Author : Maman Maama Category : Romance
kudina tunda akwai kudi a tare da ni sai dai haka na hakura dan nasan bazata karba ba.
Washegari, lokacin kwana na biyu a gidan, kwana na biyu rabona da gida, da yamma mijinta ya dawo kamar yadda ta fada kuma yadda naga tana ta shirin taryar sa tun safe, sai na tuno da zuwan Umar Zaria sanda nayi ta shirin dawowar sa da kuma tsarabar da ya dawo min da ita. Sai na samu kaina da yi mata addu'ar Allah ya kare mata mijinta ya raba ta da mugun ji da mugun gani irin wadanda nayi ta haduwa da su.
Muna tare da ita a falon ta ya dawo, ya mike da sauri ta tafi taryar da yayin da ni kuma naji ni odd a gurin, banso ya shigo ya same ni ba. Na dauke ido na daga kansu a lokacin da ta dane jikinsa shi kuma ya daga ta suna dariya. Sai naji sun tuno min da wani abu, naji zuciyata ta motsa da memories masu cike da zaki da kuma daci.
Ina jin tana masa Magana kasa kasa, ban san abinda take cewa ba amma na fahimci kokarin sanar da shi wanzuwa ta a gurin take yi dan kar ayi abin kunya. Sai ya ajiye ta sannan suka karaso but still yana makale da ita duk da dan kokarin ture shin da take yi cikin dabara.
"Bakuwa muka yi?" ya fada da rich husky voice din sa. Na daga kai na kalleshi. He is dark skinned, giant, and very handsome. Tun daga jikin sa, shigarsa, yanayin sa, da confidence din da yake fitowa daga jikin sa zaka fahimci kalmar rich may just be his surname.
Na gaishe shi "ina wuni? Ya hanya?" Yayi murmushi yana kara jan matarsa zuwa jikinsa "lafiya lau. Ya gida?" Sai kuma ya rada mata wani abu a kunne. Na sunkuyar da kaina yayin da Diyam ta janye daga gare shi tana dariyar abinda ya gaya mata duk da ban san menene ba sai kuma tace "Jidda ce fa? Ka tuna Jidda kawata ta taura science?" Ya dan yi shiru yana tunani sannan yace "wadda kuke kuka tare?" Duk muka yi dariya tace "yeah. Ita fa. After shekara da shekaru Allah ya sake hada mu" ya gyada kai, "yayi kyau. Yayi kyau sosai"
Sai nace "uhmmm lokacin sallah yayi. Bara in je daki inyi sallah" duk suka amsa sannan na fita da sauri na rufe musu kofa tare da sauke ajjiyar zuciya. Ina ma ina ma? Ina ma Umar is not who he is? We could have be just like Diyam da Sadauki.
Ban sake ganin ta ba sai dare, tazo ta tabbatar bama bukatar komai ni da yara, ta danyi wasa da Yasmin da ta wuni tana kunci, sannan ta fita.
Na kwanta rigingine ina kallon ceiling, ina jin abinda ya motsa dazu a zuciya ta yana kokarin hana ni tunani straight, nasan dama it is there, bakin ciki ne kawai ya danne shi and I intend to cigaba da danne shi har ya tafi gabaki daya.
And I heard my foolish heart asking me "ko me Umar yake yi yanzu?" Nayi tsaki tare da juyi ina kallon yaran mu da suke bacci a gefe na "Yana can yana ta hauka, that's for sure" Na amsa wa kaina.
A wannan daren ma haka na kasa bacci, na ringa yi ina mafarkan Umar yana ta haukan, da kuma mafarkan Abba yana kumfar bakin in ya kamani sai na lahira ya fini jin dadi. A haka har agogo ya kai kan karfe ukun dare. Na jawo handbag dina na dauko wayata da kwananta biyu a kashe na kunna ta, messeges suka yi ta shigo wa kamar an bude famfo, sai da ta gama settling sannan na shiga messeges din na ga kusan duk daga Umar ne, har ba zan iya irga adadin su ba. Na kashe kawai na karanta.
"I know I have been a very bad husband. Na san nayi miki abinda zuciya ma ba zata iya dauka ba. And I deserve ko ma menene daga gare ki. But please, just talk to me. Reply me ko da da alphabet daya ne. Ko da da kalma marar ma'ana ne. So that in san cewa you are okay. Please Jidda."
Na fita daga kan sunan sa ina fatan a cikin messages din akwai wanda zan iya using a matsayin shaida akan sa.
Na ga kuma na yaya Tahir "call me"
Na fita and I resist the urge to open my WhatsApp, amma sai na bude instagram, hoping to find pictures and videos da zasu debe min kewa har bacci ya dauke ni. But the first post a saw was from Umar, yayi posting around 12 na daren ranar.
Hoton hannunsa ne with my band on it, ya juyo dai dai gurin rubutun "beauty queen". I noticed yadda strings din duk suka tsufa wadansu ma dun tsinke. Yayi captioning picture din
"Be Safe. Please"
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing in kika yi kin ci amana kuma ke da Allah*
*The Phone Call*
Na kife screen din wayar tare da jan karamin tsaki, sai kuma na juya baya na tare da jan abin rufa na rufe har fuskata, mintuna kadan sai na bude idon sannan na juyo na kuma daukan wayar na sake duba post din nasa.
"Be safe. Please"
Na runtse idona ina jin hawaye suna zubowa daga idona suna bin gefen fuskata zuwa cikin kunnena. Na kuma bude idon tare da sake kallon hoton, sai na shiga cikin comments naga yan uwan mu da abokan arziki suna ta yi masa jaje, from their comments na fahimci an dauka bata muka yi ko sace mu akayi, wadansu ma suna tunanin kidnapping din mu akayi, cikin masu yin jajen har da Bashir. But nasan shi Umar din ya san ba sace mu akayi ba, Umma da Abba ma sun sani. Sai na samu kaina da tambayar kaina ko me suke ciki? Ko wadanne matakai suka dauka na ganin sun gano in da muke? Ko kuma sunyi fushi sunce sun bar wa duniya mu?
Na fita daga instagram din sannan na kashe wayar na mayar da ita cikin jaka na ajiye, amma bacci ya gagari idona and my stupid heart want to know halin da Umar yake ciki. It belongs to him dama na sani, it always does, but a hankali it will learn to live without him. Sai na hakura da baccin na tashi nayi alwala nayi sallah ina rokon Allah ya bani juriya da karfin zuciyar fuskantar battles din da suke gaba na, the battle with iyayena, with yayana, with the society and with my heart.
Washegari Diyam ta same ni da maganar cewa tayi wa mijinta magana ta kuma ya amince da in zauna a tare da su zuwa muga yadda Allah zaiyi da ni, ya kuma ce in bashi address din gidan mu da kuma na Umar dan ya saka a ke bincika min halin da suke ciki kuma muke sanin duk moves din su dan musan move din da zamu yi mu kuma.
Sannan kuma yace in zauna in bari su nemo ni da kansu, in their struggle to find me zasu fahimci how much they love me, sai dai kuma in lokaci ya ja da yawa ba tare da sun samo ni din ba sai ni in neme su saboda auren da yake kaina. Ya kuma yi min alkawarin tsaya min da duk karfin sa na jiki da na aljihu, yana kuma yi min fatan alkhairi.
Naji dadin haka sosai, naji dadin kulawar su da shawarwarin su da maganganu masu dadi dana samu daga gare su, sai naji ina fatan ina ma dai al'umma zasu yi koyi dasu? Ina ma dai sauran mata zasu zama kamar Diyam suke taimakawa tare da tsayawa yan uwansu mata a duk sanda suke buƙatar hakan? Amma mata da yawa su suke haka rami su binne yaruwarsu mace dan kawai suyi replacing position din ta in a society. Sun manta karma, what ever you do will be done to you.
Time started moving, slowly at first sai kuma ya fara gudu, days turned in to weeks and week turned to month
Har na yi wata daya a gidan Diyam. At first rayuwar da wahala, na kasa adapting haka yara na ma musamman Yasmin har sai da tayi ciwo farkon zuwan mu kuma har yau bata warware ba. She kept to her self and cry for her Daddy some times, other times kuma ta kan saka ni a gaba da tambayoyin yaushe zamu koma gidan mu? Me muke yi anan? Ina daddyn su yaushe zai zo ya dauke mu?
Asad kuma ya saki jikinsa daga farko, musamman da babbar yar Diyam Subay'a tazo gidan take kuma daukan sa suyi wasa har ta koya masa swimming a pool din gidan, amma daga baya shima sai ya fara gajiya ya fara damuna da tambayoyi, daga karshe ma sai ya tsiri yin kuka kusan kullum da daddare yace shi gurin Daddy zai tafi ya kwana a can.
I kept telling myself cewa zasu saba, nima zan saba, but in reality kullum in suna kukan nima rufe kaina nake yi a toilet inyi abina in wanke fuskata in fito cos I was also battling with my own heart amma na riga na yanke hukunci kuma I don't think zan chanja magana, na gama auren Umar.
Diyam har been so supportive, ta taimaka min sosai da kalamai da shawarwari sannan tana iyakacin kokarin ta gurin debe min kewa a hanyar ja na a jiki da involving dina a dukkan household activities dinta, but bana shiga musamman in nasan mijinta yana nan, in yana gida kullum ina daki duk da nasan gidan ba lallai ne ma in na fito mu hadu ba but bana son in zama na takura musu in any way.
In sunyi baki ma bana fitowa, wannan kuma shawara ce muka yi da ita dan bamu san irin bakin da zata yi ba maybe wadanda suka san ni ne ko kuma suka ga cigiya ta wadda a yanzu babu inda cigiya ta bata kai ba. Kuma duk mutane sun tafi akan cewa sace mu akayi ni da yara saboda son da Umar yake yi mana.
Mijin Diyam ya taimaka min yayi amfani da connections dinsa gurin karbar min leave daga gurin aiki, wannan shine kadai sakon da na tabbatar Umar ya samu daga gare ni. And a ranar da daddare bayan na kunna wayata kamar yadda na mayar aladata sai naga sakon sa.
"Thank you. Thank you for letting me know you are safe"
Nayi tsaki ina jin haushin yadda ya dauka saboda shi nayi haka. Wata zuciyar ta bani shawarar inyi masa reply ince ba dan shi bane ba wata kuma ta ce in rabu da shi, kulawa ma ai yabawa ce.
Na kan turawa yaya Tahir sako duk sanda na bude wayata, telling him am okay, ina kuma rokonsa da ya gaya wa Umma cewa lafiya ta kalau, he kept insisting in kira shi amma naki, ya fara tambayata inda nake shima ban bashi amsa ba. Kamar yadda ban taba bawa Umar amsar sakonnin sa da yake turowa endlessly duk rana duk dare ba, most of which bana ma karantawa, da yawa dana karanta kuma rantse rantse ne akan cewa karya Asabe take yi masa, sai kuma alkawarirrikan cewa ya tuba ya daina halayyar sa, da yawa daga ciki kuma kalaman soyayya ne da nuna irin son da yake yi min da irin halin damuwar da yake ciki na rashina da yaran mu a tare da shi.
"I loved you yesterday, I love you today, and I will love you tomorrow and forever"
One of the messages said. And I immediately deleted it.
Wanj lokacin kuma fada ne, har da masifa sometimes
"You think ba zan iya rayuwa ba sai da ke? To kinyi kuskure. Ki fi ruwa gudu. I will live just fine with or without you"
Ko sai daya ban taba bashi amsa ba
Sanda mukayi wata daya ne wata rana da dare bayan na kwantar da yara sai Diyam tazo tace in je inji Sadauki. Na saka one of the hijabs da ta bani na bita a baya muka hau samansa, the first time da na shiga bangaren sa kenan and I couldn't help but noticed irin tsari da kuma irin kudin da aka zuba a gurin. Yana zaune akan carpet yana wasa da twins din sa, na zauna can gefe tare da gaishe shi. Ya amsa sannan yace "an kawo min labari, maman ki tayi tafiya zuwa kasar iyayen ta. Ethiopia ko?"
Na ja numfashi na bude ido sannan na rufe baki da hannu na cikin mamaki "umma ta tafi Ethiopia?" Ya ajiye Aabid da yake kan cinyarsa yace "kamar murna naga kina yi? I thought zaki ji babu dadi ne ta tafi garin su a lokacin da ake tsakiyar neman ki?"
Diyam ta zauna kusa da shi tace "murna take taya Umma, Umma tunda aka haifeta bata taba taka kafarta zuwa kasar iyayenta ba saboda Abba ya hana ta. Babu abinda take so a rayuwar ta fiye da taje garin su kuma yanzu burinta ya cika taje"
Naji hawaye ya taho min, Allah sarki Umma ta, "amma ya akayi ta tafi?" Na yi tambayar more to myself. Sai Sadauki yace "I am guessing Abban ku ne ya tura ta can neman ki. Maybe ya dauka can kika tafi" na sake girgiza kaina cikin rashin fahimta nace "maybe. But I doubt that. Bana jin Abba zai karya kambunsa na cewa ba zata je garin su ba just saboda na bata. Bana jin I am that important to him. Bana jin zaiyi magana biyu akaina"
Diyam tayi murmushi "Jidda kenan. Kina son Yasmin?" Na bude ido ina kallon ta, sai ta sake tambayata "kina son Yasmin? Zaki iya karya wani alkawari da kika yi saboda ita?" Nace "of cause ima son ta mana. Ba kuma abinda ba zan iyayi saboda ita ba in dai bai sabawa islam ba" tace "to haka Abba. Iyayen mu basu iya nuna soyayya ba, musamman mazan, suna ganin in suka nuna wa matansu ko yayan su so hakan zai rage musu kwarjini a idon su amma kuma suna son mu kamar yadda muma muke son yayan mu"
Nayi shiru still not believing that. Sai kuma nace "but na kan yi wa yaya Tahir text message in gaya masa ina nan lafiya lau, kuma ina using number dina ne, that ought to show them ina kasar nan ne ban bar kasa ba"
Sadauki yace "really? Then maybe baya gaya musu. Maybe yana da nashi dalilin na kin gaya musu. Ko kuma yana gayawa Umma ita ce bata gaya wa Abba with hope that zai barta ta je garin su, and now she got her wishes"
Nayi shiru ina jujjuya maganar, naji dadi da Umma ta samu damar ziyartar danginta a saboda wannan abin da ya faru, lallai komai yana da nashi good side din, but my heart ached for her idan har yaya Tahir baya gaya mata sakona.
Muryar Diyam ta sake dawo dani cikin hayyacina "and there is another news, ban san good news zan ce ba ko kuma bad" na dago ina kallon ta ina jin kirjina yana bugawa, sai ta juya ta kalli Sadauki, nima na kalle shi, sai ya gyara zamansa yace "it is about your husband. An kore shi daga aiki"
Na rufe ido na na bude, absorbing the news. Sannan kuma a hankali nace "me ya aikata?" Yace "well, ance tun da kuka bar shi ya bar zuwa aiki saboda ya tattara hankalin sa gabaki daya zuwa neman ku. Sai suka bashi quiry, maimakon ya amsa sai ya je ya samu wanda ya rubuta masa query din ya mammare shi sai da aka fitar da shi daga gurin" na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsu na ban ce komai ba, wato haukan da nace Umar yana can yana yi da gaske yi din yake yi kenan.
Diyam ta taso daga kusa da mijinta ta dawo kusa dani ta dafa ni "kiyi hakuri Jidda, kiyi ta addu'a kinji? Kiyi ta addu'ar Allah ya zaba muku mafi alkhairi gabaki daya, kiyi addu'ar Allah ya sa abinda muke fata ya tabbata, Allah yasa wannan abin da ya faru ya zamanto silar shiryuwar sa in akwai shiriya a tare da shi, ke kuma Allah ya duba kokarin da kika yi kuma kike kanyi ya zaba miki mafi alkhairi a rayuwar ki" na dago kai ina kallon taima jin zuciyata a bushe sannay nace "ameen Nagode Halima" na juya na kalli mijin nace "Nagode sosai. Allah ya saka da alkhairi"
Diyam ta mike ta koma kusa dashi sai yayi murmushi tare da jan hancinta yace "ameen. I can do anything for Sadiyam" ta bata rai tana matsawa daga kusa dashi tace "ka takurawa hancina, so kake ka nane min shi ko" yayi dariya "son shi dai na ke yi"
Sai na fahimci sun ma fara mantawa dani a gurin, na tashi na fita sannan na fara sauka daga benen ina hada stairs bibbiyu a lokaci daya haka kawai nake jin wani memory yana zuwa kaina.
Muryar Umar "kin takurawa kunnena wallahi" muryata "laushi ne dashi, dadin tabawa"
Nayi sauri na kawar da memoryn daga kaina sannan na doshi dakin da aka sauke mu a ciki.
Ina kokarin shiga dakin naji magana, na dan kara sauri thinking Yasmin ce ko Asad wani ya tashi yake nemana. But ina shiga naga Yasmin a zaune a bakin gado hannunta rike da wayata ta saka a kunnenta.
"Eh gidan mai kyau ne Daddy, har da swimming pool"
"Ban sani ba"
"Akwai twin babies"
"Sunanta Aunty Halima"
Cikin seconds biyu na karasa inda take na warce wayar da sauri tare da daka mata tsawa "Yasmin!" sannan na daga hannu da niyyar marin ta. Ta zame daga kan gadon ta sauko kasa ta dunkule