Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   3 / 61

6K to 9K   out of 182.7K words

yaran suka fara kai mata duka.
Tayi kukan kura, ta Waga allonta saukewa Habiba allonta a fuska, wani uban ihu Habiba ta kurma, jin danshi a hancinta.
Tamkar namiji a filin dambe, haka Rumaisa ta zage ita kaWai ta dinga dukan yaran nan, yadda ta dun?ule hannu tana kai naushi, kai ba ka ce 'ya mace bace.

Da ?yar da siWin goshi wani mutum ya rabasu, saboda Rumaisa akwai taurin kai, zuciyarta a bushe ana rabasu tana cigaba da kai duka.
Ta Wau allonta ta nufi gida, tana ta huci, duk da dukan da tayi musu sai dai jikinta duk yayi tsami ita ma. Dama ga jikin nata babu daWi ji

Sai dai kash, tuni wasu daga cikin yayyen yaran maza suka samu labari, suka yi gaba zasu datse Rumaisa a hanya, su zaneta.


Ayshercool
08081012143

[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ?ANWAR MAZA

? ? ? BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Ku yi subscribing YouTube channel Win mu, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Page3

'yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ?arfin namiji da na mace ba Waya bane ba.
Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da wa ake.

tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta dur?usa ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ?wale masa kai da dutse.

Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.

Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ?afarsa ta faWi ?asa, wani dan?o ya Wauko a aljihunsa, ya fara dukanta da shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ?yar a kan ?afafuwanta.

Ta yi kukan kura ta kafa masa ha?ora a kafaWarsa, tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ?ashinsa ya ji ha?oram Ruma, sai ka ce mayya.

Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama da raWaWin jifan da suka sha, ya sanya ta dur?usa ta Wauki takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.
Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar wal?iya haka take she?a da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball Win su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ?artin mazan nan take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a tsakiyar filin ?wallon ta rirri?e shi.

Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.

Ri?eta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma ta?i magana sai ajiyar zuciya take yi.

Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a tsanake ya ce 'Menene?" Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi take.

Haushi ne ya fara kama shi ya ce "Dan ubanki menene, me aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?" Yayi mata maganar a hasale.

Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ?wace mata.
?an shiru yayi sannan ya ce "Amma ina fatan baki yi kukan a gaban yaran ba?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai na ?ara miki".

Cikin sheshe?a ta ce "Ban yi ba"

Aliyu ya ce "Bari na canza kayana muje, Waya bayan Waya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke zancen"

Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball Win su, shi zai tafi.

Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta Sace musu, suka ha?ura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da zasu naWa mata duka, dan tayi musu Sarna sosai.

Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce "Ke amma ba a banza zan je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball Wina da takalmina".

Cikin hanzari ta ce "Eh na yadda, zan wanke maka"
ya ce "To shikenan"

Ya sakata a gaba har ?ofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro yace a kira masa Sani.
Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta fama da kafaWarsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi da manjagara a wurin ba ha?orin Wan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka take, leSe yayi suntum ya kusa haWewa da hancinta, bakin ya?i rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da tukunyar ?arfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.

Sani ne ya fito yana waige-waige, yana neman wanda ya aiko a kirashi, Aliyu yayi caraf ya dan?e shi.
Zazzare ido Sani ya hau yi, Aliyu ya ce "Kai, kaine ka tattaro abokan ka ka daki Ruma ko?"

Cikin fitsara Sani ya ce "Nima ?anwata ta daka, kuma ta Satar mini da tayata".

"Kuma saboda kai mahaukaci ne, sai ka tattaro abokan ka maza su daketa, saboda baka da tarbiyya ko? Meyasa ba ka bari ?anwarta ka ta rama da kanta ba?".

Fizge-fizge Sani ya fara, yana yiwa Aliyu rashin kunya, aikuwa Aliyu ya dinga kifa masa mari, har sai da bakin Sani ya mutu, fuskarsa duk tayi ja. Ya saka shi a gaba zuwa gidan abokansa da suka yi yin?urin dukan Rumaisa.
Duk da irin Sarnar da Ruman ta musu da duwatsu, hakan bai hana Aliyu kama yaran Waya bayan Waya ya zane musu jikinsu ba, sannan ya saka Ruma a gaba yana rarrashinta suka tafi gida.
Ko da suka je gida, yanayin Ruman Mama ta kalla ta ga kamar ba ta da gaskiya, amma ta share ba ta kula ta ba, dan idan ta biye wa halin Rumaisa kullum sai ta daketa.

Da daddare bayan sallar isha'i duk suna zaune a tsakar gida, Rumaisa na ta tunanin me zata ci yau, dan yau ma ma?iyin na ta Mama tayi, wato tuwo, Allah ya sani yau ba ta jin za ta iya cin wannan tuwon, gashi haryanzu ranta a Sace yake a kan abin da ya faru, dan marin da Yaya Aliyu ya yiwa Sani bai gamsar da ita ba, ji take ba zata huce ba sai ta fasa masa kai, ko ta hankaWa shi kwata, ga? kuma tuwon nan da Mama tayi ya sake ?ara mata Sacin rai.

Yasir ne yayi sallama, hannunsa ri?e da leda, duk suka amsa masa, banda Rumaisa da ta yi zurfi a tunani.
In da Rumaisa take ya ?arasa, ya jijjiga kanta ya ce "Ke tunanin me kike?"
HaWe rai ta yi ta ce "Meye kuma na dakar mini kai?"

Yasir ya ce "To kwalba uwar sharri, ni ban dakar miki kai ba"

Tsaki ta yi ta ce "Ai na saba in dai ?arya ce"

Dire mata ba?ar ledar yayi a cinyarta, ya wuce Wakinsu.
BuWe ledar tayi ta kwance, gurasa ce fal ta masu tsire a ciki.

Murmushi ta yi ta Waga murya ta ce "Na gode rabin ran"

Daga Waki ya ce "Ko ba rabin rai ba, tun da na baki abin duniya ba, uwar son zuciya"

Rumaisa ta ce "kai dai Allah yayi maka albarka, kamar ka san ba son wannan tuwon nake ba, tunani kawai nake me zan ci? Wannan tuwon ne yake toshe mini kai bana gane karatu sosai, Allah dai ya biyaka rabin raina "

Murmushi Yasir yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.

Ya gama abin da yake ya fito tsakar gida, zamansa yayi dai-dai da shigowar dodonsu, wato Yaya Umar.
Cikin muryarsa ta ?asaita yayi sallama.
Duk suka amsa masa, ba tare da ya kula kowa ba, ya ajiyewa Rumaisa leda da indomie ya ce "Tashi ki dafa mini" tabbas ba dan Mai sunan Baba ne ba ba zata yi ba, ita a rayuwarta tana son ko aiki zaka sanyata, ka lallaSata shi kuwa mai sunan Baba bai san wannan ba, ya bada umarni a bi kawai ya sani mutum ya ?i kuma jikinsa ya gaya masa.

Haka ta tashi ta je ta kunna wuta ta Wora masa.

Rumaisa na tsaka da aiki, suka ji sallama, kai da jin yadda aka yi sallamar, ka san babu alheri a tare da mai sallamar.
Mama ta amsa tana faWin maraba.

Jin yanayin yadda aka yi sallamar ne ya sanya Rumaisa faWuwar gaba, ta tsaya cak tana sauraron abin da zai biyo baya, dan ta san babu wanda zai aikata abin da za a zo ana musu wannan sallamar a daren nan idan ba ita ba.
Mama tayi wa matar nuni da tabarma dan ta zauna, amma matar ta ce "A'a ba ma sai ma zauna ba, ai abin bana zama bane na"

?an zuro kai Ruma tayi daga Kitchen, domin taga wacece, tozali tayi da Habiba da ?aninta Sani.
Ita ba zuwansu ne ya Waga mata hankali ba, babu tantama ta san ?ararta aka kawo, amma tashin hankalin ta, Mai sunan Baba yana nan.

"Ban sani ba ko ke ce ki ka sanya 'yar ki ta dinga abin da ta ga dama a cikin unguwar nan, saboda tsabar rashin mutunci da rashin ta ido, ta kama mini 'ya ta daka, kalli fuskar Habiba, kuma duk da haka bai isheta ba, ta Wauko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.
Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki ya haye, ya fashe ta ri?e kai sai kuka take, shima Sani kalli fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?" Ta ?arasa maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya yi, leSen sama ya Wage ya kusa danganawa da hancinta, duk dadashi a waje.
Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta ?unshe baki tayi dariya ?asa-?asa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma kamar an naushi fura.

Jiki a sanyaye Mama ta ce "Dan Allah dan annabi kiyi ha?uri, yaran yanzu ne sai addu'a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan nata ba, amma kiyi ha?uri".

Haidar yayi gyaran murya ya ce "Mama nine, su meyasa yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai zasu daka.....

"Rufe mini baki ban tambayeka ba" Mama ta dakatar da haidar cikin tsawa.

Mama tayi ta bawa Babar su Habiba ha?uri, amma ba kunya babarsu Habiba ta ce "An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da suka ga dama, saboda tana ta?amar ita ?anwar maza ce, sai tayi ta isakancin da ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana ma?ota da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini 'ya, shi kuma ya zo ya zage ?wanji a kan Wana".

Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta ya ce "Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban mace kina cewa 'ya'yanta basu da tarbiyya, tana baki ha?uri kina cigaba da ?anan maganganu, kar Allah ya sanya ki ha?ura Win, ki kai duk in da zaki kai ki je ki faWa, kuma ko yau wani ya kuma yin?urin taSa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa duniya ?anwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri"
Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haWe rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.

Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ?an?antar mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.

Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ?ofar Kitchen Win ya ce "Ke kuma fito nan munafuka" aikuwa kamar munafukar ta fito tana sunkuyar da kai ?asa.

Ya ?are mata kallo sannan ya ce "Muna zaman zamanmu lafiya aka haifeki, shegiya kamar rainon iblis, duk gidan nan babu mai fita ya Wauko magana sai ke, tana zaman zamanta kin saka an zo har cikin gida ana gaya mata maganganun banza saboda ke, kai ma saboda hauka dan me zaka biye mata ku je kuna dukan 'ya'yan mutane? Waye ya aiketa ta tsokane su?".

Ran Aliyu ya Saci, ya harzu?a ya ce "Bafa maganar hauka a nan, yarinyar nan hijjabi a hannu suka biyota, ba dan filin ball Win mu na hanya ba, haka zasu haWu su yi mata duka, yara maza ba mata ba, har sun fara dukanta baiwarsu ce ita, ko kuma ce musu aka yi ba ta da gata?.

"Shut up! Ita ka san me tayi musu, wannan Yarinyar da rashin jin tsiya, ai gara su zane ta gobe ba ta kuma ba, ki cigaba da zuwa ki na janyo mata magana, wallahi ba zaki Wora mata hawan jini a banza ba, da ki cigaba da Wauko mata magana ana zuwa ana gaya mata maganar banza, gara na takeki na murWe miki wuya ki mutu kowa ma ya huta".

Tun da Mai sunan Baba ya fara sababi, Sentence Winsa na ?arshe ne ya ba?anta mata rai, wai ya murWe mata wuya ta mutu su huta. Ta yi shiru ya gama bala'insa ya ce ta wuce ta cigaba da yi masa aikinsa, ya fice.

Rumaisa tana aikin tana kuka, wato ma ba'a sonta, wai da suna zaman zamansu aka haifeta, ta hana mahaifiyarsu kwanciyar hankali.

Usman ne yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama Wan nan naki yana da matsala, na yi shiru ne kar na tanka masa yayi mini tijara, amma ba damar yarinya ta motsa sai faWa, ke Ruma" ya kirata.
Ta goge hawayenta, ta fito daga Kitchen Win.

Ya kalleta ya ce "Duk shegen da ya takaleki kar ki raga masa, ki ci uabnsa idan yafi ?arfin ki muna nan, yaran unguwar nan marasa mutunci, ki ka zama nusara raina ki zasu yi, duk Wan da ya miki ki ci ubansa ko mace ko namiji mun tsaya miki".

Mama ta ce "Zinnuraini, kai ne kake zigata ta Wauko magana?".

"A'a Mama bance ta Wauko magana ba, amma duk wanda yayi mata, ta rama babu nusari a cikinmu, ?anwarmu ba zata zama nusara ba, mu ci uban mutum ya zo kawo ?ara mu ?ara masa"

Martanin Yaya Usman ne ya Wan sanya hankalin Rumaisa ya kwanta, ta kammala yiwa Yaya Umar aikinsa ta je ta nemi wuri ta kwanta, ko gurasar da Yasir ya bata ba ta ci ba.
Tana kwance lamo a kan katifarta, ta ji muryar Huzaifa a kanta yana cewa ki cigaba da Wauko magana, ai gara ya murWe miki wuyan ki mutu kowa ma ya huta da tijararki da rashin hankali.
Banza ta yi masa, kamar ba da ita yake ba, dan idan ta ce zata biyewa Huzaifa faWa za suyi, kuma a kowane lokaci mai sunan Baba na iya shigowa, yadda yake a ?ule da ita ta san sai jikinta ya gaya mata, idan ya dawo ya tarar suna faWa da Huzaifa.

Da safe bayan gaisuwa ba abin da ya haWata da mutan gidan, tana kwamce a Waki, 'yan mazan suka gyara komai na gidan, suka Wora abin kari. Ko ta kan abincin safen ba ta bi ba, ta saye gurasarta a hijjabi, ta Wau allonta ta tafi makarantar allo.

Sai dai ashe tuni labari ya iske shugaban makarantar su, a kan faWan da suka yi jiya, malam babba ya tara su ya ce sai ya zane su.
Idon Rumaisa yayi tsilli-tsilli, dan kusa bulalar malam Babba akwai Wan karen zafi.
Kan Malam Babba ya kai ga zuwa ya yanke musu hukunci, ta zari allonta ta kwasa da gudu, ya tsaya yana ?wala mata kira, amma tayi burus ta bar makarantar ta kama hanyar komawa gida, dan a rayuwar Rumaisa ba ta ?aunar duka ko kaWan.

A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce ya ce "Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina Makarantar kuma?"

Ta tura baki ta ce "Kashi nake ji shine na dawo gida"

Tsaki yayi ya ce "Haka dai kika iya, wannan uban cin da kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da tusar tsiya" banza tayi masa ta raSe shi ta wuce tana murguWa masa baki, ba tare da ya sani ba.

Ta shiga cikin gidan tana ciccin? magani, ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa Wauke take da murmushi saSanin fuskar Yaya Umar.

Babu tunanin komai, ta faWa jikinsa tana murmushi.
Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce "Autar Mama, tun Wazu zaman jiran dawowarki nake yi".

"Babban Yaya, yaushe ka dawo?"

"Tun Wazu na dawo, nace kina ina aka ce kin tafi makarantar allo".

"Wayyo daWi, yaushe rabon da na ganka, gaba Waya gidan babu daWi, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murWe mini kai su huta".

Waro ido yayi ya ce "Wane mara ta idon ne yayi wannan i?rarin a gidan nan?" Ta waiwaya sannan a hankali cikin raWa ta ce "Waye banda ?aninka, ya tsaneni wallahi".

Yayi murmushi ya ce "Ai ba wanda ya isa ya taSa mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo".

Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faWin "Iya rigima, ya halinki?"

Sake waro ido ta yi ta ce "Yaya Abdallah".

Ya amsa da "Na'am uwar rikici".

"HaWa baki kuka yi duk kuka dawo yau kenan?"

Abdallah ya ce "Eh haka ne, su Baba Atine suna ta gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci"

Ta taSe baki ta ce "Waye zai barni na je garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi" Gaba Waya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.
Sai da aka jima sannan ta shiga Waki ta ajiye allonta.

Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta

3 / 61