamarin ki ya zaba miki mafi alkhairi a rayuwar ki"

Nace "ameen" sai ya mike yace zai koma gida ya turo min Farhan da Amira su taya ni harkar asibiti, ni kuma sai na lissafa masa abubuwan da nake bukata waɗanda zasu taho min da su.

Bayan ya tafi sai na zauna na fara tunanin Abba da iyaye ire-iren sa, they thought they are doing what is best for us, kuma tsoronsu ne ya saka bama iya sakin jiki mu gaya musu magana dan muna ganin ko munyi ba zasu saurare mu ba, but if we find a way to tell them zasu fahimta, kuma insha Allah a karshe za'a samu fahimtar juna dan suna son mu kamar yadda kowane iyaye suke son yayansu, kawai dai basu iya nuna soyayyar bane ba kamar iyayen zamani.

Bai jima da fita ba Umar ya dawo, daga alama daga masallaci yake, ya dawo gaban Yasmin ya tsaya yana kallon ta ya sunkuya yayi kissing goshinta sai kuma ya dauki takardun bills din da na ajiye a gefe ya juya zai fita, har ya kai bakin kofa kuma sai ya dawo ya bude jaka ta ya dauki ATM card dina ya sake fita.

Na bishi da kallo ina lura da yadda yake tafiya kamar zai fadi. Sai kuma na tashi na shiga toilet nayi alwala na fito nima nayi sallah. Ina idarwa su Farhan suka shigo tare da wani da ban gane ba, har da kayan dubiyar sa a leda ya kawo wa Yasmin sannan yayi min ya mai jiki ya tafi, bayan ya tafi ne Farhan ta gaya min wai sunan sa Sadiq, suka duba Yasmin tare da jajanta abinda ya faru da kuma godiya ga Allah da abin ya tsaya a haka, muna tare kira ya shigo wayata daga Aunty, na dauka ta tambayeni asibitin da muke na gaya mata tace gasu nan zuwa ita da Baba, nayi mamaki saboda nasan shima Baban ba lafiya ce da shi ba.

Kafin su zo ne Umar ya dawo daga siyan magani, yana tafiya yana dafe bango kana ganin sa kasan ba lafiya ce dashi ba sai na tashi na karbi ledar hannunsa na fara yi masa fadan cewa shima fa bashi da lafiya har da shi aka bawa gado, kafin in karasa fada na ya fado jikina, saura kadan mu zube a kasa gabaki daya sai na rike shi da kyar na karasa da shi gadon da aka kwantar dashi, na kuma tura Amira ta kira ma'aikatan asibitin.

Ina kwantar da shi ya rike hannuna ya dora shi akan kirjinsa, ina jin yadda jikin sa yayi zafi sosai kamar ana gasa nama. Yana magana a hankali amma ban ma ji mai yake cewa ba kuma bani da niyyar sake tambayarsa dan ban damu da inji din ba, sai da nurse ya shigo sannan na zare hannuna daga cikin nasa na kuma gaya wa nurse din cewa in ba allura yayi wa Umar ba to ba zai kwanta ba, kuma zai iya faduwa in yana yawo.

Bai jima da yin bacci ba Baba suka shigo tare da Aunty, na tausaya halin da naga Baba a ciki, na durkusa har kasa na gaishe shi ya amsa tare da tambaya ta abinda ya faru ni kuma na bashi labarin kiran da police suka yi min da kuma abinda suka ce min, Aunty sai ta fara kuka "mun shiga uku mun lalace. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta fada tana dafe kan Yasmin da ta dan bude ido kadan tana kallon su. Baba ya ja kujera ya zauna yana ambaton hasbiyallahu wa nieemal wakeel. Sai duk suka yi tagumi suka yi shiru suna tunani, jimawa can Aunty tace "har yanzu kuma su Mama babu wanda yake daukan waya, ko kunyi waya da Mufida?" Na girgiza mata kai kawai. Baba ya juya yana kallon Umar yace "shi kuma wancan fa? Me ya same shi shi kuma?" Nace "faduwa yayi ana gaya masa maganar, shine suka bashi gado ya dan huta" ya gyada kai yace "shi namiji shine da faduwa ke mace ke ce a tsaye? You really are a very strong woman Jidda, da wasu matan ne da yanzu sun cika asibitin nan da koke koke da fadar maganganu marasa dadi, amma ke ga ki nan a tsaye akan yar ki har da sokon babanta da ya kasa daukan kaddara"

Nayi murmushi ina jin dadin yabon da yayi min, amma kuwa anya ni din strong woman ce? Ni da ko mutum na gani yana kuka sai na taya shi ko da kuwa bansan dalilin kukan nasa ba, ko dai wannan ma is another kind of strength?

Muna cikin jajanta maganar sai wayar Aunty tayi kara, a lokacin already ana kiraye kirayen sallar ishai, ta kalli wayar tace "alhamdulillah, ga Mubaraka nan tana kira na maybe sunyi waya da Mama" duk muka yi shiru muna sauraron ta ta daga wayar "Mubaraka" sai kuma ta bude ido tare da saka salati "asibiti kuma? Mun shiga uku" "to gamu nan zuwa, yanzu kuwa".

Ta dago kai tana kallon Baba, yace "what now?" Ta hadiye yawu tace "Mama ce, wai ashe ta fadi ne a gidan bikin da suka je da Mufida, ashe wai tun dazu suna asibiti da ita, sai yanzu mufidan ta kira Mubaraka ta gaya mata, yanzu mubarakan taje gurin su shine ta kira ni".

Nan take wani tashin hankalin ya karu akan wanda already ake ciki, a karshe sai Baba yace da Aunty taje ta nema wa Yasmin da Umar transfer zuwa asibitin da Mama take, sai mu tafi can kawai gabaki daya tunda yana ganin can din ma zasu fi samun kulawa tunda private hospital ne. Babu jimawa aka gama komai aka yi releasing din mu muka tafi a ambulance din asibitin, su kuma su Baba suka biyo bayan mu a mota. Muna zuwa aka sake duba Yasmin aka sake tabbatar mana da cewa ba'a taba ta ba, suka kuma bamu dakin da da zamu kwana saboda suna so suyi monitoring dinta sosai saboda buguwar da tayi a kanta dan su tabbatar babu wani internal injury. Ni dai daga nan ban san ya suka kare da Umar ba, ban kuma bi ta kan Mama ba na tafi na cigaba da kula da ƴata, su Farhan ma suka yi min sallama suka tafi da driver din su Baba zasu biya gidan su dauki Asad sannan su tafi dashi gida sai da safe zasu dawo.

Sai da na nutsu sannan nayi waya da Umma na gaya mata abinda ya faru, na tabbatar mata babu abinda ya samu Yasmin sannan bayan munyi sallama sai na kira Diyam itama na gaya mata, hankalin ta ya tashi sosai tayi min jaje sannan tayi min alkawarin zata shigo da safe ta ga jikin Yasmin. Daga nan sai na tashi nayi sallah nayi godiya ga Allah tare da adduoin neman cigaba da kariya daga dukkan masifu. Har zan kwanta sai na gwada number din Mufida dan inji jikin Mama tunda ance tare suka zo asibitin, sai dai wayar tata bata shiga ba, sai na kira Aunty ita kuma tace min jikin da sauki duk da dai har lokacin basu san abinda yake damunta ba, likitoci dai suna tunanin firgita tayi amma basu san abinda ya firgita ta ba.

Kafin in kwanta na samu Yasmin ta tashi na dan bata juice da biscuit a cikin kayan da saurayin Farhan ya kawo mata, ta dan ci kadan sai ta koma ta kwanta amma sai ta kasa baccin tace sai dai in taho kan gadon mu kwanta tare, dole na katse duk abinda nake yi na kashe fitila ba hau gadon muka kwanta tare ta kankame ni ta cusa kanta a kirjina tana ta sauke ajjiyar zuciya cikin tsoro. A haka bacci ya dauke mu.

Sanda na farka dare yayi sosai, ina kokarin mikewa naga Umar akan sallayar da nayi sallah akanta, nayi mamakin yadda akayi ya shigo ama sai na tuna banyi locking kofar ba, sai dai na koma na kwanta. Next farkawa da nayi sai na ganshi a zaune a gaban gadon da muke kai hannayensa rike dana Yasmin, duk da duhun dakin sai da na fahimci yadda idanuwansa suka kumbura kuma suka yi ja. Na jima ina kallon sa ba tare da ya lura ina kallon sa ba, sai kuma na juya na cigaba da

89 / 106