Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   10 / 61

27K to 30K   out of 182.7K words

a kwance yana waya, kuma da alama da mace yake wayar.
BuWe baki tayi, ta tsaya tana kallonsa. Zumbur ya tashi zaune, ya katse wayar ya ajiye ya haWe rai ya ce "Zo nan" ba musu ta ?arasa in da yake.

"Me ki ka ji?"

Ta ce "A ina?"

"Ina tambayarki kina tambayata? Nace me ki ka ji?"

"Wallahi ban ji komai ba, kawai dai na ji ka ce....." Sai kuma ta yi shiru.

"Ba zaki faWa ba sai na taka ki?"

Ta tura baki sannan ta ce "Na ji ka ce, wai kwalliyar ta tayi kyau, kamar farin wata".

"Sai kuma me?"

"Shikenan na ji wallahi "

"To na rantse da girman Allah, idan ki ka sake ki ka faWa, wallahi sai na yi miki dukan tsiya, ?anwar abokina ce ba wata ba"

"To ai ni dama ban ce zan faWa ba, mama ce ta aikoni" daga haka ta shiga duddubawa mama kwanukanta.

Aikuwa ruma ta fito da kwanuka a hannuta tana faWin mama "Kin ga kofin ki, an sha fura a ciki sha zumamu ya siWe miki kofi tas, har Sera ya fara ci. Kin ga plate Win ki har da sauran alalar da ki ka yi tun sati biyu da suka wuce".

Yasir ya ce "To munafuka, uban waye ya saka ki wannan sharhin?"

Mama ta ce"Ai ba ?arya ta yi ba, ku yi ta kwasar mini kwanuka kuna kaiwa Wakin ku, sai na bi na tsinto abina, ?azaman banza kawai"

Mama na tsaka da mitar sai ga Aliyu ya shigo, ya ce "Ina ruma"

Ta ce "Gani"

"Yo sauri, abokaina ne na filin ball suke tambayata kina ina, shi ne suka biyo ku gaisa, saura kiyi wani haukan da zaki zubar mini da mutunci ".

Murmushi ta yi ta ce"A'a ba zan zubar maka da mutunci ba, bari na sako gyalena"

Yana maganar ya fice, Huzaifa ya ce "Mama ke ba a zo gaishe ki ba, sai wannan yarinyar lallai ruma".

Ta fito daga Wakin mama da sauri, ta kalli Huzaifa ta ce "Ka yi mini Addu6, Allah ya sa su bani kuWi" tana gaya masa ta kwasa da gudu ta fita waje.

Da fari gaishe su tayi kamar nutsatsiya, suka amsa mata cikin mutuntawa.

"Ya makaranta ya rikici2?"

Ta ce "Makaranta lafiya ?alau, amma ni bana rikici" suka din ga jan ruma da hira ita kuma tana zuba, Aliyu sai hararta yake amma ta cigaba da zuba.

Dariya suka dinga yi mata, suka babbata barka da salla, ko Wan cewa ba zata karSa Win nan ba tayi ba, zuruf ta mi?a hannu ta karSe tana godiya.
Wani mugun kallo yake wa ruma, amma ko saurararsa ba tayi ba.

Ta duba a cikin kuWin da aka bata, akwai Wari biyu da ta tsufa sosai, ta kalli wanda ya bata ya ce "?an uwanmu Wan canza mini wannan, ba zata karSu ba" buWe baki Aliyu ya yi yana bin ruma da kallo.

Aikuwa ya karSa ya canza mata wata, ta ce ta gode ta shige gida.

"Mama kin ga abokan yaya Aliyu sun bani, kuma sun ce suna gaishe ki"

Mama ta ce "To madalla"

"Mama gashi ki ajiye mini, ki Wora da lissafi, idan kin manta ni ina sane da lissafin, dan Allah mama kar na zo karSar kuWina ki fara ce mini, abubuwan da ki ke mini ba da kuWina ki ke yi mini ba, wallahi mama da za ayi lissafi ban san iya adadin kuWin da nake bin ki ba"

Cikin gatse mama ta ce "To Anty ruma, ki zauna ki lissafa duk kuWin da ki ke bina, na biyaki"

"Dan Allah mama da gaske ki ke?"

"Eh mana" murna ta dinga yi tana cewa 'Ai mama kuWin da nake binki, sai ma zauna musamman na yi lissafi, tsaf sai na zama attajira da kuWin nan, unguwar da muke zuwa a bani kuWi ai da yawa"

Yasir ya ce "Ba zaki taSa hankali ba".

Aliyu ne ya shigo rai a Sace yana hararar ruma.
Kawar da kanta tayi gefe ta?i kallonsa.

"Dole ki kawar da kai mana, yarinyar nan ana bata kuWi ta karSe, wai har da cewa wai wata ba zata karSu ba, da yake ke ki ka basu ajiya"

"Yaya ba kyau mayar da hannun kyauta baya fa"

"Zaki mini shiru, ko sai na mareki, mara kai kawai"

A ranta ta ce "Ohoo dai, tun da Allah ya sa na karSa".

Bayan sallar isha'i yaya Umar ya dawo, duk sun daddawo suna gida, ana ta hira.
Ruma tayi gyaran murya, ta kalli Yaya Usman ta ce "Mama kin san me?"

Mama ta ce "A'a".

Usman ya zubo mata ido, kowa ya yi shiru yana sauraron wani shirmen zata faWa.

Ayshercool
08081012243

(INCLUDE ME IN YOUR PRAYERS PLEASE =?O?)
[05/07, 5:40 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.

P9


Wani irin kallo Usman yake mata, amma ta basar ta ce "Mama kin san me yaya Usman ya yi?"

Mama ta ce "A a sai kin faWa"

Usman ya ce"Haka muka yi da ke ruma?"

"Oho ni dai bana munafurci da rashin gaskiya, duk abin da aka yi mama bata nan sai na gaya mata, ba zan ga ana ba dai-dai ba mama bata sani ba na yi shiru".

Kamar ya yi kuka ya ce"Amma haka muka yi da ke?"

Mama ta ce "Gaya mini ina jin ki"

Ruma ta kalli Usman ta ce "Sai dai ka yi ha?uri fa, amma wallahi sai na faWa a gaban kowa da kowa, ba zan zuba ido ana abin da ba dai-dai ba"

Ba dan ya san idan ya yin?ura zai yi mata wani abu mama zata hana ba, da sai ya kife Ruma da mari, ya san idan ta Waga maganar nan akwai damuwa, zai sha faWa da mita.
Uwa uba ga Yaya Umar a zaune a wurin, kuma ba shi da tabbacin iya abin da ruma ta gaya masa ta ji, shi kaWai Win ta ji, dan kawai Waga kai ya yi ya ganta a tsaye lokacin da yake wayar.

Ta gyara zamanta sannan ta ce "?azu, da ki ka aikeni kai tuwo gidan mai ?uli, na ganshi a ?ofar gidan su wannan abokin nasa Yahaya, shi da abokansa sun dawo daga idi, ko gida ba su zo ba, ya zauna an fito da abinci sun haWu suna ci, kuma kin hana hakan"

Ajiyar zuciya ya yi, yana hamdala da ba wancan zancen ta yi ba.

Mama ta ce "To wannan abun ne ki ke ta zuzutawa, ai shima ya zo ya Wau abinci ya fita da shi sun ci tare"

"To mama sai aka ce ya je ya zauna a ?ofar gida yana cin abinci ai rashin kamun kai ne, kuma ke ki ka ce rashin kamun kai ne fa".

Mama ta ce "To shikenan, za a yi masa faWa".

"To mama kiyi masa faWan mana yanzu"

A fusace ya ce "Ke wai ni sa'an ki ne?"

Umar ya ce "Maganinku kenan da ku ke wasa da ita"

Can ta sake gyara zama ta kalli mama ta ce "Mama, kin san wani abu?"

"Ke na gaji da wannan shirmen naki fa" mama ta faWa cikin ?osawa.

"Mama ba shirme zan ba, Wazu na ga Habiba a masallacin idi, da tsofaffin kaya na ganta".

"To ina ruwanki? Kin ga ina rabaki da sabgar munafurci amma ba zaki dai na ba ko?"

Jiki a sanyaye ruma ta girgiza kai ta ce "Mama so nake a bata kaya Waya a cikin kayana" gaba Waya juyowa suka yi suna kallon ta jin abin da ta ce.

Huzaifa ya ce "Kina da hankali kuwa?"

"Amma dai ka san tun da nake ni ba mahaukaciya ba ce ko? Mama dan Allah a bata ita ma ta saka sabon kaya"

"Rufewa mutane baki, mara zuciya nan babarta ta zo ta ciwa mutane mutunci, amma ki ka cigaba da shishshige mata, ba za a bayar ba Win" Aliyu ya faWa yana zaro ido.

Mama ta girgiza masa kai, ta dubi ruma ta ce "Allah ya kaimu gobe, sai ki zaSi wanda zaki batan"

Murmushi ruma ta yi ta ce "Na gode mama, Allah ya saka da alkhairi, to zaki Wan zuba mini naman kazar ita ma na kai mata ta ci, na san su basu yanka kaza ba".

Yasir ya ce "Dama ta yaya zasu yanka, wannan babar ta su tana kiwon kaji kamar su kasheta, amma ba zata yanka su ci ba, bayan talauci har da son zuciya"

"Ka daina zagar mini babar ?awa dan Allah"

Mama ta ce "Kin ga, tashi ki wuce ki je ki kwanta"
Ta mi?e ta shige Waki, mama ta mayar da idonta kan Aliyu ta ce "Aliyu, kar ku hora yarinyar nan a kan halin rowa, duk rashin jin ta tana da tausayi da son taimako, idan har abin da za ta yi bai saSawa shari'a ba ku ?yaleta"

Aliyu ya jinjina kai. Ruma kuwa ji take kamar ta janyo washegari, ta kai wa habiba wannan kayan, ita ma ta saka ta ji daWi.

Washegari da wuri ruma ta yi wanka, ta yi kwalliyar salla da Waya daga cikin kayanta, ta zauna ta Waukarwa Habiba set Waya na atamfa har da ribbon da abin hannu.
Mama bata hanata ba, ta ?ulle mata nama ta bata ta kai wa Habiban.
Har zata Wauka ta fita, ta tsaya ta ce "Mama, dan Allah idan ta yi kwalliyar zamu je gidan 'yan ajinmu mu yi wasa".

Mama ta Wan Sata fuska ta ce "Amma dai kin san babna son wannan abun ko, ba na son yawace-yawace"

Ta Wan marairaice ta ce "Dan Allah mama, kin san bana yawo, daga aike sai makaranta, yanzu fa salla ce".

"Shikenan, na ji, saura kuma ki je ki zauna sai an nemo ki, ina da ina zaku je?"

Ruma ta lissafa mata, mama ta yi ajiyar zuciya ta ce"Yanzu ?arfe goma da rabi, kar ki wuce sha biyu, idan ki ka wuce abin da zai zo biyo baya ba zai yi miki daWi ba".

Cikin murna ta ce "Mama da wuri zan dawo in sha Allah " ta yi waje ta na murmushi.

Kai tsaye gidansu Habiba ta nufa, ko da ta je ta yi ta sallama, shiru ba a amsa ba.
Tsayawa ta yi a tsakar gidan ta cigaba da sallama.
Sani ne ya le?o yana amsawa, yana ganin ruma yayi saroro ya ce "Ke uban me ki ka zo yi mana a gida?"

Hararsa ta yi ta ce "To ina ruwanka ai ba wurinka na zo ba, ba yayana yayi maka tsakani da ni ba, babu ni babu ba, ko kuma na kira shi, ya zo ya ?ara kumbura maka fuska"

Tana tsaka da maganar, sai ga babar Habiba ta fito daga banWaki, tana ganin ruma ta tsuke fuska ta ce"Ke me ki ka zo yi mini a gida?"

"Gurin Habiba na zo"

"Da izinin wa ki ka zo wurin Habiban?"

Habiba ce ta fito daga Waki, hannunta ri?e da kwanon tuwo da miyar kuka, tana ganin ruma ta ce "Laaa ruma, kin dai na zuwa makarantar allo "

Ruma ta ce "Ba na ganki a masallacin idi ba ki ka ?i kulani"

Habiba ta ce "Wallahi ruma ban ganki bane ba? Ya salla?"

"Lafiya lau, wurin ki na zo, zo ki ji?"

Mamaki ya cika babar su Habiba, ta ri?e haSa ta ce "Habiba, wato cigaba da shiga sabgar yarinyar nan ki ka yi ko?"

Habiba ta girgiza kai ta ce "Wallahi Ummanmu ba kulata nake yi ba, na daWe ma bamu haWu ba".

Ruma ta mi?owa Habiba leda ta ce "Kawo miki na yi, ki zo ki karSa ki gani"
Babu musu ta ?arasa ta karSi ledar, taga Winkakkiyar atamfa ga abin hannu da ribbon, sai kuma ?ullin nama.

Habiba ta ce "Ruma wannan na waye?"

"Naki ne, in gaya miki, kayan salla na? kala goma sha biyu da hijjabai, har da abin hannu da sar?a, shine na ce bari na kawo miki Waya, ki saka mu je yawon salla".

Babar su Habiba ta ce "Ba ta so ba zata karSa ba, bana son shishshigi, ba ta kayanta ce muku aka yi tana bu?ata? Ita ma tana da kayan salla"

Idon Habiba ya cika da hawaye ta ce "Wallahi Umma bani da kayan salla, ina son kayan dan Allah ki bar ni na saka".

Ruma ta ce "Dan Allah Umma ki bari ta saka, mun shirya ai mun dai na faWa, dan Allah ki bari ta saka"

Umma ta kalli yadda Habiba ta rungume kaya tana kuka, wai tana so, haka ta ?yaleta. Habiba ta shiga Waki ta saka kayan, aikuwa tamkar dan ita aka Winka su suka yi mata kyau.
Sani ya din ga ce wa habiba mara zuciya.

Abin ka da ?uruciya, tuni habiba ta shirya a cikin kayan, duk da babar Habiba na jin haushin ruma, hakan bai hanata rawar jiki wurin raba naman kazar da ruma ta kawo ba, fan kuwa an daWe ba a haWu ba.
Daga haka suka fita nasu yawo.

Tamkar awakai haka suka dinga yawo, kusfa kusfa gidajen ?awayensu, wasu a haWu a rabu da su ?alau, wasu kuma a ?are da faWa. Ruma ba ta tashi tuna kashedin mama ba, sai bayan azahar tana ta gararanbarta a gari.

A suwkane ta nufo gida, tana ta tunanin yadda za ta kare kanta a wurin mama, dan ta san zuwa yanzu ana can ana nemanta kamar kuWin guziri.

Yaya Usman ta hango a tsaye a jikin wata mota, ya sha kwalliya, shi da abokansa, da alama fita za su yi.
Da gudu ta ?arasa in da yake tsaye ta ce "Yaya ussy, me ka ke yi a nan?"

"Ban sani ba, wuce ki tafi gida, ki kai aiken da aka yi miki" abin da ya faWa ne ya sanya ta fuskanci kamar mama ba ta neme ta ba, dan haka ta ce "Dan Allah ina zaka?".

"Zamu Wan fita chilling ne"

"Meye chilling kuma?"

Ya haWe rai ya ce "Cewa na yi fa ki tafi gida ko?"

"Dan Allah ka yi ha?uri, zan bika dan Allah"

"Ke wai ni sa'an wasanki ne? Ba zaki wuce ki tafi gida ba?"

Ta sake marairaice wa ta ce "Dan Allah Yaya"

Ri?e rigarsa tayi tana kallonsa kamar za ta yi kuka. Tunawa ya yi da haushin ?in tafiya da ita zai iya sanyawa ta tona masa asiri.

Yayi ?asa da murya ya ce "To ki je ki tambayo mama, idan ta yarda sai mu tafi"

"Wallahi na san idan na tafi, tafiya zaka yi"

"Shegiya sai ka ce mayya, idan na tafi da ke a ina zan saka ki motar ba space" yayi maganar a ?ule.

"Sai na zauna a cinyarka" duk yadda ya so ya yakice ruma, ta?i ta nace, gashi ya san zai sha kunya, idan har ruma ta tona masa asirin yana waya da budurwa, dan ya san sai dai ya kasheta bayan ta faWa zare idonsa ba zai hanata faWar abin da ta yi niyya ba.

Haka ya sakata a motar, dama ta abokinsu ce, ita kaWai a cikin maza, sai zaginta yake, amma ko a jikinta, ya sakata a gefensa.

Abokansa sai dariya suke masa, suna "Ka ga ?anwar maza, suke mulkin amma dole a biki ko ba a so" ba wanda ta kula a cikinsu suka tafi.

Wurin sha?atawa suka je, duk abin da suka ci sai da suka sayawa ruma ita ma ta ci, da ta ji ta ?oshi ta kalli Usman ta ce "Yaya ussy, a samo leda a Waure mini sauran na tafi da shi gida"

"Saboda kowa ma bashi da hankali kamar ke? Wallahi baki isa ba" ba dan ya ji daWin fitar ba, ya azalzali abokansa suka koma gida, saboda yadda ruman ke ta zubar masa da mutunci a idon abokansa.

Ko da suka je gida, mama a kiWime take, tun sha biyu ake nemanta ba a ganta ba.

Bin su da kallo mama ta yi, ta dubi Usman ta ce "A ina ka ganota?"

"Nima a hanya na ganta bayan la'asar, zamu fita da abokaina, ta nace sai ta bini, na kira Aliyu a waya na gaya masa muka tafi da ita".

"Ku ka je ina?"

"Wurin wani cin abinci ne, ni da su Isma'il ne"

"Kuma ita kaWai a cikin maza Usman, ka san tun yaushe yarinyar nan ba ta gidan nan, ka ga tashin hankalin da na shiga kuwa? Wallahi yau sai kin ci ubanki"
Abdallah ya ce "Wallahi mama ko ba ki daketa ba, sai na zaneta yau, ki yi mata bugun shekararriyar dawa, yarinyar nan ta ci a bata gado a Asibitin mahaukata".
Mama a tsananin fusace ta janyo ruma, ta din ga turjewa tana ihu, mama ta zaro bulugari ta dinga bugunta da shi tana kurma ihu tana neman taimako.

Mama ba ta saba tarbiyya da duka ba, amma idan ta kai bango jikin mutum yana gaya masa, sai da Usman ya ?waci ruma da ?yar a hannun mama.

Tun daga ranar, mama ta ce ba zata bata sauran kayan sallar baz gashi an aiko mata da kayan salla daga can garin su, ga dangin mahaifin su ma, sun Winko mata kaya, sun aiko mata da su, duk mama ta ce ba zata sake sakawa ba ta gama kwalliyar salla.
Washegari ta na ji ta na gani mama ta shirya, ta tafi cikin gari, ta bar ruma a gida.

Gidan duk ya yi mata babu daWi, sai faWace-faWace take da su Yasir.
Suka gama suka fice suka bar ta a gidan. Ta ji babu daWi rashin tafiya da ita da mama ba ta yi ba, gaji da zama ta tashi tana neman abun yi.
?akin 'yan mazan ta shiga, ta fara gyara musu ta ci karo da shaddar yaya Umar ya sa?aleta.
Wani tunani ta yi, ta kwaso shaddar ta fito da ita tsakar gida. Ta zuba ruwa a bokiti ta tuttula omo ta zunduma shaddar nan a ciki, ta koma ta cigaba aikin gyaran Wakin.
A ?alla shaddar nan ta kai awa biyu a ruwa, ruma ta fito ta jagwalgwala ta shanya. Ai kuwa shaddar nan gaba Waya ta daina wannan shining Win da take yi saboda azabar omo.

Aka jima, ya haWa wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.

Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta du?ufa tana guga.
Ya tsaya yana ?o?arin gane me take gogewa.

"Wai meye wannan ki ke gogewa haka?"

Ta Wago ta kalleshi ta ce "Kayan yaya Umar ne, na ga ya sa?ale su a Waki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa".

Abdallah ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?"

"To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?"

"Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?" Ai suna cikin maganar ruma ta ?one gaban rigar.

Dafe kai ta

10 / 61