JIDDA Kallo Daya, Zuciya Daya By Maman Maama

Author :  Maman Maama Category :  Romance

Chapter   62 / 106

183K to 186K   out of 316K words

aiko wa da auncle Muhammad return tickets din mu sannan hankalina ya tashi, ba wai Nigeria din ce bana son komawa ba gidan Umar ne bana son komawa.

Amma haka suka tattaro mu, tare da goma ta arziki suka sako mu a jirgi muka dawo. Umar ne yaje dauko mu a airport, dashi da yaya Tahir da Amira. Har da sabon dinki naga yayi da sabuwar hula. Su Yasmin suka tafi gurinsa da gudu suna murna, ya rungume su daya bayan daya briefly sannan ya wuce su ya taho inda nake tahowa ya karbe jakar hannuna ya ajiye a gefe sannan ya rungume ni, without minding su Yaya Tahir da kuma tarin mutanen da suke gurin. Ya sauke ajjiyar zuciya "God! I missed you" ban ce komai ba har ya sake ni sai na wuce shi na tafi gurin su Amira ina murnar ganin su.

Gidan mu muka tafi, Umma tana can tayi shirin taryar mu bakinta har kunne, ranar wuni mukayi ina ta bata labarurrukan garin su da bata taba zuwa ba ina kuma nuna mata hotunan dana dauka tare da cousins dinta da yayansu, most of which bata sani bama. Naje na gaishe da Abba ya amsa min yana ta cin magani, na kuma fahimci a dalilin tafiyar da nayi ne dan tun kafin inyi ta ya nuna baya so, ina saukowa Umma tace in je in gaishe da Hajiya sai na fita na danyi shawagi na dawo nace naje, dama Farhan bata gidan wai taje gidan yaya Hudallah.

Tun da na shiga gidan ban kuma bi ta kan Umar ba, ban sani ba ko ya tafi ko yana nan oho, na dai ji Umma tana aiken a kai masa abinci da lemo, har akayi magrib akayi isha sai ga Abba ya shigo daga masallaci "Hauwa? Jidda kina ina?" Na mike daga kan sallayar da nayi sallah ina dafe kaina, nasan tawa ta same ni, "Jidda ta zama kurma ne ko kuma bebiya ta koma?" Na daga labule "gani Abba, ina sal......"

Bai tsaya jin karshen maganar ba ya fara fada "iskancin banza iskancin wofi, dan Allah ya hada ki da miji mai hakuri sai ki mayar da shi sakarai? Jidda anya kina son ki shiga aljanna kuwa? Mutumin da aljannar ki take karkashin kafarsa shine kike wulakanta wa? Kin bar yaron nan yana ta zarya yaje ya dawo yaje ya dawo amma ba zaki fito ku tafi ba? Na rasa munafurcin me kuke yi ke da uwar taki a daki, dama ni wannan tafiyar taki ban so taba dan daga haka zaki fara kokarin fin karfin mutane"

Yayi tayi babu comma babu fullstop, sai ga Hajiya ta fito daga dakin ta "sai hakuri Alhaji, yaran zamani sam basu san darajar aure ba musamman in sun samu miji mai sakar musu, kuma suna ganin sun yi karatu sai su ga kamar sunfi karfin suyi biyayya ga miji ballantana iyaye"

Sai ya kama benen sa ya fara hawa yana cigaba da fadan sa, ita kuma tana daga kasa tana taya shi, na juya ina kallon ta, ban san sanda zuciya ta debe ni ba nayi kanta kamar zan rufe ta da duka, Umma tayi sauri ta rike ni tana salati "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Jidda lafiyar ki? Me kike yi haka?" Hajiyan ta shige daki da sauri ta rufe kofa. Sai kawai na kife kaina a jikin Umma na fara kuka. Ta janye ni daga jikinta "ki fita maza ku tafi kar Baban ki ya jiyo ki, maza dauko mayafin ki ku tafi" na sake ta na shige daki na yayo mayafi na na dora akai ba tare dana lura ko dai dai na saka ko akasin haka ba, Amira ta dauko Asad da yake bacci ta jawo hannun Yasmin suka biyo ni a baya.

Yana mota ya dan kwantar da kujerar ya kwanta ya dora hularsa akan fuskar sa. Na bude gaba ya saka yara a ciki sannan na bude baya na shiga. Ina jin Amira tana yi min sallama amma ko ta kanta ban bi ba. Ya bude fuskar sa sannan ya juyo yana kallona "kun fito ashe, nazo kuma sai nayi tunanin baku gama ba sai na zauna a mota, don't want to rush you" naji wani haushin sa ya kara cika min ciki, always pretending to be the perfect husband.

Ya tayar da motar, I was half expecting him yace min in dawo gaba amma bai fada ba sai ya ja muka bar layin, muna hawa titi nace "gidan yaya Tahir zaka kaini" ya juyo da sauri "what? Common Jidda" na dauke kaina gefe tare da sake maimaita wa "gidan Yaya Tahir zaka kaini, ko kuma ka ajiye ni anan in hau adaidaita in tafi, your choice"

Ya sauka daga kan titin ya juyo sosai "Jidda please, ba mun gama maganar nan bane ba wai" na daga idona na saka a cikin nasa, "ka gama dai, amma ni ban gama ba dan ko farawa ban yi ba, ranar da zan gama ita ce ranar da zaka bani takarda ta"

Muka zauna muna kallon juna sai ya cire idonsa daga cikin nawa ya dafe kai da hannu daya sannan yace "okay. Gidan Tahir kike son zuwa? Let's go to gidan Tahir"

Can muka tafi, luckily muka same shi a gida tare da amaryar sa da take ta faman laulayin ciki. Tayi ta mitar wai ban gaya mata zamu zo ba bata tanadar mana komai ba. Na danyi mata murmushi kawai. Ina zama naga Yaya Tahir ya dauki waya sai kuma ya fita waje, ya jima a wajen sai gashi ya dawo tare da Umar sai yace matar ta dauki yara na su shiga ciki, sannan shi kuma ya fara magana

"Jidda Doctor Umar yace min kun su matsala, yace yayi miki laifi a bisa rashin sani kuma ya baki hakuri amma kin ki hakura. Haka ne?"

Na dago kai nace "ya gaya maka abinda yayi?" Ya girgiza kai "bai gaya min ba, amma yace bada sanin sa ne yayi laifin ba. Haka ne?" Na daga kai ina kallon Umar nace "ban sani ba Yaya, ban tabbatar ko yana sane yayi ba ko kuma baya sane, abinda na sani shine ba wannan ne karo na farko daya aikata the same abu ba, ba na daya bane ba ba kuma na biyu bane ba, kuma daga dukkan alama bana jin zai zama na karshe"

Ya juya yana kallon Umar sai Umar yace "haka ne. Na kuma dauki responsibility na dukkan laifina, da wadanda nayi ina sane, da wannan da nayi cikin rashin sani, duk na dauka naji na amince cewa nayi ba dai dai ba. Sannan kuma na bata hakuri. Nace dan Allah, dan Annabi tayi hakuri, sannan kuma nayi alkawari ga ubangiji, gare ta sannan kuma yanzu a gurin ka a matsayin shaida cewa wannan shine na karshe. Dama kawai nake so ka rokar min ita ta sake bani ta karshe. Idan har abu makamancin wannan ya sake faruwa nayi alkawarin duk hukuncin data yanke zan karba ko da kuwa wanne iri ne, kuma...."

Nace "yaya wannan alkawarin nasa ba na daya bane ba ba kuma na biyu bane ba, in yayi ma karyawa yake yi kuma bana jin wannan karon ma zai cika shi, dan Allah yaya ka shiga maganar nan....." Yace "na shiga ai Jidda, ba gani ba ina cikin maganar? Kuma yanzu alkawarin da yayi yayi shi ne a gaba na dan haka na zama shaida, idan ya karya all you have to do is tell me ni kuma zan dauko maganar mu sake bude ta mu gani, zan tuna masa da alkawarin da yayi na cewa zaki yanke masa dukkan hukuncin da kika ga dama and I will make sure he keeps his promise" ya karasa yana kallon Umar da alamar warning a muryarsa, sannan ya kuma juyo wa kaina yace "amma for now, kin ga na farko Doctor ba sa'an ki bane ba gaba yake da ni kaina ba ke ba, na biyu kuma mijin ki ne, mijin da Annabi yace da za'a iya saka wata halitta tayi wa wata halitta sujjada da ance mata tayi wa mijinta sujjada karewar biyayya kenan, amma kuma duk da wannan daukaka da yake da ita sai ya baki hakuri yace dan Allah dan Annabi kiyi hakuri, to me yasa ke kuma ba zaki hakura ba? Me yasa ba zaki sake bashi dama ba kamar yadda ya nema?"

"Nima kuma ina baki hakuri on his behalf, kiyi hakuri, amma kuma ki saka a ranki cewa wannan shine na karshe, ni kuma in kika yi min biyayya zan tabbatar miki da hakan"

Na share hawaye na da bayan hannuna sannan na ja hanci nace "shikenan yaya, na hakura, amma wallahi wallahi ya sani, idan maganar nan ta sake maimaita kanta wallahi na gama aurensa" na fada ina kallon Umar cikin ido.

A hanya babu wanda yace komai a tsakanin mu har muka je gida, yana yin packing na fito na dauki Asad na shigar da shi ciki na kwantar dashi a daki, ina fitowa shi kuma yana siga da Yasmin, yayi min murmushi na dauke kaina na wuce shi na koma waje na fito da kayan mu wadanda tun daga airport suke cikin booth, sai ga shi ya dawo ya dauki jaka daya ya miko min hannu zai karbi dayar "ki barsu zan shiga dasu" na wuce ban bashi ba kuma ban ce komai ba.

Ina shiga kayana na cire kawai na shiga wanka, ina fitowa na fara shirin bacci sai gashi nan ya shigo da kayan bacci a jikinsa shima ya tsaya yana kallona "ki taho dakina" ya fara yana kallona ta mirror, ban ce masa komai ba har na karasa shiryawa ta a gabansa na saka kayan bacci na sannan nazo na wuce shi na shiga dakin nasa na gau gado na kwanta tare da lulluba, ya shigo shima ya sake tsayawa a bakin kofa, sai na yaye bargon irin yadda yake yi nace "kazo kayi abinda zakayi and then leave me alone"

Sai naga yayi murmushi, sannan kuma sai yayi dariya yana girgiza kai, "Jidda kenan. You think wannan ne dalilin da yasa na ce ba zan rabu da ke ba?" Na dauke kai sai ya zauna a bakin gadon yace "nace ba zan sake ki bane ba saboda ke matata ce uwar yayana kuma ina son ki, and I am not going to give up my family for a mistake din da ban san ma nayi shi ba, yes, abinda kike magana akai shima ina son sa, but I am not going to do it har sai lokacin da ke da kanki kika ce min kina so" na bude ido ina kallon sa "lallai kuwa zaka shirya jira har zuwa ranar da jaki zai fitar da kaho" yayi dariya sannan ya kashe fitila ya hawo gadon "it is going to be sooner than you think"

Ina jin sa ya shigo cikin bargon sannan ya matso jikina, na janye jikina daga gare shi na sauka na dauko wani abin rufar, sai na tattara bargon na saka a tsakiyar mu sannan na lulluba da wancan abin. Sai naji yayi chuckling sannan yace "goodnight".

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only



*wannan littafin na siyarwa ne bisa amana, idan baki siya ba kar ki karanta, idan kuma kin siya kar kiyi sharing, in kika yi kinci amana kuma ke da Allah*

*Asabe*

Kwanaki suka wuce bayan dawowa ta gidan Umar, na cigaba da harkoki na na cigaba da kula da gida na da kuma ƴaƴana, shima Umar din kuma ba wai share shi nake yi ba kawai dai baya gaba na. Zan dafa masa abinci zan gyara masa dakin sa zan kuma bashi dukkan kulawa, un kuma yayi min magana zan amsa masa in ya saka ni abu zanyi, amma murmushi na bai kuma ganinsa ba a cikin kwanakin nan, duk kuwa labarin da zai zauna yayi ta bani sai dai kawai in zauna in jishi but I found his jokes not funny at all, sannan a gado ma bana kin zuwa dakin sa, kullum can nake kwana amma zan tabbatar na saka barrier a tsakanin mu kuma zan juya masa baya, watarana ma kaina nake mayarwa kusa da kafafuwansa inyi kwanciya ta. Sai dai na kan farka mostly cikin dare in ganni rashe rashe a jikinsa, in yaga na farka yakan yi korafin wai ni na taso na dawo jikinsa, duk da ni na tabbatar shine yake cire barrier din dana je sakawa ya dawo jikina.  But bana kula shi, nasan neman magana yake yi, in na ga haka sai in tashi in gyara inyi kamar ban san me yake yi ba.

A cikin wadannan kwanakin sai na fahimci wani abu, Umar ya chanja, baya bukatar in tuna masa lokacin sallah dan har wani application naga ya saka a wayar sa wanda yake alerting dinsa duk lokacin da lokacin sallah ya shigo, kuma yana kadawa yake  ajiye duk abinda yake yi yayi alwala ya fita jam'i, sai na fara saka ran cewa a office ma haka yake yi.

Sai kuma ya dawo da karatun da yake cewa muyi kafin tafiyar mu Ethiopia, in ya dawo daga masallaci sai muyi karatu tare kafin gari ya karasa wayewa, a wannan karatun na fahimci yasan Alqur'ani, duk da yakan yi mistakes in gyara masa ko kuma wani lokacin inyi mistake ya gyara min. Wannan karatun shi ya kara bringing us closer together, I felt at peace a duk lokacin da muke yi dan haka duk wani zafi dana dauko da wasu maganganu da na gama shiryawa cewa zan yaba masa sai inji sun narke tare da zuciyata. I started thinking maybe this is it. I kept reminding myself cewa case din Mammy asiri aka yi masa dan nice babbar shaidar hakan, maybe da a cikin hayyacin sa yake da ba zaiyi ba, maybe abin yafaru ne dan ya zamanto sanadiyyar shiryuwar Umar, maybe da gaske yayi deserving another chance from me, a last chance.

Wannan plus kyautatawar sa gare ni  ya cigaba da sauko da zuciyata, na cigaba da rangwanta masa har ya kai muna zama muyi hira dariya kamar yadda muke yi a da, gado ne dai lamarin ya gagara, duk kuwa da cewa yana fadi yana kuma kara fadi a messages din da har lokacin yake turo min kusan kullum cewa shi bai ma tabbatar yayi ba, kuma ko yayi din shi ba zai iya tunawa da lokacin da yayi ba, but to me na kasa cire abin a raina, na kasa daina picturing dinsa a gado tare da yar yayata. A duk lokacin da nayi irin wannan tunanin na kan ji raina ya baci sosai, na kan ji bazan iya kuma muamalar aure da Umar ba, amma da zarar yazo da kalaman sa da kyautatawar sa sai inji maybe zan iya, with time.

Tun Umar yana hakuri yana nuna kamar bai damu da rashin bashi kulawa a shimfida da nake yi ba har hakurin sa ya gaza, ya fara zama frustrated kamar yadda yakan zama a duk lokacin da muka samu sabani irin wannan har nayi masa fushi irin wannan. Ya zama very edgy, shi kadai ma fada yake yi ko da ba'a taba shi ba, yayi wa yara fada yayi min fada yayi wa maigadi fada, ranar nan ma remote din TV yayi jifa dashi wai yaki dannuwa. In yana haka sai dai kawai in kalle shi in tabe baki amma bana kula shi dan nasan abinda yake damunsa kuma ban damu ba tunda na bashi shi yace ya hakura har sai ranar da naji ina nema da kaina, ni kuwa banga wannan ranar ba, dan ni in dai wannan abin ne zan iya rayuwa ta babu shi.

Sai kuma ya tsiri ciwo, daga yau yace ciwon ciki yake yi sai gobe yace ciwon kai jibi kuma zazzabi. Ni kuma sai in mika masa paracetamol da ruwa duk da sarai na san me yake so. A haka watarana ya dawo daga office da rana wai baya jin dadi wai zazzaɓi yake yi. Nayi masa fatan Allah ya sawake sannan bayan ya shiga daki na bishi da paracetamol da ruwa, na tarar da shi ya cire kaya ya ware ac ya kuma tsayar da fanka a kansa sannan ya dunkule guri daya. Na tsaya ina kallon sa, sai na tuno da washegarin ranar da aka kawo ni gidan dana fito daga daki na same shi in exact situation like this.

Na tsaya a gefe kansa "ka tashi ka sha magani" ya juyo ya kalle ni da jajayen idanuwa "go away" na tsaya ban tafi ba "ka tashi kasha magani in dai da gaske kake baka da lafiyar" ya sake juyowa yana kallona "in kuma ba da gaske nake ba fa?" Na bata rai "sai inyi tafiya ta in cigaba da aiki na, girki nake yi dama na dakatar dan in baka magani in kuma baka bukata ba shikenan ba".

Ya miko min hannun sa daya "bani maganin" na mika masa sai ya damki hannun nawa ya jawo ni na fado kansa, Allah yaso robar ruwan a rufe take da sai yayi mana wanka da ruwan. Na fara kokarin mikewa sai ya zagaye hannuna a waist dina ya matse ni a jikinsa "gotcha" na bata rai "ka sake ni Umar" yace "in naki fa?" Nace "sai in bar ka da Allah" yayi dariya "dama haka Allah yace mata ta ringa azabtar da mijin ta? Uhmm?" Na juya ido "azabar me nayi maka? Dukan ka nayi ko kuma wuta na dauko na saka maka a riga?"

Ya fara kokarin juya ni ya mayar dani kasa "kin san abinda kike yi ai, kin san abinda nake so ai, ban san me kike so inyi ba, ban san ya kike so inyi da raina ba, kin san maganin ciwo na amma kin hana ni" nace "I thought zazzabi kace kana yi, ga magani kuma na kawo maka

62 / 106