JIDDA Kallo Daya, Zuciya Daya By Maman Maama

Author :  Maman Maama Category :  Romance

Chapter   65 / 106

192K to 195K   out of 316K words

saw something da ya saka zuciyata tsayawa a makogwarona, wani abu a cikin dan karamin zip din jakarta wanda yake makale ba lallai ka ganshi ba in dai ba bincike kake yi ba kamar yadda yanzu nake binciken neman kudi, na dauko shi ina jujjuya shi a hannuna dan in tabbatar shi din ne, na kuma tabbatar din dan nasan shi sosai, yana nan a dakin Umar kwali guda, a condom.

"Condom?" Na fada hankali "me condom yake yi a jakar Mufida?" Jin tana kokarin fitowa sai na mayar da shi na ajiye mata jakarta na fita.

But I was shocked, really shocked dan da kyar na samu na kammala breakfast sai gata ta fito ta sha kwalliya tana waya, ta zauna tana cin abinci da sauri wai sauri take yi, nace "bara to inzo in kaiki gida" sai ta girgiza kai da sauri "ba gida zan je ba, school zan shiga" tana spill 2 yanzu, wai wani course ne guda daya ya rike ta, Umar yace wai lecturer din ne marar kirki ya ki barin ta ta fita har yau.

Nace "okay to sai in kaiki school din ma ai ko" sai ta ajiye spoon din hannunta tana kallo na da murmushi tace "why are you being nice to me? Ko so kike ki yi bribing dina kar yaya Doctor yayi miki kishiya" nayi dariya "my dear sweet Mufida, ni ai naci dubu sai ceto. Dan Allah in kun tashi yi masa auren ku auro masa uku a rana daya" tayi dariya a lokacin da Umar yake shigowa gurin sai yace "dama na dade da sanin cewa ba kya kishina, kuma zan baki mamaki, sai kin zo kina kuka kina rokona "dan Allah yaya Doctor ka fasa auren nan wallahi ko mai kake so zanyi maka" Mufida ta sake dariya ni kuma na bata rai "zaka sha mamaki wallahi. Allah dai ya kaimu lokacin" babu wanda yace ameen a cikin su.

Sai Mufida tayi mana sallama wai zata tafi, and I followed her kamar rakata zanyi sai na labe a bakin gate ina so inga inda zata yi, and I saw her cross the street ta tafi wajen wata mota da take fake a gefen titi da tinted glass, ta bude ta shiga suka tafi.

Hankali na ya tashi a ranar kwarai da gaske, na wuni ina tunanin abinda zanyi da wannan information din dana samu, ni dai na tabbatar ba zan doshi Mama da shi ba sai dai ko Umar, in ma kuma Mama zata ji daga Umar din zan so ace kar ta fahimci daga gurina sakon ya fito dan ba zata yarda ba sai ma kara tsanata da zata yi tace nayi wa yarta sharri.

Shima kuma kansa Umar din ban san ta yadda zan nufeshi da maganar ba amma kuma nasan yin maganar shine dai dai a matsayi na na matar sa dole in sauke hakkinsa in gaya masa gaskiya, ita ma kuma Mufida kawata ce kuma yarinyar kirki ce ba zan so abinda nake tunani a kanta ya zama gaskiya ba.

And I decided zan gaya masa, but dole in zama careful. A ranar da daddare muna cin abinci na gaya masa, nace "ni kuwa Doctor ya zancen auren Mufida ne? Tunda aka yi na Muhsina naji an daina maganar nata" yana cin abincin sa ya daga kafada yace "taki, tace sai ta gama school, iyayen ta kuma sun goya mata baya sunce a barta tunda ta kusa gamawa, dan ma wannan dan iskan lecturer din ya rike ta da yanzu service take yi" nayi shiru ina jujjuya abincin gaba na, naji idon sa a kaina sai na dago kai muka hada ido yace "I know that look, what is it?" Na ajiye spoon din hannuna nace "dazu da ta tafi, wani ne ya dauke ta a mota" ya ajiye nasa spoon din ya rungume hannunsa yana kallona "wani kuma? Kuma baki san shi ba?" Da daga kafada, "ban san shi ba, ban ga fuskar sa ba glasses din motar are tinted" yayi shiru, and I saw his nostril suna budewa suna rufewa da sauri, abinda yake yi in ransa ya baci, sai nayi dropping bomb din. "Kafin ta fita, sanda tana wanka, ina neman kudi a jakarta, I saw a condom"

Ya mike da sauri har sai da kujerar da yake kai ta fadi, ya nuna ni "you saw something that looks like a condom, amma baki tabbatar ba, right?" Na mike tsaye nima sannan nace a nutse "I know what a condom looks like, condom na gani ba abinda yake kama da condom ba" ya dafe kansa "maybe tsinta tayi, maybe bata san ma menene ba ta dauka ta saka a jakar ta, maybe ma ba jakar ta bace ta wata ce ta ara, maybe kuma wani abin ne na makaranta ya kawo sai sunyi binciken da suke buƙatar condom. It can be anything"

Nace "maybe. Maybe not. Allah kadai ne ya sani sai kuma in anyi bincike sannan za'a tabbatar. Mama ya kamata ka nuna wa ta saka ido a kanta, kai ma kuma ka saka ido a kanta, in kun ga wani abu sai a gaggauta yi mata aure, shine dalilin da yasa na gaya maka dan ayi wa tufkar hanci tun yanzu".

Ban san ya suka yi da Mama ba but Mufida told me a waya cewa Mama ta takura mata, yanzu ta hana ta zuwa ko'ina sai ranar da take da lecture din nan guda daya da ake binta ita ma kuma tare da driver zasu je ya jira ta ta gama su dawo gida tare, har timetable din su Mama ta aika aka kawo mata dan haka tasan ranar da take da lecture da ranar da bata da ita.

Naji dadin hakan, at least za'a dakile ko ma menene yake faruwa da ita.

Bayan wannan ya wuce, lokacin tafiya aikin hajji yayi sai ga Surayya ta kira ni tana ta murna tagaya min zasu je hajji ita da Bashir "wallahi Jidda abin mamaki, kawai yazo yace ya biya min zamu tafi tare. I am sooo happy" na taya ta murna "Masha Allah. Allah ya kaiku lfy ya dawo da ku lafiya yasa karbabbiya za'a yi" 

Sai kuma ta nuna min target dinta na yi wa mijinta addu'a a gaban ka'aba, tare kuma da shawartar sa da shima yayi wa kansa addu'a, na nuna mata cewa hakan dai dai ne. Fews days bayan nan suka tafi.

Sai dai.......

Bayan sun dawo banji labarin sun dawo ba, ina ta lissafi amma shiru, har satittika suka wuce, ina son tambayar Umar amma bana son yi masa maganar duk data shafi Bashir. Sai na gwada number dinta, sai kawai naji ta shiga, a raina nace sun dawo kenan.

Muka gaisa da ita sosai sai nayi mata mitar yadda bata gaya min sun dawo ba. Sai tace

"Hummm. Jidda kenan. Zan baki labarin abinda ya faru tunda already kin riga kinsan halin da nake ciki. Kin san Bashir a Saudiyya na kama shi da mace turmi da tabarya?"

(Wannan abin ya faru da daya daga cikin readers din Jidda, she told me the story, ni kuma nayi deciding saka shi a cikin labarin dan in nuna wa masu karatu how deep zina can cut into a person's Iman, yadda har mutum zai iya tafiya macca da niyar sauke farali sai kuma ya buge da aikata zina a cikin gari mafi tsarki a cikin ranaku masu alfarma)

Naji kamar zan yar da wayar hannu saboda yadda maganar ta razana ni. Nace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" tace "Wallahi. Kin san dai nasan yana yi amma ban taba kamashi in the act ba sai a can, na dawo daga masallaci inda na dauki tsahon lokaci ina nema masa shiriya sai na zo masaukin sa na tarar da shi turmi da tabarya da wata matar da ban sani ba. Bayan sun ganni sun kuma san na gansu sai na juya na koma masallaci, banyi masa addu'ar shiriya ba sai nayi wa kaina addu'ar Allah ya bani iko da nasarar rabuwa da aurensa. Sai a lokacin na gode wa Allah da ya karbi dan dana haifa bai raya shi ba, sai a lokacin na fahimci abinda ake cewa akan duk sanda mutum yayi addu'a da iklasi ana karba sai dai in ba alkhairi bace sai a chanja masa da mafi alkhairin ta, sai lokacin da na fahimci jimawar da nayi ina yiwa Bashir addu'a ita ce Allah yayi amfani da ita ya nuna min kiri kiri cewa shi ba mai shiryuwa bane ba, sauran kuma hukunci ya rage nawa?"

"Ko maganar banyi masa ba na rabu dashi, amma muna saika a airport sai nayi hanyar gidan ubana kuma ina zuwa na gaya masa cewa na gama auren Bashir, suka dage lallai sai na koma ni kuma nayi musu hauka, na zauna na ringa rusa ihu ina cewa wallahi ba zan koma ba, babanmu har da dauko bulala zai dake ni ni kuma nace sai dai ya kashe ni amma ba zan koma ba, a ka shiga tsakani dai aka hana shi dukana"

"Amma can you believe har yau Bashir bai biyo ni ba kuma iyayensa ma basu zo ba? Na ji baban mu ya fara mita kasa kasa, na san shima ransa ya baci da abinda suka yi. Insha Allah Jidda wannan shine karshen wahala ta"

"Ni kam na kai limit dina na hakuri, nayi iyakacin iyawa ta ubangiji ma ya sani. Ba zan koma gidan Bashir ba, Allah ya sani. Ina kuma kyautata zato na a gare shi ina saka ran zaiyi min chanji na alkhairi"

Na jima ina lissafin maganar Surayya, zancen limit din da ta fada got me thinking about komai yana da limit, rayuwa, lokaci, haihuwa, komai yana da farko kuma yana da karshe, ma'ana hakuri ma yana da limit, akwai lokacin da mutum zai kai limit din sa na hakuri in yace zai yi crossing kuwa to tabbas zai tarwatse ko kuma ya tarwatsa wadanda yake tare da su.

A year pass by, tun da muka yi case din Mammy. And then one day ranar friday na dawo daga aiki da magrib, lokacin ana ta sallah a masallatai sai na tarar maigadin mu baya nan ya tafi masallaci, ya saya bakin gate din bai rufe shi sosai ba, na tsaya kenan da niyar yin horn ko Asabe tana kusa sai ta zo ta bude min sai na hangi wani abu daga crack din da bai rufu ba a gate din. Asabe ce a tsaye Umar yana tsaye a bayanta, too close, tayi wata magana sai yayi murmushi sai kuma ta juya ta bashi wani abu da yake hannunta, and I noticed wayarsa ce, ya karba ya saka a aljihunsa sannan yasake yi mata wata magana suka yi dariya.

My heart was boiling a lokacin, Umar din da ko guri daya baya zama da Asabe amma ya akayi suka yi irin wannan tsayuwar kuma me ya kai wayarsa hannunta? Me suke cewa?

Nayi horn, sai naga sun kalli gate a tare sai yayi mata magana ita kuma ta shiga cikin gida da gudu, shi kuma sai ya taho zuwa gate din ya bude karamar kofa ya fito yana murmushi, ya zo window na, "welcome back Madam, nawa zaki biya in bude miki gate?" Naji haushin yadda yake kokarin yi min wasa, Umar ba karamin pretender bane ba nace "no barshi kawai Baba Adamu ya idar da sallah sai ya bude min, kasan shi namiji ne ya tafi masallaci" sai ya saka hannu ya ja hancina "kin ci sa'a sunan ki Hauwa'u, sunan matata ne, da ace Jidda sunan ki da ba zan bude miki ba" ya bude gate din na shiga da motar sai yace min zai je masjid, ya fita.

Na jima a motar ina zaune na jingina kaina da jikin stirring ido na a rufe ido na, a hankali na furta "ya Allah" sai kuma na bude motar na fita da sauri na shiga cikin gidan. Yasmin tana kallo, Asad kuma yana game. Suka mike da sauri suka tarye ni nayi kissing din su daya bayan daya sannan nace "ana sallah kuna zaune ko? Maza aje ayi alwala. Kar a jika jiki amma" suka wuce sai kuma nace "ina Asabe?" Yasmin tace "ta shiga dakin ta yanzu da gudu" na gyada kai kawai sai na bita dakin, ina shiga naji dakin yana warin ta.

Tana kwance ta lulluba, na tsaya a kanta sannan na sa kafa na dake ta "ke Asabe!" Tayi shiru kamar ba da ita nake ba sai na daka mata duka "ke! Kar ki raina min hankali mana" ta tashi zaune tana mitsitstsika ido kamar wadda ta tashi daga bacci "mommy kin dawo?" Naji kamar in sharara mata mari "kar ki raina min hankali wallahi zan ci ubanki, uban me kike yi a waje" tace "waje kuma mommy? Ni ina nan ina bacci fa, ni banje waje ba" na damki rigarta na daga ta sama "uwarki kenan na gani tare da Umar a waje ko?" Ta fara karkarwa "mommy dan Allah kiyi hakuri, wallahi ba wani abin muke yi ba" nace "me yake ce miki?" Tace "hoto ya nuna min a wayarsa" nace "hoton me?" Tace "hoton sa ne, kawai nuna min yayi yace yayi kyau shine nace yayi kyau" na saki rigarta na fita daga dakin hannu na guda daya a dafe da kirjina ina jin zuciyata kamar zata fito na shiga dakina na rufe kofa sannan na jingina da jikin kofar. "innalillahi wa inna ilaihir rajiun".

Ba wai maganar da sukayi ce ta taba ni ba, ba kuma yadda naga sun tsaya din ba, a'a yadda yake munafurta ta tare da nuna kamar basa ma yi wa juna magana amma kuma a bayan ido na har sunyi sabawar da zai dauki hoto ya nuna mata ya tambayi opinion din ta, sannan kuma da yaji na dawo yace ta tafi daki tayi pretending kamar bacci take yi shi kuma yaje ya tsayar dani da surutu har ya bata damar kwanciyar.

Tabbas Umar bai daina halinsa ba. A cikin gidan mu kenan a gaban ƴaƴan mu, Allah kadai yadan abinda yake yi a waje. Wata zuciyar ta gaya min cewa in tattara Asabe in auna ta kauyen su, sai kuma nayi tunanin idan na dauke Asabe daga gida na hana shi kula ta a gida zan hana shi kula wadansu a waje ne? Sai na yanke shawarar zan barta, sai dai zan saka ido a kansu sosai maybe ta nan zan kama shi. But amma kuma anya? Umar? Umarul Faruq? Asabe fa? Yarinyar da har yanzu daga ni har shi bama iya cin abin da ya shiga hannun ta, bama iya amfani da cup ko spoon din da tayi using. Anya ban zurfafa zargi na ba akan Umar?

Amma kuma duk da haka zan saka ido a kan su sosai, kuma ba zan nuna wa Umar ina zargin wani abu ba, dan da zarar ya fahimci wani abu zai rufe duk wata kofa da zata sada ni da gaskiyar magana.

Da ya dawo daga masallaci yayi ta kame kamen tsokana ta da yara, ni kuma nayi iyakacin kokari na na ganin na boye damuwa ta amma na kasa, har muka je daki muka kwanta sai cewa yayi. "Dazu da na dawo daga office na tarar yaran nan basu dawo daga islamiyya ba, hankali na ya tashi nayi ta tunanin inda suka tsaya, kin san yanzu yanayin da ake ciki na rashin tsaro, nayi ta tunanin da ina da number din yarinyar nan da sai in kira su inji me ya tsayar da su. Shine bayan sun dawo na karbi number dinta, saboda gaba" nayi shiru kawai ina kallon sa, rashin gaskiya a rubuce a fuskarsa, jin ban ce komai ba sai ya cigaba "ina cikin karba ne ma kika dawo".

Na danyi murmushi, wato ya lura na gansu tare, wannan kame kamen duk na rufe gaskiya ne, na girgiza kaina nace "ka kyauta. Allah ya kare mana su" ya kwanta tare da lumshe idonsa, ina ganin yadda yayi ajjiyar zuciya sannan yace "ameen" nima na kwanta a kusa da shi na rufe ido na, abinda ya manta shine ranar Friday ne babu islamiyya.

Tun daga ranar na saka ido a kan Asabe sosai, ina lura da duk wani move din ta a gidan sai dai ko kadan ban taba nuna musu ina lura da su ba. Amma kuma inda zan gane cewa Umar ya iya covering tracks dinsa ko kallo ban taba ganin yayi mata na kirki a gaba na ba, hantarar nan dai ce da tsawa da kyara, amma ban daina lura da su ba until one fateful day, da weekend, ranar ana muku mukun sanyi duk muna gida har yara. Muna falo gabakidaya Umar yana ta wasa da yayansa yana yiwa Asad doki suna zagaya falo ni kuma ina kwance da Yasmin a jikina ina karanta mata story book. Sai aka yi knocking, na je na leka sai naga wata yarinya yar aikin makota na wadda suke islamiyya aji daya da Asabe. Ta gaishe ni na amsa sannan tace tana neman Asabe, sai nace ta zagaya ta kofar kitchen ta baya ta shiga, Asabe tana bayan ko kuma dakinta.

Na koma na cigaba da abinda nake yi sai Yasmin ta fara complain din sanyi yayi yawa, Umar yace rashin motsa jiki ne yake saka mu jin sanyi ni da Yasmin amma shi da Asad ai basa jin sanyin, sai yace a fita waje ayi skipping, a ga wanda baya exercise a cikin mu, a ga wanda jikin sa yayi nauyi. Muka fara musu nace zan iya shi kuma yace ba zan iya ba. Yasmin ta tashi da gudu ta tafi dauko mana skipping rope a dakin su ni kuma na dauki cups din da muka sha juice na tafi zan mayar kitchen.

Store (dakin Asabe) da kitchen kusan a tare suke amma kofar kowanne daban sai dai kofofin a jikin juna suke. Ina shiga kitchen din naji an ambaci sunana sai naja na tsaya a bakin kofa, muryar Asabe naji

"ke tsoron mommy fa yake yi kamar mala'ikan da zata cire ransa haka yake tsoron ta"

"Ya ke tsoron ta ko ke kike

65 / 106