Author : Maman Maama Category : Romance
kallon kofar sitting room din amma na dauke kaina nayi kamar bansan me yake yi ba. "Gani ance kana kirana" ya dan yi jim sannan yace "kin san dalilin kiran naki ai ko?"
Nayi shiru. "Jidda me yasa kike rufe min duk wata kofa da zata sada ni da zuciyar ki ne? Me yasa ba zaki bani dama ba?" Na dan kalle shi "to ba gani na fito ba? In bana so in baka dama ai ba zan fito ba ma ko?" Yace "Kamar yadda baki fito ba ranar nan? Ki ka ce ace ba kya nan?" Nayi shiru ina jin nauyin sa, ashe yasan ina gida a lokacin.
Ya cigaba "yanzu ma jikina yana bani cewa matsa miki aka yi kika fito, dan gashi ko gurin zama kin ƙi ki bani" a raina nace wannan mutumin ko dai dan duba ne? Allah dai ya shiga tsakanin nagari da mugu. Sai nace "ina wani abu ne a cikin gida shi yasa, bana so in dade sosai" ya danyi yar hirarsa shi kadai wadda in za'a yanka ni bansan me yake cewa ba, a karshe ya hakura yayi min sallama ya tafi.
Washegari Umar ya dawo. Wannan karon bayan magrib yazo kuma tun a aiken farko yace ace inji Umar, nayi kokari sosai wajen boye excitement dina, Amira harda riga ni shiryawa wai zata je ta gaishe shi sai da Umma ta hana ta "bana son kwadayi, dan ya baki kudi ranar nan shine zaki koma masa?" Ta hakura ta zauna amma ranta bai so hakan ba. Ni kuma na shirya na saka hijab dina na dauki takarda ta na fita.
Sai da na bude kofar sitting room din sannan na leka waje, yana tsaye a gaban motar sa idonsa yana kallon kofar da yake saka ran zan fito. Muna hada ido yayi min murmushin da naji shi a ko'ina na jikina, ban san sanda na mayar masa ba sannan ba tare da nace komai ba na koma ciki shi kuma ya biyo ni.
Ganin yana zama a kasa ya saka yau na riga shi zama a kasan. Shima ya zauna sannan na gaishe shi. "Ya mutan gida? Ina Amira" "tana ciki" na amsa "ina Farhan? Ita ba zata zo mu gaisa ba?" Nace "zata zo mana, ba ka neme ta bane ba" yace "ita ma Amira ai ban neme taba, dan tana da kirki ne ya saka tazo" nace "wato Farhan bata da kirki kenan ko? To sai na gaya mata" ya daga hannu "kar ki hada ni da ita, dan naga alama a gurinta ne zan kafa gwamnati na. Nayi murmushi "tabbas. Dan ita ce babbar aminiya ta" yace "har Mufida? Sai na gaya mata"
Na danyi dariya "kar ka hada ni da ita, dan naga alama nima ta gurinta zan kafa tawa gwamnatin" yayi dariya sosai sannan yace "tabbas, dan kaf sisters dina nafi ji da ita, but she is a little bit stubborn, abinda na fahimci shine ya karfafa kawancen ku" na rike baki "ni yanzu stubborn ce?" Yace "sosai ma, gashi har yanzu kin ki cewa I love you Umar" na jawo hijab zan rufe fuska yace "na daina tsokanar ki, dan Allah kar ki hana min kallon kyakykyawar fuskar ki mana, dan Allah" ya fada murya kasa kasa yana hade hannayensa alamar roko.
Na saukar da hannu na kasa amma na kasa daga ido na dan ina jin idanuwan sa akan fuskata. Na fara wasa d band din hannuna, sai naji yace "ni fa kishi ne dani" na dago ido nace "kishin me fa?" Ya nuna band din "wannan" nace "wannan kuma? Menene abin kishi a wannan?" Yace "ina kishin attention din da kike ba shi, sai zuciyata take gaya min kamar wani ne ya baki shi" na bude ido "wani kuma? Wallahi ba wani ne ya bani ba, yan sport club din makarantar mu ne suka bamu as soveniers, in baka yarda ba ka tambayi Mufida"
Yace "ban yarda ba, ita ma kuma in ta gaya min ba zan yarda ba saboda duk bakin ku daya" nace "gaskiyar kenan. Wallahi" yace "kina so in yarda?" Na gyada kai sai ya miko min hannun sa yace "ki bani. Nasan in na wani ne ba zaki bani ba. In baki bani ba zan tabbatar saurayi ne ya baki" na fahimci wayo yake son yi min amma babu yarda zanyi sai na cire na mika masa, sai kawai naga ya karba ya saka a hannun sa.
Nace "yayi maka kadan ai" ya nuna min hannun, "yayi min dai-dai dai. Dama ai ke yayi miki yawa" na kalla naga yadda yayi masa kyau sosai a kan farar fatarsa kuma ya dace da zobban azurfar da suke yatsunsa. Ya karanto rubutun jiki "beauty Queen. Lallai ko waye ya bada wannan sunan da zan ganshi da sai na bashi kyauta, ya bawa Baby na sunan daya dace da ita"
Nayi murmushi ina so in mayar masa da kalaman sa in gaya masa shima kyakykyawa ne amma kunya ta hana ni, sai na wayance da zuwa kiran Farhan su gaisa, daga nan sai hirar ta koma mu uku a inda yayi ta bamu labaran sanda yake makaranta da irin wahalhalun da yasha a wajen karatu. Sai bayan ishai sannan yayi mana sallama na raka shi bakin mota ya shiga. "Bye Baby" ya fada yana murmushi sannan ya tafi.
Sai bayan ya tafi sannan na tuna da takardar dana fito da ita zan bashi amma tunda na dora ido na akansa na manta batun takarda. Gashi bani da number din sa ballantana in kira shi kuma na san ba karamin fada Umma zata yi min ba in taji ban bashi ba, Sai na koma na dauke ta na daga kujera na saka ta a can ciki yadda babu wanda zai ganta da niyyar in ya dawo sai in bashi.
Zuciyata fes na koma cikin gida, muka ci abinci muka sha hirar mu a tsakar gida sannan muka je muka kwanta, sai dai muna kwanciya Farhan ta dauko wata maganar data bata min farin ciki na "gyneacologis ko?" Nace "eh, me yasa kika tambaya?" Ta danyi dariya "ni tunda ya fada kawai naji kunyar sa ta kama ni" na mike zaune "saboda me?"
Ta mike itama "Jidda likitan mata fa kenan. Hakan yana nufin duk wani abu da kike dashi a jikinki har ma wanda baki san kina da shi ba shi ya san da shi. Hakan kuma yana nufin duk sanda yace ya tafi gurin aiki to y tafi duba mata ne, in nace duba mata ina nufin parts na mata, including the most private parts. Duk patients dinsa fa mata ne"
Naji wani abu mai zafi ya taba zuciyata, na fara kokarin neman amsar dazan bata amma na rasa sai ta koma ta kwanta cikin tsokana tace "daga yau ki saka a ranki yasan komai da kike boyewa a cikin hijab dinki" na daka mata duka a baya "karya ne wallahi. Yasan dai na wasu marasa lafiya amma ba nawa ba" ta tashi tana sosa inda na dake ta tace "da naki da nasu duk daya tunda duk mata ne" nace "a'a wallahi, bai san nawa ba kuma nawa special ne ba irin na kowa bane ba" na kwanta ina kallon ceiling amma zuciyata tana kuna, ita kuwa dariya take yi, da alama bata san irin ciwon da maganar ta ta ji wa zuciyata ba.
Har sai da ta gama dariyar ta sannan nace "kuma ai aikin sane haka, aiki yake yi ba wai kalla yake yi dan yana son ya kalla din ba, babu komai a zuciyarsa sai neman yadda zai warkar da patients dinsa" sai data tashi ta matsa sannan tace "bayan kalla har tabawa yake yi" tayi tunanin zan kai mata duka ko wani abu amma sai n juya baya na ina jin raina yana kara baci, sai na samu kaina da tambayar kaina me yasa Umar ya zabi ya zama likitan mata?
Why not likitan yara? Ko likitan maza jinsin sa? Ko kuma likitan daya daga cikin manyan cututtukan da suka addabi al'umma. Why likitan mata? Amma sai zuciyata wadda take a cike taf da soyayyar sa ta bashi uzuri da cewa idan har maza basu karancin bangaren mata ba to za'a samu matsala a bangaren tunda mata basu cika samun damar yin karatu kamar maza ba, he is just doing a job to earn a living and save lives.
Washegari ya dawo, amma kamar ranar daya bani takarda yau ma mota ya tsaya "na manta ban karbi form ba, I hope kin cike?" Na gyada kai "na fito dashi ma jiya zan baka kuma sai na manta" yace "nima mantawar nayi, da maganar nazo a raina amma ina ganin ki na manta da komai sai ke" nayi murmushi kawai dan nima hakan take, sai na koma n dauko masa na dawo na bashi, briefly ya duba sannan ya shiga mota ya koma.
Washegari Musa ya dawo, ya tarar da yaya Muslim a sitting room dan haka ya shiga suka gaisa sannan ya nemi ya kira masa ni, ina jin cewa shine na tashi na fita a raina ina son in gaya masa gaskiya dan ya daina wahalar zirga zirga mu daina bata wa juna lokaci, gaskiyar ita ce baiyi min ba a matsayin miji amma bashi da wata makusa kuma na tabbatar mata da yawa zasu karbe shi hannu bibbiyu.
Na shiga na gaishe shi ya amsa da fara'ar sa yana jin dadin na gaishe shi, sai naji na sake jin rashin dadin abinda zan gaya masa. Nace "yaya Musa, kai mutumin kirki ne sosai, Abba da Umma ma duk sun yaba da kai, amma ba Abba da Umma ne zasu zauna da kai in ka aure ni ba" ya mike tsaye "ke zaki zauna dani kuma ke baki yaba dani ba ko?" Na mike nima nace "ba haka bane ba. Bana jin shi so yana tafiya ne a haka. Bamu da zabi akan wanda zuciyar mu zata so ko kuma take so....."
" Ke taki zuciyar bata so na" ya karasa min, "kin nuna min haka, but you don't have to say it please" na sunkuyar da kaina nace "kayi hakuri, na dauka hakan shine dai dai" sosai nake jin babu dadi a raina. Amma sai naji yace "ba kya sona saboda shi ko? Saboda shi yana da mota ni bani da ita? saboda yafi ni abin duniya?" Na dago kai da mamaki ina kallon sa, ya gyada kai "yes, na san wanda yake zuwa gurinki da farar Benz, na dauka cewa akwai sauran true love a duniya, na dauka akwai sauran yammatan da zasu zabi talaka akan mai kudi, na dauka zanyi amfani da soyayyar da nake yi miki in ribato taki soyayyar, na dauka....."
Na daga masa hannu "ko kadan ba ina son Umar bane ba dan wani abun da yake dashi, ban taba karbar ko kwandala daga hannun sa ba, na dauk in nayi maka bayani zaka fahimta sannan kayi min uzuri" ya danyi murmushin takaici yace "na fahimta kuma nayi miki uzuri....."
Kamar daga sama aka daga labulen dakin Umar ya shigo, daga dukkan alamu yazo ne ya rasa dan aike kuma yaga kofar gurin a bude sai kawai ya shigo, hannun sa daya rike da key din motarsa dayan kuma rike da manyan ledoji biyu masu dauke da tambarin sahad stores. Ya tsaya yana raba ido a tsakani na da Musa, sai kuma ya ajiye ledar hannunsa akan kujerar kusada shi yace "ohh sorry guys, na dauka Tahir ne a ciki ko wani" ya kalle ni "I will wait outside" nayi saurin gyada masa kai duk da kururuwar da zuciyata take yi min a cikin kunnuwa na.
Yana fita Musa ya kalli ledojin daya ajiye sannan ya kalle ni yana karyayyen murmushi yace "kuma kika ce baki taba cin ko kwandalar sa ba, am sure aljanu yayi wa siyayya bake ba" na fara kokarin kare kaina "wallahi....." Sai kuma naga kamar rantsuwar bata da amfani sai nayi shiru, ya girgiza kai "save it" yace tare da kama hanyar fita, har sai daya kai bakin kofa sannan ya juyo yace "in kin chanja ra'ayin ki, gidan mu yana nan a bakin layin nan" sannan ya karasa fita.
A daidai lokacin ne kuma naji tashin motar Umar, da sauri na wuce Musa na fito a dai dai lokacin da Umar yaci tayar mota ya bar layin a guje, na tsaya ina bin motar da kallo, Musa ya karaso ya tsaya a kusa dani shima yana kallon motar sannan ya juyo ya kalle ni yace "yayi fushi, daga dukkan alama yana da kishi, amma kar ki damu in dai yana son ki da gaske zai dawo".
Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank
Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020
Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020
Please banda kira, WhatsApp only
*💔 Jidda 💔*
*By*
*Maman Maama*
*Episode eight : Bashir*
Bai dawo ba har bayan sati daya, shima kuma Musa bai dawo ba. A cikin satin nan gabakidaya hankali na a tashe yake kusan kullum sai nayi wa Farhan mita a daki "yayi fushi dani Farhan. Watakila ma ya dauka yaudarar sa nake yi Musa nake so, bai san a lokacin da ya gan mu da musan ma ina gaya masa bana son shi ba ne ba"
Ita kuma sai tayi dariya, ita abin wai dariya yake bata "lallai Jidda kinyi zurfi da yawa, wai ke din ce kike tada hankali akan namiji? Jiddan dana sani ce kuwa? Ni ina ganin wannan dama ce a gare mu da zamu gane in da da gaske yake son ki, dan ni a ganina dan wannan abin bai isa ace ya barki ba, sai dai in dama ba da gaske yake ba" tabbas gaskiya ta fada, sai dai in dama ba da gaske yake ba, amma anya kuwa? Rashin sa yana nufin rashin chance dina na karatu.
Kusan kullum sai na kira Mufida munyi ta hira duk da nasan basa tare amma na fahimci hakan yana kwantar min da hankali dan nasan lafiyar sa kalau, ko dai ya fasa ne ko kuma yayi fushi sosai.
Kullum kuma ina saka ran inji ko Mufida zata yi min maganar sa amma shiru. Ina ta tunanin ko ni inyi mata in gaya mata yazo kuma ga yadda muka yi dashi ko da kuwa ban nemi shi ta bangaren ta ba at least ban rufe ta da komai ba, kar daga baya taga kamar na munafunceta. Amma still na kasa yi mata maganar. Ranar nan kuma sai gata tayi min da kanta "yanzu mutumin ki ya kira ni wai dan Allah in tura masa hoton ki, nace nima bani da shi" ta karasa maganar tana dariya. Naji wani sanyin dadi a raina amma sai nace "wanne mutumin nawa kenan?"
Tace "kya ji da shi ma can, na sani ai kuna tare da yaya Doctor amma kina ta wanibasarwa ko?" Na dan yi murmushi "to kinga laifi nadan na basar da shi? Ji nake kanwarsace ta bani shawarar in rabu da shi" sai ta danyi shiru, na dauka zata chanja topic amma sai naji tace "Yaya Doctor ne yana da wuyar sha'ani Jidda, ke kuma ba experience kuke da shi akan samari ba shi yasa na baki shawarar rabuwa da shi dan banyi tunanin da gaske yake ba" nace "amma me yasa kika yi wancan tunanin? Mai yasa kike tunanin yaudara ta zaiyi?" Tace "shi yana daukan irin wannan relationships na yammata da samari ne kamar wasa, in yayi budurwa sai kun gama sakin jikin ku da ita sai ya tubure yace shi fa ba da gaske yake ba kawai friendship ne. Ni wannan abin na gudar miki."
"A yanzu haka Mama babu abinda take so irin taga yayi aure, ita da kanta take samo masa yammatan da take ganin maybe zai so amma sai yace shi basu yi masa ba. Kinga kafin ya tafi India akwai wata second cousin din mu da Mama ta hada su sukayi dating sosai har mun fitar da anko fa, kawai bawan Allahn nan sai yaje ya samu Baba wai Mama zata yi masa auren dole"
Ta karasa maganar tana dariya nima sai naji maganar ta bani dariya "wallahi yarinyar baki ga yadda kowa ya ringa tausaya mata ba yadda kika san zata mutu akan sa amma yace shi wallahi baya son ta, haka ya hada kayansa yayi tafiyar sa India, haka Mama tayi ta bawa iyayen yarinyar hakuri. To irin haka nayi gudun kar ya faru dake shi yasa nayi warning din ki a kansa, saboda yana da saurin shiga rai musamman ke da babu kowa a zuciyarki, bana so kiyi ending up like cousin din can ta mu" na gyada kaina ina fahimtar ta kuma ina jin dadin abinda tayi min sannan na bata labarin so far abinda ya gudana tsakani na dashi, har form din da ya kawo min da zuwan da yayi gurin Abba na.
"Yanzu still kina tunanin ba da gaske yake ba?" Tace "I can't say gaskiya. Ina tsoron in bada shaida a kansa kuma yazo ya bani kunya" ta karasa tana dariya, sai kuma tace "amma dai abinda zan iya cewa shine ban taba ganin yayi going this far ba, ban taba ganin yayi getting involved with iyayen yarinya ba. I think ya kamata in bawa Mama wannan labarin...." Nayi saurin katse ta "na shiga uku rufa min asiri. Ki bar maganar a tsakanin mu please, in yana so Mama ta sani da kansa zai gaya mata" a haka muka kare maganar. Sai dai ni bata kare a zuciyata ba haka nayi ta bitar maganganun Mufida a raina. A karshe sai na yanke shawarar in Umar ya gama fushinsa ya dawo to zansan yadda nayi na tambayeshi game da relationships din da yayi a baya dan inji nasa side of the story din.
Ranar nan muna cikin waya da Mufida Farhan ta shigo, sai take min sign da in karbi number din Umar a gurin Mufida ni kuma sai na harare ta kawai, da ta sake