Author : Maman Maama Category : Romance
ta dawo min a raina.
"Ka samo min mai da kwari haka. Young"
"Saura in kawo maka wata ita kuma kace.............."
Na kawar da maganar daga raina tun kafin in kwada masa mari maimakon in tashe shi daga bacci.
Na dan daki pillow din da yake kai kadan, ya motsa hannun sa amma bai tashi ba sai nayi knocking a cikin bed frame, louder than I intended to. Yayi juyi sannan yayi blinking "ka tashi kayi sallah"
Ya bude ido yana kallona nima na tsaya ina kallon sa, zuciyata tana gaya min in damki wuyan sa in shake shi har sai ya daina numfashi.
"Ka tashi kayi sallah" na sake fada, knowing in dai na juya na tafi ba tare da ya watstsake ba to zan dawo in tarar da shi ya koma.
Sai naga yayi murmushi still idonsa a kaina, na juya ina sake maimaitawa "ka tashi kayi sallah"
Kafin in yi taku biyu naji ya jawo ni na fado kansa, sannan yayi juyi ya mayar da ni kasan sa yana dariya "got ya!" Na rufe idona saboda wani daci da takaici da naji a zuciyata, ya kawo bakinsa dai dai kunnena "menene ma naji kina fada jiya da dare? That you missed me right? You have no idea how much I missed you too"
Na bude ido na ina kallon fuskarsa a saman tawa, yayi min murmushi tare da daga min gira, nace "really? A ina kayi missing din nawa? Ni kuwa ni na tabbatar kayi missing dina tunda na gani ganin idona" ya bude ido "my God! Fushi kike yi wai? Am so sorry kinji Baby?" Ya fada yana kama kunnuwan sa, "bacci, gajiya, ban san ma sanda nayi baccin ba kamar a mafarki naji kina yi min magana, maimakon in farka kuma sai na cigaba da mafarkin"
Na sake rufe idona tare da juya kaina gefe ina addu'ar neman Allah ya kara min kwarin gwiwa kar in wanka masa mari, shi bai san ma me nake yi ba sai yace "let me show you abinda ya faru a mafarkin" ya fada yana kokarin daidaita fuskarsa akan tawa, na tattaro duk karfin da yake gare ni na ture shi, kasancewar bai shirya hakan ba sai gashi ya fadi kasa a gefen gado "ouch" ya fada yana rike kugun sa, na mike tsaye ina gyara hijab din jikina.
Ya bini da kallo "what was that for?" Nace "ka tashi kayi sallah" sai na fita na barshi.
A dakina na sake komawa sallaya ta, ina jinsa ya shigo ya kunna fitila sai kuma ya kashe ya fita, sai na jishi kuma ya fita masallaci. Yana fita na tashi nayi locking kofa ta dan nasan yadda ya fara abin nan yana dawowa daga masallaci nan zai taho. Ai kuwa yana dawowar nan yazo ya murda kofa ya jita a rufe ya dan yi knocking sau daya ban kula ba sai naji ya shiga nasa dakin. Na mayar da idona na rufe sannan na jingina kaina a jikin gado ina jera addu'ar neman karfin zuciya.
Sai da gari ya fara wayewa sannan na tashi na fita na shiga kitchen na soya plantain da kwai na dafa tea na kawo na ajiye akan dining table sannan na koma dakina na kwanta na lulluba kamar mai bacci. Zuwa can na jishi ya fito, ya sake shigowa dakina ya jima yana kallona sannan ya fita.
An jima kadan ya sake dawowa, kamshin turaren ya sa na fahimci har yayi shirin fita. Ya durkusa a gaba na sannan ya bude lullubar da nayi "wai fushin ne kike yi har yanzu?" Na bude ido ina kallon sa sai naga fuskarsa ta chanja yanayi ta nuna alamar damuwa "subhanallah. Jidda kuka kikayi haka?"
Na mayar da ido na na rufe ina jin ciwon yadda yake nunawa kamar ya damu da damuwata, ina ma dai zai fito da fuskarsa ta gaskiya ya wulakanta ni a gaban idona kamar yadda yake wulakanta ni a bayan idona? I mean akwai wulakancin da yafi wanda yake min a duk sanda ya kwanta da wata mace bayan ni?
Na dan bude bakina kadan nace masa "ba kuka nayi ba, kaina ne yake min ciwo" sai ya saka hannu ya dafa goshina "ga jikin ki ma yayi zafi wallahi. Tun yaushe?" Nace "jiya da dare"
Ya danyi shiru "ba dan zanyi reporting taron da naje ba da sai in zauna in kula da ke, ga rashin lafiya ga yara kuma. Ko in ce Mama ta turo Mufida ta zauna miki kafin in dawo?" Na girgiza masa kai ina jin haushinsa yana kara lullube ni. Yace "ki ci abinci kisa magani, ba zan jima ba zan dawo reporting kawai zanyi kinji? In nazo sai inga yadda za'a yi da ciwon nan" ya fada yana murmushi "maybe ma ciwon nawa ne" ya karasa da dariya a muryarsa.
Sai kuma naji ya hau kan gadon yayi kissing yayansa "wadannan sun sha fitina jiya duk sun kasa tashi" ban kula shi ba ya sauko ya fita, bai jima ba sai ya kuma dawowa "baki da lafiya amma har kika iya yi min abinci Jidda?" Na bude ido kawai ina kallon sa bance komai ba sai ya dawo ya sunkuyo yayi kissing dina "I love you. Allah yayi miki albarka" sannan ya tashi ya fita.
Na mayar da ido nana rufe ina jin hawaye suna fitowadaga cikin su. Ina ma inama, ina ma yadda Umar yake nuna wa a zahiri haka badini dinsa take, da nafi kiwa dace da miji a duniya amma kash......
Bai jima da tafiya ba yaran na sa suka tashi, daga nan nima a dole na tashi nayi musu wanka sannan muka fita na basu abinci na fara kuma aikin gyaran gida suna ta bata min da niyyar taya ni suke yi. Ina ta lissafin dawowar Umar dan nasan gab yake da dawowa da zarar sako na ya je gare shi.
A cikin biyu daya zai faru, is either Bashir ya gaya masa abinda ya faru ko kuma shi ya bude messenger dinsa ya gani, wannan shine dalilin da yasa na barshi ban goge ba dan sakon ba na Bashir bane ba, it is more to him, shi Bashir kawai sanarwa ce dan yasan na sani ya daina raina min hankali.
Har na gama aikina sannan na samu guri na zauna, yayana at both sides of me ina jiran shigowar sa.
A zaman da nayi a gurin sai na samu kaina da tunanin karuwan Umar. Ni bani da wani problem whatsoever da su saboda bani da hadi da su, Umar shi nake da problem da shi tunda shine mijina, infact ni tausayin su ma nake ji na yadda suka mayar da rayuwar su suka wulakanta kansu. Na tuno Zuwaira da confidence dinta sanda ta shigo gidan nan da yadda take gaya min cews Umar nata ne ita kadai, a karshe yayi mata dukan kawo wuka kuma ya rabu da ita.
Na tuna wannan ƙaruwar da suke kira da Zahra, na tuna maganar da Umar yayi a kanta "duk balloons din kirjin sun sace" and they laughed, amfanin ta ya kare a wajen sa, and yayi watsi da ita like the trash da ta mayar da kanta.
Dukkan su biyun nan da ma wadanda ban sani ba kuma bana fatan sani, babu wani string da yake attached tsakanin su da Umar, baya son su ko kadan amfanin su a gurinsa kawai a kan gado ne su biya masa bukatar sa in ya gaji da su ko kuma ya samu wadda ta fi su yayi watsi da su kamar shara, har da tukuicin cin mutunci.
To wacce irin rayuwa ce wannan suka jefa kansu a ciki? Saboda dan abin duniyar da zai basu wanda ba tabbatar va zai amfane su ba a duniya da kuma a lahira tunda babu albarka a cikin sa.
Ina ma dai zan iya yi musu magana da su da masu hali irin nasu dana tuna musu da cewa mazan nan fa da suke bata rayuwar su saboda su babu wani abu mai kama da soyayya a tsakanin su, in fact, kamar ma basu dauke su a matsayin mutane ba in nayi la'akari da maganar da Bashir yayi akan ita Zahra
"She was once your favorite pet"
"Pet" for goodness sake a matsayin abinda suka dauke su kenan "pet" "dabba"
Sannan kuma yace "ya kayan da na aiko maka da su?"
"Kaya"?
I hope za su ga irin wadannan messages din maybe da sun fahimci matsayin su a gurin maza irin Umar da Bashir.
Ina zaune naji tsayuwar motar sa, Yasmin ta mike da sauri tayi hanyar bakin kofa tana murnar zuwansa kamar yadda take yi kullum.
"Daddy! Daddy"
Sai ya bude kofa ya shigo kamar wanda aka jeho shi daga sama. Idanuwan sa a waje kirjinsa yana dagawa da sauka da sauri, kofofin hancinsa suna budewa da rufewa da sauri.
Na mike tsaye muna kallon juna, tabbas sako na ya isa gare shi.
"Jidda!"
Ya kira sunana without noticing Yasmin da ta makalkale kafarsa, yayinda Asad shima ya rarrafa inda yake da sauri yana murna. Soo innocent.
Na zauna tare da nuna masa kujerar da take kallon waddanake zaune a akai.
"Bismillah. Ka zauna muyi magana"
Ya saka hannu ya dauki Asad, sannan ya kamo hannun Yasmin suka karaso inda nake, sannan ya nuna wa Yasmin hanyar daki "go and play mamana" sai ta tafi da gudu, ya sauke Asad shima sai yabi bayan Yasmin din. Maimakon ya zauna kamar yadda nace din sai yayi kneeling a gaba na tare da fara kokarin kamo hannu na, na janye hannaye na gefe sannan nace "ka ga sakona kenan?"
Yayi shiru bai ce komai ba, fuskarsa kamar duk sanda na kama shi da laifi irin wannan, cike da tashin hankali. "Jiddah ki tsaya inyi miki bayani" na girgiza kaina ina kara rike hawaye na. "Bana bukata. Bayani in dai daga bakin ka zai fito kuma akan wannan maganar bana bukatar jin sa. Na tsane ka Umar, bana son ganin ka tsantsanin ka nake ji"
Ya dafe kansa "innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Jidda ina sonki kin sani, ina sonki Jidda fiye da rayuwata" na tura shi baya da hannuwa na biyu "so? So kake yi min magana akai Umar? Soyayya indai irin taka ce Allah wadaran ta Umar, ko makiya na ban musu fatan samun soyayya irin ta ka wadda babu komai a cikin ta sai tarin dacin rai da kuna zuciya"
"Wallahi Umar ba dan daga jikinka Yasmin da Asad suka fito ba da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Da jiya babu abinda zai hana inyi screenshot na maganganun batsar ku da Bashir inyi posting a facebook tare da tagging dinku da duk wadanda suka san ku"
"Amma kasancewa ta uwa ba zai barni inyi hakan, dab bata sunan ka yana nufin bata sunan yayana, wanda a yanzu su kadai ne link din da nake dashi da kai. Wannan kuma shi yasa nake zaune a gidan nan a yanzu, dan su ba dan kai ba. Amma ina so ka sani cewa zaman da zanyi saboda su shima yana da iyaka, akwai lokacin da zan dauke su mu bar maka gidan ka, ka rubuta ka ajiye ranar tana nan zuwa in dai har baka dawo kan hanya ba"
"Na baka chance na farko saboda kowa a duniya yana bukatar second chance, Na baka third chance saboda ina sonka a lokacin, wannan soyayya ta saka naji ina saka ran zaka shiryu muyi rayuwa har mu tashi a lahira mu cigaba da rayuwa a matsayin mata da miji a aljanna"
"Yanzu kuma zan jera maka wasu sharadai guda uku, idan ka bisu shine zan sake baka wani chance din, idan kuma kaki kamar yadda na fada maka zan dauke yayana dan bazan bari su tashi a cikin kazantar rayuwa irin ta ka ba"
Da sauri ya gyada kai "say it. Ki fadi ko menene kike so inyi wallahi zanyi" ban kula da marairaice war da yayi da kalar tausayin da yayi ba na cigaba
"Na farko zaka rabu da Bashir, da duk wani abokin da kuke irin wannan harkar da shi, zaka yanke duk wata mu'amala da take tsakanin ku"
Ya gyada kai "na yarda"
Na cigaba "na biyu zaka daina social media. Duk wani social media account dinka zaka rufe shi ba zaka kara budewa ba har sai ni da kai mun tabbatar da cewa ka bude wani sabon shafi a rayuwar ka, shafi mai kyau"
Ya sake cewa ya amince
Nace "na uku. Zaka kara aure"
Ya bude ido sannan ya girgiza kai da sauri fuskarsa cike da mamaki "aure? Aure fa kika ce Jidda. Ki rufa min asiri kiyi hakuri amma ba zan iya kara aure ba wallahi" nace "lallai kuwa zaka shirya rayuwa kai kadai a gidan nan dan ni kam ba zan iya cigaba da zama da kai a haka ba haka zalika yayana ba zasu zauna da mazinaci a matsayin uban su ba"
Yace "naji zan rabu da Bashir, naji zan daina social media amma Jidda ba zan iya aure ba Jidda ba zan iya yi miki kishiya ba kin sani" nace "kishiya? Kishiya fa kake magana? Kishiyoyi nawa ka riga kayi min already a waje wadanda ban san da zaman su ba? Bana jin ko mata uku zaka aura a rana daya zanji zafin da nake ji yanzu a zuciyata, idan kayi auren duk randa baka tare da ni at least nasan dawa kake tare na kuma san cewa ita din da kai kadai take tare ba sharing kuke yi kai da abokan ka ba"
Yace "to saboda me zanyi auren ne wai? Na fahimci argument dinki akan abokai da media amma ban fahimci dalilin kara aure ba, I have got you Jidda, you are all I want and I need, bana bukatar wata mace kuma..."
Nace "I am not good enough for you Umar, tunda har zaka tsallake ni duk da rokon da nayi maka akan ka tafi dani amma kaki ka dauki karuwa ka tafi da ita then na tabbatar da abinda na jima ina doubting, cewa nayi maka kadan"
Ya saka hannunsa a cikin gashinsa, fuskarsa tayi jawur yace "wallahi Jidda kin ishe ni, duniya da lahira kin ishe ni, you are more than enough for me matsalar ba daga gare ki bane ba daga gare ni ne, I am so stupid and so greedy and so selfish and so ......"
Na mike "yes, duk wadannan sunayen ka ne kuma bayan su din akwai wadansu da yawa wadanda suka fi wadannan muni ma, nauyin igiyar auren ka da take wuyana ce kawai ta saka ba zan zauna in kira ka da sunayen daya bayan daya ba, amma ka sani ni na gama magana, ko dai kayi abubuwan nan guda uku dana lissafa maka ko kuma ka neme mu ni da yara ka rasa, in zamu tafi kuma zamu biya gurin Mama da Baba a hanya mu rattaba musu bayanin dukkan halayyar ka sannan mu kara gaba. Zabi ya rage naka"
Na wuce daki da sauri, ya biyo ni yana kiran sunana amma ban amsa ba kuma ban waiga ba har na shiga dakina sannan na turo kofa, sai kuma na jingina a jikin kofar ina barin hawayen da nake rikewa suna karasa fitowa, na jishi ya zo bakin kofar yana kiran sunana amma bankula shi ba kuma ko da nayi niyyar kulashin ma banajin muryata zata fito saboda sheshshekar kukan da nake yi
"Jidda dan Allah kar ki rufe kanki a daki, kin san baki da lafiya in ciwon ki ya tashi ya zanyi?"
Sai na zame na kwanta a bakin kofar na cigaba da kuka na har ya gaji da magiyar sa ya tafi.
Na jima anan sai kuma na tuna da yayana, na tuna cewa zasu iya jin yunwa kuma ban dora abinci ba sai na mike na shiga toilet na wanke fuskata tare da noticing yadda idona ya kumbura, na fita na tarar da su a falo Yasmin tana wasa da wayar Umar Asad kuma yayi bacci akan kujera, Umar kuma bansan inda yake ba.
Sai na shiga kitchen na dora ruwa akan wuta duk da bansan me zan dafa ba sannan na dauko tumatur da albasa na fara yayyanka wa, ban jima ba na yanke hannuna, na cigaba sai na sake yankewa again wannan karon deep dan gar jini yana fita sosai. Na tafi sink ina wanke hannun sai ga Yasmin ta shigo tana kallona tace "Mommy yunwa. Zan sha tea"
Na dauke ta na dora ta a sama nace "sorry mama, bara in hada miki kinji?" Sai na dauko cup na sauko da kayan tea na fara hada mata, har na gama na mika mata ta karba tana kallona sannan naji tace "mommy kin sa yaji a tea"
Na karbi cup din daga hannunta cikin mamaki sai kawai naga ashe yaji na zuba mata instead of milo, madara na zuba mata da sugar da yaji, ba dan Allah ya saka mai yawo bace ba da Allah kadai yasan abinda zai faru da ita. Nayi sauri na zubar da tea din da sauri sannan na dauke ta na rungume a kirjina ina jin hawaye na suna dawowa. Ta dago kai tana kallona "mommy kuka?" Na girgiza kaina "idona ne yake ciwo Yasmin" sai ta goge min hawayen tace "ki daina kuka kisha magani" na ajiye ta nace "to Yasmin"
Sai ta kuma cewa "mommy tea" na dauko wani cup din na sake hada mata, making sure wannan karon ban zuba yajin ba sai na mika mata ta zauna a kasa tana sha.
A lokacin ya shigo, kallo daya zaka yi masa ka fara tunanin tambayarsa ya jiki? Dan zaka dauka daga asibiti aka sallamo shi.
"Jidda ina so muyi magana please"
Na juya bayana ina mayar da kayan tea din dana sauko da su nace "babu maganar da zamu yi tunda har baka shirya barin abarka a cikin wandonka ba" ya juya ya kalli Yasmin da take bin mu da kallo sannan ya tashe ta zaune yace "mamana je ki falo ki sha tea acan kinji?" Ta kalle ni sannan ta juya ta fita.
"Jidda dan Allah mu daina irin wannan maganar a gaban Yasmin, kin san dai yawo ne da ita ko"
Na juyo ina kallon sa da mamaki a fuskata nace "wai kana