JIDDA Kallo Daya, Zuciya Daya By Maman Maama

Author :  Maman Maama Category :  Romance

Chapter   53 / 106

156K to 159K   out of 316K words

karya a baki kawai ka iya yin ta amma baka iya controlling emotions dinka. Abinda bakinka yake fada daban abinda fuskarka take nunawa daban. Farkon auren mu bana ganewa sai daga baya na kara fahimtar ka.A duk lokacin da kayi min karya ina ganewa sai dai nakanyi shiru dan a zauna lafiya. Ka nemi Maryam, that's a fact, kuma in har yanzu baka yarda ba to kayi rantsuwa da Allah cewa baka neme ta ba"

Nayi shiru ina kallon sa amma bai ce komai ba kuma bai kalle ni ba. Sai na cigaba "sanin ka nemi Maryam shi ya sa nayi tunanin sanar da iyayenka ina yi maka kwadayin addu'ar su, dan na fahimci tunda har ka iya neman kawata to Allah ne kadai yasan yawan wadanda kake nema, maybe har a cikin yan'uwa ma, natan ne dai ya fito tunda tayi niyyar tona maka asiri a guri na"

A lokacin muka shiga gida yayi packing ya juyo "Jidda" na daga masa hannu "please ka rike maganganun ka bana son ji, not now please"

Muka yi shiru muna kallon juna, sai a lokacin muka ji sheshshekar kukan Yasmin. A tare muka bude kofa muka fita muka kuma bude kofar baya a tare, na riga shi daukan ta na rungume ta ina shafa bayanta "Yasmin? Menene kike kuka?"

Ta dago kai tana kallona "ba Mama bace tayi miki fada kuma shine kuke fada ke da Daddy"

Na sake rungume ta ina jijjiga ta kadan, a raina ina mamakin wayon yarinyar "ba fada muke yi ba Yasmin, magana kawai muke yi kinji" ya zagayo ya miko hannu zai karbe ta sai na wuce shi na tafi cikin gida shi kuma ya dauko Asad da yake ta baccin sa hankalinsa a kwance.

Ya wuce dashi daki ya kwantar dashi, ni kuma na zauna a palo da Yasmin a jikina ina rarrashin ta. Sai gashi ya dawo da magungunan da ya siyo min tun a asibiti a hannun sa da kuma robar ruwa, ya ajiye min a gefe na sannan ya saka hannu ya dauki Yasmin "Yasmin, mu je daki ki kwanta kinji, ki bar mommy kinga bata da lafiya, yanzu ma zanzo inyi mata allura, shi yasa dazu a mota take cewa bata so ni kuma nake cewa sai nayi mata, wai ita tsoron allura take yi. Ba fada muke yi ba kinji mamana?"

Da haka suka shige ciki ni kuma na kwanta akan kujera na rufe ido na ina sauraron yadda kaina yake tsananin sarawa, trying so hard not to think about maganganun Mama. Motsin sa naji ya dora hannun sa akan nawa da yake kan goshina. "Ciwon kan ne ko? Ki tashi ki sha magani"

Na dan bude ido na kadan na kalle shi ina jin haushin yadda fuskarsa take nuna damuwa a kaina. Na ture hannun sa daga kan nawa "ina ruwanka da shan magani na? Ina ruwanka da lafiya ta?" Ya zauna a gaba na tare da bare maganin sannan ya bude robar ruwan "dan Allah ki sha, in kika samu lafiya zamu zauna muyi maganar kinji?"

Nace "babu wata magana da zamuyi ni da kai, saboda mun gama magana tsakanin mu ya saka na kai maganar gurin iyaye dan nayi tunanin zasu fahimta za kuma a samu maslaha, I was wrong, amma yanzu ma ba zan hakura ba, gurin nawa iyayen zan kai maganar tunda Allah yasa nima ina da iyayen kuma suna so na nima"

Yace "Jidda please, ki daina maganar zuwa gidan nan dan Allah. Ni bana so maganar nan ace ta kuma fita daga tsakanin mu, we i solve this together, ni da ke" na jiya kaina "I thought we can, tunda nasana halinka I kept thinking I can change you, yanzu na fahimci I can't, tunda har ka iya neman kawata nan gaba ban san wadda zaka nema ba kuma, Amira? Ba zan jira gar sai hakan ya faru ba. wallahi Umar a yanzu abinda yasa kawai nake cikin gidan ka gida daya ne, saboda bani da lafiya nasan ko bakin titi ba zan iya zuwa ba, amma duk sanda naji sauki abu daya ne zai hanani tafiya gidan mu"

Yayi saurin rike hannuna tare da cewa "menene? Me kike so?" Nace "ka koma gida ka samu Mama ka gaya mata cewa duk maganar da na fada gaskiya ce, kayi mata admitting mummunar dabiar ka kamar yadda kayi min, sai kuma ka roke ta take maka addu'a ta kuma baka shawarwari"

Ya fara girgiza kai "Jidda Mama fa kike magana akai, mahaifiya ta ta yaya zan iya gaya mata maganar nan. Dazun ma ba wai dan in bata ki naki karbar maganar ba sai dan ba zan iya ba. Mahaifiya ta ce fa Jidda" na mike tsaye "saboda mahaifiyar ka ce shi yasa nake ganin ita ya kamata ta fara sanin halin da kake ciki, ko ba komai nasan ba zata yi disowning dinka ba kuma ina tunanin sai tafi kowa damuwa da kuma nema maka mafita. Amma ba zata yi hakan ba har sai ka amsa laifin ka"

Ya sake cewa "I can't, Jidda I can't" na fara tafiya "then I have nothing more to do with you, daga na samu lafiya zan kama hanyar gidan mu tunda ni ma haifata akayi, nima kuma nawa iyayen suna so na kamar yadda nake son su"

Ya riko hannu na ya mika min maganin, "to naji, ki sha magani amma, kinga in baki sha ba ai ba zaki samu lafiyar ba" na karba na jefa a baki na kora da ruwan da ya miko min sannan na wuce shi na shiga dakina na kwanta. Na fara tunanin yadda tafiya ta zata kasance zuwa gidan mu da zarar na farka naji jikina yayi karfi kuma na daina jin jiri.

Sai dai sanda na farka maimakon inji jikin da sauki sai ma karuwa da naji ciwon yayi, lokacin tsakiyar dare ne kuma zan iy cewa ba dan da sauran kwana na a gaba ba da a daren zan bar duniya, amma da taimakon Allah da kuma kasancewar Umar Doctor na wayo gari, da assuba ya dauke mu ni da yara ya ajiye yaran a gidan su sannan ya zarce da ni asibiti.

Muna zuwa aka bani gado, aka kuma fara bani taimakon gaggawa saboda bayan bp na da yayi sama ga asthma ta data tashi ta rike min numfashi na, a very dangerous combination. A dole suka saka min oxygen sannan suka yi min allurai, Umar duk ya wani rikice, ni kuma rikicewar tasa tana kara kona min rai da kara saka min jin haushinsa, dan haka sai kawai na mayar da ido na na rufe, a haka bacci ya dauke ni.

Kwana na daya a asibitin ya matsa lallai sai an sallame ni, yace shi zai cigaba da kula da ni a gida, ni kuma na lura gani nake yi insecurities ne suke damunsa gani yake yi kamar zan fi saurin tafiya gidan ne daga asibitin kamar yadda nake ta gaya masa a duk lokacin dana bude ido na. Sai dai muna shiga gidan na jawo jaka na fara hada kaya na kuma nace yaje gidan su ya dauko min yayana dan ba zan tafi in barsu ba.

Ya karbe jakar yana mayar da kayan ni kuma ina sake debowa ina mayar wa cikin jakar, ina sakawa shi kuma zai dauke ya mayar cikin wardrobe. A karshe dai ya zagaye ni da hannayensa ya kankame ni a jikin sa "Jidda, Jidda. Ki tsaya hakanan please. Listen to me please"

Na fara kokarin kwace kaina shi kuma ya ki cikani a haka muka fada kan gado, da yake ba lafiya ce ta ishe ni ba kuma karfi na ya kare sai na kwanta lakwas shi kuma ya samu yadda yake so "dan Allah ki tsaya ki saurare ni Jidda. I know I have hurt you more than yadda nake tunani ma, kuma da kinsan nadamar da nake ciki yanzu a zuciya ta da kin sassauta min Jidda. Wallahi Jidda yarinyar nan ta jima tana nemana ban taba gaya miki bane ba saboda kar ranki ya baci, ta jima tana yinkuri bani kanta kyauta, kuma....... Jidda ban san me yazo kaina ba a lokacin dan Allah kiyi hakuri..... I had no idea plan dinta kenan..... I didn't know what I was doing or thinking...... Jidda dan Allah kiyi hakuri...."

Na lumshe idona hawaye yana zuba daga idon nawa, hawayen da nake jin su tamkar turiri ne da yake tahowa daga zuciya ta. Finally yayi accepting cewa yayi.

Nace "aikin gama ai ya riga ya gama ai. Ka riga ka zubar min da mutunci na ka kuma ya shi a kasa. Ka kuma zubar da duk wani sauran abu da yake tsakani na da kai accept for yayan da suke tsakanin mu da kuma igiyar auren ka da take wuyana. Abu dayaya rage shine a kiyaye gaba. Abinda nake tsoro shine ranar da zan ganka in the act a cikin gidan nan tare da wata shakikiya ta ko taka"

Yayi sauri ya rufe min baki "Jidda don't say that please. Wallahi, kinji na rantse miki wallahi ko? Hakan ba zata  taba faruwa ba. Insha Allah Jidda in kika kara min wata dama, nasan banyi deserving kowacce dama ko alfarma a gurinki ba, amma in kika bani, bazan baki kunya ba Jidda nayi miki alkawari. We have come sooo far Jidda. Kar mu bari duk kokarin mu ya zama for nothing. Ki sake gaya min wadansu sharudan, ko menene zan bi kamar yadda nabi wadancan"

Nace "wadancan din ai baka bisu ba gabaki daya, da nace kayi auren ai baka yi ba" ya langwabe kai kamar zaiyi kuka "Jidda aure fa kike magana akai, shi aure ai ba haka kawai ake yinsa ba sai da niyya tunda ibada ne kuma sai na samu wadda nake so na kuma yarda cewa zan iya sakata cikin iyali na kuma ta haifa min yaya. Bani da niyya Jidda kuma bani da wadda zan iya aure a yanzu. Ki fadi wani sharadin please, in karamar wayar kike so in ajiye wallahi zan ajiye ta, in daya aikin kike so in bari in nemi wani source of income din wallahi I will do it indai hakan sai faranta miki"

Na girgiza kaina "ni fa duk dadin bakinka na gama jinsa, na gaya maka ai abinda nake so Umarul Faruq, kaje ka samu Mama ka gaya mata cewa duk abinda na fada gaskiya ne ba karya nake yi maka ba. Wannan ne kadai zai nuna min you are willing to change, sannan kuma zai samar maka abinda kwadayin sa ya saka na gaya mata in the first place, zai samar maka addu'ar ta data Baba, kuma za'a samu zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mu, dan a yanzu ka riga ka shafa min bakin fenti a idonta, fentin da bana jin zai gogu anytime soon"

Yayi shiru yana kallon fuska ta, ina kallon adam's apple dinsa yana ta motsawa sannan ya rufe idonsa ya bude "Okay. Okay. I will do that. Amma a matsayin alkawari cewa zaki ajiye maganar zuwa gida and it will be karshen maganar nan tsakani na dake, we will never mention it again"

Na lumshe idona na bude sannan na gyada kai, "na yarda. And I really hope we will never mention it again" ya danyi murmushi, fuskarsa tana nuna hankalin sa ya fara kwanciya, sai yayi kissing goshina da cheeks dina yace "you are a very good wife Jidda, you don't deserve me, but insha Allah ba zan kuma baki kunya ba. Allah yayi miki albarka"

He kept his own side of the bargain, ya je kuma yayi abinda mukayi dashi zaiyi din. Ban dai san ranar da yaje ba amma nafi tunanin kwana biyu bayan munyi maganar ne ranar da yaje ya dauko yara. Na kuma tabbatar da yaje din saboda baƙin da nayi washegari. Mama, Muhsina da Mufida.

Tun daga yanayin shigowar su na gane babu lafiya, na zauna na gaishe da Mama taki amsawa kuma na lura babu wanda yayi min magana a cikin su Mufida, sai kuma Mama ta bude min fanfon bala'i ta inda take shiga ba tanan take fita ba.

Tace ni na matsawa Umar na saka shi ya amsa laifin da ba nasa ba kawai dan ya faranta min, saboda nayi masa sharri tayi min fada, shi yasa na dauki fushi da shi har na kirkiri ciwon karya na saka lallai sai yaje yace karyar da na fada akan sa gaskiya ce.

"Kin san kuwa hukuncin kazafin zina a musulunci Jidda? Kin taba kamashi turmi da tabarya da mace? Kin san kuwa in aka kaiki Shari'a court a yanzu bulala nawa za a yi miki?"

"To wallahi ki shiga hankalin ki Jidda, kin rikita min yaro kin susuta min shi baya jin maganar kowa baya kuma ganin kowa da gashi sai ke. Farko na dauka soyayyar gaskiya ce yake yi miki har ina taya shi son ki, sai yanzu da abin ya fara wuce gona da iri sannan na fahimci ba haka kika bar shi ba, amma ki je ki biya malamin da yayi miki aiki a kansa dan tabbas yaci kudinsa, ke kuma ki jira ni, daga nan har Maiduguri sai naje na karya dukkan sihirin da kika yi masa"

"Sannan kuma ina ja miki kunne, wallahi wallahi kika kuma bin dana da wannan muguwar maganar har wani yaji, ko da kuwa babansa ne wallahi court ce zata raba mu ni da ke"

Tun da ta fara maganar na sunkuyar da kaina ina jujjuya zoben Umar da yake hannuna, ban dago kai ba har ta gama maganar ta kaf ballantana in tanka mata. Tana gamawa sai ga Umar ya shigo kamar daga sama yana huci, na daga kai ina kallon sa, daga gani nasan kiransa akayi amma ni bani bace na kira shi ba, jikina ya bani Mufida ce.

"Mama!" Ya fada, ta nuna masa hannu "ka kiyaye ni Faruq, kar kasa inyi maka mummunar magana" na mayar da kaina kasa na ma daina kallonsa, ya zauna a gaban ta sai ta mike, suma yayan suka mike tare da ita. Muhsina taja tsaki "aikin banza aikin wofi" ya mike kamar wanda akayi wa allura yayi kanta uwar ta shiga tsakani "kar ka sake ta taba min yarinya akan wannan munafukar abar da kake kira da mata"

Yaja baya ya tsaya baice komai ba har suka fice.

Yazo gabana ya durkusa ya rike hannuna, sai na dago kai na kalle shi nace "sannu da zuwa, a kawo maka abinci?" Bai ce komai ba na mike na shiga kitchen na sauke abincin dana riga na kammala, na juye a warmer na fitar da shi waje, har yanzu yana nan a inda na barshi a zaune.

Na rike kugu "ko sai nazo na dauko kane? Wake da shinkafa fa nayi kuma dan nasan kana so" ya mike yana kallona "manja ko man gyada?" Nace "manja" sai ya miko min hannun sa na kama zuwa dining, na ja masa kujera ya zauna "ki ce yau zan ci abinci da yawa kenan?" Nayi dariya "what do you mean? Ban iya girki ba sai wake da shinkafa?" Yace "ni na isa ince haka? Kawai dai ina son sa ne" nayi kissing tsakiyar kansa "shi yasa nayi maka"

Wannan shine tushen samun matsala tsakani na da in laws dina, daga ranar suka yanke duk wata alaka tsakani na da su, ko da zanje gidan in gaishe da Mama ba zata amsa ba, Muhsina da muhibbat duk sun daina kulani, hatta Mufida ta chanja min ba kamar da ba duk da dai nayi tunanin Mama ce take hana ta kula ni.

But I also kept my end of the bargain, ban je gidan ba kuma ban kuma yi masa maganar ba sai dai wannan abin da ya faru ya koya min wani darasi da da ban sani ba, yanzu kuma na sani sannan ina kira ga duk matar da mijinta yake da hali irin na mijina. Kar ki yarda ki sanar da iyayensa, I repeat, don't do it. Bance dukkan su ba zasu yarda ba but 80% na iyaye are selfish a kan yayan su. Wasu daga cikin su ma sunsan halin da yayan nasu suke ciki amma in kika fada sai kiyi bakin jini.

Yes, it is a good idea idan suka sani din, but let them find out da kansu.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar ki yi sharing, idan kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*The Visitors*

Yasmin ta fara zuwa makaranta, and I got a little bit busy tunda ni nake dukkan hidimar kaita morning and evening schools dinta da kuma dauko ta. Sai naji wannan dan abin da nake yi ya rage min damuwa da yawan tunani, a lokacin sai na fara tunanin ya kamata in fara aiki tunda dama cikin Asad ne ya hana ni kama aikin kuma ga Asad har yana neman yin shekara daya. Amma bukukuwan da suke gaban mu a lokacin sai suka saka na dakata da maganar aikin tukunna.

Bikin Muhsina aka fara yi. A lokacin bikin ne na kuma tabbatar wa kaina da cewa akwai matsala sosai tsakani na da in-laws dina, basu sakani a cikin komai na bikin ba kamar yadda suka saka ni a lokacin bikin Muhibbat. Sai card kawai Mufida ta turo min ta WhatsApp.

Farko cewa nayi ma ba zan je ba "Doctor bana jin zan je bikin nan, bana son mu samu problem a cikin mutane" ya girgiza kai "nooo that will never happen. Mama ce fa, her barks is always more than her bit. Ranar nan fada ne kawai tayi amma bana jin ma abin yana ranta har yanzu"

Na ji shi dai kawai amma ban yarda ba, "dan Allah Jidda ki je, in baki je ba shine mutane zasu iya samun abin fada"

Sai kuma yaya Mubaraka

53 / 106