JIDDA Kallo Daya, Zuciya Daya By Maman Maama

Author :  Maman Maama Category :  Romance

Chapter   85 / 106

252K to 255K   out of 316K words

shikenan. And then it goes on kowanne kana ganin cewa shine na ƙarshe amma wanne ne zai zama na karshen? A kowanne second ubangiji yana iya daukan ranka shin ka taba tunanin abinda zaka tarar acan? Ba abu mai kyau bane ba Umar, ni da kai mun sani. You are a good man I know, a good husband and a good father but you are not a good muslim. Which is abinda ya kamata ya fara zuwa a farko kafin sauran characteristics su biyo baya. Ko nayi maka maganar addini you will pretend to me cewa ka gyara bayan in reality ba ka gyara din ba, bayan ni da kai munsan cewa ba ni zaka gyarawa ba kan ka zaga gyarawa saboda kabarin ka daban nawa daban, littafin ka daban nawa badan. Ni yanzu nawa littafin nake kokarin gyarawa shi yasa na bar gidan ka, saboda zama a gidan ka zai gurbata min dan abinda nake tanadar wa kaina saboda ranar gobe kiyama"

Yace "duk naji kuma duk na yarda da dukkan maganganun da kika fada, kuma dan dai ba zaki yarda bane ba amma ina tabbatar miki da cewa kusan duk abinda kika fada abinda nake kokarin yi kenan a yanzu. Abinda kawai ban fahimta da maganar ki ba itace da kika ce wai cigaba da zama da ni zai bata miki ibadun ki. How? Jidda shi auren nan fa gabaki dayan sa ibada ne, ibada nake yi ibada kike yi kema. Me yasa ba zaki zo mu nemi aljannar mu tare ba?"

Nace "yes, aure ibada ne, shi yasa in akayi dai dai sai a samu lada in kuma akayi akasin haka sai a samu alhaki. Ni turbar da na ke bi a zamana da kai ba ta samun lada bace ba ta samun alhaki ce Umar" yace "ta yaya?" You have being nothing but good to me. In ma akwai wani abu da kika yi ni na yafe miki Jidda, sai menene kuma? Shin ba kya ganin cewa kema taki jarabawar kenan? Kema aure na shine naki jarabawar?" Ya sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannuna nace "haka ne, tabbas auren ka shine jarabawa ta Umar" sai ya saka hannunsa biyu ya rike fuskata "then come back to me. Ki dawo mu hadu muci jarabawowin mu tare"

Sai na dora hannayena akan nasa da suke rike da fuska ta ina jin yadda yatsunsa suka sirance fiye da yadda na san su. Idona cikin nasa, a hankali Nace

*"You don't get it, do you? Ba wai zama da kai shine cin jarabawa ta ba rabuwa da kai ne"*

Nan take yanayin fuskarsa ya chanja, kamar wanda aka kwadawa mari, na cigaba da cewa "Allah yasan yadda nake son ka Umarul Faruq, shi yasa ya bani kai a matsayin miji kuma ya sa ka kasance da halin ka. Dan ya gani ko zan bi hanyar dai dai in rabu da kai ko kuma zan bi son zuciyata in cigaba da zama da kai"

Sai ya karbe hannun sa daga cikin nawa sannan ya mike kamar wanda aka yi wa allura yace "nooo. You are messing up the whole thing. In aka jarabci mutum hakuri yake yi akan jarabawar sa har a karshe ya samu abinda yake bukata. Wannan shine cikakken imani"

Na mike tsayen nima sannan nace "ni a fahimta ta, ita jarabawa tana iya zuwarwa mutum ta kowacce siga, zata iya zuwa a sigar abu mai kyau ko akasin haka. Misali. Za'a iya jarabtar mutum da kyau ko da dukiya ko da mulki, ko da fame, ko da ilimi, ko da wata baiwa ta musamman dan aga ya zaiyi da ita. Ko kuma a jarabce shi da muni, ko da talauci ko da kaskanci, ko da cuta, ko da wata musiba dan aga yadda zaiyi shima. Yadda ake cin jarabawa kuma shine sai mutum yayi kokarin bin hanyar Allah da Manzonsa a cikin jarabawarsa. Idan talauci ne sai mutum ya guji sata ko wani abu da zai kawo masa haram duk kuwa da halin talaucin da yake ciki, idan arziki ne sai mutum ya fitar da zakka, yake sadaka yana taimakawa addini da dukiyar, haka dai. Ba wai yayi hakuri da halin da yake ciki shine cin jarabawarsa ba"

"A case dina kuma. Allah da kansa ya fada a cikin Alqur'ani A cikin suratun Nur, Aya na 3, Allah SWT yana cewa:

الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ ۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ.

*Mazinaci ba ya aure face da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci ko mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai*

*An haramta wannan akan muminai* wannan ita ce ayar da malamai da alkalai da yawa suke amfani da ita wajen raba aure idan daya daga cikin ma'auratan ka kasance mazinaci. Umar ubangiji da kansa yace ya haramta min ni da nake ba mazinaciya ba zama da kai da kake mazinaci, umar gaya min wani abu da yake sama da ayar ubangiji? Gaya min ta yadda in naki bin wannan ayar bayan na santa kuma bayan na tabbatar kuma kai da kanka ka tabbatar min da halayyar ka ta yadda zan yi wa ubangiji bayanin a ranar lahira, Gaya min idan rabuwa da kai ba shine cin jarabawa ta ba. Gaya min idan cigaba da zama da kai ba son zuciyata ba ne ba"

Na fada ina kuka sosai. Sai ya dawo zuwa gabana ya tsaya, expression din fuskar sa unreadable, yace "menene dalilin da yasa kika kira ni? Idan har kin yanke wannan shawarar menene dalilin da yasa kika kira ni har kika bari na ganki na taba ki na kuma saka ran cewa zamu dai dai ta?"

Nayi shiru ina kallon sa cikin mamaki, yana nufin bai amince da ayar dana kawo masa ba ne ko kuwa menene? Na share hawayena nace "I called you to say goodbye. Zan yi tafiya zuwa Ethiopia kuma bansan sanda zan dawo ba. Abba yace zai baka lokaci ka rubuta takarda ka bashi, in kuma baka rubuta ba zai......." "Zai kaini court" ya karasa "the same threat each and every day har na haddace. Now I have a question for you. Kina tunanin you can just walk out of this marriage and live happily ever after?" Nace "not happily ever after, dan mumuni baya rabuwa da jarabawa har sai an zare ransa daga jikin sa. But yes, I can live happily, and you can too in dai ka..."

Ya tura ni baya da karfi har na fada kan kujera, yace "haka kika ce? Haka kike tunani? That you can live happy without me? Kina ganin ni kamar ba zan iya rayuwa ba sai dake ko? Here is a news flash for you, I will live happily without you too. Ba dai kina ganin zaki sake aure ba? To karkarin ta dai daya zaki aura ni kuwa hudu zan aura kuma duk wadanda suka fiki komai wadanda kuma zasu zauna dani suyi hakuri dani komai halina. Ko kina ganin idan kin rabu dani ne zan daina abinda nake yi? Ba dai takarda ba? Kar ki damu zan aiko miki da ita kafin ma ki tafi din in yaso ki tafi da ita a matsayin guzuri"

Sannan without another look at me ya dauki key din motarsa da yake kan kujera ya juya zai bar falon, na bishi da sauri na rike hannunsa a bakin kofa "Umar, kar ka fita like this, ka tsaya ka nutsu... " Sai ya zare hannunsa daga cikin nawa ya juyo yana kallo na, yana yin idonsa yana tsorata ni sannan yace "goodbye Hauwa'u".

Na daske a gurin har naji karar bude kofar motarsa da rufewa, sannan naji ya ja motar a guje, na daga labule ina lekensa sai na ga ya hau titi da gudu ba tare da ko signal ya saka ba ballantana ya jira motocin da suke wuce wa su gama wucewa.

Na lumshe idona na tare da ambatar innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Abinda na kira Umar dan shi ban samu nayi achieving dinsa ba, I thought he will understand, yana da ilimi ba jahili bane ba, I thought inna gaya masa ayar Allah zai fahimci hujja ta kuma zuciyar sa zata yi sanyi ya nutsu ya daina wannan damuwar akan rabuwa dani yayi concentrating akan cin tasa jarabawar nima ya barni nayi concentrating on mine. In da rabon zamu koma watarana idan ya gyara rayuwarsa, maybe, in haka Allah ya tsara, sai mu koma din.

But definitely not now. Kuma ba nan kusa ba.

Na zauna bakin kujera tare da sauke ajjiyar zuciya, at least dai Abba bai kama mu ba.

Sai kuma nayi wani tunani cikin jin tsoro, tunda har Umar yaki tsayawa ya saurari maganar Allah, to me zai saurara kuma?

*Umar*

Tukin motar kawai yake yi blindly. Ransa a matukar bace, shin wai me yarinyar nan ta dauki kanta ne da har zata kira shi da mazinaci ita kuma mumina? Tana ganin she is too holy for him har tana cewa zama da shi zai kaita ga halaka wato shine halakar ko? Bayan duk abinda yayi saboda ita? Bayan duk abinda yake kan yi saboda ita? To hell with her then.

Zai tabbatar mata dacewa ita din ba kowa bace ba face just a passing episode in his life and he will do just fine without her, watarana zata juyo ta kalle shi tayi nadamar abinda tayi masa.

Zuciyarsa ta gaya masa cewa But first dole yayi proving to himself cewa zai iya rayuwar ba tare da ita ba. Kafin daga baya yayi proving to her.

Automatically hannun sa ya sauka akan wayar sa ya dauko ta yana neman wata number, number din wata yarinya ce da aka hada su da ita gab da tafiyar Jidda kuma tun daga lokacin bai kuma bi ta kanta ba sai yau.

Babu bata lokaci ta dauka "lallai yau wannan jumaar tawa ce, tunda har doctor Faruq ya tuna dani kuma ya kira ni"

Ya danyi gyaran murya yace "ko kuma ni ince jumaar tawa ce tunda har kika dauki kira na"

Tayi dariya cikin jan hankali tace "da can ma da ka kira zan dauka, ba ka kira ba shi yasa ban dauka ba" yace "to yanxu ai gani na kira ko? Kaina bisa wuyana ina kuma bada hakurin rashin kira" tace "to anyi hakurin. No ai ba zan iya fushi da kai ba" yace "ko? Show me sai in tabbatar" ta sake dariya "Kana tantama ne? Just tell me when and where ni kuma zan tabbatar maka" yace "now" tace "yanzu yanzu? Da urgency haka?" Yace "sai kin zo ma sannan zaki san girman urgency din" cikin sigar hillata tace "how big" yace "very, come and see"

Tace "can't wait. Kazo ka dauke ni in the next 30 minutes, I will get ready for the big urgency"

Ya juya motar da zuwa hanyar gidan su, few minutes ya kai shi unguwar ya samu inuwa yayi packing ya gyara kujerar sa ya kishingida yana jiran ta gama shiryawa ta fito. Yasan shirin da take nufi ba zai wuce shaye shayen magunguna irin nasu ba, to get herself in the mood, amma shi har yanzu baya jin sa in the mood and that hurts him.

Ya dauko wayarsa ya shiga internet ya fara neman abinda zai saka shi in the mood din. Bai jima sosai ba ta shigo tayi kwalliya sosai irin tasu ta matan bariki. Kamshin da take yi kawai da kuma kallon da take yi masa ya saka yaji ya fara samun mood din da yake bukata, ya takarkare ya jefa mata his best smile tare da cewa "you look good, really good" ta juya idonta tace "kai ma haka" sannan ta dora hannunta akan cinyarsa can sama sama ta dan matsa da salo irin nata tace "shall we? Na matsu inga iyakacin matsuwarka".

Bayan mintina kadan suka je gidan gonar su Dr Bashir. A lokacin masallatan juma'a suna kokarin fara huduba. Yayi horn mai gadin ya leko cikin shirin tafiya masallaci sannan sai ya koma ya bude masa ya shiga da motar ciki, gidan gonar katon gaske ne mai cike da dabbobi kala kala, daga side daya kuma na gidan anyi gini wanda baban Dr Bashir yayi a matsayin gidan saukar bakin sa amma kuma sai dan nasa shi da abokinsa suka mayar da gurin gidan saukar nasu bakin tun bayan auren Umar, da a gidan Umar din suke aikata duk taasar su, bayan yayi aure kuma shine suka dawo nan saboda seclusion na gurin da kuma kasancewar babu kowa a gurin sai mai gadi da masu kula da dabbobin wadanda ba ko da yaushe ne ma suke zama ba. Gidan bakin dan karami ne, madaidaicin falo ne da kuma ɗakunan guda biyu masu dauke da toilets a ciki.

Umar yana shiga sai ya zagaya da motar sa bayan building din yayi packing din ta a kasan wata bishiya, in da kullum idan yazo dama anan yake packing saboda tsaro, baya son ya bar motarsa a inda tsautsayi zai iya sakawa wani ya gani.

Ya fita da sauri ya zagaya gaban building din yana kwallawa mai gadi kira, mai gadin ya taho da sauri ya miko masa key din dakunan dan yasan su yake tambaya, Umar ya karba ya juya ba tare da yace masa komai ba ya bude kofar gidan ya shiga yarinyar ta sa ta bishi a baya cikin karairaya. Maigadin ya bisu da kallo cikin takaici sannan ya girgiza kai tare da karanto addu'ar neman tsari daga shaidan a zuciyarsa.

Sai da suka shiga suka turo kofa sannan ya juya yana kallon gate din, Dr Bashir ya kira shi dazu ya ja masa kunne akan kar ya sake ya tafi wani gurin dan zai zo anjima, kar yazo ya tarar baya nan, shi kuma gashi yana son zuwa masallaci, yasan dai abinda zai kawo shi ba komai bane ba face irin abinda ya kawo abokin sa, dan sun saba dama zuwa wani lokacin ma sukan zo tare, dan haka yasan abinda Bashir din zai nema a gurinsa ba zai wuce bude gate ba da kuma mukullin dakunan aikata alfashar tasu, dan haka sai ya dauki sallayar sa ya fita ya dan tura gate din kadan amma bai rufe ba yadda ko Bashir din yazo kafin ya dawo daga masallaci zai iya budewa da kansa, cikin kuma dama abokinsa yana nan dan haka a bude yake.

*Mama*

Tun ranar Alhamis da Farhan da Amira suka kai mata su Yasmin take jin babu dadi, tabbas taji dadin ganin jikokin ta wadanda girman kai ya hana ta zuwa ta gansu tun da taji cewa sun dawo gida tare da Jidda. Haushin Jidda take ji sosai a ranta tana ganin cewa kusan dukkan abinda yake faruwa da ɗan ta a yanzu laifin Jidda ne, me yasa a matsayin ta na mace ba zata zauna ta rufe sirrin mijinta ba? Bayan laifin ma Umar yayi rantsuwa cewa bai kai ga aikatawa ba amma zata tashi hankalin ta ta kwashi yaya ta shiga duniya bayan akwai mazan da suke yin abinda ya ninka na Umar muni kuma matan su haka suke hakuri da su suna zaman aure suna rufe sirrin su ko dan yayan da suke tsakanin su. Amma ita Jidda da yake shafaffiya da mai ce ba za ta yi haka ba, ta gwammace ta yi ta yawo tana barbadawa duniya labarin abinda Umar yayi da kuma ma wanda bai yi ba. Gashi yanzu a sanadiyyar hakan har ciwo ya kama Baban sa yana kwance, ga wannan tsinannen auren da Baban yayi rantsuwa akan sai ya makala wa Umar, wai Umar din ta ne za'a aurawa yar mai gadi? Wannan wacce irin masifa ce? Kuma ma ba wannan ba, abinda yafi kona mata rai shine yadda alhajin ya dora kishiyar ya akan dukkan abinda ya shafi sabon auren da yake neman yiwa Umar din, ta kuma tabbatar da cewa ya gaya mata duk abinda ya faru da kuma dalilin yin auren dan ita ya saka ta kai yarinyar asibiti ma wai a duba ko an yi amfani da ita, amma kamar yadda Umar din ya fada ai ba za'a gane waye yayi amfani da itan ba. Sai dai kuma babu hujjar da zata nuna cewa ba Umar din bane ba. Bakin cikin ta shine yanzu ita auntyn zata yi ta yamididi da zancen a cikin dangi da kuma cikin dukkan wadanda tasan sun san Umar kuma suna ganin mutuncin sa.

Sai dai in tasan wata ai bata san wata ba. Ita tasan ko da ace Umar yana aikata abinda Jidda take cewa yana yi to kuwa tabbas a cikin biyu akwai daya, ko dai akai aljanun da suke saka shi yi ko kuma asiri akayi masa, in kuwa asiri ne to tabbas auntyn ce tayi shi dan in banda ita bata ga wanda yake da motive na yi wa Umar asiri ba bayan ita auntyn, ko dan daukakar da yake samu da kuma soyayyar mahaifin sa gare shi.

Ana kawo mata yaran bayan ta rungume su cikin jin dadi sai ta saka aka mai musu kayansu dakin ta, ta kuma kira Umar a waya ta sanar dashi lallai yazo ya saka a gyara musu tsohon dakin Muhsina kuma ya siyo musu duk abubuwan bukata dan sun dawo kenan.

Aunty tana jinta tace "na dauka sun zo su gan mu ne kawai? Na dauka zasu koma gidan su idan Allah ya taimaka an daidaita maman su ta dawo dakin ta?" Sai Maman tayi shiru bata ce komai ba, amma ita a ranta in da son samu ne tafi son Umar ya cire Jidda a ransa dan ba matar zama bace ba tunda ita ba matar rufin asiri bace ba, in komai ya lafa ita zata nema masa mace ta gari ya aura wadda zata kare masa mutuncin sa da martabar sa a duk inda yake.

Amma kuma sai taji tausayin Umar din sanda ya shigo gidan ya rungume ƴaƴan na sa kamar zai mayar da su cikin sa, suma suna ta murnar ganin sa Yasmin har da hawayenta sannan suka yi ta bashi labarin inda suka je

85 / 106