Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   60 / 61

177K to 180K   out of 182.7K words

to zasu yi ?o?arin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaWai a lokacin da babu wanda zai taya ni ?watar ?ancina, sannan na fuskanci abun da yake bani tsoro, aikuwa na Wauka, ai tunda na gane ?an unguwa sun gane lagona su kai ?arata gida mama tayi mini faWa na fetsare, ka kai ?arata gobe na yi maka abun ya fi na jiya, idan ka kawo ?arata aka tambayeni na yi in ce eh, zaSi ya rage a kasheni ko a barni da rai.
Wallahi ammi idan ya ce wa masu cewa ya kasheta yayi Win, ya gani idan za a cigaba da takura masa, duk wanda ya damu ya kai ?ara, ko kuma tun da Wan sanda ne ya kamosu ya yanke musu hukunci, su faWi yadda aka yi suka san kasheta ya yi, ko kuma ya kullesu ba rannan wata haka ta yi ba, wannan kwamishiniyar ba aka ce wani ya Sata suna ba, aka kai su gidan yari, ko decoration of character ko me ake cewa oho dai".

Duk da damuwar da adam yake ciki, sai da ya tattara hankalinsa yana sauraron rumaisa, duk da ba kallon in da take yake yi ba. Shi wasu lokutan har tsoro take bashi, ta wani fannin maganganunta a kan gaskiya suke, da maganar hankali da shirme haka take kwaSa kayan ta.

Ammi ta ce "Waii, rumaisa an gaisheki, ban taSa ganin yarinya irinki ba, ke kuwa ya ?an bindiga suka iya zama da ke?"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Haka suka zauna da ni, amma na ci ubana ba ?arya ammi. Ni fa tun da ga kano aka Waukemu da ?an bindiga, har kaza suka sai mini da na ce ina jin yunwa, suka nuna mini wata jaka, cike da bullet, har da bindigogi, shugabansu ne fa ya zo in da aka yi garkuwa da mu, ya sakeni ni da sabir, shi wanda ya sai mini kaza, ammi garin da na je, idan ka yi noma ba zaka taSa ba sai ?an bindiga sun yi maka izini, ni na je na Wauki masara aka je aka gayawa mai gari, da nake a gidansa.

Da aka yi garkuwa da ni, baki ji abubuwan da suka faWa a gabana ba, na ce idan na kuSuta sai na faWa suka ce kona faWa a banza, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, na yi ta karanta musu, ba ?a??autawa sai Allah ya kawo mini anty aisha, daga baya kuma muka kuSuta ni da sabir"

Ammi ta yi wata irin ajiyar zuciya ta ce "Amma abun da mamaki, wannan wane gari ne haka?"

Rumaisa ta Waga kai ta kalli adam, sannan ta ce "Na manta sunan garin"

Adam tambayoyi ne fal a ransa, amma girman kai ya hana ya tambayi rumaisa, gashi ammi ta fara taSo abubuwa masu muhimmanci, amma rumaisan ta kauce ta?i magana.

Ruma ta yi wa sabir kiss, ta mi?awa ammi shi ta ce "Ammi, bari mu tafi, kar mu yi dare ba mu je gidansu Hauwwaliya ba".

Ammi ta ce "To madalla, Allah ya tsare dan Allah ku gaida mamanku, ku jira bari na baku kuWin mota".

Ruma ta ce "A'a muna da kuWi, na ga kaya na gode sosai da sosai, baba mai farin rawani ma, ya bani kaya har da kayan gara masu daWi da zuma da nono, da kilishi na gode sosai"

Ammi ta takura ruma, ta basu dubu biyar suka tafi.

Bayan tafiyarsu ammi ta kalli takawa ta ce "Adam, dan Allah ne ka fuskanta game da yarinyar nan, ji yadda take magana kamar ana karanta mata?"

"Ni banga komai ba sai shirme da rashin nutsuwa a tare da ita".

Ammi ta ce "No, maganganunta abun dubawa ne, a duk lokacin da duniya ta nemi juya maka baya, ka kama Allah ka nuna musu zaka iya rayuwa kai kaWai, kar ka yi ?o?arin lallai sai an yadda da kai"

Ya numfasa ya ce "Ammi wannan shirmenta ne kawai na ?uruciya, da rashin sanin ciwon kanta, yaushe ta zo duniyar balle ta san me duniyar ke ciki, tana tunani ne a iya ?ar ?aramar duniyar ?wa?walwarta, bari na tafi masallaci ".

Ammi ta ce "Shikenan Allah ya taimaka".

Sai dai maganganun rumaisa suka cigaba sa shiga suna fita a cikin kwanyarsa, kamar maganganun ta na bisa turba.

Rumaisa sai da suka je gidansu Hauwwaliya, ?afar Hauwwaliya ta yi kyau sosai, suka din ga murna da ganin rumaisa, ana yin sallar magariba, Yasir ya tasata a gaba suka tafi gida.
A hanya yasir ya yi ta yi wa rumaisa faWa a kan tsinannen surutunta yayi yawa, ko a jikinta tun da muradinta ya cika.

Bayan sallar magariba, Adam da kansa ya je gidansu Jabir, ya tarar da shi da Jamil suna tare.
Jabir ya ce "Ka gama jan ajin ka neme ni kena?"

"Jan ajin me fa?"

"Ai ka fini sani, ka ce zamu haWu amma na yi ta kiran wayoyinki ka ?i Wagawa"

Adam ya ce "Ba ?in Wagawa na yi ba, kaWaici nake bu?ata ne, abubuwa sun sha kaina da yawa".

Jamil ya ce "Ai kai dama yanzu sai ana yi maka uzuri"

"Hmm baku ga abun da yake ta yawo a social media ba, game da mutuwar aisha? Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin yaWawa a media dan a Sata mini suna"

Jamil ya ce "Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun Wazu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?"

"Ba ni da isasshen lokacin da zan Sata wurin ?o?arin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani ?orafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu" yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya faWa.

Jabir ya waro ido ya ce "Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da Sata maka suna?"

"Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da ?o?arin wanke kaina, za su cigaba da ?o?arin kaini ?asa, idan na tsaya a kan ?afata na cigaba da karSar duk abun da za'a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta"

Jamil ya ce "Amma kana ganin hakan mafita ce adam? Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye"

Adam ya ce "In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni"

Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.

Jabir ya ce "To, bari mu ga zuwa yaus??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????he wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora"

Adam ya amsa da Amin, ya mi?e ya ce "Bari zan shiga gari na ga Bashir, gobe in Allah ya kaimu zai bar gari, ina da muhimman abubuwan da zamu tattauna".

Jamil ma tashi yayi ya ce "bari nima na gangara gida, na gaida Alhaji, sannan na wuce gida sai sa safenku".

Jabir ya ce "To Allah ya bamu alkhairi"

Kamar yadda Jamil ya faWa, gida ya wuce ya je ha gaida mama da turaki, sannan yayi aniyar tafiya gidansa, Samha ce ta bi yo shi, tana kiran sunansa.
Ya tsaya yana jiran isowarta, ko sa ta ?araso, hannunsa ta ja ta ce "Mu je motarka mu yi magana" bai musa mata ba suka wuce motarsa, suka shiga.
Shiru ne ya Wan ratsa, daga bisani ya Wan numfasa ya ce "Ina jinki"

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "A duniya bayan mama bani da wani kamarka yaya jamil, mama ta kasa fahimta ta, ban sani ba ko kai zaka fahimceni, domin kuwa kaine dai-dai da zamanin da muke ciki"

Jamil ya ce "Haka ne, ina saurarenki".

"Yaya jamil game da takawa ne"

Ya dubeta ya ce "Takawa again, me kuma ya faru?".

"Maganar nan ce dai ta shekarun baya, tun da Aisha ta mutu ina son maye gurbinta, na so na je wurin baba da kaina, amma sai na ga rashin dacewar hakan, ka taimaka yaya kai kaWai zaka fahimci halin da nake ciki"

"Wai ke samha ba zaki ?yal adam ba kamar baki da zuciya? Duk cikin tarin samarinki babu wanda zaki fitar ki aura sai shi dai?"

Kamar ta fashe da kuka ta ce "Da zan iya cire shi daga zuciyata da tuni na yi, dan Allah ka taimakeni yaya jamil"

Jamil ya Wan yi shiru sannan ya ce "Zan fara yi wa adam Win maganar na ji mai zace"

Da sauri ta ce 'A'a dan Allah kar ka gaya masa yanzu, turaki zaka fara yi wa zancen"

"To amma kin san magana yanzu ba zata yiwu ba, tun da haryanzu ana cikin alhinin mutuwar nan"

"Ohhj God, to sai zuwa yaushe kenan?"

'dole ki yi ha?uri, lokaci ya Wan tura kaWan"

"To shikenan na gode, ina saurarenka ka gaida gida " ya jinjina mata kai, ita kuma ta buWe motar ta fita, tana jin a jikinta kamar a wannan karon za ayi nasara.


Kamar wutar daji, haka Zancen mutuwar aisha, ya cigaba da zaga gidan jaridu, da kuma kafafen watsa labarai, yayin da ta Sangarensa ya?i cewa kowa komai, kuma ya?i magana da kowane Wan jarida.
A yau babu tsammani, mai girma turaki ya karSi ba?uncin wambai da misalin ?arfe tara na dare.
Turaki yayi mamakin ganin Wan uwan nasa a wannan lokacin, amma ya Soye mamakinsa, ya karSe shi.

Wambai ya ce "Na san zaka yi mamakin ganina a wannan lokaci, sai da ba komai ne ya kawoni ba, illa zuwa in sake tabattar da abun da kunnuwana suke jiye mini, kuma ka yi burus, ba ka ce da ni komai ba"

Cikin rashin fahimta, turaki ya ce "Meke nan kake nufi?"

"Maganar rasuwar ?ar wurinka aisha mana, ko kai ba ka jin jita-jitar da ke ta yawo a kan mutuwarta?"

Turaki yayi murmushi ya ce "Alhamdilillah, da kai da kanka ka ce jita-jita ne, nima haka nan na tsinci zancen"

"Turaki na zuwa na yi domin mu yi wasan barkwanci ba, gaskiyar lamari zaka sanar mini, gaba Waya mutuncin masarauta na nema ya zube, martaba da kimar gidanmu adam na ta cigaba da rusata sa shi da uwarsa, wannan wane irin abu ne?"

Turaki ya girgiza kai ya ce "Na san mai Wakina ce ta je ta gaya maka wasu abubuwan, maganar da ke yawo a gari, tabbas aisha ta mutu a hannun 'yan bindiga, amma ba adam ne sila ba, ko ya kasheta ya sha jininta ba kamar yadda ma?iya ke ta kwarmato, kuma yarinyar da aka tsaresu tare ta zo da yaron wurin aisha".

"Turaki kana nufin goya masa baya wurin Soye laifinsa, dan me za a ce a ?asar waje ta mutu a Soye gaskiya, wannan banzan aikin da yake yi na shishshigi ga manyan ?asar nan da kawo ?arshensu, ai gashi shi zasu kawo ?arshensa, ko iya wannan labarin an yi mana mummunan tambari, a ce an samu babbar zuriya kamar ta mu da ?arya. Dan haka dole a hukunta adam, sai ya yi wa duniya bayanin yadda matarsa ta mutu domin wanke ahalinmu daga mummunan zargin tsafi da kisan kai, ga uwa uba ayar tambaya a kan yaron da ake ce nasa ne, na baku awanni arba'in da takwas, idan har bai yi abun da na ce ba, matakin da zan Wauka a kan sa ba zai yi muku daWi ba.
Kai banda tsabar rashin sanin ciwon kai, kamar ba ?arka ba wane irin abu ne haka?"

Turaki ya ce "Da Adam da A'isha, duk tsatso Waya ne, kuma ?a?anmu ne, dukkansu.....

Bai ?arasa ba, wambai ya Waga masa hannu tare da faWin. "Ba nasiha nake bu?ata ko tunatarwa ba, martabar ahalinmu da sarautarmu nake ?o?arin karewa, dan haka ayi abun da muka umarta, ko a ga ba dai-dai ba"

Turaki yayi ajiyar zuciya, ya bi wambai da kallo, da ya tashi fuuuu ya fice.

Yayi ajiyar zuciya yana jin wani irin matsanancin tausayin Adam.

Duk wannan kumfar bakin da wambai yayi, ya biyo bayan ziga da kuma famfon da Mummy ta je har gida ta yi masa tare da taimakon hajiya sauda, shi kuma kamar kullum ya hau kai ya zauna ba tare da bincike ba.

Rumaisa har islamiyya ta koma, in da malamai da Walibai suka din ga yi mata barka da arziki na kuSutowa daga hannun ?an bindiga, sai dai a wannan karon ma, duk yadda ?an bugun ciki, suka so ta basu labarin abun da ya faru da ita ?i ta yi, wasu har suna cewa rumaisa ta koma saliha.
Bayan tashi daga islamiyya, ta wuce gidansu habiba, dan tun da ta dawo ba ta je gidan su habiba, suka rungume juna suna tsalle a tsakar gida.
Daga bisani suka zauna suka hau hira, mamansu habiba ta zubo musu Wan wake, suka kewaye suna ci suna hira.

"Ruma ina yaya Aliyu ne?"

Ruma ta kalleta ta ce "Meyasa ki ke nemansa?".

"A'a, tun a asibitin nan ban kuma ganinsa ba"

"To meye haWinki da shi, to idan son sa ki ke yi, zaki dinga sai mini kayan daWi kina bani"

Waro ido habiba ta yi ta ce "Astagfirullah, dan Allah ruma ki daina yi mini haka, baki san kirkin da ya yi mini ba lokacin da nake zuwa gidanku da ki ka Sata, mai sunan baba yayi ta hararata, shi yake rarrshina ya dawo da ni gida".

Ruma ta kwashe da dariya, ta ce "Allah sarki habibata, kamar ba nan muke kwasar dambe da ke ba, ke ni shawara zaki bani ma"

"Shawarar me" habiba ta yi maganar tana suWe hannunta.

"Mutumin nan da ya ?wace mini jaririna, wai ya zan yi da shi ne in karSo Wana?"

"Wai ?wace jaririn suka yi gaba Waya to saboda me?"

"Saboda wula?anci mana, kullum da tunanin yaron nan nake kwana nake tashi, babarsa fa cewa ta yi ta bar mini shi, amma ya ?wace mini shi. Habiba kin san in da kotu take? ?ararsa zan je na kai, ba dama an ce zulai ta kai ?ara kotu al?ali ya bata Wan ta ba, to nima kotu zan kai shi".

Habiba ta Wan yi shiru ta ce "Tsoro nake ji ruma, kin san ba a wasa a kotu"

"Na sani, ai ba wasa zamu je ba, ?ara zamu kai".

Habiba ta ce "To, a unguwar su babanmu akwai kotu, dama za ayi sauka a gidan, sai ki zo mu je".

Ruma ta yi murmushi ta ce"Amma na ji daWi habiba, Allah ya kaimu in sha Allah sai an bani Wa na, bari na tafi gida" ta mi?e suka fita tsakar gida suka wanke hannu, ta yi wa maman Habiba sallama sannan ta tafi gida.

Idan har da wanda za'a zarga a kan mutuwar aisha, to ba kowa bane ba face ni mahaifinta, domin ni na Soye ainihin abun da ya faru, adam ba matsafi ba ne, bai kashe aisha ba, kuma bai yi tsafi da gangar jikinta ba, a madadinsa, ina mai baiwa al'umma ha?uri na Soye ha?i?anin gaskiyar abun da ya faru.

Mummy ta yi jifa da wayar hannun ta, bayan kammala karanta abun da turaki ya sanar da ?an jarida, ya wanke adam.

Ayshercool.


*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*




Masifa mummy take kamar ta ari baki, duk ?o?arin da ta yi, amma turaki lokaci Waya ya watsa komai.

Takawa ma mamaki ne ya kama shi, da ganin abun da turaki ya ce, ya wanke shi ya Wau laifin, bai jira komai ba ya tafi gidan turaki.
Bayan an yi masa iso ya shiga sun gaisa da turaki, ya dubi turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai,? na ga abun da ka gayawa manema labarai, amma ni yakamata na Wau wannan laifin na magantu ba kai ba".

Turaki ya murmusa ya ce "A'a mu Win ne dai yakamata, wambai ya zo nan ya nemi mu sanya ka fito duniya ka bayar da ha?uri, a kan abun da ya faru, wai sunan masarauta na neman Saci saboda kai, hakan ya sanya ni na bayar da ha?urin, kar ka ji komai"

"Amma Allah ya taimake ka..."

Turaki ya girgiza wa adam kai ya ce "An rufe wannan babin, ina ?a ta?"

Adam ya ce "Wace ?ar ta ka?"

Turaki yayi murmushi ya ce "?a ta yarinyar da ta kawo jikana, rumaisa"

Adam ya Wan tsuke fuska ya ce "Tana gidansu"

"Allah sarki, duk lokacin da aka ganta, ace muna gaisuwa, Allah ya ?ara mata lafiya" turaki yayi maganar yana murmushi, yana tuna lokacin da rumaisa ta zauna a gabansa tana ta zuba shirme son ranta.

Haka adam ya tashi ya tafi, yana ta tunani kala-kala a ran sa. Idan har turaki zai fito duniya ya kareshi, zai iya fuskantar duniya ya ce duk mai cigaba da zarginsa idan yana da hujja. Kansa na kashe aisha ya je ya nema mata hakkinta a kotu.
'kar dai shawarar wannan yarinyar mara kan gado zaka Wauka, ta kai ka ta baro' wata zuciyar ta gargaWe shi, tsaki ya ja ya kawar da wannan tunanin a ransa.

Maganar da turaki ya fito ya yi, ta ?ara yamutsa hazo, kowa da abun da yake faWa, yayin da hakan ya ?ara tunzura wambai, turaki ya ?ara zubar musu da mutunci ta hanyar kare adam.

Yau kwanaki kusan bakwai rabon rumasa da jaririnta, dan haka ta shiga damuwa ba kaWan ba, tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. Wata irin ?ishirwar son ganin yaron ke damunta.
Ta gama shirinta tsaf za ta tafi makaranta, ta fito daga gida har ta nufi hanyar makaranta, ta kalli kuWin makarantarta a hannunta, kawai ta canza hanya, ta nufi titi.

Ta san kuWin hannunta ba zai kai ta gidansu takawa ba, dan haka ta saSi hanya da ?afafuwanta ta dinga tafiya kamar mara hankali.
Tun da sanyin safiya, har rana ta Waga ta fara jin zafinta sosai a jikinta. Idan ta gaji ta zauna ta huta, idan ta huta ta tashi ta cigaba. Sai da ta ci fiye da rabin tafiyar sannan ta samu napep ta yi masa magiya ya Wauke ta, shi ma in da ya ajiyeta da sauran tafiya, ta sauka ta cigaba.

Sai dai da ta ?arasa, tana zuwa ?ofar gidan, security suka tare ta.

Ta kalli wanda ya sha

60 / 61